Showing 138001 words to 141000 words out of 210924 words
"DT ya d'an girgiza kai kafin yace " I'm sorry Jalal but you really need to come with us..... Juyowa Jalal yayi yana kallon Zubaidah wacce bata fahimci me ake ciki ba...
"DT pls is there something we can do, pls Amir.... Cewar Ansar cikin tsananin tashin hankali..
"Girgiza kai Amir yayi kafin yace " Attorney I'm sorry but there's not.... All I can say shine get him a lawyer.... Hafiz yayi saurin matsowa kafin yace " I am, I'm his lawyer... Ya dafa kafad'un Jalal yace " I know you are innocent, I know you didn't kill him, zan tsaya har sai gaskiya Ya fito.....
"Kasa furta komai Jalal yayi sai ambaton Allah da yake yi cikin zuciyar sa...
"Amir ya d'an dubi Sargent yace " Cuff him.... Kamo hannun Jalal Sargent yayi ya zura su cikin handcuffs.....
"Daga Annah har Zubaidah mutuwar tsaye sukayi tamkar gumaka... Hamma kuwa tuhumar 'yan sanda ya soma yi yayinda zuciyar Hadiza ta cika pam da farin ciki..
"Kallon Detective Amir yayi kafin yace " Just a minute pls... Detective ya gyad'a masa kai kafin ya k'arasa gaban Zubaidah da Annah wanda dukan su biyu hawaye ne kurum ke fita a idanun su...
"Jalal yakai hannayen sa da suke d'aure cikin cuffs ya rik'o hannayen Zubaidah da Annah kafin ya soma fad'in" I didn't...... Muryar sa ta soma sark'ewa a hankali yaci gaba da fad'in" it shall all pass kunji wata rana sai labari..... "Annah kasa resisting hawayen ta tayi ba ta iya furta koda kalma guda ba...
"Zubaidah kuwa girgiza kai take tana kuka sosai.... Cikin tsananin kuka take fad'in" Pls don't leave me ya Jay dan Allah kar ka tafi ka barni, nasan wann duk a cikin sharrin su ne....Hannu ya d'ago ya share mata hawayen ta kafin yace " Take care kinji.... Ki kula min da kanki da Annah na, I love all so much..... Daidai nan Sargent ya jawo hannun sa suka soma tafiya...
"Binsu ta shiga yi tana fad'in" Ina zaku kai min miji, ku dawo min da mijina, he's not a criminal, he's innocent.... Dan Allah ku dawo mun dashi... Ta k'arasa gaban Ansar tana kuka sosai take fad'in" Ya Ansar zasu tafi dashi, sun tafi dashi.. Ta dawo gaban Hafiz tana fad'in" Barr pls do something, don't let them take my husband zan iya rantsewa bashida laifi.... Ganin babu mai iya tankata cikin su yasata dawowa wajen Annah tana fad'in" Annah pls kice su dawo dashi, I can't lose him..... Pls..... Hamman ta ne ya k'araso Ya rungume ta shima kukan yake harda majina...
"Hadiza ta tab'e baki tace " Haba haba abu yak'i ci yak'i cinyewa, gaba d'aya kowa sai shan wahala yake akan ki ke rai guda, ina ke ina shari'a da wad'an nan mutane, tun farko da baki fara magana ba da baki shigar da k'ara ba da abun bai kawo har nan ba, sai kace akan ki aka soma fyad'e wa 'yammata... Toh ai yanzu ga nan irinta kina gani, Ba budurci kurum ba harta Jalal d'in sai kin rasa sa..... "
"Ansar da Hafiz mota suka shige suka bi bayan su Jalal... Annah kuwa girgiza kai kurum tayi hawaye na ci gaba da zuba mata ta nufi cikin gida don bata iya fahimtar komai..
"A zuciye Zubaidah ta k'arasa gamida d'aga hannu zata kwad'a ma Hadiza mari.... Ganin Hamma datayi a gefenta yasata sauk'e hannun idanun ta na ci gaba da ambaliyan hawaye.. ..
"Ayyiriri hiyye lallai Zubaidah wuyarki tayi k'wari, yau har nice kike d'aga min hannu zaki mara lallai kuwa zaki iya marin wann lusarin yayan naki.... Ki musa mana idan k'arya nake, muna zaman zaman mu a garin mu muka baro a dalilin ki.. Kowa na shan wahala a dalilin ki, ko ina mukaje muna kaffakaffa da rayuwar mu duk a sabida ke, ke ko tsoron hakkin mutane bakiji,... Toh wllhi bari na fad'a maki, duk abinda ya sameni ko ya sami d'ana a sabida ke bazan tab'a yafe maki ba, ... Ta bita da uwar harara kafin ta kuma jan tsaki tace " Annoba kawai... Daga haka Hadiza tasa kai ta wuce cikin gida....
"Durk'usawa Zubaidah tayi a wajen saman gwiwoyin ta, tabbas duk abinda Hadiza ta fad'i haka ne, everyone has to suffer because of her selfishness, why is all this happening, why why.... If only batayi pressing charges ba, da duk ba'a kawo wann peak d'in ba.... She can't take it anymore, she just can't.... Ta k'arashe zancen zucin nata tana girgiza kai cikin tsananin kuka m...
"Hamma ne ya durk'usa ya shiga share mata hawayen yana lallashin ta, yana fad'a mata ko d'aya ba laifin ta bane, duk abunda ke faruwa muk'addari ne daga Allah.... Rungume Hamman ta tayi tana ci gaba da kuka mai tsuma zuciya.....
***************
"Allah ya taimake ka Abbah mun shirya zamu wuce.
"Mai Martaba ya jinjina kai cike da jin dad'i irin wanda bai tab'a ji ba kafin yace " Ubangiji ya kaiku lafiya ya baku nasara Abdullah.. Baban ka Ciroma yana waje zaku tafi tare, ku biyu tak na amince na d'aura ku bisa wann Al'amri, duniyar nan banida wanda na aminta dashi tamkar kai Abdullah... Yaya Ciroma kuwa yaya nane mahaifin mu d'aya nasan zaku rik'e min amana, ku taho min da d'ana lafiya...
"Shattima ya kuma rusunar da kai kafin yace " Abbah insha Allah zaka same mu muna masu rik'e amanar ka tsakani da Allah.
"Mai Martaba ya jinjina kai kafin yace "Tashi kaje Allah yayi maka albarka...
"Shattima ya amsa da ameen kafin yayi godiya ya fice Mai Martaba na masu fatan sauk'a lafiya....
"Babu yanda Shattima baiyi ba akan suyi amfani da private jet d'in companyn Mai Martaba *Modibbo Cooperation Company* amma fir Baba Ciroma yak'i yace da mota zasu tafi kuma Shattima zaiyi driving, ko kad'an Shattima baison musu wa babban mutum kuma mahaifin abokin sa kaman Baba Ciroma, d'an girgiza kai kurum yayi kafin yace " Shiknn Baba tunda ka zab'i hakan, amma magana ta gaskiya isan dare zamuyi sosai, tunda Gombe da Abuja ba Gombe da Bauchi bane....
"Baba Ciroma ya gyad'a Kai kana yace " K'warai kuwa Abdullahi. Kai bakasan tafiyar mu a mota zaifi sirri ba koh, .. Ai idan munje ba kai tsaye zamu nuna kanmu ba, sabida guje ma abokan gaba da mahassada, kasan duniyar nan ta cika famm da azzalumai....
"Jinjina kai Shattima yayi kafin yace shiknn Baba Allah Ya kaimu lafiya....
"Baba ciroma na murmushi ya amsa da ameen Audullahi.....
*******************
"What..!!! No no uncle don't even start, ta yaya zaka ce za'a sayar da gidan Dad d'ina bayan kasan wann gidan ne kurum ya mutu ya bar mana... Labib yace cikeda d'aga murya...
"Alh Kasim ya d'ago ido tsegege yana kallon sa kafin yace " Labib kasan dai bazan lamunci duk wani iskanci da iya shege da ka min a baya ba, masu waye nake yin wann, duk ba akanku bane, su waye suka fara jawo min experiencing wani abu mai kama da kariyar arziki, duk ba ku bane, idan baka sani ba ka sani gidan mahaifin ka is never yours don kuwa har rana mai kaman ta yau ba'a gama biyan bashisshikan sa na banki ba.... Snn waye za'ace ya biya ba ni bane, recently na rasa jirgina da ta shak'o kayan masarufi, nasan kasan wann zancen don babu yanda labarin bai isa ba a nahiyar Africa... Dole a sayar da gidan Jamil ku dawo nan gidan kaida mahaifiyar ka, tunda it can contain us all, our company is going bankrupt sabida d'unbin asaran da mukayi, da kuma cire shears d'insa da Alh Tahir yayi.... Labib ya d'ago yana duban Alh Kasim kafin yace " Uncle don't tell me the Marafa'a and the Dasuki's are not more business partners, me ya faru....
"Daidai nan Salim Ya turo k'ofar parlorn ya shigo, .. Alh Kasim ya dubesu dukan su biyu, sai yanzu ya tuna ashe lokacin da Alh Tahir ya mutu suna prison... D'an gyaran murya yayi kafin ya basu labarin k'onewar company d'insa da kuma mutuwar da yayi a cikin wutar...
"Girgiza kai kurum Labib yake yana fad'in" You are a monster Uncle, you're not human, I'm pretty sure is all your doing....
"Salim kuwa tsalle yayi ya cakumo wuyar mahaifin sa yana fad'in" You killed her father.... Why why Dad, Kausar is the love of my life and and ka jefa rayuwar ta cikin garari..... I'll never forgive you for this Daddy....
"Enough...?!!! Alh Kasim ya daka masa tsawa kafin yaci gaba da fad'in" You are all stupids, you ungrateful children, I did it all for you, to save you from going to jell..... I'm suffering because of you, I almost lost my company because of you.... If only you didn't rape that girl.. Things will be different... Ku ne, kune silan komai.....
"But we are not heartless like you.... Labib ya fad'i cikin d'aga murya.... Daidai nan Barr Munir ya shigo cikin tashin hankali yake sanar dasu abinda ya samu Tariq....
"Gaba d'aya suka fice cikin tsananin tashin hankali....
Sameena ce ๐๐พ
[1/23, 22:28] โช+234 803 619 0581โฌ: ๐๐๐๐ *ZUBAIDAH*
76
*ยฉSameena Aleeyou...โ๐พ*
_๐KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ๐ค_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*For All Cat Lovers ๐ป*
"Tunda ya dawo gida hankalin sa ya gaza kwanciya gaba d'aya Innah ta kasa gane kansa, d'aki ya shige k'arshe ya b'alle buttons d'in wuyar rigar sa ya nufi d'an k'aramin fridge d'in dake a cikin d'akin ya d'au kwalban whisky ya shiga kwankwad'a zuciyar sa naci gaba da tafarfasa...
"A hankali yake furta " I've already started and I'll accomplish it, all of you must get what you deserves... Yayi wata murmushi kafin yace " Now Jalal dole kowa ya yarda kai Ka kashe Tariq... I got rid of you two... And the remaining two. The Dasuki's Salim and Labib.... I'll come for you too... Ya d'aga kwalban whisky shi kad'ai snn yace da kansa cheers Umar to the beginning of your success..... Ya k'arashe yana fashewa da muguwar dariya....
**************
"A tare su Alh Kasim suka shigo asibitin gaba d'ayan su... Mum d'in Tariq sai sharb'an kuka take kaman ranta zai fita, Alh Maina kuwa zama kurum yayi gamida dafe fuskar sa da duka hannaye biyu...
"Duk wani basu baki dasu Alh Kasim suke ba fahimta suke ba, a haka Dr ya fito daga theater room d'in yana zame gloves d'in hannayen sa, a tare suka mik'e gaba d'aya suka nufi Dr...
"Dr how's my son... Tell me he can go through this, tell me pls.... Cewar Alh Maina cikin rawar murya... Mum kam tuni ta wuce ta nufi d'akin saida Salim yayi saurin k'arasawa ya rik'o ta.. " Fad'i take" Let me see my son.. Just let me see him, he needs me right now.... Haka Salim Ya ringa k'ok'arin rik'eta dukda fuzfuzgewar da take....
"Dr ya d'an shafi goshin sa kafin ya dubi Alh Maina yace " Follow me to my office... Babu musu ya shiga binsa tamkar rak'umi da akala.. Alh Kasim na biye dasu...
"Dr ya d'ago yana dubansu kafin yace " I'm sorry Alh Maina.... "Jin wann kalma yasa Alh Maina soma girgiza kai yana fad'in" No no I can't lose him, he's my only son.... "Alh Kasim ya dafa kafad'ar Alh Maina kafin yace " Ka kwantar da hankali friend everything will be alright,....
"Doc ya d'an fuzar da iska kafin yace " Alh Maina your son isn't die yet, but... But... I'm sorry to say ya sami internal injury in his brain.. The same wajen da ya samu a kwanaki, a wancan karan munyi k'ok'ari mun cire jinin coz bai tab'a k'wak'walwar sa ba.... Buy this time aroundwe just couldn't, already ta shiga cikin kansa sosai, magana ta gaskiya d'anka rayuwar sa tana cikin tsananin had'ari.... Dukda rayuwa da mutuwa na Allah ne, amma ko yayi rai memory d'insa zaiyi matuk'ar wuya ya dawo..... Snn ya sami problem a medulla spinalis d'insa, ko zaiyi rai he won't be able to walk again...... Dr ya d'anyi shiru yayinda Alh Maina ya soma girgiza kai kurum... Alh Kasim kuwa cewa yake who ever did this to him must pay....
"Dr ya d'ago hannu kafin yace " Try to calm down Alh and pls if possible kar a bari mahaifiyar sa taji wann, shiyasa na keb'e daku.... "Alh Kasim ya jinjina kai kafin yace " Haka ne Dr mun gode sosai..
Kamo kafad'un Alh Maina yayi suka nufo reception yanda su Labib suke... Har lokacin Salim na zaune gefen Mum dake cizgan kuka...
"Basu sami ganin Tariq ba don kuwa yana intensive care unit, banda sautin na'uran bature baka iya jin komai a wajen....
"Salim Ya dubi Labib kafin yace " I can't believe Jalal is capable of murder...
"Labib Ya d'an fuzar da iska kafin yace " Me either.... Ko Jalal zai kashe wani bazai kashe Tariq ba, among all of us yafi shiri da Tariq..
"Salim Ya d'an tab'e baki kafin yace " That girl changed him completely, we don't know him anymore.... Idan kuwa ya kashe Tariq toh kuwa duk muna cikin list d'insa, he'll surely come for us... I'm just terrified....
"Tsaki Labib yayi kafin ya fashe da dariya yace " Coward police already got him arrested, ka daina jin tsoro he won't come for you.... Mama boi... I thought prison did change you ashe babu abinda ya ragu.. You still Salim Dasuki.... Labib ya kuma fashewa da dariya..
"Gajeren tsaki Salim yayi kafin yace " Stop joking around already, this is a serious matter you know...
"Dariya Labib ya kuma yi daidai nan Barr Munir da Alh Kasim suka k'araso yanda suke..
"Alh Kasim ya dubesu kafin ya soma murmushi yace " You boys are lucky ku gode ma Allah...
"Kallonsa sukayi da alaman tambaya d'auke a Face d'insu...
"Alh Kasim yayi murmushi yace "Nasan baku gane me nake nufi ba, amma yanzu zan fayyace maku nufi na, abinda muka hanga maku nida Barrister..
"Saida ya karkata babbar rigar sa kafin ya soma fad'in" Is something very easy, Nasan dukan ku kunsan Jalal bazai iya kashe Tariq ba... Suka gyad'a kai a tare
"Alh Kasim ya kuma gyara tsayuwa kafin yaci gaba da fad'in" According to Jalal's statement Tariq kafin ya mutu yayita rok'onsa Ya kashe sa, amma bai kashe sa ba, snn kunsan tun ba yau ba, Tariq Was planning to commit suicide, yanzu abu ne mai sauk'i zamu fad'a wa Zubaidah... If she dropped the charges, we will set her husband free. Nasan she will definitely do it right away... Kunga idan tayi haka muka sai muce zamu bada testimony d'in mu in court cewa Jalal bai kashe Tariq ba, hasali ma Tariq ne me yunk'urin kashe kansa ku da kuka rayu dashi a prison zaku bada wann shaidan.... Kunga daga nan no more worries, an rufe babin Zubaidah har abada....
"Dariya suka tunsture dashi su duka biyu, Salim harda hugging Dad d'insa yana fad'in" Nice suggestion ever Dad, ...
"Labib kuwa cewa yayi " Uncle baka tab'a burgeni irin ta yau ba....
"Alh Kasim ya murmusa kafin yace " Ai nasha fad'a maku all this fad'i tashi da nake yi I'm doing it for your future ne.. So yanzu abinda nike so daku, keep this between us, no one should know, not even your Mums kun gane...
"Gyad'a kai sukayi cike da jin dad'i kafin suka fice daga asibitin....
*****************
"Tafiya suke kan shara bisa kwalta duk wani lungu da sak'on hanyar Gombe to Abuja tsaf Shattima ya haddace su akan sa...
"Baba Ciroma sai goga ashwakin munafunci yake yana zazzare idanu....
"Banda sautin k'ira'ar Shuraim cikin suratu Yusuf babu abinda ke tashi a motar...
"Sun d'an wuce Bauchi kad'an har sun wuce wani k'awye dake d'an gaba da Narabi kad'an Baba Ciroma ya dubi Shattima yace