Showing 96001 words to 99000 words out of 210924 words
goge hawayenta kafin ta fice cikin sauri,... Ameera dake lab'e tana jinsu kallo tabi Zahida dashi cike da tausaywa har ta fice, dukda k'arancin shekarunta kafin ta turo k'ofar d'akin yayan nata ta shigo.... Yanda Zahidah ta barsa haka nan yake zaune a wajen tamkar gunki.... Kai tsaye dispense Ameera ta wuce ta tsiyayo masa Ruqaya glass cup ta mik'a made, d'ago kai yayi yana kallonta kafin yasa hannu ya karb'a gamida rik'o hannunta ta zauna gefensa, a hankali ya furta " Umma should not no about this kinji little...
"Gyad'a masa kai tayi a hankali cike da tausayawa yayan nata......
*********************
"Wayarsa ta ringa nema baya shiga, i zuwa lokacin damuwa ya nuna sosai a fuskar Zubaidah, a jima ba'a jima ba sai ta lek'a k'ofarsa amma shiru, Annah kan tasan halin d'an nata ba lallai ne su gansa yau ba, don haka gaba d'aya duk'ufa addu'ar kariya ta shiga masa.
"Har wajajen k'arfe 12:00am na dare bai dawo gidan ba, Zubaidah kuwa har Barr Ansar ta kira amma ya sanar da ita basa tare, hankalinta Ya tashi sosai, tunaninsa ya hanata sukuni.... What if ya tafi kenan bazai dawo gareta ba, .... Da sauri ta soma girgiza kai ita kad'anta take furta " No... No I know he will come back for me, nasan bazai tafi Ya barni ba.....
"Annah dake kwance kamar mai bacci a hankali ta juya mata baya cike da tausayin halin dasuke ciki....
"Wajajen shabiyu da d'auriya taji k'aran tab'a k'ofarsa zumbur ta mik'e ta rufa hijabi saman rigar baccinta ta nufi waje....
"Tsaye ta hangosa k'ofar d'akinsa shima ita yake kallo, a hankali ta soma takwa har ta isa garesa..... Wasu k'wallan ta hango cikin idanunsa..... Gaba d'aya ta daburce ta rasa da wanne zata soma masa, hak'uri ne ko Me..... Bata ankara ba saiji tayi ya rungumeta very tied yana kuka da iya k'arfinsa.......
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:24] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
58
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Ya jima yana rungume da ita gam gam cikin jikinsa yana kuka kaman k'aramin yaro, rik'on da ya mata ya hanata motsa koda hannayenta ne, very tied ya rungumeta hawayensa gaba d'aya sun jik'a kafad'unta....
"Jikinta yayi sanyi sosai, k'irjinta yaci gaba da harbawa da sauri da sauri, bata tab'a jin yanayin data tsinci kanta ciki a yanzu ba her whole life. Tausayin Jalal yana fizgarta a hankali ta soma yunk'urin d'aga hannunta amma saiji tayi Ya kuma matseta yana fad'in" Pls let me hug you, don't let me go pls....
"Ji tayi k'afaduwanta suna barazanar kasa d'aukarta zuciyarta Ya karaya bata tab'a ganin sa cikin irin wann yanayi ba, she needs to be strong, she needs to remain steady.....
"Cikin rawar murya take fad'in" I'm here... I'm here for you kaji, pls ka daina kukan nan it hurts...... Ta k'arashe maganar cikin tsananin rawar murya..... Jin yayi shiru kaman an d'auke ruwa sai bugun zuciyarsa datake jiyowa daga k'irjinsa dake manne mat da nata yasata sauk'e ajiyan zuciya.... Sun jima a haka kafin tayi anfani da hannunta guda ta bud'e k'ofar d'akinsa suka shige ciki, Kan katifarsa ta zaunar dashi har lokacin bai iya cewa komai ba,..
"D'an kallonsa tayi taga ya k'urama waje guda rinanun idanunsa, a hankali ta furta " Barin d'aura maka ruwan zafi a kitchen then you take shower... Bai amsata ba har ta fice....
"Tana shiga kitchen flask d'in abincin data ajiye masa ta d'auko ta kunna risho tayi warming abincin kafin ta d'aura ruwan wanka wadatacce a tukunya ta nufi d'akinsa da tray a hannun ta...
"Annah tabi Zubaidah da kallo har ta shige d'akin Jalal, sauk'e ajiyan zuciya tayi gamida zama zama gijif cikin sofa.....
"Yanda ta fita ta barsa yana nan a wajen saidai yana looking sick, ajiye tray d'in tayi bisa darduman dake gaban katifar sa kafin ta soma serving nasa tana fad'in" Kaci abinci kafin ruwan yayi zafi yanzu zan juyo maka, but make sure you eat.... Har lokacin bai iya ce mata komai ba sai kallon da yake binta dashi....
"Gaba d'aya saitaji she's not comfortable, d'an mik'ewa tayi tana fad'in" I... I zan duba ruwan pls eat something.... Ta fad'i sanda take k'ok'arin mik'ewa, .... Ji tayi Ya rik'o hannunta gam cikin nasa... K'irjinta yaci gaba da lugude, hakan yake mata a duk sanda jikinsu ya had'u...
"A hankali ta zauna a gefensa gamida kallonsa a fizge.... "Kasa cewa komai tayi har lokacin hannunsa na rik'e da nata... "Jiyo muryarsa tayi yana fad'in" I'm not hungry....
"Ta d'ago ta dubesa da sauri kafin tace " No you must be, nasan bakaci komai ba tun safe, pls you need to have something in your system, if not you'll fall sick...
"Kallonta yake yanda duk ta wani daburce kafin yace " If only I could.... Bazan iya cin komai ba Zubaidah I lost my appetite....
"Sauk'e deep breath tayi tana kallon yanda yake murza 'yan yatsun hannunta, wani yanayi maras fasaltuwa ta tsinci kanta a ciki.... Muryarsa ta jiyo yana fad'in" Ta gaya maki..? Ta gaya maki who are really my real parents.. Pls tell me did she tell you..... "Cikin rawar murya yayi maganar...
"Dabara tayi ta cire hannunta daga cikin nasa kafin ta shiga k'irga 'yan yatsunta tana girgiza kai alamun a'a. A fili tace " But .... Saurin katseta yayi da fad'in" Don't cover up for her.... I can't believe she kept the truth from me all this while... Why did she do that.. Why why... Wanene ni, menene asalina, su waye iyayena suna raye ko sun mutu, idan sun mutu suwaye danginsu, idan suna raye a ina suke.... I need her to explain all these.....
"D'an shiru Zubaidah tayi kafin tace " She must have her reason,...... Da sauri yace " And what is the reason, who knows maybe.... Maybe I'm only a street child or maybe I'm a Bastard..... Da sauri Zubaidah ta katse sa da fad'in" Ka daina fad'in haka pls, ..... "Girgiza mata kai yake kana ya d'agi face d'inta suna kallon juna kafin yaci gaba da fad'in" Idan kinji ana b'oye maka asalinka tabbas bashida kyau ne ko tushe,..... I'm sorry Zubaidah but I really need to leave, bazan iya ci gaba da zama ba, ... I'm sorry I failed you, I couldn't make it up to you.... Ko bana nan ki sani cewa Jalal me k'aunarki ne.... Muryarsa yaci gaba da rawa sanda yake fad'in" promise me ko na tafi You'll keep fighting, I know you're strong, don't back down until they all get what they deserves, kici gaba da magana da muryan matan duniya, kar ki gaza har sai kin karb'a wa mata 'yancinsu na cin zarafin da gurb'atattu daga cikinmu ke masu...... "Girgiza kai kawai take tana hawaye take fad'in " No... No... No pls don't, don't leave me, I can't do it all alone, Don Allah kar ka tafi ka barni nima tafiya zanyi.....
"Manna goshinsu yayi su duka suna hawaye yake fad'in" You don't deserve me Zubaidah, baki cancanceni ba, you deserved someone who has good family background, you suffered alot, kin cancanci ki kasance cikin farin ciki....Ni kaina bansan kaina ba a halin yanzu I don't wanna add more pressure for you bayan wanda kike ciki..... Da d'an k'arfi ta furta "No ni bana son kasancewa da kowa sai kai, you and you alone, I don't care who your parents might be, all I want is to be with you..... Ta rage murya sosai tana girgiza kai take fad'in" Pls don't leave me... Please..... Please...... Rungumeta yayi sosai cikin jikinsa bata san sanda itama ta k'ank'amesa sosai ba.....
"Hadiza dake mak'ale jikin window taja dogon tsaki a hankali kafin tace " Insha Allah sai ka tafi, sai muga uban da zaici gaba da tsaya mata, munafukan banza munafukan wofi... Ji yanda suke kuka suke rungume juna kaman zasu cinye juna.... Ta kuma tab'e fuska ta matsa gefe tana rayawa a ranta inama itane ta sami miji haka mai k'aunarta gangariya kaman yanda Zubaidah ta samu, ta tuna yanzu zataje ta tarar da wann sullutun mijin nata wani k'unci ya kuma tokare mata mak'oshi a fili ta furta dole ma bayan komai Ya lafa na d'auki d'ana mu gudu, naje na sami gangariyan miji irin Jalal na aura... Haka ta wuce d'aki zuciyarta cike da Kishi da takaicin duk k'ok'arinta ganin ta k'ask'antar da rayuwar Zubaidah bata cimma burinta ba saima d'aukaka da soyayyan mutane da take dad's samu.......
"Sun jima suna rungume da juna yaci gaba da lallashinta yana fad'in" It's okay please, ki daina kukan haka, I won't leave you, kinji I'll stay no matter what, we will finish this together I promise you kinji Baby, I'll give Annah chance to explain, and no matter what she's still my Mother ....
"Lamo kawai tayi cikin k'irjinsa sai shan zuciya da sauk'e ajiyan zuciya da take yi akai akai....... A kunnenta yake rad'a mata "Baby could you pls stay here for a while, let me feel your presence pls..... Kasa ce masa komai tayi sai lugude da k'irjinta keyi.... Runtse idanunta tayi sanda taji numfashinsa dabb da fuskarta, shima lumshe idanunsa yayi sanda fuskarsu tayi daf dana juna suna jiyo d'umin numfashin juna..... A hankali ya sauk'ar mata light kiss kan lips d'inta.... Wani shokin ne Ya mamaye illahirin joking.....
.
Runtse idanunta ta kuma Yi sanda taji na k'ok'arin rabata da hijabinta, ..... "Memory d'in abunda Ya faru da ita ya shiga dawo mata, ta shiga jiyo sautin ihun su Salim a kunnuwarta ta tuna yanda suka keta mata rigarta har k'asa, ta tuna Jalal ne ya soma rik'ota Ya mik'ata ma Labib cikin Maye... Runtse idanunta ta kuma yi da k'arfin gaske ta shiga daddamk'e hannayenta....." Da sauri Ya saketa daga rungumar da ya mata..... Ganin yanda ta soma loosing control ta basa tausayi sosai.....
"Hijabinta Ya rufa mata kafin ya soma fad'in" I'm sorry.... I'm sorry baby I didn't mean it. Kiyi hak'uri kinji, bazan sake ba kinji har sai ranar da kika amince mun...... D'agota yayi still tana hawaye, Ya rakota har k'ofan parlorn Annah kafin yace " Goodnight baby..... Kanta a k'asa ta shige da sauri gamida turo k'ofan ta maida ta rufe....
"Tsayuwa tayi jikin k'ofar ta kuma runtse idanunta tana sauk'e ajiyan zuciya a hankali... Ta jima a wajen kafin ta samu ta d'an saita kanta snn ta shige d'aki cikin sand'a....
"Kaman b'arauniya haka ta wuce cikin sand'a ta kwanta.... Duk a zatonta Annah bacci take amma sai taji tace " How is he...???
"Gaban Zubaidah Ya yanke Ya fad'i wayyo Allahnta ji tayi tamkar Annah ta ga duk abunda sukayi da Jalal... Saida ta sauk'e ajiyan zuciya snn cikin d'an daburcewa tace " Eh... Eh lafiansa Lou Annah.... Bata kuma iya k'arawa da komai ba saiyi ma Annah saida safe da tayi.....
"Sauken ajiyan zuciya Annah tayi zuciyarta cike da jin Dad'in samun Zubaidah cikin rayuwarsu......
"Moment d'in da suka kasance da Zubaidah lately ya d'an gusar masa da bak'in cikin da yake ciki, ko babu komai akwai improvement sosai a tsakaninsu, he's hopping one day zata mance komai ta koma normal a hankali....
*****************
"Washe gari haka Zubaidah ta ringa jin kunya, tana son ta shiga ta dubasa amma tana jin kunyan ta yaya zasu soma had'a ido after what happened yesterday...
"Annah ta gama had'a kari snn tace ta kaima Jalal..... Kaman ta mata musu amma ta kasa d'aukan tray d'in tayi ta nufi d'akinsa.... Karaf suka kusa cin karo da Hadiza Hamma na biye da ita a baya yana tambayan ina Jalal d'in" Shakka babu Hadiza ne ta tasosa a gaba,.
"Kallon Zubaidah dataci magani take kafin ta soma murmushi tana wani kalle kalle, dariya ta soma a hankali take fad'in" Hiyye kice kin waye kin soma had'a shimfid'i da Miji..... Harara kawai Zubaidah ta galla mata kafin tayi wucewarta.....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:24] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
59
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kallo Hadiza ta rakata dashi gamida tab'e baki, k'wafa tayi gamida fuzgo hannun Hamma tace " Toh wuce mu tafi me k'anwa kana gani bamu isheta kallo ba balle gaisuwa.... Bata jira cewarsa ba ta shiga turasa da iya k'arfinta.....
"Da sallama Zubaidah ta shiga d'akin nasa kanta a k'asa, d'aura agogo yake a hannunsa da alama shiryawa yake....
"Da murmushi saman face d'insa ya amsa sallaman nata, Kallo yake kan binta dashi, she looks different yau, bai tab'a ganin kwalliya saman fuskarta ba dukda yau d'inma powder kawai da lip gloss ta shafa tayi looking different, ta k'ara kyau sosai kuma har ransa yaji dad'i this shows she's moving on,...
"Ohh why is he giving me that look, is awkward,.... Ta fad'i cikin zuciyarta, gaba d'aya sai taji dama bata shafa powdern ba,..... " Cikin d'an daburcewa ta soma gaidasa...
"In...ina kwana.
"Karb'an tray d'in yayi ya ajjiye bisa darduma kafin yace" Lafia Lou "Miss Beauriful.
"Miss Beauriful" ta maimaita a zuciyarta, jiya ya kirata Baby yau kuma Miss Beauriful.... Kaman yasan tunanin da take yace " You look gorgeous Miss Beauriful, so how Was your night, did you sleep well... Ya tambaya yana kallon face d'inta.
"Wasa take kanyi da 'yan yatsun hannunta , a hankali ta gyad'a kanta tana fad'in" Lafia, yaya jiki.?
"Still kallonta yake kafin yace " Naji sauk'i yanzu..... Zo ki zauna ya fad'i yana nuna mata gefe dashi... Babu musu ta k'arasa ta zauna...
"A hankali ya furta Serve me Miss Beauriful...
"Oh I'm sorry ta fad'i sanda ta soma d'aukan plate da spoon.
"Um um Miss Beauriful I can't eat any solid, tea kawai is okay....
"Are you sure..? Ta fad'i tana d'an kallonsa sai snn taga yanayin shigarsa yayi matuk'ar kyau, cikin Red Armani shirt da Faded Blue Jeans, bata iya jure kallonsa da sauri ta sadda kanta k'asa...
"Zubaidah ya kira sunanta sounding serious.
"D'agowa tayi ta kuma dubansa " Hannunta ya rik'o kafin yace " Thank you for been here....
"With a smile on her lips tace " Haka ne ya kamata, you've always been there for me..... Sun jima suna kallon juna kafin sukaji sallaman Annah...
"Zubaidah ce ta iya amsa sallaman ta nufi k'ofa ta bud'ewa Annah. Suka sakar ma juna murmushi kafin Annah tace " Daughter ya tashi kuwa..?
"Gyad'a mata kai tayi kana tace " Eh ya tashi Annah ki shiga ni barinje nayi sharan nan, ta k'arashe maganar tana bawa Annah hanya...
"Hannunta Annah ta rik'o snn tace " Muje Daughter kema ya kamata kisan komai, besides he's your husband..... Kaman rak'umi da akala haka Annah tajata suka koma ciki....
"Yana nan tsaye yanda Zubaidah ta barsa idanunsa tabb k'walla yake duban Annah, itama k'wallan ne cikin idanunta.....
"A hankali ta soma furta " I'm so sorry son...... Bai jira ta k'arasa ba ya k'araso da sauri gamida hugging d'inta yana fad'in" Pls don't Annah, you've nothing to apologize, on the contrary I should be the one to apologize, I'm nothing but an ungrateful.... Meyasa zanyi fushi dake after all the sacrifices you did for me. Kiyi hak'uri pls, I shouldn't have reacted that way...... " Girgiza kai ta soma gamida rik'e face dinsa tace " No Son this is all my fault, da ace na fad'a maka gaskiya tuntuni da ba haka ba... But believe me I kept it from you because I don't wanna lose you, and all I wanted back then is to keep you safe...
"Kamo hannunta yayi ya zaunar bakin katifarsa hannunsu rik'e cikin na juna yake fad'in" A iya zamana dake ban tab'a tunanin bake kika haifeni ba, sabida you've always been a good mother to me, ko a baya lokacin da na kasance the mysterious child , you never neglect me, nasan koma su waye iyaye na iyakacin kulan da zasu bani kenan, you raised me all alone, you my Mum and My Dad at the same time,