Showing 111001 words to 114000 words out of 210924 words

Chapter 38 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22867

nan sai ni, toooh sun min waya daga asibitin sun sanar dani ya farfad'o.... Toh Abba dama inaso na biya na dubasa idan akwai wani abu sai nayi settling kafin nayi tafiyar......

"Subhanallahi.... Mai Martaba ya fad'i fuskar sa cike da nuna damuwa. Snn ya d'aura da " Haba Abdullah yaya baka sanar damu ba, bayan kasan duk ranar juma'a mukan shiga asibiti duba marassa lafiya....

"Kai a k'asa Shattima yace " Ayimin afuwa Abba, amma jiya ne ma abin ya faru shiyasa ban sami zarafin sanar da kai ba. ....

"Shiru Mai Martaba yayi haka kurum Ya rasa dalilin samun faduwar gaba da yayi a dalilin wann labari da Shattima ya basa... D'agowa yayi bayan wucewar wasu 'yan dak'ik'ai kafin yace " Kaje Abdullah snn maganar tafiya Kano mun janyeta cikin satin nan har sai Allah Ya bawa bak'on ka lafiya.... Snn a kula dashi k'ark'ashin kulawar mu har Allah Ya basa lafiya.....

_(Tabbas ba k'aramin Al'amari bane zaisa gaban Sarki fad'uwa)_

"Kai a k'asa Shattima ya ringa jero godiya had'i da addu'ar girma da arziki wa Mai Martaba kafin yayi masa sallama ya fice......


"A daidai hanyar sashen Mai Babban D'aki ya hange Zahida alamun sashen Mai Martaba ta nufa.... Cikin sauri kaman me shirin kifawa haka ya fice ya nufi motar sa......

****************


"Damn it.... Damn it, cewar Alh Kasim had'i da buga table d'in dake gabansa kafin yaci gaba da fad'in" Sun mayar min da company kaman ofishin 'yan sanda.... It's all because of that stupid girl... If only I could kill her with my own hands......

"Mik'ewa Barr yayi yana shafa kansa da hannaye biyu kafin yace " Calm down Mr President.....

"No.. Don't ask me to calm down, I'm sick and tired of everyone accusing me just like that, da abunda nayi da abunda banyi ba..... Cewar Alh Kasim cikin tsananin fushi

"Barr yace Alh Kasim, first we need to think of who could have possibly do that, muddin aka ce anyi attacking Jalal toh fah mune za'a soma zargi, duk wanda yayi attacking Jalal fansa yake nema akanmu tunda mune dole za'a soma zargi....

"Alh Kasim yayi shiru yana muzurai kafin yace " That must be Hajiya Raliya and her daughter, sune kurum suke neman revenge akaina, sune zasuyi haka don ace ni nake yunk'urin kashe Jalal....


"Barr ya fashe da dariya kafin yace " This is ridiculous Alh Kasim.... Ta yaya zakayi tunanin Hajiya Raliya would do something terrible like this, .... That woman and her daughter are not capable of murder..... It's clearly someone's wants to see Jalal dead.....

"Toh waye kenan.. Alh Kasim ya tambaya yana mai tsare Barr da idanu....

"Tafe hannu Barr ya soma yana wata muguwar murmushi kafin yace " It's Umar.... That jerk is really insane, I'm quite sure he won't stop har sai yaga babu me numfashi cikin su hud'un, Jalal, Labib Salim da kuma Tariq... Kar ka mance he shot Salim a wajen nan, kar ka mance yanda yayi reacting ranan he's eyes full of seeking for revenge. Zaiyi komai just to be with that girl.... "



"Gyad'a kai Alh Kasim yayi yana huci kafin yace " I won't let him drag me into his mess.....

"Murmushi kawai Barr keyi kafin yace " Come to think of it....... Alh Kasim you are already in the mess ko ince we.... Don't forget mu muka jawo shi cikin wann mess d'in from the very beginning, we can't get rid of him just like that, ni dai a gani na what we should do kawai mu kirasa mu sanar dashi mun san komai he's behind of what happened to Jalal, yayi laifi ya b'uya a inuwar mu tunda mune main suspect na police... " He should just obey us ko meye muka saka shi yi tunda shid'in abokin aiki ne, if not we would expose his little secret.. Ko yaya kace..???



"Dariya Alh Kasim ya fashe dashi kafin yace " Shiyasa nake sonka Barr wann moleliyar kan naka ba a banza ba, now just call the idiot right away don karma yayi tunani zai b'ace mana, we have eyes everywhere..


************

"Tun daga nesa Mum ke rakub'e rakub'e tana tunanin shiga d'akin.

"Dad ta hanga ta cikin glass yana zaune kujera Me kallon na Tariq. A hankali tasa hannu ta tura k'ofar d'akin....


"Me kike yi a nan Dad ya tambaya yana watsa mata mugun kallo....


"Dan Allah ka barni nagan d'ana na rok'i arzikin ka kar ka koreni pls....

"Get out of here, you've no right over my son. Bakiji kunyan zuwa nan ba, you should be ashamed of your self.... I hate you I hate you Karima...... Ya k'arashe yana zama bisa kujeran had'i da goge hawayen idanunsa..... Kaman wanda aka mintsili Tariq haka ya bud'e ido.... Da sauri Mum ta k'arasa wajensa tana fad'in" Son Tairq my So....... Bata kai aya ba ya shiga k'ok'arin tashi dukda bandage d'in dake d'aure a kansa da wuyarsa kasancewar ya sami internal injury anyi masa aiki..... "Cikin zafin nama yake fad'in" Me kike yi a nan,.... Get out I don't need you in my life, just go back to your lover or what ever you call him.... You are despicable Mum I hate you for good, just get outta..... Muryarsa ya sark'e sakamakon tari da yaci k'arfin sa..... Hankalinsu gaba d'aya Ya tashi ganin yanda Tariq ke tari kaman zai amai da kayan cikinsa.... " Mum tayi kansa a rud'e tana kiran sunan sa yayinda Dad ya fice kiran likita a guje, nan d'aya daga cikin polisawa masu tsaron Tariq yabi bayan Dad........


****************


"Fitowarsu kenan daga cikin company d'in sakamakon wayar da Jane ta masa ta sanar dashi Hajiya Farha babu lafiya...

"Daga can bakin company d'in ya hangi Hadiza..... Wata murmushi ya sake don yasan ba'a ganin Hadiza haka nan... Da sauri yace da driver d'insa su koma cikin company, nan yasa security guda d'aya ya shigo da Hadiza....



"Suna zaune a wani meeting room madaidaici shida Barr security ya turo k'ofar yace da Hadiza " You can enter Miss.... Kallonsa kawai Hadiza tayi gamida tab'e baki tayi shigewarta don bawai ta gane me yace bane...


"Tun daga nesa Barr yake sud'e baki don kullum yayi tozali Hadiza haka yake yi, ....

"Alh Kasim ya mik'e yana murmushi kafin yace mata bissmillah ya k'arashe yana nuna mata kujera.

"Zama tayi tana watsa wa Barr kallo ganin idanunsa k'yam akanta, ba tare da b'ata lokaci ba ta gabatar masu da abinda ya kawota....

"K'uri Alh Kasim yayi ma hoton data mik'a masa yanason gano fuskar mutumin jikin hoton...... Marigayi Alh Ma'aruf Kumo ya ambata cikin zuciyarsa tabbas shine ko shakka babu wann Alh Ma'aruf ne snn wann matarsa ce wanda sukayi dabi a kotu..

"Murya har na rawa Alh Kasim yake nuna ma Hadiza hoton kafin yace " In.... Ina kika san wad'an nan.... ??


"Hadiza ta juya idanu kafin tace kai zan tambaya ina ka sansu, koda shike nasan kai kayi ajalinsu da zalunci irin naka......

"Alh Kasim ya kafeta da ido kafin yace " Be careful with your language lady......

"Tab'e baki tayi kafin tasa hannu ta fizge hoton tayi masu nuni da d'an matashin yaron dake jikin hoton tace hala kun gane wann fuskar...??

"Barr ya matso sosai yana kallon fuskar yaron, it's looks quite familiar, a ina yasansa??

"A fili Barr ya furta " ANSAR KUMO....... Shitttt.... Ansar Kumo. Ma'aruf Kumo, shakka babu d'ansa ne.....

"Daddy Ya mik'e gamida cire hulan kansa yayi jifa dashi yana fad'in" Make shirin faruwa dani, bayan na gama da Ma'aruf Kumo da iyalansa ashe na kashe maciji ne ban sare kansa ba..... No wonder that imbecile is doing all his best to defeat us in court, but I won't let that happen, I'll finish him just like I did to his family..... He has no clue what he's getting him self into..... Kallon Barr yayi kafin yace " Get me Faisal right now... Daga haka yasa kai Ya fice sai huci yake tamkar kububuwa, gaba d'aya ji yake duniyar na neman juya masa.....



"Hadiza ta mik'e tana fad'in" Ni kazo ka sallame ni dun wallhi bana aikin banza...... Barr Munir yasha gabanta yana wani tand'e harshe uwa tsohon maye yake fadin " Relax I'll take care of you..... Muje mota na baki kud'in aikin ki..... .

"Babu musu Hadiza tabi bayansa tana narka masa wata uwar harara, don ko babu komai tasan Habibun ta yafi wann fasali, hasali ma ba don kyau da Allah yayi masa ba da bata aure sa ba sabida lalurar da yake fama da ita......

*********************

*Prison*

"Zaune yake yayi jigum akan gadonsa wanda yake tamkar na 'yan makarantar kwana..... Kallon yanayin wajen kurum yake kanyi da mutanen dake wajen, wanda ko a mafarkinsa bai tab'a hango kansa a wajen makamancin haka ba, kai ko karen gidansu d'akinsa yafi nan balle ma'aikata..... Wai yau shi Salim Dasuki ne yake rayuwa a irin wann wajen, it's all because of her, that filthy mere girl, bak'awyiya Me kiwo, wai yau a dalilinta yake experiencing wann horrible experience d'in... This is a nightmare...... K'walla masu zafi suka ciko idanunsa..... Da k'arfin gaske ya daki bunk d'in dake gefe dashi.....


"OgaChuna Ya bud'e ido a hankali kafin ya malmalo wata ashar ya watsa wa duk wanda ya tadashi daga baccinsa gashi yau ranar hutunsa ne....


"Salim kam a maimakon ya basa hak'uri sai zaginsa daya soma, AI wata wawan tsalle ogachuna yayi ya cakumo Salim Ya shiga kilansa uwa Allah ne ya aiko sa...... "'yan d'akim kuwa sai ele suke suna wasa ogachuna..... Shigowar Labib kenan rik'e da bokiti, a tamanin ya yar da bokitin ya shiga k'watan d'an uwansa yana bawa Ogachuba hak'uri..... Ina Ogachuna bayaji baya gani, fad'i yake, let me teach this spoilt brat a lesson, ba kana gadara kai d'an Kasim Dasuki ba ko shi Kasim d'in ne yazo nan da kansa dole yabi ogachuna a sannu, coz this is my palace, I rules here....

"Saida Labib yabawa Ogachuna hak'uri ya tabbatar masa da zaran sun fita daga prison d'in nan zaiyi masa hiring good lawyer wanda zaiyi handling case d'insa shima ya fice snn Ogachuna ya hak'ura ya k'yale Salim, bisa wann yarjejeniya, har wani dad'i ogachuna yake ji snn yabawa Salim hak'uri shi kuwa sai foffozewa yake, ga jikinsa bai saba da wahala ba duk Ya wani tattauje Ya sauya kamanni....

"Labib ya jawo Salim gefe yana fad'in" You're very stupid you know, how could you got Into a fight with that d'an fashi.... Hararansa kawai Salim yake yana goge jinin bakinsa don sai yanzu yake ganin duk laifin Labib ne, idan da ace basu biye nasa ba, da yanzu yana nan tare da Kausar d'insa.. He did that to ruin his marriage with Kausar......


"Labib yaci gaba da fad'in" Guy we need to put up with everything around this place na d'an wani lokaci ne, we will soon get out of here and take our revenge Ya k'arashe maganar yana marking sauran kwanakin da Ya rage masu a shiga kotu jikin wata 'yar kalandar dake manne gefen gadonsa....

"Hararansa kurum Salim yayi gamida kwanciya kan gadonsa zuciyarsa ta cika fam da k'unci......



***********


"Ana kiraye kirayen sallan magrib suke shiga garin ta Gombe.......



Sam sam..... Sameena ce 😍
[1/23, 22:26] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

65

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*




"Bayan ya gama bawa Shattima labarin duk abunda ya faru, Shattima ma ya basa labarin yanda akayi suka samesa, dukda jin jikin da Jalal keyi bai hanashi yima Shattima godiya ba cikin muryarsa da bai fita sosai....

"Shattima ya girgiza kai kana yace ka daina min godiya haka pls Jalal, idan da inada ikon cire maka ciwon nan gaba d'aya da nayi.... This is the least I can bro....

"Murmushi Jalal ya d'anyi kafin yace okay bro, can you plz help me with a phone, I really need to call my family, inason jin halin da suke ciki coz nasan who ever did this to me kasheni yayi niyyan yi..... Snn nasan their lives might also be in danger.... I need to protect ZUBAIDAH... Ya k'arashe cikin rage sauti sabida rad'ad'i na ciwo da yake ciki......

"Tausayin Jalal ya cika zuciyar Shattima, gaskiya irinsu Jalal basuda yawa a duniya, despite his situation but he still thinks of his family, .... Sauk'e ajiyan zuciya Shattima yayi kafin yace " Jalal babu abinda ya sami family d'inka, according to police your family already knew about this.... Snn banida contact d'insu I should have called them.. Amma most important shine ka sami lafiya... Already 'yan sanda suna bincike, sun so suyi interrogating naka amma sabida yanayin jikin naka Dr yace a bari saiko zuwa gobe idan ka dad'a samun k'arfin magana....

"Shiru kawai Jalal yayi yana tunanin for how long zai zauna a nan waye zai kula da Zubaidah like he does, snn wani hali Annah ke ciki yanzu yasan for sure ta shiga tsananin damuwa....

"Muryar Shattima ya tsinkaya yana amsa sallama. Wata mata ce mai kama sosai da Shattima saiko wata 'yar budurwa wacce bazata wuce shekaru sha biyu ba....

"Shattima ya mik'e yana fad'in" Umma sannu da shigowa..... Umma kam bata iya amsa Shattima ba sai kallon data bi Jalal dashi, haka kurum taga tamkar tasan mai irin fuskar....

"K'arasowa sukayi itada Ameera suka zauna a wani coach dake gefe sunai ma Jalal sannu...


"Jalal ya d'an soma k'ok'arin mik'ewa yana son zama, Umma tayi karaf tace haba haba d'ana Don Allah kar ka tashi na yafe ka wllhi, sannu kaji sannu da jiki....

"Jalal na murmushi yake d'an amsawa da k'yar, nan Shattima yayi introducing Umman sa da k'anwarsa ma Jalal....
"Suka soma gaisawa shida Umma, sai faman jansa da surutu take sai ka rantse sun saba tun tuni,.... Abun har ya soma damun Shattima don likita yace Jalal kar yayi surutu sosai sabida aikin da aka masa, Yasan halin Umma idan ta ringa jero ma Jalal tambayoyi sai yasha kunya kafin ta basa kunya gwara ya katse zancen...
"Ya kai dubansa ga Ameera wacce ta sake baki da hanci tana kallon Jalal kafin yace " Little bazaki gaida abokin nawa bane...


"Ameera kam da baki bashida burki koda yake sak Umma ta gado. Bud'an bakinta sai cewa tayi " Mr Handsome yaya jiki...

"Murmushi kawai Jalal yayi kafin ya amsa mata.....

"Takaicin duniyar nan ya cika Shattima, ai tuni ya mik'e kafin a kuma b'anb'aro Wata yace " Umma tashi na rakaku kinga yanzu za'a kira isha kinsan Baba baison tuk'in" Malam Halliru da dare.....

"Harara kurum Umma ta watsa masa don sarai ta d'ago nufin Shattima baiso taji labarin 'yan fashin da suka tare su Jalal ne.... Mik'ewa tayi ba don taso ba ta shiga sallama da Jalal, shi kuwa harga Allah yaji dad'in company d'in Umma, haka yayita masu godiya had suka fice.

"Shattima na jan hannu Ameera ta kuma turo kai ta k'ofar tana d'agawa Jalal hannu tace " Allah k'ara sauk'i Mr Handsome....

"Jalal kam sosai yarinyar ta basa dariya kai family d'in Shattima sun burgesa da gani shida k'anwar nan tasa Tom and Jerry ne dukda ratan dake tsakaninsu a shekaru, ga Umman nasu kanta akwai barkwanci....


"Wata uwar rank'washi Shattima ya zuba wa Ameera bayan sun fito daga ward d'in kafin yace " Wato tsabagen kin rainani iskancin naki har ya tashi akaina ya koma abokai na.....

"Turo baki Ameera tayi kafin tace " Toh ba gaskiya na fad'a ba yaya wllhi yafika kyau..... Gajeren tsaki kawai yayi ya shiga jawota da kunne har jikin mota...

"Umma dake zaune a owners corner tab'e baki tayi kafin tace " Ai idan bakuyi ba baku had'u inuwa guda ba....


"Mal Halliru gaisawa suke da Shattima lokaci guda yana dariyan fad'an Shattima da Ameera.... Har saida yaga ficewar motar su daga haraban asibitin kafin ya sa kai ya koma cikin asibitin.... A daidai hanyar da zai sada ka da ward d'in ya hangesu.... Cike da mamaki yake binsu da kallo don kuwa tabbas ya gane Annah da Zubaidah, sai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login