Showing 72001 words to 75000 words out of 210924 words

Chapter 25 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22922

" Kayi alwalan ka I'll make some coffee, it will help you...

"Gyad'a kansa kawai Jalal yayi kafin ya shige bathroom...

"Gaba d'aya jikin Shattima yayi sanyi, kai wani babban Al'amari na shirin faruwa dashi,...

*************

"Washe gari tun ida sallahan asuba suka nufo suleja, to their greatest surprise Dr Khaleesat is there too, tana ganin Jalal ta sakar masa murmushi tace " You can go through this, don't worry kaji, we would find her...

"Murmushin k'arfin hali kurum ya sakar mata ba tare da yace komai ba..

"Annah ta rungumesa tana maida hawayen da ya kufce mata, Murya na rawa Jalal ke fad'in" Annah I couldn't find her, what if something bad happens to her, I'll never forgive my self...... Shigowan Hamma Habibu da Hadiza ne ya katse su don dama sunji tsayuwar mota...

"Kai tsaye hannun Jalal ya k'arasa ya rik'e yana fad'in" Jalal ka samo mun k'anwata, ka samota koh, nasan kai kad'aine zaka iya kular min da ita, ka fad'a min ka samota tana cikin k'oshin lafiya, idan wani abu ya sameta Inna da Baffah zasu gani daga makwancin su koh, zasu ce ban kula da ita ba ko,........

"Tausayi ya cika illahirin zukatan mutanen dake wajen.

"Hannayensa Jalal ya rik'e gamida zaunar dashi saman dakalin dake a veranda d'in kafin yace " Ka kwantar da hankalinka Hamma, I promise I'll find Zubaidah where ever she's, nayi alk'awarin zan samota duk yanda take da izinin Allah koda hakan zai zama sanadin rasa rayuwata, ka kwantar da hankalinka Zubaidah bazata so ganin hankalinka a tashe ba, kayi mata addu'a kaji...

"Haka Hamma ya ringa gyad'a kansa yana goge hawayensa da riga tamkar k'aramin yaro.....

"Kaman daga sama sukaji wayar Annah na ringing, Hadiza tayi saurin shigewa d'aukar wayan don Annah kam bataci ta kula waya ba.

"Jin muryar Zubaidah cikin wayar yasata fitowa da sauri tana fad'in itace Zubaidah ce.....
"Daga d'aya b'angaren kuwa Zubaidah cewa take " Ki bani Annah da Hamma na,..... Daidai sanda Annah ta fizgi wayar, Jalal kam mutuwar tsaye yayi yana binsu da Kallo.

"Daughter where have you been, we were all worried about you, Annah tace cike da nuna damuwa...

"D'an jim Zubaidah tayi duk sai taji babu Dad'i, Annah bazataji dad'in abunda tayi ba, despite all her efforts on her. A hankali take fad'in" Annah ina nan lafiya shiyasa ma na kira na sanar daku don kar ku damu, I just want some space ne, I'll come back to you soon, ina Hamma na.... Ta k'arashe a hankali.

"Annah bata iya furta komai bar, sai manna wayar a kunnen Hamma Habibu da tayi....

"Shida baya tareda su ya tafi duniyar kuka jin muryar Zubaidah a waya yasa sa mik'ewa zunbur yana murmushi,
"Zubaidah, Zubaidah na, Zubaidahn Baffa da Inna, ina kikaje.... "Jalal ya damu dake..... Gaba d'aya suka dubesa jin statement d'insa...
"Hamma yaci gaba da fad'in" Nima na damu dake, Don Allah ki dawo garemu kinji k'anwata, duka muna sonki, muna sonki....

"Share hawayen da ya zubo mata tayi kafin tace " Nima ina sonku Hamma, zan dawo kwanan nan kaji, kar ka d'aga hankalinka idan ba haka ba kuma bazan dawo ba, ka kwantar da hankalinka kaji.....


"Muryar Jalal taji cikin wayar yana fad'in" pls come back, if you want I'll leave the house, but pls don't put your self in danger, Hamma is worried so much about you, ki dawo don Allah ko kuma ki fad'a mun yanda kike, I'll get you right a way....

"Cike da masifa take fad'in" I won't listen to your lies again, I hate you even more, snn kar kayi tunanin zan dawo nan kusa, and lastly don't you dare involved police idan ba haka ba, wllhi kaji na rantse I'll leave you all for good, snn bazan dawo ba...

"Yanajin sanda tayi tsuka ta kashe wayar.....

"A hankali yana mai lumshe ido ya k'arashe da " I love you.... Be safe dear.......

"Gaba d'aya suka k'ura masa idanu cike da tausayawa.
"Dr Khaeelsat tace yi mun dialing number d'in, babu musu ya sake dialing amma sai jinta yayi a kashe, a sanyaye yace " is switch off..!!
"Gyada kanta tayi kafin tace let's talk private, babu musu yabi bayanta...

*************
"Mik'a ma Zulaihat wayar tayi tana mai zama bisa sofa ta shiga share hawaye, Zulaihat ta dafa ta kafin tace " Meyasa bazaki koma ba, suna sonki, you're so lucky da kika sami family haka masu sonki da yawa ta k'arashe zancen sanda take cire sim d'in da zubaidah tayi amfani dashi don dama extra sim d'inta ne wanda take solo ma Alhazawanta dashi, ..

"Girgiza kai Zubaidah tayi kana tace " No bazan koma ba, snn ko zan koma sabida mutane biyu ne, Annah da Hamma na, su kad'aine basa min k'arya...

"Zulaihat ta sauk'e ajiyan zuciya kafin ta mik'e tana gyara mayafinta tace " Okay ni zan fita breakfast na kitchen, ki shiga kici duk abinda kike so, zaki iya kulle gidan gaba d'aya.
"Gyad'a Kai Zubaidah tayi kafin ta dubi Zulaihat tace " Na gode, thank you for your kindness.
"Gajeren murmushi kawai Zulaihat tayi kafin ta suri jakarta tace " See you soon.

"Window Zubaidah ta k'araso tana lek'en Zulaihat da Imam, Imam harda mata murmushi da waving, bata kulasa ba sai sauk'e labulen da tayi ta k'arasa ta rufe k'ofar parlorn....

*************
"Annah dasu Jalal harma da Dr Khaleesat suka ja gefe suna tattauna lamarin bayan Dr sun gama ganawarsu da Jalal, ,
"Shattima yace " Nifa ina ganin we should report that to the polic, the earlier the better...

"Girgiza kai Jalal yayi kafin yace " Tace muddin mukayi reporting bazata dawo ba,.

"Are you sure babu wanda ta sani ko a cikin Abuja ne, Dr Khaleesat ta tambaya.

"Da sauri Annah ta kuma d'ago kai ta dubi Shattima, ta tuna kwanaki ya kawo masu budurwarsa, cikin sauri ta k'arasa gabansa tace " Kai kuwa ina yarinyar da kazo da ita kwanaki gidan nan, matar da zaka aura don ban mace ba haka ta fad'i mana, ita kad'ai Zubaidah ta sani me yuwa gidansu taje...

"Jalal yayi saurin mik'ewa yana recalling tabbas anyi haka...

"D'an jim Shattima yayi harga Allah Ya mance tare suka zo da Zulaihat amma ta ya ta zama matar da zai Aura, rabonsu da waya ma yana ganin tun wancan lokacin ne, k'ila ita tace masu haka knn...
"Da sauri ya furta "Zulaihat, Annah ta gyada kai tace k'warai...


"Kan kace Me Jalal ya fuzgo hannun Shattima yana fad'in" Muje pls take me to their house....

"Wait Jalal wllhi bansan gidansu Zulaihat ba, ban tab'a zuwa ba...


"Wani mugun kallo Jalal ya watsa masa kafin yace " Matar da zaka aura d'in ne baka san gidansu ba,

"Matar da zan Aura..? Shattima ya maimaita.

"Annah ta gyad'a kai tace "K'warai haka tace mana,.

"D'an girgiza kai kawai Shattima yayi kafin yace " Wllhi ko gidansu ni bansani ba........ Baikai aya ba Jalal ya shak'ure masa wuya yana fad'in" K'arya kake, then why did you bring her here, meyasa ka kawota nan.... Usman yayi tsalle yana k'ok'arin ceton Shattima...... Annah ta tafi da sauri tana Janye Jalal....


"Da k'yar aka k'waci Shattima daga mak'uran da Jalal ya masa....

"Janye hannun Jalal Annah tayi suka wuce d'aki rai b'ace...

"Ni bansan yanda zaka kai wann zuciyar taka ba, haba haba Jalal, idan kayi haka me kake tunanin Habibu zaiyi, You always let your temper get the best of you, kamata yayi ka nustu musan abin yi, idan neman Zulaihat d'in za'ayi sai ayi, and wnn yaro da ka masa haka bai deserving haka ba, he's here to help he cares about you, me kake tunanin Usman zaiji .

"D'an shiru yayi amma har lokacin huci yake a hankali ya furta " I'm sorry Annah....


"D'an dafa kafad'arsa tayi ta sassauta murya kafin tace " Son I know this is difficult for you, it hurts me ganinka a wann condition d'in, but we all need to remain steady, akwai mutanen da suka fimu rauni cikinmu, think about her brother abin yayi affecting d'insa sosai, pls kayi composing kanka kaji Son, and Dr Khaleesat bazataji dad'i ba regarding what you did earlier, tashi muje and apologize to them...

"Gyad'a kansa yayi kafin ya mik'e jiki a sanyaye..



"Gaba d'aya basuji zafin abinda yayi ba, saima tausaya masa da suka yi, Shattima ya dafa sa kafin yace " I know exactly how you feeling, and I'm willing to help Jalal, na kira wayan Zulaihat munyi magana tace " Zubaidah bata wajenta, but she sounds very wired like something is wrong with her, batayi rawan kan nata data saba ba, she was quite strange , the best abu shine mu fita mu nemi resident d'inta...


"Gaba d'aya sunji Dad'in shawarin Shattima, Jalal ya d'an dafa kafad'arsa yace " I'm sorry again Shattima, murmushi kawai yayi yace " That's what bothers are for, let's get going the earlier the better...

"Gaba d'aya suka gyad'a kai, Dr Khaleesat ma Office tace zata wuce ganin k'arfe takwas tayi snn tace " suyi keeping nata update duk abinda ake ciki, a tare suka fice, Dr Khaleesat ta nufi motar ta yayinda Su Jalal suka wuce Ride d'in Shattima...

***********
*Sheraton Hotel, Abuja*
"Kallon d'akin da yake kwance a ciki yayi, ya dubi suturun dake jikinsa masu d'an karen tsada, his life is different now, komai ya canza, he's rich handsome and educated, abu guda da ya rasa shine ZUBAIDAH She suppose to be here with him enjoying the luxury, this is the life he's been dreaming of, finally ya samu, what next now???? Ya tambayi kansa. Zuciyarsa ne ta basa amsa kai tsaye
"GET HER BACK, Get your girl back, she's yours, she's meant to be with you no one else, get back what's rightfully yours...

"Mik'ewa yayi ya soma shiryawa, cikin drawer ya hangi tsohuwar phone d'insa wanda tunda yayi kud'i ya jefarta ya sai iPhone8, sauk'e ajiyan zuciya yayi sanda ya tuna irin baran baran d'in da sukayi da iyayensa sanda ya koma masu yayi kud'i dare d'aya, gaba d'aya basu yarda da arzikin nasa ba, d'an tab'e baki yayi kafin ya d'au wayan halama sun kirasa, duba wayar ya soma yi yaga sakk'wanni da kira masu yawa, yyawanci na abokinsa Balele ne da Zulaihat, na Zulaihat ya soma dubawa, ya shiga kiran wayarta yaji a kashe, ita kuwa masu amsan kud'in gidan haya ne da Shattima suka sakata kashe wayarta, ya kira ya kira a kashe, karanta sak'on data tura masa yayi,
"D'an jimm yayi kafin ya furta " I shouldn't have abandoned you anyway, you help me sanda na zo, fita yayi ya wuce Mall ya soma mata shopping, kaya sosai ya saya mata kafin ya nufi gidanta......




Sameena ce
[1/23, 22:21] โ€ช+234 803 619 0581โ€ฌ: ๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜ *ZUBAIDAH*

47

*ยฉSameena Aleeyou...โœ๐Ÿพ*

_Queen Samy Novels Forum...๐Ÿ“–๐Ÿ“š_



*Dedicated To All Victims Of Rape...*



*"Salam. Ina rok'on Allah yayi maki albarka fiye da k'ok'arinki, Ya shirya maki iyalanki fiye da tarbiyarki, Yayi maki Rahama fiye da tubanki, Yaji k'anki fiye da tunaninki, Ya k'ara azurtaki fiye da nemanki, Ya karb'i ibadunki fiye da k'wazonki.... Allah yayi ma Mahaifanki gafara ba tareda binciken ayyukansu ba, Allah Ya rufa maki asiri duniya da lahira.... Ina maki barka da Jumma'ah*

*"Sak'onki a gareni ๐Ÿ’…๐ŸผMaman Sadiq๐Ÿ’…๐Ÿผ......๐Ÿ‘†๐Ÿฝ*

*Na gode na gode k'warai da gaske da kyawawan addu'o'inki da nuna k'aunarki a gareni, Ubangiji ya saka maki da khairan, Sameena na k'aunarki, Alkhairin Allah Ya kai maki duk yanda kike... ๐Ÿค๐Ÿคthe whole chapter is yours dear๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*


"Imam don Allah ka bar duk abinda kake kazo muje, wann mutumin ba mutunci ne dashi ba, wai Ya kira Tariq ma bai d'aga wayarsa, he's talking nonsense, wai saidai ya kwana dani tukunna zai d'aga min k'afa, kasanni bakina baya shiru nan na gaggaya masa magana son raina, probably nasan yana hanyan zuwa gidan ya min watsi da kaya ga Zubaidah tana can pls kayi sauri.... Ta k'arashe maganar tana yarfe hannu...

"Daga d'aya b'angaren Imam yace " Gani nan zuwa, just send me your location, cikin sauri ta amsa gamida tura masa....

*******

"Tana zaune gaban kayan kallo tana kan duba plates d'in da suke jere a cikin drawer d'in dake mak'ale jikin TV stand, yawanci Americans films ne saiko Nigerian films, bangon d'aya kaset d'in ne yayi mugun d'aga mata hankali don kuwa abin babu kyaun gani basai ance maka bluefilm bane, k'irjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri, tayi saurin jifa da kaset d'in ta shiga k'ank'ame jikinta ita kad'ai tana matsawa jikin garu.... Hakan yayi daidai da soma knocking, Zubaidah ta kuma firgita, toshe bakinta tayi da iyaka k'arfinta da duka hannayenta biyu, tsoro da firgici ya mamaye ta baki d'aya.... Da alama mai knocking gajjiya yayi kokuwa ya tafi.

"Cikin sand'a ta isa jikin labulen window tana lek'awa, kasa gasgata abinda idanunta suka gane mata tayi, is that really him, ba don ta masa faran sani ba tabbas zata ce bashibane k'ila an canza sa, this one's different from the Umar she knows, sanye yake cikin kaya na alfarma hannunsa rik'e da d'an makullin mota, fuskarsa sunkuye yana rubutu jikin takarda, gama rubutun da zaiyi ya k'arasa jikin wata da ba sai ance maka taji kud'i ba, Zubaidah tana gani ya shiga lodo kaya yana ajiyesu bakin k'ofar had'i da d'aura note d'in saman shopping bags d'in....

"Sulalewa tayi a wajen k'irjinta na barazanar tarwatsewa, ta nemi kukan da take ta rasa, tana jin tafiyar motar tayi saurin fitowa ta d"auki note d'in.... Abinda ta gani a ciki yafi komai girgizata.

_Hello, I've been calling your number wasn't going, I wanted to thank you for your kindness and for accommodating me, snn to be honest with you, akanki na soma sanin Wata mace so bazan mance ki a rayuwata ba, when ever you've time pls phone up me.. ... UMAR_

"Durk'ushewa tayi a wajen kaman zararriya ta soma fad'in" No bashi bane, it wasn't him, Umar bazai tab'a yin haka ba,....... Kuka mai k'arfi ya kufce mata, tana tsaka da kukan taji an daki windown dake gefenta da sauri ta mik'e tsaye tana tattare hijabinta.

"Wani murtuk'ek'en mutum bak'ik'irin ta gani idanunsa tamkar garwashi sai muzurai yake, tsawa ya daka mata tuni ta yarda takardan dake hannunta, ta shiga ja da baya.

"Da kakkausar murya mutumin ya soma fad"in" Ina zaki gudu munafukai kawai, tsayawa zakiyi ki fad'a mun yanda shegiyar k'awar taki ta tafi, don nasan plan kuka had'a tunda na gaya mata zanzo amsar kud'ina tunda daduro ba k'anwar uwarta bane balle na ubanta, shegu kawai kunsan bazaku iya biyan kud'in haya ba kuka baro gidajen iyayenku kuka fito daduro, toh wllhi akanki zan amshe kud'ina, munafuka harda wani hijabin munafunci saikace sallahn kuke, .......

"Jiki na kararwa Zubaidah ke ja da baya tana fad'in "Wllhi bansan kom...... Bata kai aya ba ya kai mata sura tayi wani tsalle had'i da ihu, daidai nan Zulaihat da Imam suka shigo,....

"Zulaihat baki na rawa take fad'in" Duguja wani irin bura'uba ne wann yaya zaka tsorata min k'awa.... Wawan naushi ya kai mata a baki saida jini ya fettsesu... Zubaidah ta kuma sakin wani k'ara cike da firgici, Imam kuwa kukan kura yayi ya cakume Duguja da duka, Ai Zubaidah na ganin haka, ta zura hannu bakin k'ofa ta suri jakarta ta soma gudu tamkar zararriya... Zulaihat dake kwance shame shame a k'asa da k'yar take iya k'walla kira wa Zubaidah amma inaa, ko juyowa batayi ba, tamkar mahaukaciya haka take gudu bisa layin, mutane 'yan layin kuwa wanda akasarinsu karuwai ne suka fito bama ido abinci sai shewa ake memakon ayi yunk'urin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login