Showing 114001 words to 117000 words out of 210924 words

Chapter 39 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22863

bai shaida namijin da suke tare dashi ba.... Cikin sauri Shattima ya k'arasa garesu...

"Annah ashe kuna tafe barkanku, barkanku da zuwa, sannun ku... Shattima ke fad'i sanda ya k'arasa gamida mik'awa Ansar hannu sukayi masabah... Tuni Annah da Zubaidah sun gane Shattima, gaba d'aya suka shiga gaisawa had'i da jajen abinda ya faru da Jalal. .. Jin Annah ta soma jero masa godiya yasa sa saurin cewa "Mu k'arasanku ciki, Jalal d'inma bai jima da farkawa ba.... Shattima ya soma yin gaba yayinda suka d'unguma gaba d'aya suka bi bayansa ..


"Yana kwance saman gadon idanunsa a rufe, kaman mai bacci, yana sanye cikin wata rigar ash color da ake sanyama duk wani patient a asibitin, jin an tab'a k'ofa had'i da sallaman su yasa shi Bud'e idanunsa a hankali..

"Da mugun mamaki yake binsu da kallo don kuwa bai tsammaci ganinsu ba, two women d'in da yafi so a rayuwarsa, his mum and the love of his life matar sa Zubaidah....

"Tun daga nesa idanuwan su suka cika da k'walla.... Jalal ya d'an soma yunk'urin mik'ewa Annah ta k'araso da sauri ta rik'esa tana girgiza kai alamun kar ya tashi ... Duk iya k'ok'arinta ganin ta maida kukan ta inaa saida kukan ya kufce mata.... Fuskarsa take shafawa tana fad'in" Meyasa suka maka haka bayan baka masu komai ba, why why....... My little boy, my son..... Kuka yaci k'arfin Annah.

"Hannunsa maras cannula ya d'ago snn ya shiga goge mata hawayen yana girgiza kai cikin murya na marras lafiya yake fad'in" Pls don't Annah, ki daina kuka kinji Annah na.. Mu godewa Allah basu cimma burinsu akaina ba....

"Annah ta rik'e hannunsa ta sumbata kafin tace " Allah Ya baka lafiya Jalaluddeen. Allah Ya shiga tsakanin ka da mugu... "Murmushi kawai Jalal yayi kafin yace " Ameen Annah nah.... Ansar ya d'an mik'o masa hannu sukayi musabaha kafin suka soma gaisawa... Jalal zai soma yima Ansar godiyar d'awainiyar da yake da family d'insa Ansar yayi saurin kawar da zancen da fad'in" Don't even start patient if not nasa Annah ta goge ka cikin 'ya'yan ta coz I'm her new son.. kasan anfi son sabon d'a.... Gaba d'aya suka murmusa idan ka d'auke Zubaidah dake rakub'e bayan k'ofa, gaba d'aya she's feeling guilty for what happened to Jalal, she feel responsible.


"Waige waige ya d'an soma yi da kansa, gaba d'aya Sun d'ago nufinsa, neman Zubaidah yake, tabbas idan bai b'ata gani ba, Ya ga wann fuskar da a kullum yake kwana yake tashi da ita....

"Shattima da Ansar suka fice suna hira tamkar sun saba da juna...


"Annah ta juyo ta kalli Zubaidah wacce fuskarta ke duk'e, ba sai ance maka hawaye take ba, juyowa tayi tana duban Jalal wanda ya kafe Zubaidah da idanu kafin tace " barin d'an zauna a reception ta fice tana d'an murmushi tana goge ragowar hawayen dake idanunta.....


"A hankali ta d'ago idanunta da suke jik'e da hawaye ta sauk'esu kan kyakkyawar fuskar sa.... Kallonta kawai yake babu ko kyafta idanu..... Takowa ta ringayi a hankali tana tuno tun farkon had'uwarsu da irin k'alubalen da suka fuskanta ko ince wanda suke kan fuskanta har rana mai kaman ta yau.....

"Cak ta tsaya gaban gadonsa ba tare da ta iya furta koda kalma ba.....

"Hannu Jalal ya mik'a ya rik'o hannunta...... A hankali ta soma fad'in" I'm sorry.... I'm sorry Ya Jay....... Kuka mai k"arfi ya kufce mata..... Kwanciya saman k'irjinsa tayi ta shiga rusa kuka mai tsuma zuciya....

"Dukda rad'ad'in ciwo da yake ji bai hana zuciyarsa yin sanyin dad'i ba..... Hannunsa maras cannula d'in yasa ya dafe bayanta a hankali ya d'an rungumeta ido a lumshe yana shak'ar k'amshinta. A hankali ya soma furta " Please Zubaidah...... Shiru ya d'anyi sabida har cikin b'argo da tsokarsa yake jin zogin kukan nata.... A hankali yaci gaba da fad'in" Pls ki daina kukan nan, it hurts kinji...... Tsit yaji ta daina kukan sai ajiyan zuciya da takeyi, sharkaf ta jik'a masa gaban riga da hawaye..... D'an dafe jikin gadon yayi yana k'ok'arin tashi.... Cikin sauri ta mik'e tana k'ok'arin taimaka masa had'i da goge hawayen idonta.... Kallonta kawai yake yana murmushi had'i da d'an ciccije leb'e sabida wajen aikinsa dake masa zogi....

"Pillow ta saka masa jikin garu ya d'an kishingid'a .... Kallonta yake kanyi yanda taketa faman goge ragowar hawayen... Hannu ya bud'e mata kafin yace " Come here....

"Babu musu ta k'arasa ta haye gadon gamida shigewa jikinsa, a hankali yake shafa kanta yana fad'in" Zubaidah bana so kina blaming kanki bisa duk abubuwan da suke faruwa, non of this is your Fault Miss Beauriful...... D'ago ido tayi tana duban fuskar sa na d'an wasu dak'ik'ai kafin ta sadda kan nata k'asa ta soma fad'in " But I don't wanna see you suffering, you don't deserve all this.... I'm sorry to say, but I already made up my mind..... I'm dropping the charges,....

"D'agota yayi da kyau yana dubanta kafin yace " You what?? No no Zubaidah you ain't going to drop the charges, Ko kin janye k'ara ko baki janye ba Alh Kasim Won't Leave us alone so as his children Labib and Salim.. ... Kallonta yake ido cikin ido kafin yaci gaba da fad'in" I won't allow to do that.... " But Ya Jay..... Bata kai aya ba ya katse ta yana girgiza kai yake fad'in" We can't make peace with those heartless until they all paid for their evil crimes.... Pls Baby don't give up kinji.... You're not doing this for your self alone, you're doing this for the entire ummah, akwai mata da yawa who are suffering from your experience, but they couldn't have chance to talk,..... Kinsan irin dad'in da suke tsintar kansu ciki lokacin da labarinki ya isar masu, I'm quite sure zasuyi farin ciki, and this is not a REVENGE it is your right your freedom, don't back down baby, you are not alone.... You have us all.....

"Kallon Jalal take soyayar sa da tausayin sa na ratsa zuciyarta, he's an Angel fad'awa jikinsa tayi ta rungume.... Ya d'anyi k'ara sabida ciwon sa data d'an fama..... Da sauri ta mik'e tana fad'in" Oh my I'm sorry, I'm sorry kaji, does it hurt.... Kallonta kawai yake da siraran idanunsa yanda duk ta daburce gaba d'aya..... Mak'aleta ya kuma yi da side guda snn ya soma fad'in" Hey relax is nothing serious...

"Ta d'an kallesa tace are you sure..?

"Gira ya d'aga mata dimple d'insa sai lotsewa suke kafin yace " Naji sauk'i tunda nayi tozali dake, oya tell me, what happened kika rame haka, dukda hijab ne jikin ki I can see that you lost weight....

"D'an turo baki tayi kafin tace ba ba kaine ba, I was afraid I might lose you....

"Cike da jin Dad'in kalamanta yake shafa 'yan yatsun hannunta kafin yace " Nothing will tear us apart kinji sweetheart oya give me a kiss ya k'arashe yana turo mata pink lips d'insa wanda suka k'ara jazir kaman fresh tomatoes.... Zaro ido waje tayi tana dubansa .... Kashe mata ido yayi kafin yace " Yeah a speedy recovery wishing kiss...

"Tafukan hannayenta tasa ta rufe fuskanta dasu.... Murmushi Jalal yayi kafin yace " I'm serious miss beautiful......

"Turo baki ta kuma yi kai a langab'e kafin tace " Pls Ya Jay.... Fah zan maka kuka...

"Okay sai na kira Dr Khaleesat ai... Kukan shagwab'a ta soma masa yayi saurin kwantar da kanta saman k'irjinsa kafin yace " Okay okay fine, but you I'm owing you a kiss ko bacci kike zan amshe kiss d'ina....


"Bacci ina zaka ganni bayan anjima kad'an zamu tafi masauk'in mu...

"Hannu yasa yana zame hijabinta yake fad'in " You must be kidding baby, ina kuma zakije after all kinzo jinyar mijinki ne.......Knocking d'in da akayi ne ya katse masu zancen nasu yayi saurin maida mata hijabinta snn yabada izinin shigowa, Zubaidah zata sauk'a daga gadon yayi saurin rik'eta yana rad'a mata stay right here baby....

"A hankali take fad'in" Ya Jay pls mana..... Daidai nan Dr ya shigo rik'e da files..... Murmushi ya sakar masu kafin Ya soma gaida Jalal, Zubaidah ma ta gaidashi cike da jin nauyin yanda Jalal ya hanata sauk'a a gadon.... Su Annah ne harma dasu Shattima suka take wa Dr baya....


"Wayyo wani sabon kunya ya mamaye Zubaidah, kaman gadon Ya tsage ta shige ciki, .Dr yace amma dai wad'an nan sabin aure ne...

"Ansar yayi karaf yace " Newlyweds ne ai Doc,

"Dr yayi murmushi yace I see..... Jalal dai murmushi kawai yake yi yana satar kallon Zubaidah... A hankali ta samu ta zame ta sauk'a daga gadon sanda Dr ya soma bayani wasu Shattima.....





Sameena ce ๐Ÿ‘Œ๐Ÿพ
[1/23, 22:26] โ€ช+234 803 619 0581โ€ฌ: ๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜ *ZUBAIDAH*


66

*ยฉSameena Aleeyou...โœ๐Ÿพ*


_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION (United we stand Divided we fall) ๐Ÿค_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*



*For All My Avid Readers ๐Ÿ˜ป*



" Dole Shattima yak'i su Annah da Ansar suyi kwanan hotel. He keeps insisting saidai su kwana a gidan su tunda akwai wadataccen masauk'i ..
"Kai tsaye hotel d'in da sukayi booking d'in suka wuce suka d'auko kayayyakin su, Ansar bai damu ayi masa refunding kud'in sa ba..
"Saida suka biya asibiti suka ajjiye wa Zubaidah kayanta da d'an kayayyakin Jalal data taho masa dasu snn suka nufi gidan su Shattima..


"Ummah gaba d'aya ta rasa ina zata saka su sabida karamci, a tak'aice dai sun samu tarba mai kyau da dattako a gidan Baba Waziri wato gidan su Shattima.
"Ansar d'akin bak'i aka sauk'e sa wanda yake a kusa da d'akin Shattima yayinda Annah ta sauk'a a d'akin Ummah, Nan fah Ameera ta ringa zubawa Annah surutu musamman dataji tare suka taho matar Mr Handsome, gaba d'aya ji tayi ta k'agu taga Zubaidah. Saida Ummah ta shigo ta korata parlor kafin ta fice ta k'yale Annah, Baba Waziri na shigowa gida Shattima da Ummah sukayi iso masu Annah. Sosai yaji dad'in sauk'an su a gidan da Shattima yayi snn yayi masu jajen abinda ya faru da Jalal, Ya shaida masu ranar sati wato ranar juma'a shima zai duba Jalal d'in insha Allah. Dashike yana daga cikin tawagan Mai Martaba masu raka sa dubiyar asibiti duk bayan sauk'owa daga sallan juma'a..
"Sosai Annah tayi masu godiya da wann karamci nasu..

"Abincin Annah har uwar d'aki aka kai mata, Su Ummah ba'a sama ba'a k'asa sai jan Annah da labari take, Annah kuwa ganin irin sakewa da dattako na Ummah dukda ta lura tanada son jin k'wak'waf hakan bai hanata gaya mata duk abubuwa na iftila'i da suke fuskan ta ba musamman Zubaidah da Jalal.... Sosai Ummah ta tausaya masu musamman Zubaidah, harda d'an share k'wallan ta, gaba d'aya Ummah sai tayi sanyi, bayan wucewar d'an wani lokaci suka ci gaba da labarin su tamkar sun jima da sanin juna......

****************

"Tea ta gama had'a masa half cup snn ta k'arasa jikin gadon had'i da mik'a masa cikin tsanaki...

"Bai karb'a ba sai kafe ta da idanunsa masu rikirkita mata lissafi da yayi...

"Oh gosh ita fah bata jure wann kallon nasa ta fad'i cikin zuciyarta... Kaman yaji abunda tace ya koma ya kwanta had'i da lumshe idanu...

"Zaro ido waje Zubaidah tayi tana tambayar kanta " What's going on with him, kodai yaji zancen zucin nawa ne... Ko kuma dogging shan tea d'in yake son yi ba, wani b'angare na zuciyarta ya raya mata hakan....

"A hankali ta bud'e murya ta soma ambato sunan sa " Ya Jay ka tashi ka sha tea d'in it's done..... "Shiru ya mata still idanunsa a lumshe...

"D'an rausayar da idanu tayi kafin ta d'an d'ale gadon gefen sa ta kuma kirawo sunan sa... Ido a lumshe yake fad'in" I'm okay bazan iya sha ba...

"Ta d'an marairaice murya tace " But you heard what Dr said earlier, you need something in liquid in your system, oya pls tashi ka sha ko kad'an ne.....

"Mik'ewa ya d'an yi ta jera masa pillows ya kishingid'a kafin ta kuma mik'a masa mug d'in" Mak'e mata kafad'a yayi tamkar k'aramin yaro kafin yace ." Zatayi magana yayi mata nuni da hannunsa mai cannula kafin yace " Baby can't hold the cup,... Ya fad'i cike da shagwab'a...

"Okay fine, idan dai zaka sha zan baka a baki.... Ta fad'i sanda take kai cup d'in bakin sa.... Jalal kuwa kashe mata idanu yayi kafin yace " that will be even much better,.... Haka tayita basa a baki har saida yace mata ya ishe shi... Kwanto da ita gefen kafad'arsa yayi kafin ya soma tambayar ta school tunda yasan tana gab da rubuta jarabwan shiga makarantar gaba da sakandare....

"Kina karatun kuwa...? Ya tambaya sounding serious...

"Gyad'a masa kai tayi kafin tace" Na taho ma da books d'in you'll help me with mathematics koh...

"Shafa kanta yayi kafin yace " Good girl shiyasa nake k'ara sonki nasan you won't neglect your studies sabida tunane tunane, what about Dr Khaleesat, ta dawo kuwa...

"Girgiza kai tayi kafin tace " She's on vacation, tazo shekaran jiya tayi mana sallama akan yau zasu wuce Singapore da mijinta, and. And... We've talked alot.....

"Gyad'a kai yayi kafin yace " Yayi kyau,... Ya rik'o yan yatsun hannunta yana murzasu a hankali idanunsa a lumshe yake fad'in" Zubaidah thanks for coming into my life....

"Karkatowa tayi gamida k'ura masa idanu ba tareda ta furta koda kalma ba.... Sun jima a haka kafin ta d'an soma k'ok'arin zare jikinta... " Bud'e idanu yayi yana dubanta kafin yace " ina zakije..?

" Books d'inta dake saman d'an wani stool gaban couch ta nuna masa kafin tace " Karatu zanyi, you also need some rest, kaga wajen aikin ka har waje biyu ne nasan by now sun maka tsami, ka d'an jima kana zaune ai ya kamata ka kwanta haka nan, is getting late ma...

"Gyad'a mata kai yayi kafin yace " You're right sweetheart,.... Murmushi tayi ba tare da ta furta komai ba ta shiga gyara masa wajen kwanciyar.... Idanunsa akanta duk wani movement nata ya d'an rik'e yatsan ta guda yace " Ke a ina zaki kwanta....
"Nuni ta masa da couch d'in kafin tace " Don't worry it's okay by me, beside couch d'in wadacecce ne, ta jawo bedcover ta rufa masa kafin tace " Oya go to sleep, and if you need anything I'll be right here.... Ta k'arashe tana murmushi.... Har ta juya taji ya kuma rik'o hannunta.... Kallonta yake babu ko k'yafta idanu har saida ta kasa jurema kallon nasa ta sadda kanta k'asa.. " Daddad'an voice d'insa ta jiyo yana fad'in" Miss Beauriful can't I have a goodnight kiss...???

"Gaban Zubaidah yayi wani irin fad'uwa jin sigan da yayi maganar da ita da kuma irin murza yatsun hannunta da yake yi cikin tsanaki.... Sunfi minti uku a haka tama kasa d'agowa ta dubesa... D'an tasowa yayi ya kai bakinsa saitin kunnenta kafin yace " You owed me 2 kisses, oya je kiyi karatunki I'll be watching your beautiful face har nayi bacci..... A hankali ta janye hannunta tana murmushi har ta isa wajen karatun nata.....

"Idanunta naga book amma rabin hankalinta naga Jalal ne, idan ta d'an sata kallon sa saiko tayi sa'a shima ita yake kallo.... Kashe mata ido yake yi had'i da murmushinsa mai kashe 'yan mata... Murmushi kawai Zubaidah keyi kafin ta d'aga book d'in sama ta rufe face d'inta dashi....

"Can dai taga kaman yayi bacci don kuwa duk subansa da takeyi idonsa a lumshe take gani, a hankali ta bud'e jakarta ta ciro nyt wears d'inta yalwataccen riga da wando cottons ta nufi bathroom a hankali snn ta canza kayan had'i da rufa hijabinta.... Batasan duk akan idon Jalal tayi komai ba... Tana shirin kwanciya bisa couch ta tsinkayo voice d'insa yana fad'in" Baby pls can I ask a favor..??

"A d'an zabure ta juyo tana ware idanu kafin tace " Sure"

"Jalal ya murmusa kafin yace " Could you please sleep beside me... Please..... Ya k'arashe cikin salo na rage sautin voice d'insa...

"K'irjinta sai dukan uku uku yake, she can't say no to him.... A hankali ta soma takowa har gaban gadon sa kafin ta tsaya cak.... D'an mirginawa yayi kasancewar babu drip a hannun nasa, kunsan dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login