Showing 99001 words to 102000 words out of 210924 words

Chapter 34 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22904

na gode Annah I can't ever repay you for that,....

"Murmushi tayi gamida d'an jawo kunnensa tace " But you still owe me an explanation, things are different now, you've Your Own Family... What I meant kana da aure yanzu and batu na aure batu ne da ya kamata ya zama pure and transparent. .. Juyowa yayi ya d'an kalli Zubaidah itama shi take kallo, saurin kawar da nata idanun tayi...

"Annah tayi murmushi ta rik'o hannun Zubaidah dana Jalal kafin tace " 'ya'ya na yau zan gaya maku wanene d'ana Jalaluddeen....


"Shekarun baya, iyayena sun kasance fulani makiyaya masu yawo gari gari, a garin Dukku ta jihar gombe a nan ne iyayena suka zauna suka jima har suka haifemu nida yaya na guda d'aya tol, Lado, ina matashiyar budurwa Allah yayi masu rasuwa su duka biyu a jere a Jere, Haka muka ci gaba da kiwonmu nida Lado, watarana Lado ya auro wata mata Lantana, wann mata bata da mutunci sam, haka ta ringa gallaza mun har saida na gwammace nayi aure koda mahaukaci ne, don na huta da azabar Lantana.

"Inada wani saurayi Malam Ibrahim saidai shi yaren mu ba d'aya bane, Lado ya k'ek'ashe bazan auri had'e ba, nace masa musulmi ne shima amma Lado ya k"ek'ashe wai had'e ne, k'arshe Lantana tace a badani amma bani da gadon shanun mahaifa na , nidai nace naji na aminta..... A haka aka Aura min Ibrahim badason ran Lado ba... Kunsan bafulatanin mutum da rik'o.... Na d'au shekaru Allah bai bani haihuwa ba, kwatsam watarana saiga ciki, na haifi yarona namiji kyakyawa mijina ya zab'i a saka masa Jalaluddeen, har akayi suna Lado da Lantana babu idonsu, bayan suna da kad'an mijina ya fita gona sai gawarsa aka kawo mun, naci kuka sosai, kuma nasan tunda Lado yace baya son auren nan tofah sai yanda k'arfinsa ya k'are... Ina nan ina takaba, watarana Lado yazo gidan maimakon ya min ta'aziya sai masifan da ya ringa surfa mun k'arshe yace " Saura wann had'en da kika haifa mana a uzuriya shima sai na kashesa, nan na gane Lado ne ya kashe mun miji, asubahin fari na had'a kayana na bar gari, nabi Daji, abunka da bafulatana sam tafiyar bata dameni tunda dama mun gada, Jaririn yarona ya kasa jure tafiyar a hanya Jalaluddeen Allah yayi masa cikawa, naci kuka har na gode Allah, daga baya naci gaba da tafiya tunda banida wani zab'i.... Bayan kaman kwana guda ina zaune k'ark'ashin wata bishiya na hange abu an duk'ulk'ulesa, koda na k'arass sai jin kukan jariri nayi, cike da firgici na tsuguna na duba dun tabbatarwa, ai kuwa jariri ne aka yasar sa wajen, d'aukosa nayi ina jijjiga shi ina mamakin wani mahaluk'i ne zai yasar da d'ansa haka ni gashi ina kukan rashin nawa da na yi..... Saida na duba jaririn sosai naga yanayin suturan dake jikinsa na tabbata ba iyayensa bane suka jefar dashi, wani mugu ne me neman ganin jaririn a mace. Koda na d'auki Jaririn nan na rasa me zan kirasa, zuciyata lokaci guda ta fad'a mun Jalal ne ya tafi Allah Ya kawo maki wani. Take na ambaceka da Jalaluddeen....

"Ta d'an ja fasali tana dubansu gaba d'aya hawayene ya wanke fuskokinsu kafin taci gaba da fad'in" Kasancewad a lokacin d'ana bai jima da mutuwa ba sai naci gaba da shayar da kai, na yanke shawarin dawowa gida da kai tsoron kada kaima ka galabaita..... Koda na koma Lado frightens me again, cewa wllhi sai ya rabani da wann had'en.... Jin haka ya haifar min da firgici, don lakaci guda Allah Ya saka mun soyayyar ka fiye da d'ana dana rasa. Da wann dalili ya sanya ni sayar da wasu 'yan kadarana dukda Lantana ta kwashe kusan duka kayana. Na shiga mota nazo garin Gombe, a nan ne na had'u da iyalan Dasuki family na soma masu aiki har na shiga makarantar yak'i da jahilci don na samu na gudanar masu da aiki yanda suke so, bafulatani da saurin fahimta tuni na fahimci abubuwa.... Na soma rainon yaransu wa'enda suke tsara da Kai wato Labib da Salim, jin dadin aikin da suke yi tare dani yasa su aminta dani sosai dukda k'arancin shekaru na a wancan lokacin... Hajiya Farha mahaifiyar Salim tayita kawo mun zancen aure a wancan lokacin nak'i aminta na nuna mata ni babban buri na shine nayi raising d'inka well, banyi aure ba balle 'ya'yan mijin ko shi mijin ko matarsa su tsangwame ka... A haka har muka dawo Abuja tareda su, wanda hakan ma yafi mun ko babu komai nayi nesa dasu lado..... Wann shine labarinmu Jalal,..... Ta k'arashe tana goge hawaye.....

"Cikin kuka Zubaidah ta rungumeta tana fad'in" Ashe ba ni kad'ai bace na had'u da iftil'ai na MATAN YAYA ba, you also suffered from some of my experiences.....
"Annah tace haka ne Zubaidah shiyasa duk me nemanka da sharri ka tura masa aniyarsa, har a gurun Allah kaine ka fishi....
"Basu ankara ba sai ganin Jalal sukayi durk'ushe gaban Annah yana kuka sosai..... K'arshema d'aura kansa yayi saman cinyoyinta yayi mai isarsa " He's out of words, but all he knows is that he owes Annah his life... She's a Heroin to him, she's his savour his everything,... He wasn't mistaken she sacrifices her life for him to survive, what on earth would he do to repay her all she's done for him, amsar shine babu wanda ya wuce ya k'aunaceta a matsayin mahaifiyarsa ya kuma ci gaba da yi mata addu'a har k'arshsn rayuwarsa......


"Fita wajen aikin da baiyi ba kenan sai wajajen LA'asar ya fice ya nufi garejinsu, cike da mamakin rashin jin Usman, shirun nasa yayi yawa....


"Yana isowa abokan aikinsa suka soma gaidasa suna masa jajen abinda ya faru, don labarin is everywhere now, chan jikin wata Tanka ya hangi Baban Usman wanda dama shine mai garejin, tunda ya hangi Jalal ya b'ata fuska...


"Da sallama Jalal ya k'arasa yana fad'in" Barka da maraice Baba, mun sameku lafiya...

"A ciki ciki Baba ya amsa ba tareda ya k'ara da komai ba, Jalal ya d'anyi Jim kafin yace " Baba a min afuwan rashin zuwa aiki kwana biyu, hakan ta kasanc...... Dakatar dashi Baba yayi kafin yace " Jalal a gaskiya bazan b'oye maka ba, bazaka iya ci gaba da aiki a wann garejin ba, nasan kanada k'wazo amma gaskiya dole ka ajiye aikin nan....... "Zaro sogayen idanunsa yayi baki har na rawa yake fad'in" Baba kayi hak'uri, inada iyalai kuma da wann aikin kawai na dogara, Baba idan fashin da nayi ne I promise to make it up to you, i'll work harder na kuma k'ara extra working hours in fact zan iya zuwa har a ranakun hutu, but pls don't fire me....

"Jalalu saidai fah kayi hak'uri don a gaskiya banyi shirin rasa wann gareji ba, yau kwana hud'u knn wasu mutane majiya k'arfi suna zuwa suna nemanka, snn sunce duk randa sukaga k'afarka a nan sai sun kashe.. Ni kuwa inaji ina gani bazan bari tashin hankali ya samemu ba, shiyasa ma nace masu ka bar aiki, yau shekaru kusan ashirin kenan da Bud'e wann gareji ba'a tab'a samun matsala ba saida kazo, snn ban tab'a samun sab'ani da d'ana Usman ba saida kazo, akan nace bazan k'ara aiki dakai ba, Usman yayi zuciya yayi tafiyarsa can Katsina garin mahaifiyarsa... Kaga kuwa ajiye aikinka shi yafi alkhairi Malam Jalal....



"Ya jima yana tsaye a wajen kaman an dasa kafin yace " Haka ne Baba, I'm surrounded with alot of troubles, and the last thing I want is to drag you in, na gode Baba, ttaimakon da kayi Allah Ya biyaka. pls idan kanada layin da zan sami Usman ka taimaka min dashi.....

"Yaro don Allah ka tafi kafin mutanen nan su riskeka a nan, kayiwa Allah ka tafi....

"Hak'uri Jalal ya basa kafin ya soma tafiya, gaba d'aya 'yan garejin basuji dad'i ba har suna murna Jalal ya dawo....


"Koda ya dawo gida a baranda ya zauna saman dakali gamida yin tagumi yana tunanin rayuwa, wann shine kad'ai aikin da yake yi gashi ya rasa, how would he support his family, how, a hankali ya soma anbaton Allah... Daidai nan yaji hannun Zubaidah a kafad'unsa.
"D'agowa yayi ya dubeta gamida sakar mata murmushi k'arfin hali...

"Har yanzu tunani lake ta tambaya tana mma zama d'an gefe dashi...

"Fuzar da iska yayi kafin yace " Tunani nake yanda zan rik'eku na ci daku da halal and to give you the life that you deserves.

"Pls ka daina sa ma ranka damuwa we are living a good life haka ma Alhamdulillah.... Gyad'a kansa yayi a hankali kafin yace " that was then Zubaidah, ina tsoron rayuwar da zamu fiskanta a yanzu, cos I'm.. I'm jobless, I lost my Job, I was fired, those Imbeciles will never leave us alone ...
"A tak'aice ya labarta mata komai...

"Idonta ya kawo ruwa, a hankali ta soma furta, Why life has to be so selfish..... Da sauri ya rufe mata baki kafin yace " Kar kiyi butulci wa rahaman ubangiji, this is all part of the trials in life, dole ubangijinmu ya jarabce mu ta yanda bamuyi tsammani ba, Allah Ya bamu ikon cin jarabawarmu.. I know we can survive this, we can go through it okay, Allah bazai barsu ba da sannu zai kamasu lokaci guda kaman yanda yayi wa pir'auna..... Rungume juna sukayi yana lallashinta.....


"Daga chan Hadiza ta hangosu rungume da juna ta saka shewa tana tafe hannu tana fad'in" Ah fillo an waye, Zubaidah kece mak"ale a k'irjin namiji.... A fusace ya d'ago zaiyi magana Zubaidah ta girgiza masa kai alamun a'a, a hankali ta furta " Let her be, this is all she knows.... Haba nan fah Hadiza ta k'ule ta soma surfa masifa wai Zubaidah zaginta take da harshen nasara, yaushe ta waye tazo birni, waya koya mata wanka har ta zama mutum, ... Fuuu ta wuce kirawo Hamma...


"Hayaniyarta ya d'aga Annah, Zubaidah kam tagumi kawai ta rapka tana tunanin yaushene zata rabu da masifar Hadiza... Jalal ya dubeta cike da damuwa, kai kodon Jarabar Hadiza zai karkad'e takardunsa ya nemi ko wani irin aiki ne ya d'auke matarsa ya rabata da wann Lunatic Woman d'in... Gaba d'aya bai iya hayaniya ba, amma sabida jarabar Hadiza yanajin zai koya......




**********************

*Marafah Construction Company*

"Har wajajen 11:00pm Alh Tahir bai fito daga company d'inba kasancewar kaya mai yawa ake sauk'ewa a store d'insa mai d'iban containers sama da d'ari.... Suna nan cikin store d'in shida muk'arrabansa suna tantance kayan nan suka soma him smoke ya gauraye ko ina, nan suka soma tari, securities suka shiga k'ok'arn danna abin kawo d'auki, the worse part d'in shine gaba d'aya exit na company d'in an gargark'amesu, babu hanyan tsira.....




Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:25] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

60

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*




"Kausar zaune saman gado tana kuma bin takardan sakin da yau Pappy ya karb'o mata daga wajen Salim a prison, goge hawayen idanunta ta kumayi zuciyarta na mata zafi, ta tuna satuttuka k'alilan baya tana cikin farin ciki sai gashi yau ta tsinci kanta da akasin haka, lallai ubangiji abin tsoro ne.... Shigowar Asmah cikin wani irin kuka yasa Kausar mik'ewa tsaye zunbur tana tambayarta lafiya...?

"Cikin shesshekar kuka Asmah take fad'in" Kausar Pappy.... Pappy ne, ...

"Rik'eta sosai Kausar tayi kafin tace " Asmah me ya sami Pappy na ina yake..... Bata iya amsata ba sai mik'a mata wayarta datayi nan taga yanda company d'in keci da wuta fire service sai k'ok'arin dakatar da wutan suke amma sun kasa.... Cikin sauri Kausar ta nufi downstairs tana fad'in" Pappy must be home ai, no My Pappy is at home, nothing bad will happen to him,.... Sandarewa tayi jikin staircase ganin Mumsy durk'ushe gaban mutum an rufesa da farin k'yalle....

"Wani fincika Kausar tayi gamida k'walla uban k'ara nan ta zube a k'asa sumammiya..... Mutanen dake parlon suka bi takanta Mumsy kam ita kanta hankalinta baya jikinta....


"Wasu securities biyu ne suka kuma shigowa parlon suka dubi Mumsy suka ce " Hajiya we are sorry we couldn't stop the fire...... Basu kai aya ba Mumsy tace " Ku fice mun a gida don Allah, na rasa abin da yafi dukiyar da take kan k'onewa, ku fice mun kafin nasa a fitar daku..... Ta k'arashe maganar tana kwantar da kai saman k'irjin Pappy....

"A hankali take fad'in" Meyasa ka tafi ka barmu Tahir, bazan iya rayuwa babu kai ba, why why Pappy.... K'arasowa Kausar tayi ta zube akan Mumsy tana wani irin kuka mai ban tausayi.... Wann dare gabaki d'aya Iyalan Alh Tahir Marafa haka sukayisa yanda sukaga rana haka sukaga dare.... Kan kace Me gida ya cika da jama'a abunka da Mutum mai yawan hidima da jama'a......


********************

"Washe gari da sassafe Ansar yazo d'aukansa maganar tafiyarsu Dukku sabida bincike da 'yansanda zasu aiwatar a yanda incidence ya faru, snn sunaso suyi reaching Dr d'in as soon as possible, ..

"Har k'ofar gida suka rakosu, idanun Zubaidah yayi rau rau Jalal ya gane hakan,... A hankali ya matso yanda take sanda su Annah suke kan magana da Ansar dashike shima gwani ne wajen zuba surutu....ya d"an rage tsawonsa saitin kunnenta yake rad'a mata...

"Hey don't cry, I won't stay long there, just a couple of days kinji Miss Beauriful, and Hamma zai ringa rakaki sch... Take care I love you..

"A hankali ta furta " You too take care......


"Wayan Ansar ne ya soma ringing a zatonsa su Detective Amir ne don tare zasuyi tafiyar, ga mamakinsa Lambar Asmah ya gani...

"Murmushi ya d'anyi data dace da kyakywar face d'insa wanda yake wankan tarwad'a kafin ya d'an ja gefe ya d'aga yana fad'in" Hello my Annoying Attorney kin tashi lafi....... Bai kai aya ba jin yanayinta.... " Cike da tashin hankali Ansar yace " Asmau Lafiya... Make faruwa..??

"Cikin kuka take fad'in" Ansar Pappy ne, My uncle has gone...... Bata gama yin shiru ba ya shiga jero salati da addu'o'i.... Kuka ta fashe mashi dashi sosai, Ansar ya shiga lallashinta hankali tashe... Cike da jimami suka k'arashe wayar, Ya maida dubansu gasu Jalal Wanda kwacaukwan hankulansu kega fuskar wayar Jalal... Jiki a mace ya k'araso garesu, Annah ta d'an subesa kafin ta k'arasa don kuwa suma news d'in da yanzu suke ganinta a wayar Jalal ta matuk'ar girgizasu.....


"Ansar kaji labarin ko, ta tambaya tana dubansa...

"Idonsa jazir yace " Kuma kunji koh, Alh Tahir Allah Ya masa rasuwa a sakamakon gobara da companynsa tayi... Annah ta gyad'a Kai tace gacan labarin da yanda wuta taci company d'in a wayar Jalal, ..

"Da sauri Ansar ya k'arasa ya amshi wayar Jalal yana gani...

"Ko menene yayi causing wutar sai Allah. Cewar Annah...

"Jalal ya d'an shafe gishinsa kafin yace " Wutar tafi kama da kunnata akayi, don daga waje ta soma ci kafin ta shige ciki...

"Ansar har lokacin kallon video d'in yake kafin yace " Definitely wann kunnata akayi...

"Annah tace " Toh wa zai masa wann aiki na zalunci haka....

"A hankali Ansar ya furta ALH KASIM.... Sunji abunda yace gaba d'aya suka juyo suna dubansa..

"Meyasa zai masa haka, after all he was his business partner...cewar Jalal fuska cike da damuwa...

" Fuzar da iska Ansar yayi kafin yace " Kafin Alh Tahir ya rasu sunyi baran baran da juna, The Marafah's and the Dasukis are now against each other.... Annah ta danyi jimm kafin tace " Exactly na tuna lokacin da d'yarsa Kausar tazo nan don taimaka mana tabbas basa good terms...

"Ansar yace " So sun zo nan before su sameni..?

"Da mamaki suke duban Ansar, ..... Dafe kai ya d'anyi kafin yace " Banso kuka sani bar, but ya kamata ku sani coz mun zama d'aya yanzu...

"Kausar da cousin d'inta Ansar su suka had'ani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login