Showing 198001 words to 201000 words out of 210924 words

Chapter 67 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22887

your hell..... Ya k'arashe yana kuma tuntsurewa da dariya..
"Fuzar da iska kawai Salim yayi kafin ya isa katifar sa ya kwanta had'i da tak'urewa waje guda...

***********

"Zahidah da Shattima ne zaune saman wata k'atuwar darduma dake shimfid'e cikin katafaren Lambun wanda yake Kore sharr ta ko ina, yayinda Jalal da Zubaidah suke zaune saman wasu 'yan duwatsu a bakin ruwan dake faman gangagara cikin duwatsun, daga ganin su zaka san zukatan su sun cika da nishad'i,.
"Hannu Jalal ya mik'a ya rungumo bayan ta had'i da kwantar da ita cikin jikin sa, yayinda Zubaidah taci gaba da jefa k'ananan duwatsu cikin ruwan,...

"Zahidah da Shattima dake zaune saman darduman su na picnic d'in sai faman murmushi suke suna kallon su, sosai suka burge su, .
"Zahidah tasa bayan hannun ta tana share hawayen da suka zubo mata sanda Shattima ya labarta mata irin hardships da challenges da su Jalal da Zubaidah suka fuskan ta a rayuwa... " Ganin tana share hawaye yasa sa saurin mik'o mata hanki, ta amsa tana murmushi ta goge hawayen kafin taci gaba da fad'in" Sun sha wahala, but still....despite everything they've been through they didn't give up on each other, they deserve to be happy..... Tana kallon su take murmushi take maganar, taci gaba da fad'in" Just look at them, they are happy now, I'm so happy for the both of them.... Kaman daga sama ta jiyo muryar Shattima yana fad'in" And soon ours will come....

"Ta d'an dube sa tayi murmushi kafin tace " You know what Ya Shattima, Zubaidah should write her Story and share it with the world....

"Shattima ya murmusa kafin yace " Yeah hakane, labarin ta akwai tarin jarabawa da k'alubale snn ya k'unshi labarin mutane da dama, ciki harda naki, and you know what...??

"Ta kafe sa da idanu ba tareda ta iya furta komai ba...
"Shattima yaci gaba da fad'in" You are the most beautiful part of the story..... Sabida had'uwa dake da family d'inki ya sanya Jalal and his entire family cikin sabon rayuwa mai cike da farin ciki....

"Zahidah ta murmusa kafin tasa hannu ta rufe fuskar ta, kaman daga sama sai ganin Jalal da Zubaidah sukayi zaune gefen su, fuskokin su cike da murmushi. Wani sabon kunya ya kuma lullub'e Zahidah...

"Shattima ya murmusa kafin ya dubi Jalal yace " Bro now that you saw everything I've to admit that I love your only sister..... She's my inspiration, I love her with all my heart, and I promise to cherish her , love her and take care of her till my very last breath......

"Zubaidah sai murmushi take don kuwa abin ya mata kyau, tamkar taurarin cikin film. Mai da duban ta tayi ga Jalal tana jiran ganin nasa reaction d'in, murmushi ta gani saman fuskar sa, yasa hannu ya dafa kafad'an Shattima kafin yace " Bro if my sister loves you as well, then you have my unconditional support, fatana shine ku kasance cikin farin ciki, Shattima you are my brother from another mother and Zahidah is my favorite and only sister, all I want for her is a happy ever marriage..... I know you'll take care of her.... Ya ci gaba da murmushi ya rik'e hannun Shattima da hannu guda sann Zahidah da hannu guda kafin yaci gaba da fad'in" You both have my blessings, Allah Ya wuce mana gaba ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi...

"Murmushi ya cika fuskokin su, tabbas yanzu ya sami k'warin gwiwan doke Khalifa, this time around bazaiyi wasa da DAMAR SA ba... Zahidah ta k'araso ta janye hannun Zubaidah suka matsa gefe Alkyabban su sai sharan k'asa suke....

"Jalal da Shattima suka bisu da kallo fuskokin su cike da murmushi...


"Khalifa dake saman dokin sa ya hango komai, hawaye masu d'umi suka gangaro masa, tabbas idan yana son Zahidah he should let her go, ya k'yaleta ta samu farin cikin ta da wanda take so, abubuwan da ya gani ya ishe sa ishara, na farko bai zama Yarima ba snn na biyu bazai tab'a samun soyayyar Zahidah ba koda ya aureta snn na uku mahaifin sa na cikin tsananin ciwo tabbas d'an Adam ya kasance mai godiyar Allah da duk abinda Allah Ya hore masa not everything you want you get..... Juyawa yayi ya soma tafiya cike da sanyin jiki da nadaman kasancewa d'an Adam mai ji da kai da ya kasance a baya.....

**************

"K'arfe 5:30pm daidai jirgin su tayi landing a babban filin jirgin saman Abuja,..
"Annah tana rik'e hannun Kamal cikin nata, gaba d'aya sun canza sunyi kyau bakace su bane,.

"Shattima da Zahidah sun jero suma gwanin sha'awa, wani dad'i take ji finally Abbah ya barta tayi tafiya sabida Zubaidah da Hamman ta Modibbo snn zataga k'awarta Kausar....

"Gogan shima ya jero da princess d'insa, tana sanye cikin bak'ar doguwar riga abaya tayi kyau sosai, har wani shek'i ta k'ara, hannu yasa ya sakale cikin nata... D'an d'ago kai tayi tana duban sa ya sakar mata murmushi kafin ya rage tsawon sa daidai kunnen ta yace " You so beautiful my wifey I love you....

"Murmushi kawai Zubaidah tayi had'i da d'an mintsilan hannun sa.... Matse 'yan yatsun hannun nata yayi da d'an k'arfi suka sakar ma juna murmushi su duka biyu....

"Tuni Guards sun iso da motoci na alfarma, nan suka shige gaba d'aya suka nufi gidan su dake Asorock..


"Jalal zai masu ordering abinci Annah tace " No zasuyi ta dubi Zubaidah da Zahidah tace girls kun sanni babu wani sayo abinci da za'a keyi, this is not Fadah, dukan ku aiki zakuyi, I want you all to be good housewives....

"Shattima yace " Yauwa Annah hakan ma yafi... Ya k'arashe yana kashe ma Zahidah ido..

"Zahidah ta d'an turo baki tana aika ma Shattima hararan wasa kafin tace " Annah pls mana yanzu fah muka iso...
"Annah ta galla mata harara kafin tace " Girls to the kitchen, no excuses...

"Zubaidah sai dariya take ma Zahidah duk da ba wai jin dad'in jikinta take ba, haka dole Annah ta turasu kitchen...

************

"Zaune suke saman wasu brown kujeru masu shape d'in shell, daga gani ba sai ance maka na shak'atawa bane, daga ganin su kaga masoya amma sam su d'in basu fahimci hakan ba...

"Kausar ta tsiyaya masa lemonade d'in cikin cup kafin ta mik'a masa fuskar ta d'auke da murmushi..
"Murmushi shima yayi kafin ya karb'a yace " Thank you lil sis,
"Kausar ta murmusa kafin tace " At your service big bro.... Ehen you were telling me Salim's been caught ....

"Ansar ya kurb'i lemonade d'in ya had'iya yaji wata sanyi cikin zuciyar sa kafin ya ajiye saman k'aramin table d'in dake wajen yace " Yeah police sun kama sa, and you know what, his uncle reported him..... Their lives became so miserable....

"Kausar da idanun ta ke kafe waje guda suna neman ciko k'walla don kuwa duk ranar data tuna Salim da family d'insa hakan ne yake faruwa da ita, ta d'an sa bayan hannun ta ta goge hawayen sabida tuno Asmahn ta mahaifin ta da kuma Amir d'inta da tayi kana tace " They got what they deserve , non of them is innocent.... Mutum d'aya nake tausayi Hajiya Nurah mamin Labib, don kuwa I'm pretty sure Alh Kasim shine sanadin mutuwar mijin ta, ya cuce su ya ruining masu ryuwan su.... Shine sandin duk abubuwan da suka faru ko nace suke faruwa..... Ta k'arashe hawaye na gangaro mata....

"Cike da tashin hankali Ansar ya d'an turo gaba daf da face d'inta yake fad'in" It's okay lil sis, dukan su yanzu basu da wajen gudu, basu da zab'in da ya wuce suyi surrender, they'll all pay for their damn crimes.... Ki daina kukan nan kinji, it hurts, it really hurts..... Ya k'arashe fuskar sa cike da damuwa sosai.....
"Kausar ta d'ago tana duban sa, sun jima suna duban juna cikin idanu....


"Mumsy dake tsaye saman balcony kallon su take cike da so da k'auna, fuskar ta Ya cika da annuri tana mai son fahimtar abubuwa da dama, idan hakan ta kasance zatafi kowa farin ciki.... A hankali ta furta Allah Ya maku albarka 'ya'ya na...

_Ni Sameena na amsa da Ameen Mumsy_


************


"Fitowar sa daga gidan su Kausar ya ga kiran Jalal na shigowa, saida ya rage speed kafin ya d'aga yasa a speaker... Da kirari ya soma masa bayan sallama..

"Ranka shi dad'e,... Allah Ya taimaki Yarima, Allah Ya baka gidanku...

"Jalal ya murmusa kafin yace "Would you stop being ridiculous Attorney...

"Ansar yace " Toh ba gaskiya na fad'i ba... Kai fah you must adopt sarauta things like it or not...
"Yaya su Abbah, ya Gombe. Where is my Annah, nayi missing nata da delicious foods d'inta sosai fah.

"Jalal ya murmusa sanda ya saka trafficator yana sharan kwana kafin yace" Duk suna lafia... Gombe kuma mun baro shi lafia,...

"Ansar ya b'alle orbbit cwing gum ya jefa a bakin sa yana mai ci gaba da driving kafin yace " Ban gane kun baro Gombe lafia ba, don't tell me kuna Abuja...

"Jalal ya murmusa kafin yace " D'azu muka iso....

"Ansar harda wani sauk'e deep breath kafin yace " Great news ever, kasan we don't have much time left, kwana biyu ya rage a shiga kotun, ya maganar Dr d'in...

"Jalal yace " That's precisely why I called... Ka gane yanzu haka na fito daga gida gidan ka na nufa, Dr d'in yana Gwarumpa tare da Detective Mudi, so I'll fetch you up sai muje mu same su ku samu kuyi magana... And daga can zamu wuce station issue na case d'in sister inlawn mata ta..

"Ansar yace " No ba sai kaje Apo ba mu had'u a Gwarumpan nima daga Asokoro na fito yanzu haka ina hanya ma..

"Jalal ya murusa kafin yace " Kai wai tarewa ne kayi gaba d'aya a Asokoro, anya kuwa wann lil sis din naka ba ita ke b'oyeka a Asokoro ba....

"Ansar ya dara kafin yace " Kai kam sai mun had'u... Dariya Jalal ma yayi kafin sukayi sallama, ko wannen su ya maida hankali ga tuk'in da yake.....

**********

"Daga gidan inspector Mudi station d'in da aka tsare Hadiza suka wuce. Nan suka tarar da inspector Bilal shi ya tsaya masu akan komai har releasing papers d'in suka zama ready, dole aka je aka zo da Hamma don akwai yanda zai saka hannu kafin a Saki Hadiza...


"Idan kaga Hadiza sai ka tausaya mata yanda halittar ta ta canza lokaci guda, gashin kanta duk ya tuge ta d'aid'aice tayi bak'i, jikinta kuwa ta ko ina tabo ne, bakinta har tsini ya k'ara sabida azaban bugu da yake sha...

"Daga can data hango Hamma hawaye ya ciko idanun ta... Tana k'arasowa ta zube saman gwiwoyin ta, tana rik'e da k'afafun sa take sharb'an kuka tana rok'on sa gafara....
"Habibu ka yafe mun, ku yafe mun kaida Zubaidah nasan na ha'ince ku na zalunce ku, wllhi ko yanzu naga ishara, ku yafe min don Allah...

"Allah sarki Hamma tuni shima ya fashe da kuka harda shesshek'a.

"Jalal da Ansar cike da tausayawa suke kallon su, k'arshe mota suka wuce saida suka gama koke koken su kafin suka nufo mota suka wuce, Hadiza sai jero godiya da addu'o'in alkhairi take ma Jalal da Ansar....

**********

"Suna isowa gida Hadiza sai rakub'e rakub'e take, Zahidah da Kamal dake jera plates a dinning ai da gudu suka nufi stirs ganin Hadiza don kuwa sun zaci mahaukaciya ce koma aljanah....

"A tamanin su Annah da Zubaidah suka fito daga kitchen suna tambayar su lafia....


"Cirko cirko suma suka tsaya don kuwa ba don sunyi ma Hadiza farin sani ba sai suce wann tsohuwar kamun hauka ce, Hamma ne ke biye da ita yana mai ci gaba da share hawayen sa...


"Har gaban Zubaidah ta k'arasa ta durk'usa tana kuka shar shar da hawayen ta take rok'on Zubaidah gafara... Daga Annah har Zubaidah kai harma Zahidah dake mak'ale saman staircase tausayi ne ya cika zukatan su...

""Kamal kuwa da gudu ya k'araso ya rungume ta yana fad'in" Umma na kin dawo ne, nayi kewarki meyasa kika tafi kika barmu....

"Hadiza ta rungume Kamal tana mai ci gaba da kuka...

"Ta d'ago hannayen ta sama tana duban Zubaidah taci gaba da fad'in" Ki yafe min Zubaidah, ki yafe min Don Allah, wllhi tallhi hakkin ki ne, hakkin ku ne gaba d'aya ya kamani.... Annah ku yafe min, na tuba na gane kuskure na, bak'in ciki da hassada shi ya kaini ga halin da na tsinci kaina ciki, don Allah Zubaidah kice kin yafe ni....


"Zubaidah tasa bayan hannun ta ta goge hawayen ta kafin ta kamo Hadiza ta d'ago ta kana ta soma fad'in" Ni ban rik'eki ba Yaya Hadiza, ki sani na yafe ki tuntuni, Allah Ya yafe mu gaba d'aya....

"Hadiza ta rungume ta tana kuka sosai, cikin zuciyar ta kuwa bata jin zata iya fad'a masu musababbin abinda tayi har checks d'in Kasim Dasuki suka shigo hannun ta, babban dad'in dataji shine yanda ko kad'an basu tada zancen ba.... Asirin ta Ya rufu babu wanda zai sani..

"Haba Hadiza fah, an sake, wani dad'i take ji kowa ya nuna mata komai ya wuce, nan nan take da Zubaidah kaman ta maidata ciki, Zahidah kuwa sosai abin ke bata dariya, sosai matar take bata dariya, daga ganin ta kasan anyi makira ja'ira a da.....

"Zahidah tayita neman layin Kausar bata samu k'arshe kawai ta hak'ura sai bayan an gama da court case ta neme ta....

*********

"Alh Kasim ya d'aga idanu ya dubi k'ofar gidan kafin ya dubi d'an tasi d'in yace Malam nan ne... Cikin maganar sa da bai fita sosai...

"Mai tasi ya tsaya a daidai k'ofan gidan Ansar yanda Alh Kasim ya umarce sa....
"Kallon Mai tasi d'in yayi kafin yace " Malam ka taimaka min Don Allah ka warware mun keke na ka fito dani ka d'aura ni akai....

"Tsaki mai tasi yayi kafin yace " Amma dai wann mutumi nacin tsiya ne da kai, bayan na maka k'ok'ari na d'auko ka shine zaka wani ce na fito da kai, kai wllhi bazan yi ba, idan ban watsar da kai a nan nayi tafiyata ba.... Or to make you even more cripple.... Get out dalla banza kawai.....

"Ya k'arashe maganar sanda ya fito ya wurgar dashi harda jefa masa keken sa akan sa, ya karkad'e hannu ya shige motar sa yana fad'in" Banza kawai ni banma san meyasa na d'auko ka ba....

"Alh Kasim yasa bayan hannu ya share hawayen da suka zubo masa.... Kaman daga sama yaji ana horn a bayan sa... Cikin sauri Jalal ya bud'e motar ya fito yana fad'in" Subhanallah wani tsoho ne a yashe kan titi...

"Zubaidah na zaune gaban motar yayinda Annah Hadiza da kuma Zahidah suke baya.....

"Carkeke Jalal yayi yana kallon Alh Kasim dake watse k'asa, ashe shine a zube a wajen, da mugun mamaki yake bin Alh Kasim da kallo, yanda lokaci guda Allah Ya canza sa....

"Ganin da sukayi ya tsaya yana bin mutumin da kallo ya kasa taimaka masa yasa su fitowa babu shiri suka nufo wajen...

"Ai suma cak suka tsaya suna kallon ikon Allah.... Hadiza ta shiga tafe hannaye tana salati...

"Alh Kasim ya rarrafo ya k'araso gaban Zubaidah yana mai ci gaba da fad'in" Ta yafe masa...
"Mamaki da Al'ajabi ya hanasu furta koda kalma guda, tsoron duniya ya kuma cika zukatan su...

"Harta Jalal kasa cewa komai yayi sai kallon buwayar Ubangiji da ya tsaya yi.....

"Ansar ne ya turo gate ya fito don dama mai gadin sa ya sanar dashi abinda ke faruwa a Gate.. Har gaban Alh Kasim ya k'araso kafin yace " Alh Kasim yau kaine a k'asa, k'arshen tikatiki tik, ka sani Allah bazai tab'a barin zalunci ya tabbata a doron k'asa ba...
"Snn

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login