Showing 54001 words to 57000 words out of 210924 words

Chapter 19 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22880

tana hawaye kafin tace " Basumin komai ba, ka tashi daga k'asan nan you are bleeding...

"Yunk'urin tashi yayi ya kasa, a hankali yake fad'in" I can't, bazan iyaba Zubaidah...

"K'rjinta yaci gaba da lugude ga hawayen dake bin k'uncinta sanda take k'ok'arin d'aura hannunta a jikinsa, kasa tab'a as tayi sai karkarwa da hannunta keyi....

"Ganin ya kuma lumshe idanunsa alamun babu k'arfi ko kad'an a jikinsa ga jini dake bin hancinsa yasa ta runtse idanunta kafin tayi ta maza ta tallafo sa dukda nauyin da yake dashi, ga shaking da jikinta keyi, d'an dafe garu yayi tana rik'e dashi har suka shige d'aki, taimaka masa tayi ya kwanta akan gado....

"Da sauri ta fice daga d'akin gamida sakin nannauyan ajiyan zuciya, k'arasawa d'akin Annah tayi ta tabbatar Kamal ya koma bacci kafin ta fito tana tunanin ta duba Jalal ne ko ta barsa....


"Hadiza ta d'aura hannu aka tana fad'in na shiga uku ni dije, hande bim boni, yanzu ina wann shashasahn ya shiga sai Allah...

"Annah ta watsa mata mugun kallo kafin tace " Ke rayuwa komai bai zama ishara a gareki, zagin miji kin maidasa ba komai ba, ki zauna kiyita zaginsa kiga ko zagin zai fito maki dashi... K'wafa Annah tayi kafin ta ci gaba da tambayan rumfar gabanta...

"Hadiza ta bita da kallo baki a Tab'e kafin tace "Chan maki idan kinji haushi na....

"A can wani rumfar suka hangosa an saka kallon k'wallo an cika rumfar sai faman wage baki yake yana dariya.... Annah hamdala tayi ta nufi rumfar ai bata ankara ba sai hango Hadiza tayi tana jawo kunnensa tana fad'in" Yaushe ka soma cin kasuwan dare ban sani ba, hak'uri ya shiga bata yana k'ok'arin k'watar kunnensa.
"Yanda Hadiza take shiga bata nan take fita ba, hannu tasa ta shiga lalume aljuhunsa tana fad'in" Ina kud'in Lemon naka yanzu haka ka bari sun laleka ko kana nan ka hangame baki da hanci kana kallo ko, toh wllhi gwarama tun wuri ka nemo kud'in nan don wllhi bazan sake baka jari ba...

"Kuka ya soma mata Don kuwa shakka babu an lale sa tass a wajen...

"Mutanen wajen kuwa me zasuyi banda dariya...

"Annah kunya kaman ta nitse cikin k'asa, k'arasawa tayi fuska a tamke ta rik'o Hadiza da k'arfi gaske kafin tace "Idan munje gida sai kicigaba daga yanda kika tsaya uwar shi.....




"Tana kwance tunaninsa ya addabeta, yau sati guda knn babu shi babu labarinsa, k'ila ya koma Dukku ne, k'ila bazata sake ganinsa ba, a hankali ta sauk'e ajiyan zuciya, lokaci guda taji ana mata knocking, zuciyarta ta cika da addu'an Allah sa Umar ne.....
"Da azamarta ta nufi k'ofar ta bud'e fuskarta cike da fari'a....

"Cak taja ta tsaya ganin akasin sa, Tariq ta gani tsaye jikin k'ofar da ganin fuskar sa kasan babban abu na damunsa...

"D'an k'arasawa tayi snn ta basa light hug kaman yanda ta saba kafin tayi saurin d'aura fake smile a Face d'inta don kar ya gane halin da take ciki.....

"Tanata masa magana babu response, d'an jim tayi tana karantar sa kafin tace " My Tee lafiya kuwa, meke damunka..

"Kallonta ya d'anyi kafin yayi gajeren tsaki yace lafiya, me kika gani ya k'arashe maganar yana kurb'an drink d'in datayi serving nasa..

"Sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin tace " You don't seem well ne...

"Gajeren murmushi yayi da gefen bakinsa kafin yace " Na gaji ne kawai kinsan kwana biyu ban zauna ba tunda muka soma bikin Salim. Ya k'arashe maganar yana bud'e mata hannuwansa kana yace " Oya come here,
"K'arasawa tayi cikin k'irjinsa ya rungumeta very tied, a hankali salon nasu ya soma canzawa, cak ya sureta suka shige d'aki... *Allah ka tsaremu Ameen.......*



"Tafi minti biyar tsaye a k'ofar d'akinsa hannunta d'auke da ruwa da tawul, banda lugude babu abinda k'irjinta keyi, a hankali ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tasa hannu ta murd'a handle d'in, har lokacin yana nan kwance yanda ta barsa idanunsa a lumshe....

"K'arasawa tayi k'irjinta sai fat fat fat.. Yake.

"Ciwon fuskarsa ta soma gogewa da ruwa da towel d'in,
"A hankali yaji sauk'an abu mai d'umi a Face d'insa, ya bud'e lumshasshun issuing nasa da kyar, ya sauk'esu kan kyakyawan fuskarta mai cike da firgici da tsoro, a hankali ya Saki murmushi, tayi saurin sadda idanunta, bugun k'irjinta na k'aruwa, lumshe idanunsa ya kuma yi ba tareda yace komai ba...
"kyakkyawan fuskan nasa yana fad'o mata sanda ya rik'ota yana dariya yana tangad'i ya mik'ata ma Labib, ta goge hawayen da ya zubo mata ta yunk'ura zata tashi saiji tayi tattausan hannunsa cikin nata ya rik'e gamm...
"A hankali ta juyo tana dubansa har lokacin idanunsa a lumshe yake fad'in" Pls saty, pls don't leave, kar ki fita su sake dawowa, I'll never forgive my self if they harm you., let me protect you pls.....

"Kuka ne ya kuma kufce mata, a hankali ta durk'usa tana k'ok'arin toshe kukan da ya zo mata...



*Dasuki Mansion*

"Agogon hannunsa ya duba k'arfe goma da mintoci, yasan Mami tayi bacci by Now, kai tsaye Penthouse d'insa ya nufa yanda Guest d'insa yake, kaman daga sama yaji muryar Mami daga balcony tana kiransa, gabansa ya fad'i don baiso taga ciwon dake bakinsa..

"K'arasawa yayi suka had'u a parlor k'asa, sai faman kauda kai gefe yake sanda suke gaisawa,

"Ina ka fito bayan securities sunce min tun d'azu kuka dawo daga wajen sinner d'in.

"D'an gajeren tsaki yayi kafin yace " For Allah's sake stop treating me like kid Mami, wai yaushene zan girma a gidan nan a daina tuhumata ina na fito ko ina zanje, I'm a business man fah yanzu Mami, karki mance na soma aiki da Dasuki Holding, pls Mami ki daina sa ma ranki damuwa kinga Dr ya hanaki shiga damuwa tun bayan rasuwar Dad.

"Gyad'a kai Mami tayi kafin tace " Dole na damu da kai Labib coz you are my only child, ina sonka fiye da yanda kake tunani, bana fatan wani abu ya sameka Son...

"D'an jim yayi kafin yace " I love you too Mami and I promise you I'll take care of my self, yayi maki.
"A hankali ta gyad'a kanta daga haka pecking goshinta yayi yace goodnight Mami....

"Kallo ta bisa dashi, tana son tambayarsa a ina yaji ciwo amma bai bata Chance d'in tambaya ba... Kallo ta bisa dashi cikin zuciyarta tana masa addu'an kariyar ubangiji, tana son d'an nata dukda ya kasance gagararre maras jin magana musamman yanzu data rasa mahaifinsa....


"Yana shiga penthouse d'insa ya hangi k'ofar d'akin da Umar yake alamun wuta a kunne, knn beyi bacci ba, da sauri ya nufi hanyar d'akinsa saidai kafin ya cimma k'ofarsa sukayi kicib'us a bakin k'ofa......



"A haka hannunta na rik'e cikin na Jalal bacci yayi awon gaba dasu baki d'aya.....



*This all you can have for today, I hope it will shine your day..... πŸ˜œπŸ˜œπŸ˜»πŸ˜»πŸ˜‚*

Sameena ce πŸ‘ŒπŸΎ
[1/23, 22:19] β€ͺ+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

38


*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...πŸ“–πŸ“š_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*




"Faisal ya mik'a takardun hannunsa ma Alh Kasim cike da rusunawa yace" Its done Boss, na gama binciken da zanyi akansa baki d'aya, he's here to seek his revenge, yanzu haka yana gidan Labib babu wanda yasani, Boss I think Labib is using the guy, I'm quite sure he's up to something.....

"Murmushi Alh Kasim yayi kafin yace " K'warai kuwa so yake ya had'a min trap, he couldn't accept the fact that I have nothing to do with his father's death, ..... Ya kuma yin wani murmushi suka kalli juna shida Barr Munir kafin yace " Yaro dai yaro ne.

"Drawer ya jawo ya ciro wani check ya mik'a wa Faisal yace make sure anyi withdrawing kud'in nan before azahar....

"Faisal ya karb'a cike da rusunawa kafin yace " Considered it done sir... Daga haka ya fice yana saka check d"in cikin suitpocket d'insa...

"Barr ya kalli Alh Kasim yana murmushi kafin yace " Alh karfa ka mance Nephew d'inka ne don't mess his life..

"Murmushi Daddy yayi kafin yace " The boy is somehow desperate, He's trying to protect him self but he don't know how, mikewa yayi yana gyara suit dinsa kafin yace " On the contrary I'm doing this to protect him, tunda na gama da mahaifinsa snn ban bar masa komai ba kaga ai ya kamata na kula dashi.. Gaba d'aya sukayi dariya su duka biyu...
"Barr Munir kuwa cikin zuciyarsa cewa yayi shed'an ma na tsoron Alh Kasim....
"Intercom ya danna kafin ya soma magana da sakatariyansa kan ta kira wayan Labib tace yana nemansa a office dinsa....


"K'arfe 9:00am daidai ya nufi d'akin da take, a hankali yasa hannu ya murd'a k'ofan d'akin tana zaune gaban dressing miro d'aure da towel tana shiryawa...

"Ko kad'an bataji shigowarsa ba sai ganinsa tayi akanta...
"Wani uban tsaki taja kafin ta mik'e tana fad'in" Don't even know how knock.... Ta k'arashe maganar tana watsa masa harara kafin ta wuce ta nufi bathroom, da sauri Salim ya rik'ota ya rungume tsam murya na rawa yake fad'in"

"No... Pls no Kausar, don't do this to me, don't reject me pls, I can't help it anymore, I'm dying to be with you, you know how I waited so long for this .... Kissing d'inta ya soma kota ina kaman wani tsohon maye....
"Da k'arfin gaske Kausar ta turesa gefe tana fad'in" Let go of me, how dare you, na tsaneka Salim, na tsaneka.. Why can't you understand..
"Hannu tasa tana share hawayen idonta ta nufi bathroom... Da sauri ya kuma rungumota da iyaka k'arfinsa wann karan. K'afa yasa ya tura k'ofan d'akin had'i da murd'a lock...

"Jikinta ya soma rawa, kallon mamaki take masa kafin tace " What are you doing Salim, pls don't, I beg of don't....

"Bai tsaya saurarenta ba ya shiga zuge belt d'in wandonsa...
"Tsalle ta kuma yi zata tashi ya danne ta..... Sosai ya murd'e hannayenta, cikin wani irin yanayi yake sunbatar ta,..

"Bakinta bai mutu ba taci gaba da fad'in" Yanzu na tabbatar Kai ka mata fyad'e, now I believe you are capable of raping... Na tsaneka na tsaneka for good..

"Sassauta rik'on da yayimata yayi a hankali, idanuwansa sun kad'a sunyi jazur...
"Da k'yar yake iya fad'in" Kausar I couldn't help it, I'm desperate to feel your body, you know I've been dreaming of this, Kausar I love you, I love everything single thing about you... It was never my intention na maki abunda na maki yanzu but pls consider my situation, haba haba ta yaya zaki d'auki maganar wata ki amince sama da nawa, wllhi k'arya take min pls believe me sweetheart, ko saninta banyi ba, k'arya ta maki sabida ta d'auka Jalal d'an gidan nan ne, sai bayan ta basa kanta ta gane ba d'an gidan nan bane shine duk abin duniya ya dameta coz bata cimma burinta ba na auren Dasuki Family, pls believe me my love I'm telling you the truth...

"Harara kurum take watsa masa ta goge hawayen idanunta kafin tace " Naji, ka tashi ka fita idan ba so lake ni na fice na bar maku gidan ba...

"Fuzar da iska yayi gamida shafa gashin kansa kafin ya mik'e jiki babu k'wari ya nufi k'ofa, yana fita taja dogon tsaki ta shige bathroom wai sai ta sake wanka tunda ta had'a jiki dashi.....



"A parlour Salim ya tadda Mummy fuska fal fari'a take kallon d'an nata...
"Goodmorning Son, ta fad'i tana k'arasowa kusa dashi, ganin fuskarsa babu walwala tamkar ba ango ba yasata cin birki...
"Yaya dai Salim, Lafiya, ta tambaya tana k'arasowa...

"K'arasa d'aura tie d'insa yayi ya d'an rank'wafo ya manna wa Mummy peck a chick d'inta kafin yace " Good morning Mom, Daddy fah is he still asleep..

"Kallonsa kawai Mummy tayi kafin tace " Ya wuce Office tuntuni...

"Gyada kai yayi kafin yace " I'll see him at the company..

"Wai lafiya Salim, meke damunka, wani abin ne ya sami Kausar..

"Dessert d'in dake saman table d'in ya d'an cakala, kafin ya dubi Jane dake jera abinci bisa dinning yace " Jane tell Mike to get my car rady.... Daga haka ya d'auki mug ya soma sipping coffee..

"Magana nake maka Salim meke faruwa, and me zai fitar da kai bayan kana hutun aiki...

"Gajeren tsaki yayi kafin yace " Oh please Mum, I don't wanna talk about it, I already lost my appetite... Ya mik'e gamida d'aukan phone d'insa yace " Na wuce office.... Kallo Mummy ta bisa dashi cike da mamaki.. Yana ficewa ta nufi sashensa yanda aka ajiye Kausar don sai sun dawo daga Honeymoon kafin su tare a gidansu.....


"Knocking Mummy tayi a k'ofar parlorn, jin ba'a amsa mata ba yasata tura k'ofan a hankali ta shige, ganin Kausar zaune saman kujera yasata sakin murmushi, ta k'arasa ta ajiye tray d'in dake hannunta saman dining table....

"Mummy ta k'arasa ta zauna d'aya daga cikin kujerun.. Da k'yar Kausar ta iya gaisheta...

"Mummy ta tsareta da ido tana son karantar wani abu..

"Kausar is everything alright, ta tambaya tana kallon Kausar wacce hankalinga kacaukam yake ga TV...

"Sai snn Kausar ta juyo tana duvanta ta Saki wani murmushi takaici kafin tace " Everything is not alright mummy until your Son finally divorce Me, daga haka ta mik'e ta nufi d'aki... Mummy ta daskare tana binta da kallo...

"Har ta isa k'fan d'akin kafin ta juyo ta dubi Mummy da kyau tace " Banyi kama da zama matar criminal ba, so pls kisa d'anki ya sauwake min, snn kar kuyi asaran kud'inku wajen sayan tickets babu yanda zanje da Criminal son dinku, excuse me.... Daga haka ta wuce d'aki had'i da banko k'ofar ta bar Mummy nan zaune kaman an dasa....




"Mamaki ne ya ishi Annah ganin Jalal baya d'akinsa, sam batayi tunanin Jalal zai fita aiki ba sabida raunukan dake jikinsa, to her surprise ya fita, babban abin da yafi damunta shine ko gaisawa basuyi ba balle sallama, bayan tasan d'an nata ba haka yake ba... Juyawa tayi da tray d'in dake hannunta zuciyarta cike da zullumi....



"Koda Umar ya tashi ya tarar Labib ya fice, Kallo ya ringa bin gidan dashi yanda aka zubar da Naira, komai na gidan abin sha'awa ne, wnn shine irin rayuwar da yake Madelin samu, tabbas babu abinda Labib ya nema ya rasa.... A hankali ya k'arasa k'ofar d'akin Labib ya d'an tura k'ofar yajita a bud'e, sandarewa yayi sanda ya shiga cikin d'akin duk kyaun d'akin da aka sauk'esa bai kama k'afar wann ba, kai his whole life bai tab'a ganin d'aki mai kyau irin wnn ba, k'arasawa ciki yayi yana tafiya cikin k'asaita yanaji inama ace this is his life..
"Kai tsaye closet d'in Labib ya wuce yanda yaga kaya tamkar shago, komai an jerasa in an arrange manner.
"wajen suit daban wajen tie daban wajen jampa daban wajen k'anan kaya daban, Kai komai dai da wajensa.. Takalma kuwa tamkar kantinsu, drwers din agogo masu d'an karan tsada da links daban, gabansa ne ya fad'i ganin bindiga cikin drower din, ya jima yana juya bindigar kafin ya ajiye, zuciyarsa tana raya masa k'ila ya ajiye bindigar ne don kare kansa, k'ila yanada license....
"d'aukan agogo d'aya yayi yana juyawa yana kallo, label d'in agogon na jiki, idan kayi converting to Nigerian currency wajen dubu d'ari biyar kud'in agogon, d'aurawa Umar yayi a hannunsa yana kallon kansa a mirror,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login