Showing 192001 words to 195000 words out of 210924 words
d'an sami na cin abinci koda kuwa ruwan kunu ne...
"Rakub'e yake zaune k'asar gadan yana hangen mutane yanda suke wucewa suna shawagin su, ya kai duban sa ga paratan hannun sa yanda duk suka guggutsure sukayi datti sabida rashin wanka, ina ma zai sami wajen wanka yana neman na abinci, ko jiya ma satan buredi yayi a guje ya samu ya d'an ci... "Hawaye masu d'umin gaske suka shiga gangaro masa sanda ya tuno rayuwar su a baya, when everything was perfect, ... "Ina Kai bazai iya wann rayuwar ba, he needs to call his parents at least ko kud'i ne su turo masa yasan yanda zai yi,...
"Da wann tunani ya mik'e ya nufi bakin beach yanda mutane ke shawagin su, 'Yammata da samari masu ji da kansu suna ganin sa zaka ga sun soma b'oye wayoyin su don kuwa shakka babu irin su ne masu satan waya..
"Girgiza kai kurum Salim yake idan ya tuna yau shine a wann yanayi na rayuwa, wanda a da zai iya kyutan iPhones sama da hamsin a rana yau shine ake b'oye waya sabida an gansa, ya tuna shine Salim Dasuki masu had'a party da 'yammata a cikin jirgin sama arararin samaniya sabida gata yau shine shiga jirgi ta gagare sa kai mota ma ta gagare sa balle aje ga maganar jirgi.... Ya kuma sa bayan hannun sa ya share hawayen sa.....
"Yana ganin wasu 'yammata sun mik'e zasu shiga ruwa sun sha swimming trunks d'insu ya nufi yanda suka baro yana bin sauran snacks d'in da suka bari yana ci hannu baka hannu k'warya..
"D'aya daga cikin 'yan matan ne ta dawo d'aukan cream d'inta..... Nan ta hangi mutum sai masu bincike yake yana cinye sauran abincin su.... Zata yi ihu kenan ya d'ago idanun sa suna kallon juna...
"Da mugun mamaki take binsa da kallo kafin tace " Salim Dasuki, is that really you..??
"Salim Ya mik'e yana k'ok'arin k'ak'aro murmushi kafin yace " Miemie Turaki kina nan...
"K'arasowa Miemie tayi tana kallon sa cike da mamaki kafin tace " Kai what's wrong ya na ganka haka, ina su Labib Tariq and that my crush the most handsome among you... Jalal,..?? Ta k'arashe tana murmushi kafin ta rik'o hannun Salim suka zauna tace " Kwanaki naji batun auren ka, lokacin na koma Scotland shiya sa baku ganni ba, Jiya jiya muka zo k'asar nan kuma... Fasali ta d'an ja ganin Salim yayi sakare yana kallon ta kafin ta soma fad'in cike da mamaki ...."But Salim wai kaine ma kuwa, kaman ba kai ba.
"Salim ya murmusa kafin yace " I've to go Miemie, someone's waiting for me... Daga haka ya mik'e yana tafiya, saurin rik'o hannun sa Miemie tayi kafin tace " From your looks abubuwa da dama suna faruwa da kai and you don't want to share it... Anyway take this ta mik'o masa kud'i masu d'an yawa wanda zai kai dubu ashirin....
"Kallan kud'in yayi kafin ya d'ago yana duban ta, murmushi ta masa kafin tace " Ka karb'a Salim koma meye ke damun ka nasan it will help...
"Salim yasa hannu ya karb'a don ko bashida zab'in da ya wuce ya karb'an... Godiya ya mata kafin yasa kai ya fice daga wajen da saurin gaske...
"Nan Miemie ta daskare a wajen tana kallon sa har ya wuce, a haka friends d'inta suka k'araso suka same ta don sunji shirun nata yayi yawa...
"Babe meye ne kike tsaye a nan staring at nothing...?? K'awarta guda ta tambaya..
"Girgiza kai Miemie tayi kafin ta juyo ta dubi k'awatar tace " Amal I just saw something that terrifies me, Amal I'm afraid of this world, kinsan wa na gani yanzu..
"Amal ta girgiza kai tana yatsina fuska, Miemie tace " It was Salim, Salim Dasuki,, he was right here.... I... I don't know, bansan meke faruwa dashi ba but koma meye Salim yana cikin wani hali na canjin rayuwa, mahaifin sa mai kud'in gaske ne, shi ne guy d'in da na fad'a maki da yana had'a mana Party a jirgin ruwa ko a jirgin sama, ..... Na ganshi cikin wani irin yanayi, I asked him but ya ma kasa tsayuwa yayi min magana,..... Amal koma meye ne ke damun sa na tabbata baya cikin gata da jin dad'in da yake ji a da... Amal wllhi wllhi na tuba daga irin wann rayuwar wllhi na daina ta daga yau, duk kud'i irin na mahaifi na bai kai mahaifin Salim kud'i ba although mun bar k'asar gaba d'aya bansan me ya sami family d'insu ba, amma tabbas Allah zai iya juya Al'amran sa likacin da ya so, Na tuba Amal gida zan koma daga nan, naga ishara akan Salim.. kuma kema idan zaki tuba fine, idan bazaki tuba ba sai mu raba hanya....
"Cikin sauri Miemie ta kwashi suturun ta ta saka ta nufi mota, fuskar ta cike da nadama da tsoron mahaliccin ta...
"Wani wajen waya Salim Ya samu ya biya kud'i kafin ya shiga neman layin Dad dinsa shiru baya shiga, haka na Mummy ma karshe ya yanke shawarin kiran Barr Munir,
"Barr na waje ta d'an k'ofar baya domin kuwa basu isa fita ta gate ba sabida yanda journalist sukayi chaa suna d'aukan labarai... Nan yaga kira da bak'uwar lamba... Cikin sauri ya d'aga yana mai ciccije fuska...
"Kuka Salim Ya fashe masa dashi yana fad'in" Uncle I couldn't reach any of them, Uncle meyasa zasuyi neglecting d'ina, I'm suffering Uncle....
_Daga can NCC kuwa tuni anyi connecting kiran da Barr Munir yake tare da jami'an tsaro, gaba d'aya suna sauraren su.._
"Barr ya fuzar da iska kafin yaci gaba da fad'in" Things are not easy here either, you better stay where you are, if you show up here, police will have you arrested, so gwarama kayi zaman ka a can...
"Cikin muryar kuka Salim yaci gaba da fad'in" But I can't uncle, I just can't, banida kud'i banida wajen kwana, ko kasan cewa k'asan bridge shine wajen kwana na, do I have to hide my whole life...... " Okay naji bazan dawo ba, but where is My Dad, I wanna talk to him, ka had'ani dashi pls...
"Barr ya fuzar da iska, hawayen da baisan dalilin zuban su ba suka shiga fito masa kafin ya soma fad'in" Salim I'll be honest with you, we are ruined, completely, we lost the company, we lost the mansion, in short mun rasa komai, your Mum and your Aunt, mahaifiyar Labib had to move in with Jane, Salim Hajiya Farha da mahaifiyar Labib dole suka koma gidan Jane, cook d'inku mai dafa maku abinci coz they have no where to stay..... And your Dad..... He's....
"Salim da hawayen sa suka kasa daina zuba cike da shock yake fad'in" My Dad what happened to him, how's he..??
"Munir ya cija leb'en sa kafin yace " He's in a hospital right now..... Ya sami heart attack, I'm afraid he's dying.....
"Kuka sosai Salim Ya fashe dashi yana girgiza kai yake fad'in" No, no, this can't be happening, ina mummy na, I'm quite sure she must be affected... Ina take..... Daidai lokacin da Mummy da mamy suka iso wajen...
"Journalists kuwa tuni suke aikin d'aukan su ta cikin flowers, Domin kuwa shakka babu sun san da Salim suke waya, gashi sunce basu san yanda yaje ba, hakan na nufin sun san yanda Salim Ya gudu ya b'oye kenan...
"Munir ya mik'a mata wayar yana fad'in" Farha... Here..
"Da sauri ta mik'o hannu tana fad'in" Is that Salim, oh my poor boy... Tana soma magana cikin wayar ya kuma fashe mata da kuka, kuka itama take, tana rok'on sa kar ya dawo koma a ina yake, don kuwa yana dawowa police zasu kama sa, already an kama Labib...
"Salim kuka yake yana fad'in" But mummy ina so naga Daddy na, mummy pls ki barni na dawo...
"D'aga kan da Barr zaiyi yaga journalists sai d'aukan su suke, ....Shittt, Dammit... Ya furta da k'arfin gaske kafin ya fincike wayan ya kashe, Mummy tana kuka haka Barr ya fizge wayan yace dasu su shige cikin asibiti idanun journalists na kansu ne gaba d'aya...
***************
"Ai kuwa bayan wasu awanni Police suka zo sukayi interrogating nasu sabida wayan da sukayi da Salim, fir suka ce basu san yanda Salim ya b'oye ba...
"Rayuwa fah ta kuma shiga cikin tsananin matsi da tak'ura, ta kai point d'in da basu da kud'in da za'ayi jinyar Alh Kasim, dole Barr ya soma bin k'afar tsofaffin abokan kasuwan cin Alh Kasim yana rok'o kud'ad'e da sunan jinyar Alh Kasim, idan sun basa sai ya raba kud'in kashi biyu ya d'au kashi guda ya bayar da kashi guda...
"A haka har Alh Kasim ya soma samun sauk'i saidai babu baki babu k'afafu, maganar nasa ba'a iya fahimta, ga shanyewar b'arin jiki, harta bakin sa ta karkace, ba don Drs sun so ba suka sallami Alh Kasim sai don rashin kud'in ci gaba da jinya a asibitin....
"Gaba d'aya gidan Jane suka tattara suka koma, Mummy da Mammy sai godiya suke ma Jane, Jane kuwa tace " Ai babu komai tunda harta gudan nata a dalilin masu aikatau ta samu,...
"Haka zasu zauna suyi jigum suna tuna rayuwa, Alh Kasim kuwa komai fitsari bayangida saman keken guragun sa yake yin s idan ba'ayi saurin ankara an kaisa ba sabida babu baki balle yace zaiyi, ba'a gane me yake fad'i.... Tau Jane ma fah ta soma k'osawa dasu, don duk ranar da Alh Kasim yayi bayan gari a jikin sa toh fah haka gidan gaba d'aya zai wuni yana wari... Ita kanta Mummy ta soma gajjiyawa...
"Shi kuwa Barr bai fasa bin k'afafun abokan kasuwancin Alh Kasim ba yana amso kud'ad'd'e da sunan Alh Kasim kafin yazo ya cika ma rigar sa iska kafin ranar shiga kotu tazo.....
******************
"Labib ya kalli d'an sandan cike da mamki kafin yace " Are you sure Alh Kasim ya sami heart attack, police officer ya shek'e da dariya kafin yace " Ba abin mamaki bane tunda Allah ne ya kawo k'arshen ku, ku saduda ku amsa laifin ku don kuwa baku da wajen gudu, Allah Ya karya ku gaba d'aya....
"Labib girgiza kai kurum yake hawaye na fita masa yake fad'in" No, no I can't go to jell, I just can't.....Get me out of here,..... Ya k'arashe cikin tsananin d'aga murya...
"Police kuwa yayi dariya kafin yace " Kai ka sani wann ba matsala ta bace, dad'in mutum ya shuka alkhairi kenan....
"Durk'ushewa yayi saman gwiwoyin sa yana kuka da duka zuciyar sa.....
***********
*Fadah*
*A week to the Trial*
"Hannunta ya rik'e cikin nasa kafin yace " Baby we would do everything possible mu fitar da Hadiza daga jell koda zamu kashe mak'udan kud'i ne, ki daina damuwa kinji, although bamu san dalilin da yasa Checks d'in Kasim Dasuki ya shiga hannun ta ba amma nasan yanzu zata fad'i koma meye, su kansu Dasukis yanzu ta kansu suke bata Hadiza ba na tabbata. Nima ina tausayin Hamma da Kamal, sosai it breaks my heart seeing them suffering while mu muna cikin jin dad'i, koma meye tayi she's still part of us, she's our family, nasan kin yafe mata tun tuni..... Ya k'arashe yana mai murmushi yana murza 'yan yatsun hannun ta...
"Mumrmushin itama tayi kafin ta gyad'a Masa kai tana share hawayen da suka Zubo mata... Daidai wayan Jalal tayi k'ara Shattima ne me kira....
"Jalal na d'agawa Shattima yace " Prince ka fito babban gwani right now, we've got the Doctor, ka fito yanzu....
"Ai bai gama ji ba ya mik'e ya mik'e yana fad'in" Really, gani nan zuwa... Cikin zuciyar sa kuwa tafarfasa kawai yake don yasan suna yin ido hud'u da likitan nan sai yayi smashing face d'in sa... Baiko ce ma Zubaidah komai ba ya fice cikin sauri yana zura takalmi,..
"Zubaidah ta bisa da kallo tana addu'an Allah yasa lafia...
*****
"Labib ya kuma kallon officer kafin yace " Officer pls ka taimaka min da abin rubutu takarda da pen..
"Officer ya kalle sa tsegege yayi dariya kafin yace " Wata k'aryar zaka rubuta, kar ka damu zan bake... Ya mik'e yana murmushi kafin ya kawo ma Labib doguwar takarda da pen..
"Labib yayi godiya kafin ya zauna ya soma rubutu kamar haka... "
_January 15th, I Confessed....._
"Hawaye suka ci gaba da kwaranya daga idanun sa....
*Sameena Aleeyou Mrs*
[9:04PM, 2/6/2018] βͺ+234 809 781 2439β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
*95*
*Β©Sameena Aleeyou...βπΎ*
_*Dedicated To All Victims Of Rape...*_
_Wannan littafi kacaukam d'insa sadaukarwa ce ga dukk wata d'iya mace wacce tsautsayi da k'addara na fyad'e ya auka mata... Ina fatan wannan littafi nawa ya sanya murmushi a saman fuskar ki 'yar uwa π_
"Daidai k'ofar da zai sada ka da Babban gwani Jalal yaci karo dasu, burki yayi yana watsa wa Dr mugun kallo, yayinda fadawa tuni sun zube suna kwasan gaisuwa suna kod'a Jalal suna fad'in" D'an sarki jikan Sarki, Allah Ya baka gidan ku, d'an na gada, kafi d'an na koya, mai ado da tagulla da azirfa.... Allah Ya ja zamanin Yarima.... Wata naushin da Jalal yakai ma likitan nan yasa fadawan nan yin tsit suka shiga tsine ma Dr suna fad'in" Allah wadan ka D'an talakawa ka b'ata ran Yarima, ..Allah Ya wadan ka... Hattara d'an talkawa.... Allah Ya huci ran Yarima...
"Jalal huci kawai yake yana rik'e da kwalan rigar likitan nan yake fad'n" You shameless imbecile ka gama b'uyan naka, you such a coward, you should be ashamed of your self....
"Shattima ya shiga janye sa yana fad'in" Calm down Jalal, pls compose your self...
"Huci kawai Jalal yake yana watsa ma likitan nan mugun kallo ga jijiyoyin jikinsa dake tsahi idon sa da fatar sa sun koma jazir....
"Fadawa kuwa sai fad'i suke " Allah Ya taimake ka wann aikin mu ne, a barmu mu ladabta shi... Tsinannen Allah, ka sab'i ran Yarima.....
"A zuciye Shattima ya daka masu uban tsawa yace su watse a wajen baki d'aya.....
"Rik'o hannun Jalal yayi suka soma tafiya yayinda Detective Mudi ya janye hannun Dr suka nufi cikin fadah... Jalal sai faman huci yake....
***************
"Kasa ci gaba yayi da rubutun sai hawaye dake neman wanke masa fuska, ya d'aga kai sama yana kallon killataccen d'akin da aka ajiye sa, tabbas no way to escape, dole ne ma ya zauna a jail for many years, they lost everything, basu da komai balle yayi tunanin kud'in su can save them, Alh Kasim ta kansa yake bashida lafia babu kud'i babu company, snn ba'a kama Salim ba balle yayi tunanin koda ace yana da kud'in zai iya yin wani abu, yasan cewa uncle dinsa ya tsane sa , shima kuma bai son sa ko k'ank'ani.....
"Ya dafe kansa yana mai ci gaba da tunani hawaye na ci gaba da kwararo masa... He started it all, he was the one who first came up with the idea... But, ta yaya zai fara confessing, mai zai ce, daga ina zai fara...
"Take zuciyar sa ta rad'a masa start from that very night π.... Sunkuyawa yayi yana mai ci gaba da rubutu lokaci guda kaman a mafarki kaman a tunani yake jiyo murya tamkar na mahaifin sa yana fad'in"
"If you are going to confess, write everything down, ka fad'a komai kar ka b'oye ko guda, kar ka mance musababbabin abinda kayi niya a wancan lokacin shine ka b'ata auren Salim, snn ka bak'anta Alh Kasim a idanun Alh Tahir, snn kar ka mance ka saka ma Jalal k'waya a abun shansa don hankalin sa ya gushe ka cimma burin ka, mai yuwa su sauran sun aikata laifin ne domin jin dad'in su, amma kai ba haka bane, ka aikata ne sabida ka destroying uncle d'inka da d'ansa, so my dear boy kar ka b'oye komai ka fad'i komai ma Alk'ali only then you'll have peace.......
"Labib ya toshe kunnuwan sa da k'arfin gaske shi kad'ai ya tak'ure waje guda