Showing 39001 words to 42000 words out of 210924 words
gane kan Labib ba, wuni yake zubur a d'aki ba tareda ya shiga sabgan kowa ba, ranar da Alh Jamil ya cika sati guda cif da rasuwa Daddy ya had'asu a parlor, Mami Labib da kuma Barr Munir.
"Banda mugun kallo da yake watsa ma uncle d'in nasa baya komai...
"Ko darajar gaisuwa basu samu daga Labib ba, .
"Alh Dasuki yayi gyaran murya ya soma magana dangane da business d'in marigayi Alh Jamil, kama daga yawan shears d'insa dake Dasuki Holding bashin da ya ciwo daga bankunan k'asashen waje, k'arshe ya tabbatar masu Alh Jamil bashida single cent da yayi saura a Dasuki Holding sabida mak'udan bashusshukan da ake binsa...... Ai bai ida rufe baki ba Labib ya mik'e yayi kansa gamida cakumo bababban rigarsa yana fad'in" How dare you Kasim Dasuki,..... Mami a zabure ta mik'e tana daka wa Labib wani irin tsawa, Barr Munir yayi saurin k'watar mai gudansa...
"Finciko Labib dake kan faman huci Mami tayi tana watsa masa mugun kallo mamaki ya hanata magana, "Har lokacin bai dana huci ba yake nuna Alh Kasim da d'an yatsa kafin yaci gaba da fad'in" Mami let me teach this Man a lesson, how dare he zaice Dad bashi da single cent a company d'in da kowa yasan hard working d'insa ne, wllhi kayi kad'an Kasim Dasuk...... "Muryarsa ne ya sarke sanda yaji sauk'an wata mari meji da lafiya a k'uncinsa, d'agowa yayi yana duban Mami dake faman huci ga hawaye na bin k'uncinta....
"Rik'e k'uncinsa yayi yana dubanta da mugun mamaki, abune da tun tasowarsa babu wanda ya tab'a masa, mugun kallo kawai yake watsa wa mahaifiyar nasa kafin ya soma fad'in" Mami you slapped me because of this worthless Man, Mami wllhi na tabbata Dad bai amso bashi ba, idan ma ya amso toh for the sake of the company ne, snn na rantse Alh Kasim was behind my father's death......"Labiiiiiib....!
"Mami ta daka masa wani irin tsawa hawaye na bin k'uncinta, Daga Alh Kasim har Barr Munir mamakin Labib ya hanasu koda motsawa...
"K'arasowa yayi gaban Alh Kasim kafin yace " Sai na zama ajalinka, ka rubuta ka ajiye.... Daga haka ya wuce sama yana tafiya kamar wani kububuwa..... "Durk'usawa Mami tayi a wajen ta shiga rera kuka....
"Mik'ewa Alh Kasim yayi yana sab'a babbar rigarsa ya fice a parlorn, zuciyarsa kuwa tamkar zata fashe, wai shine Labib ke gaya masa maganganun da duk duniyar nan babu wanda ya tab'a gaya masa yana a matsayin yayan mahaifinsa, lallai kuwa zai saita yaron nan yanda baya tsammani.
"Kai tsaye office d'in cikin gidansa suka wuce shida Barr snn ya danna wayar Faisal yace yazo yana bemansa urgently......
"Annah ta dubesa a karo na biyu kafin tace " Kaje kayiwa su Labib ta'aziyan.
"Ajiye spanner d'in dake hannunsa yayi gamida goge gumin fuskarsa kafin yace "Annah zanje yau insha Allah da zaran na tashi a aiki,
"Gyad'a kanta tayi kafin tace " Toh shiknn make sure kaji pls, dan idan baka je ba yaukam nida kai za'ajimu,
"Murmushi yayi mai bayyana dimples d'insa kafin ya goge bak'in man da ya b'ata masa hannu ya kamo hannayen Annah yace " Annah na Annahn Jalal na maki alk'awarin zanje insha Allah.
"Murmushi tayi kafin ta gyad'a kai tace nasan zakaje Jalal, Allah shi maka albarka,...."Usman ne ya k'araso wajen yana fad'in" Ah ah Annah har kin gama kallon shagon namu, ni nan nazo na zagaya dake wajen da ake gyara manyan motoci ne....
"Annah ta murmusa tace "Kar ka damu Unman ai na gani a haka ma, ubangiji ya dafa maku cikin sana'arku.... Ameen suka amsa dashi baki d'aya fuskokinsu d'auke da murmushi.
"D'an bubbuga hannun Jalal tayi kafin tace" Toh Jalaludden ni zan wuce gida na bar Zubaidah ita kad'ai, ta juyo ta dubi Usman dake tura tayan mota tace " Usman Allah Ya saka maka da mafificin Alkhairi, ga boy d'ina ka kulamin dashi.... Murmushi Unman yayi kafin yace " Ai babu komai Annah ai nida Jalal abu guda ne, kuma insha Allah zan kula dashi kamar yanda kikace ya k'arashe maganar yana dariyawa Jalal,
"Harara Jalal ya watsa masa kafin ya k'arasa ya rik'o hannun Annah suka fice har waje ya tare mata adaidaita, har saida yaga barinsu wajen kafin ya dawo cikin workshop d'in..
"Unman sai masa dariya yake wai anya ba shagwab'a yake wa Annah ba shiyasa take treating nasa like a kid.
"Murmushi da gefen bakinsa yayi kafin yace "She's always like that, and I love her so much, she's my parents, bansan dad'in mahaifi ba sai nata, she was my only family until Zubaidah came into my life....
"Jikin Usman ya d'anyi sanyi da jin kalaman Jalal, .... Shiru ya d'an biyo baya kafin Usman yace " and you're very lucky to have them as family she and your wife Zubaidah..... "Kallonsa Jalal yayi kafin ya gyad'a Kai a hankali yace "Yeah I know.... A wani b'angare na zuciyarsa kuwa tunani yake anya shida Zubaidah zasu iya kasancewa wann family d'in kuwa, kai abun da kamar wuya tunda already ya amince zai tafi ya bata waje tasha iska, k'ila idan ta jima bata gansa ba ta mance komai...... "K'aran horn ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi....
"Wata rantsattsiyar BMW 2016 ne ta shigo cikin garejin gyaran motocin, gani yayi Usman ya mik'e da sauri ya nufi mai motan, handshake sukayi fuskokinsu d'auke da murmushi kafin yaji Usman yace "Allah taimaki Shattima, Allah k'arawa Shattima tsawon rai.... Dariya sukayi su duka biyu kafin Shattima yace "Likitan mota Allah ya shiryaka, wato dai bazaka daina min wann tsiyar ba, Unman ya kuma yin gajeren Dariy kafin yace" Rankashidad'e irin gaisuwar data kamaceku knn..
"Murmushi kawai Shattima yayi kafin yace " Kasan meye wllhi sauri nake zan wuce Kaduna yanzu yanzun nan shine nace barin zo ka kwance min wad'an nan tayun don jiya na iso Abuja kuma tun jiyan nake jin kaman suna rawa ...
"Wai urgent kake so, gaskya saidai ka barta ta kwana a nan don wllhi ni yanzuma gidan abinci muka nufa, cewar Usman
"Haba Car Doc, kar muyi haka wllhi idan sak'on nan bai isa Gombe jibi ba ran Mai martaba zai baci kaga bai kamata ayi failing d'insa ba.
"Usman ya d'an tab'e baki kafin yace "Toh wai kai inji ne, daga Gombe ka nufi Abuja daga nan Kaduna ka kuma dawowa Abuja snn ka koma Gombe shin bazai maka uzuri ba, kai sudai masu mulkin nan izza da isa ne dasu, yo ba dole mota kullum a gareji ba...
"Gajeren tsaki Shattima yayi kafin yace "Wllhi kaifah kanada iskanci Usman, ce maka akayi mai Martaba na magana biyu, yarda dani da yayi ai shiyasa ya d'aurani kan hidimominsa, snn wann sunnar sarakuna ne basu magana biyu.
"Kai Why do I have to explain my self ma, gyara ne dole ka mun yanzu yanzun nan...
"Nannad'e hannayen rigarsa yayi ya sunkuya gamida wanke hannunsa da ruwan dake a cikin buta, ya d'iba yana d'an buge wondon jeans d'insa ba tareda ya kuma ce ma Shattima komai ba.
"Karya k'afa kawai Shattima yayi gamida turo hula gaban goshi yana kallon Unman cike da mamaki, koda ke ba abin mamaki bane idandai Unman ne yayi fin haka.
"Jalal muje idan ka gama ya fad'i haka yana k'arasawa wajen Jalal da ya canza kayan jikinsa daga blue uniform d'insu na aiki zuwa shirt da Jeans, fuskarsa ruwa ya kwanta luff...
"Wanda aka kira da Jalal Shaittima yake kallo, haka kurum ya tsinta kansa da fad'uwan gaba, snn wann daga gani miskilin k'arshe ne don ko kad'an Shattima bai kawo akwai wani a wajen ba don tun fara maganarsu kanzil bai furta masu ba.
"Shattima ya k'arasa gamida mik'a masa hannu yayi masa sallama, a tak'aice Jalal ya amsa sukayi masabaha. Shattima yace "Don Allah Jalal ka taimaka min kar ka biye na wann maras kirkin wllhi tafiyace a gabana, kuma ni idanba wann garejin ba bana zuwa ko ina, ni shinema in particular yake gyara min mota, don yaga na rik'e amanarsa ne shiyasa yake min wulak'anci.....
"Usman ya katse sa dariya gamida zubar da ruwan dake bakinsa kafin yace "Ayya mai sarauta ai kuka kakai gidan mutuwa idan dai wann ne ya fini dizgi barikaji, don shi har backing d'insa ake, wann da kake gani ma sana'arsa ma miskilanci yake shiyasa nake son zuwa naga wani irin tarairaya matarsa ke masa.....
"Kallon Unman kawai Jalal yayi gamida girgiza kai kafin ya dubi Shattima yace "Am kar ka biye nasa nidashi zamu duba maka yanzun nan....
"Kutt zaka duba masa dai don ni wllhi yunwa nakeji. ..... Baibi takansa ba sai jifa masa kayan aikin dake hannunsa yayi. Shattima kuwa me zaiyi banda dariya ganin yanda Jalal yasa dole suka soma duba masa mota....
"Mintoci kad'an suka gama d'aura masa wasu tayu had'i da warming motar abinka da k'wararru. Hararansu kawai Unman keyi, k'arshe daga Sbattima har Jalal dariya suka ringa masa Shattima yayita rok'onsu Allah Annabi suje suci abinci tare a eatery fir Jalal yak'i amincewa don shi alk'awari ya d'aukar wa kansa bai kuma rab'an wani mai abin duniya..
"Haka dole Shattima ya hak'ura ba don yaso ba, Usman kuwa mita yayita masa wai ai don yasan yanada mata me girka masa a gidane shiyasa yak'i amsar tayin Shattima, Tab'e baki kawai yayi kafin yace "Ai ban rik'e k'afarka ba, a tak'aice..
"Har yau Unman baisan me ya had'a Jalal dasu Labib ba shi dai kawai yasa ma ransa lokacin shiryuwan Jalal ne Allah ya kawo har yayi aure snn ya nisanta daga su Labib.......
"Ya jima yana kalllan k'ofar gidan kaman bazai shiga ba, sai kuma ya k'arasa yayi sallama wa securities d'in kafin yace "Su masa iso da Labib, gaba d'aya mamaki ne ya ishesu don kuwa sunsan a baya Jalal bashida shamak'i da gidan amma gashi yau neman iso yake.
"Babu musu d'aya daga cikinsu ya d'aga land-line d'in dake gate d'in ya kira cikin gida ya isar da sak'on Jalal....
"Mintuna k'alilan Labib ya fito don yasan ko yace ace Jalal ya shigo ba shigowan zaiyi ba......
"Tun daga nesa suke hango juna, for the first time da Jalal yaji tausayin Labib tun bayan incidence d'in da ya auka masu, gaba d'aya Labib yayi looking aabuntausayi shakka babu mutuwar mahaifinsa ya shiga jikinsa....
"Gaisawa sukayi ta hanyar musabaha kafin Labib yace "Mu k'arasa ciki mana,.
"Girgiza kai Jalal yayi kafin yace "No ba jimawa zanyi ba, I just came to say sorry for your loss, Allah Ya jik'ansa ya gafarta masa...
"A sanyaye Labib ya amsa da "Ameen, na gode Jalal.
"Jalal ya d'an dafa kafad'arsa kafin yace "Babu komai, ka gaida Mami pls sauri nake..... Ni zan wuce,
"Har ya juya yaji muryan Labib ya kira sunan sa
. "Jalal!
"Juyowa yayi yana dubansa, har gavansa Labib ya k'araso kafin yace " Na gode k'warai, and pls ka yafe mana abunda ya fraru a baya..
"Jalal ya d'an saka hannunsa cikin aljihun wandonsa kafin yace " Nasan kun bani k'waya nasha a daren sabida hankalina ya gushe ku cimma burinku akan yarinyar, kar ka damu ni na yafe maku wann, abunda bazan iya yafewa ba shine, I'll never ever forgive my self Labib, snn tsakaninku da yarinyar wnn babu nawa a ciki, idan ta yafe maku fine, abunda na sani shine na aureta ne to protect her, and I turn out to be her worse enemy, well I promise her zan tafi far away from her until she forgets everything, I'm pretty sure my Mum will take care of her har naje na dawo......
"Labib ya shafi gashinsa cike da kunyar kansa ko ince guilty conscious da ganin idon Jalal, don kunyar duniya da Labib sunyi hannun riga.....
"I'm happy for you bro, I wish you success in life Jalal, ya karsa gamida hugging kafadarsa, sallma sukayi Jalal ya wuce, har ya b'ace ma ganinsa kafin ya shige gida......
*Gombe, Dukku*
Baffah ya kallesa a karo na biyu kafin tace " Ka tabbata tafiyan shi yafi maka zama damu a nan.
"Ummar ya rataya jakarsa a kafad'ansa kafin yace "Baffah kar ku damu insha Allah zan dawo nan bada jimawa ba, snn na tabbata aikin da zan samu a wani garin zai fiye mun nan, snn zan manta da Zubaidah mantawa ta har abada.....
"Innah ta murmusa gamida goge k'wllan da suka zubo mata ta k'arasa ta dafa kafad'arsa, addu'an samun nasara suka masa daga ita har Baffah, suna d'agawa juna hannu har ya fice daga gidan.....
"Har bakin tasha Balele ya raka sa yanda ya shiga motar da zata fitar dashi zuwa Gombe, daga Gombe naga ya nufi motar danaji ana kiran garin *Abuja*
_Toh fah readers ga Umar ya tunk'aro garin Abuja, shin Me kuke tunanin zai faru,......? Jalal yana gab da barin Zubaidah..... Would she be safe??????_
Ku biyo QueenSamy don samun amsoshin.......
Sameena ce
[1/23, 22:16] βͺ+234 803 619 0581β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
30
*Β©Sameena Aleeyou...βπΎ*
_Queen Samy Novels Forum... ππ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Wata kyakkyawar budurwa ce a gefensa wanda ak'lla bazata gaza shekaru 24 ba, farace tass amma saidai daga ganin farin zaka gane akwai surki da man kanti, tufafin dake jikinta kuwa kaida ka gani kasan me tsadan gaske ne, a hankali take taunar chewing gum kaman bata son yi.
"Tun zamansa ta kafesa da idanunta, sosai ta kwad'aitu dashi, jikinsa ne ya basa ana kallonsa, d'an juyowa yayi aikuwa nan sukayi ido hud'u, murmushi ta sakar masa har lokacin idanunta na kansa,
"Bai maida mata martanin murmushinba saima kallon window da ya soma yi, budurwar ta ciro wayarta k'irara iPhone7 ta soma dannawa....
"Har suka kusa shigowa garin Abuja wann budurwa bata daina bin Umar da mayen kallo ba. Gaba d'aya ya tsargu da irin kallon da take masa, suna isowa tasha kowa ya soma fita daga motan.
"Raba ido ta soma yi tana neman ina ya shige, zaune ta hangosa saman wani benchi yana kallon mutane masu kaikomo, murmushi tayi kafin ta k'arasa wajensa cikin salo na tafiya da dogon takalminta mai d'ankaren tsini...
"Sannu bawan Allah, ta fad'i daidai sanda ta k'araso yanda yake zaune.
"D'ago ido yayi ya dubeta, tsaf ya ganeta budurwan nan ne wacce ta tsaresa da kallo a mota.
"A tak'aice ya amsa mata daga haka bai kuma cewa komai ba,..
"K'ok'arin zama ta soma yi gefensa yayi saurin mik'ewa tsaye yana binta da kallon mamaki kafin yace " Baiwar Allah lafiya kike bibiyata...
"Murmushi tayi kafin tace " Da farko dai sunana *Zulaihat* snn ba bibiyarka nake ba hanyace dai ta had'amu, da alama Kai bak'o ne a garin nan, don naga kowa na watsewa kai kana zaune, snn dokar wann tashar idan ka wuce lokutan rufewa za'a cika tara. Amma kodayake bansan dalilinka na zama a nan ba, ina ka nufa???
"D'an kauda kansa gefe yayi yana rage girman idanunsa kafin yace " K'warai ni bak'o ne a garin nan, snn kamar yanda kika fad'i vansan dokoki da tsarin tashar nan ba, na gode k'warai da kulawarki ni zan wuce, daga haka ya sab'i hakarsa ya soma tafiya
"Kallo tabisa dashi har ya nufi gate, d'an sauk'e ajiyar zuciya tayi kafin ta ciro wayarta cikin jaka ta shiga neman layin d'aya daga cikin samarukanta da take wanka...
"Hello Tariq, pls kazo tasha ka d'aukeni yanzu dawowata daga Gombe....
"Daga d'aya b'angaren Tariq yace " Uban me kikaje yi a Gombe Zulaihat, ki fad'a min kiran wani shegen Alhjin kika amsa...
"Gajeren tsaki Zulaihat tayi kafin tace "There you go again, shiknn bazanje naga dangina ba how many times do I have to tell you, Gombe garin iyayenane..... "Katseta yayi da sauri yana fad'in
" Look karki nemi raina mun hankali na sani sarai daga Yola kika zo Abuja neman abun duniya, kuma saida kika amince min bazaki sake bin wani ba bayana wato shine kika zaga kika tafi Gombe don kinga kwana biyu ban zauna ba koh, toh wllhi kikayi wasa zan k'wace makullan gidan dana kama maki haya.....
"Dalla malam ya isheka, Why do I even have to explain my self, you don't owe me any explanation, rayuwata ce nayi yanda naso da ita, kan wani shegen gidan da ka kama min kake neman yimin gori, wllhi kaima sanin