Showing 93001 words to 96000 words out of 210924 words

Chapter 32 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22909

da take cikin tashin hankalin ganin fuskokin mak'yanta... Jalal kam tamkar dutse haka ya koma a wajen ya kasa fahimtar komai...

"Annah taci gaba da bada labarin yanda ta tsinci Zubaidah har zuwa aurensu da Jalal...

"Mai Shari'a ya gama rubuce shaidar ta kafin ya buk'aci witness na gaba wato Hadiza, itama irin tambayoyin da akayi ma Annah aka mata ta amsa komai saidai bata fad'a alak'arsu ta makirci dake tsakaninta da Dasukis ba, harta Hamma saida tambayoyi ta k'araso kansa.


"Witness na k'arshe Kausar ce yanda ta bada nata shaidan iyakacin abunda ta sani da kuma b'acewar engagement ring d'in Salim a daren bikin baikonsu, ta k'arashe bada testimony d'inta tana watsa wa Salim mugun kallo.

"Rubutu ya kumayi kafin ya jefo wa Labib tambaya.

"Labib Dasuki kaji acquisition d'in da Malama Zubaidah take akan ka, shin ka amsa laifinka...??

"Girgiza kai Labib yayi kana yace " No your Honor ban amsa ba, I'm not guilty.....

"Mik'ewa Zubaidah tayi tana kuka take fad'in" Ka fad'a ma kotu gaskiya you liar.... Order....... Alk'ali ya fad'i gamida buga benchi..... Bata bar kuka tana fad'in Labib ya fad'i gaskiya ba.... Gaba d'aya ta zama out of control, Jalal kam gaba d'aya bai ma gane me ake ciki ba, Alk'ali ya buk'aci a fitar da Zubaidah kafin shari'a taci gaba, Annah ce ta kamata ta fice da ita har lokacin bata daina kuka ba tana fad'in k'arya suke, da sauri Barr Ansar ya d'au excuse yabi bayansu..
"Barr Ansar yace da Annah is better idan suka zauna a wani parlor he can take care of everything, daga haka ya koma cikin zauren gudunar da shari'a..


"Shari'a taci gaba.....

"Alk'ali yaci gaba da fad'in" Kotu tana saurarenka Malam Labib kayi bayanin abunda ka sani game da zargin da ake maka, iyaka gaskiyanka..

"Labib yayi gyaran murya ya soma karanto k'aryar da Barr Munir ya karanta masu su fad'i a kotu kamar haka.
"Ya mai Shari'a Jalal ya kasance abokinmu wanda ba'a rabamu gaba d'ayanmu mu duka hud'u, A ranar da muka isa garin Dukku don gudanar da bikin sakun ranar d'an uwana kuma abokinmu Salim, Jalal ya fad'a mana yaga wata yarinyar da ta tafi da tunaninsa ma'ana yaga yarinyar da yake so, mukayita jan kunnensa kar ya yaudareta kaman yanda ya saba yaudaran 'yammata wayayyu a nan Abuja, a daren engagement d'in Salim Ya nuna mana yarinyar sabida mu bamusanta ba sai ranar, Ashe tana d'aya daga cikin ma'aikatan da akayi hiring nasu, so bamusan yaya akayi ba don dukanmu bamu kwana a gida ba, mun kwana ne a gidansu abokinmu Tariq Maina, babu yanda bamuyi ba Jalal yazo mu tafi gidansu Tariq yaqi zuwa yace " He needs to take care of something tonight, we didn't force him to come with us, muka k'yalesa mukayi tafiyarmu, da safe Jalal yazo mana crying yana fad'in" I forced her slept with me, this is all I know your honor, daga baya family d'inta suka k'i amincewa sabida akwai baikon wani akanta, Jalal ya roki uncle d'ina ya nema masa auren yarinyar don asirinsu ya rufu kar su zama abin kwatance a gari. My uncle did as they wanted, all of a sudden mugaji wann sharri da suka k'ulla mana babu gaira babu dalili.....

"Barr Ansar girgiza kai kawai yake sanda ya buk'aci kotu ta basa dama yayi ma Labib wasu tambayoyi, kotu ta basa dama, haka ya ringa jefo tambayoyi masu rikitarwa wa Labib Barr Munir na karesa, ... Bayan an gama da Labib ne Alk'ali yayi ma Salim same tambayan da yayi wa Labib.
"Shima yayi denying ya bada irin statement d'in da d'an uwansa Labib ya bada....

"Barr Munir ya k'arasa gaban kotu kana yace " Ya mai shari'a ina buk'atan kotu ta bani daman gudanar da shaidun da zasu tabbatar cewa lallai k'age da sharri akayi wa Clients d'ina,.. Kotu ta baka dama Barr Anka..

"Na gode ya mai sharia ya fad'i sanda ya gabatar da Umar a gaban kotu...

"Kotu tana son sanin sunan Malamin ya fadi yana duban Umar, Umar yace sunan Umar Sanda, Barr Munir ya gyad'a kai kafin yace " Ko menene alak'arka da wacce take k'ara.

"Ni Ex Fiancee d'inta ne wanda akwai baikona akanta kafin ta auri Jalal,..

"Barr ya gyad'a kai kafin yace " Ko meyasa baka aureta ba.

"Dalilin da yasa ban aureta ba shine labari ya gama yad'a gari cewa ta bada kanta ma wani d'an me kud'i snn ta bisu sun tafi tare, don lokacin da na dawo ban taarar da familynta ba gaba d'aya sun tafi...

"Barr ya gyad'a Kai kana yace " Mun gode Malam Umar, Ya juyo yana dyvan Mai Shari'a kafin yace " Ya Mai sharia wann bawan Allah tsohon saurayin Zubaidah ne wanda ada yake shirin aurenta kafin taci amanarsa ta bada kanta ma wani ta gudu ta k'yalesa, da wann hujja nake son wann Kotu Mai Alfarma ta dubi irin cin zarafin da akayi ma Babban Family responsible mutane a k'asar nan irin Dasuki Family tayi watsi da wann sharia Mara's asali balle tushe, Na gode ya Mai shari'a...

"Rubutu Mai sharia yayi kafin yace " Ko lawyern wanda take k'ara yanada tambayan da zzaiyi ma tsohon saurayin wacce take k'ara.

"Barr Ansar ya mik'e yace k'warai Ya mai sharia inaso kotu ta bani dama,

"Kotu ta baka dama Barr Kumo. Alkali yace..

"Na gode Ya Mai sharia Barr Kumo yace kafin ya k'arasa gaban Umar yace " Malam Umar ko meyasa da ka dawo daga tafiyarka baka bincike asalin abunda ya faru da Zubaidah ba ka bi maganganun mutanen gari, shin anya kasan hukuncin kafa hujja da zargi a Sharia....


"Zare ido Umar Ya farayi ya rasa me zaice ya soma 'yan kame kame... " Eh Ba zargi nake ba iyayena dasuke mak'ota dasu sun tabbatar da haka.

"Toh meyasa da kace kaji a bakin mutanen gari...... OBJECTION MY LORD... Barr Munir yace kafin ya k'arada, Ya kamata Lawyern wanda take k'ara ya gane cewa Umar yazo nan ne bada shaidan iyakan abunda ya sani ba yazo ne don a tuhumesa ba...

"Alk'ali yace korafi ya karbu Barr Kumo ka gyara Kalman ka..


"Gyada kansa yayi kafin yace " Na gode your Honor... Tambayoyi yaci gaba dayi ma Umar wanda harta Alh Kasim saida zufa ta karyo masa, shakka babu suna da aiki ja a gabansu..

"Bayan Shaidan Umar Barr Munir ya kuma gabatar da shaida na gaba Zulaihat,Yanda itama t bada nata statement d'in lokacin da Zubaidah ta gudu gidanta....

"Daga k'arshe Barr Munir ya kuma nuna engagement ring d'in Salim Alk'ali ya buk'aci ganin na Kausar tabbas iri guda ne babu aunda ya banbanta....


"Alk'ali ya bukaci ganin Likitan da yayi treating nata a asibiti in the forthcoming trial snn aka d'aga k'ara har zuwa nan da 2 ga watar October a lokacin Tariq Maina ya sami lafiya snn za'a ci gaba da tsare wa'enda ake k'ara a gida tasku har na tsawon watanni biyu lokacin da za'a gudanar da sharia na gaba...

"Snn Kotu tabada belin Jalal for he is only trying to save and protect the Victim amma hakan ba yana nufin ya wanku daga confession d'in da yayi bane....



"Barr Ansar da Barr Hafiz suka rungume juna...




" Salim fad'i yake Daddy uncle pls do something I can't stay there for two months, Labib kuwa sai huci yake yana hararan Jalal dake Zaune a wajen kaman wanda aka dasa, har saida Ansar ya kamasa suka fito, tsaye ya hangi Annah da Zubaidah.. Annah kanta a k'asa don bata san ta yaya zata soma fuskantar sa ba...

Kallonsu kawai yake babu ko kyafta idanu sai jijiyoyinsa da gashin jikinsa da suka mimmik'e.....


....Sameena ce πŸ‘ŒπŸΎ
[1/23, 22:24] β€ͺ+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

57


*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...πŸ“–πŸ“š_



*Dedicated To All Victims Of Rape...*




"Kaman k'yaftawan ido haka suka nemesa suka rasa ga journalist da sukayi chaa ma Zubaidah, Ansar ne keta faman ansa tambayoyin Journalist d'in yayi nuni masu Zubaidah kan su wuce motar sa.

"Hankalinta duk baya jikinta damuwarta kawai taga Jalal, why did he suddenly disappeared, ta tambayi kanta a hankali, sauk'e ajiyan zuciya tayi don kuwa tasan tabbas hakan nada alak'a da abunda ya faru a kotu, statement d'in Annah, ita kanta ta kasa gane komai snn bata sami zarafin tambayarta ba...

"Ansar ke driving yayinda Hafiz ya dannne masa mazaunin me zaman banza, tattaunawa suke kanyi akan trial d'in da yanda zasu reaching Doc d'in da yayi treating Zubaidah a wancan lokacin...

"Gaba d'aya Zubaidah sai taji babu dad'i yanzu kowa yasan abunda ya faru da ita, kowa na kallonta da abun, ... Jawo mayafinta tayi tana rufe fuskarta, har gida su Ansar suka kaisu, nan suka tarar su Hadiza sun riga sun iso gida, a tunaninta Jalal ya iso gida amma shiru bata gansa ba, kasa daurewa tayi ta nufi d'akin Annah don tunda suka dawo Annah ta k'ule a d'aki...


"Zaune ta sami Annah ta k'ura ma wani hoto idanu, k'arasowa tayi jiki a sanyaye ta zauna gefen Annah, pic d'in hannunta ta kalla, itace da Jalal lokacin bai wuce d'an shekaru goma ba.

"Hannu tasa ta d'an dafa kafad'un Annah.... D'agowa Annah tayi tana dubanta, bata san sanda ta rungume Zubaidah ba, duk k'ok'arinta kar kuka ya kufce mata saida ya kufce mata..

"Cikin kuka take fad'in" He's my son, he's little boy, Jalal d'ana ne Zubaidah.... How am I going to tell him, how how Zubaidah.... Rungumeta sosai Zubaidah tayi hawaye na neman kufce mata itama, but she knows she need to be strong now sabida both Annah and Jalal needs her now, they were there for her a lokacin k'uncinta dole yanzu ta tsaya masu har sai abubuwa sun lafa....

******************

"Zaune yake k'ark'ashin bishiyan hannunsa dunk'ule ya d'aura hab'arsa akai, siraran hawaye suka shiga gangaro masa...

"Ni wanene?? Who am I????? Tambayar da ya ringa nanata ma kansa kenan.

"A hankali yaci gaba da furta why, why this had to happen, why me....???
"Dafe kansa da ya masa nauyi yayi snn yaci gaba da kuka da iya k'arfinsa bashida wani zab'i da ya wuce ya fitar da k'uncin dake cikin k'irjinsa ta hanyar kuka....

"Ya jima yana abu guda tamkar k'aramin yaro, he just couldn't help.....


******************

"Rai b'ace ta ahigo d'akin yanda ta tarar Asmah na kwance saman gado tana chatting da wayarta...

"Kallon Kausar dake faman rage kayan jikinta kafin tace " So how was the trial..? How did it go??

"D'an tsaki Kausar tayi kafin tace " They denied it, sunyi k'aryarsu da suka saba, ganin Salim yau ya kuma fama gyanbon dake cina, wllhi Asmah ji nake kaman na shak'esa kowa ya huta, you should have seen his face sanda akace baza'a bada belin su ba har sai Tariq ya warke, he was screaming calling his Dad and that incompetent Lawyer Munir....

"D'an mik'ewa Asmah tayi ta zauna sanda taga pictures an soma spreading nasu kana tace " Here, gashi sun soma watsa news d'in, Dasuki Holding tana gab da rugujewa Majority shear holders suna gab da cire dukiyansu a company d'in....

"I hope they do so, Kausar tace....

"Shiru Asmah ta d'anyi gaba d'aya jikinta yayi sanyi kafin tace " I'm afraid Ansar life might be in danger, what if something bad happens to him, I'll hold my self responsible..... Ta k'arashe maganar tana kwantar da kanta bisa gwiwoyinta....

"Kausar ta ajiye rigar hannunta kafin ta k'araso ta dafa Asmah tace " Sis pls don't worry, nothing bad will happen to him okay... Insha Allah, Allah yaga niyyanmu na alkhairi ki zama mai kyautata zato.... Kallonta Asmah tayi kafin ta gyad'a kai a hankali still damuwa ne fal a Face d'inta.....


*******************

"Faisal I want you to do a clean job, Alh Kasim yace kafin ya mik'e daga kujeran da yake ya k'araso gaban Faisal yaci gaba da fad'in" I trust you among all my boys, Faisal bana so a sami failure make sure babu wani suspicious da zaiyi linking d'inmu da aikin da zakayi, ...

"Faisal ya gyad'a kai kana yace " Yes Boss you can always count on me, You've my word....

"Murmushi Alh Kasim yayi yana bubbuga kafad'un Faisal kafin yace " Good,..... Saida ya d'anja fasali kafin yaci gaba da fad'in" Apparently gobe za'a shigo da kaya *Marafa Construction Of Company* I want you and your boys to set the company on fire... Make sure komai ya k'one....

"Murmushi Faisal yayi kafin yace " Boss considered it done,....

"Daddy ya murmusa yana bubbuga kafad'un Faisal kafin yace " Maza ka tafi ka soma shiri don aikin ba mai sauk'i bane....

"Gyad'a Kai yayi yana fad'in" Yes Boss kafin ya fice...

"Alh Kasim shi kad'ai ya fashe da wata dariya kafin yace " Alh Tahir kayi kuskure mafi girma a rayuwarka, I'll surely bring you down. . . Ya kuma fashewa da wata dariya.....

******************

*Gombe*

" Meyasa wann tunani ya kasa b'ace masa, meyasa ya kasa barinsa ya huta, ko yaje kai tsaye ya fad'a wa Mai Martaba ne, toh yace masa me, snn ta yaya ma zai soma,..... Kaman daga sama yaji ana k'onk'wasa mai k'ofa da k'arfin gaske... Tsaki yaja a hankali don yasan wann iskanci ba kowa bane illa Ameera , baisan yaushe zatayi hankali ba tasan ta soma girma... A fusace ya mik'e ya nufi k'ofar yana fad'in" Kinsan Allah idan baki daina zuwa kina buga min k'ofa uwa kina bashi ba wataran sai na karyaki a gid....... Aya yasa ma maganganun nasa ganin Ameera ba ita kad'ai bane gashi daga shi sai singlet ne da gajeren wando..... Saurin komawa baya yayi lokaci guda Zahida ta sadda nata kan k'asa....

"Baki a ture Ameera tace toh ba na rako Aunty Zahida bane tunda yanzu ko parlorn Umma baka fitowa...
"Harara kawai ya galla mata gamida komawa cikin d'aki ya zura jallabiya......

"Parlour ya fito yanda take zaune, tana sanye cikin jan leshi da yayi mugun karb'anta kanta yane da Farar alkyabba....

"Saida yayi still a wajen kafin ya k'araso yana fad'in " Meyasa kika shigo mun d'aki kanki d'aya kuwa.... Ki tashi ki fice tun wuri...... In a furious tune yayi maganar...

"Mik'ewa tayi cikin rawar murya take fad'in" I'm sorry Ya Shattima nasan a kwanakin nan ina avoiding d'inka coz bana so rashinka a gaba yayi affecting d'ina sosai, but I realized that I can't bear it, bazan iya jure rashin ganin ka ba Ya Shattima pls don't neglect me....

"Take zuciyarsa ta soma masa zogi, meyasa Zahida take neman zautar dashi bayan yayi alk'awari ma zuciyarsa cewa zai mance da ita for good...

"Dakewa Ya kumayi kafin yace " Get out Zahida, I don't want to have problem with your Father, He trust me I don't wanna break that trust, just get out.....

"Kallonsa take tana hawaye kafin tace " No bazan fita ba until we talk Shattima I can't survive without you...... For the first time da ta tab'a ambatan sunan sa kai tsaye....

"A zuciye ya kuma d'agowa yana fad'in " Then you should learn, kaman yanda nima nake koyon rayuwa babu ke....Are you out of your sense, what if... What if someone sees us and implies something, especially Khalifa da akwai baikonsa akanki yana iya shigowa any moment and you quite know how he is.... kinsan irin had'arin da kike k'ok'arin jefan........ Burki yayi ganin hawaye sharkaf a idanunta, take yaji babu Dad'i, d'an matsowa yayi daf da ita gamida yin k'asa da murya kafin yace " Hey I'm sorry, kiyi shiru kinji sis, pls sorry, I don't wanna see those tears it hurts....

"D'ago idanunta da suka jik'e da hawaye tayi ta sauk'esu kan Face d'insa da tsantsan damuwa ya nuna a face d'insa a hankali ta furta pls don't leave me...

"Kauda kai gefe yayi numfashinsa na fita one after the other kafin yake furta " Zahida don't make it more difficult, ki tashi ki tafi don Allah.....

"Mik'ewa tayi tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login