Showing 135001 words to 138000 words out of 210924 words
"Hankali tashe Ansar ya k'arasa gaban Tariq yana fad'in" Kar kayi haka Tariq, kar kaji tsoron su, kar ka fasa fad'in gaskiyan da kayi niyya, kar ka bari su razana ka donmin bazasu iya maka komai ba face abunda Allah Ya k'addara.... Tariq you promised you'll tell the Jude the truth.... "Finciko sa Barr Munir yayi yana fad'in" How dare you, why just can't you leave my client alone..... " Cike da b'acin rai Ansar ya juyo gamida dunk'ule hannu yakai ma Barr Munir naushi a baki...
"Ran Alk'ali idan yayi dubu ya b'aci... "Cike da b'acin rai yake buga table yana fad'in " Silence..!!! Silence..!!!!! Attorneys respect your selves, you are not in your chambers.. "Get out of here all of you get out..... Alk'ali ya fad'i cike da b'acin rai...
"Ansar ya dafe kansa kafin ya k'arasa gaban Alk'ali yana me neman afuwa...
"Saida Alk'ali ya nuna b'acin ransa sosai kafin shari'a taci gaba...
"Bisa ga rashin k'wakk'aran hujjoji da lauyan wanda take k'ara ya kasa gabatar wa gaban Alk'ali, da kuma rashin samin takamemmen hujja da zai tabbatar da cewa wa'enda ake k'ara sun aikata lafin.. Kotu ta d'aga wann shari'a zuwa ranar ashirin da bakwai ga watan January sabuwar shekara mai kamawa.. Snn wann zama ta shari'a da za'a gudanar shine zai kasance shari'a ta k'arshe, idan babu wann k'wakk'waran hujja da zai tabbatar wa'enda ake k'ara Sun aikata laifin, kotu zatayi fatali da shari'ar... Snn kotu ta bada belin Salim Tariq da kuma Labib, baza 'a ci gaba da tsare su a gidan kasu ba..... "Daga haka alk'ali ya mik'e...
"Wai zo kaga murna a fuskokin su Salim da iyayen su.... "Rungume juna kawai suke suna masu bayyana farin cikin su...
"Ansar kuwa zubewa yayi a wajen saman gwiwoyinsa had'i da zame hular sa ta lauyoyi a hankali... Wani irin k'una da zogi zuciyar sa ke masa... "Hafiz ya shiga basa baki yana nuna masa wann ba shine k'arshe ba, yayi hak'uri ya fawalla ma Allah komai, snn ya sani iyawan sa da k'warewar sa bashine zai basu nasara ba, a'a komai sai Allah yayi... Tabbas bazasu tabbata a doron k'asa suna zalunci ba....
"Kuka shar shar da hawayen sa Ansar yake kafin ya soma fad'in" Hafiz am I that incompetent...? I failed Hafiz, I failed them all.. "Rungume sa Hafiz yayi yana calming d'insa had'i da k'arfafa masa gwiwa..
"Ansar ya d'ago yana duban Hafiz kafin ya dafa kafad'arsa yace " Bro take Zubaidah and Annah home pls.. I..... I just can't face them right now, nasan Zubaidah is completely heart broken, we let her down... Both ni da Jalal.... Pls take them home, will you??
"Gyad'a kai Hafiz yayi kafin yace " Of course I will bro... Just take care of yourself okay..... And pls don't do anything violence, just try to remain calm kaji.... Kaga what you did earlier was very wrong.... Remember kai Attorney ne, you shouldn't have let your temper get the best of you.....
"Ansar ya gyad'a kai kafin ya dafe kafad'an Hafiz yace " Haka ne friend, it won't happen again insha Allah... I just can't stand that worthless damn man ne.... But insha Allah hakan bazata sake faruwa.... Thank you for everything...
"D'an dafe kafad'arsa Hafiz yayi kafin yace " I'll go ahead, see soon... Ansar ya gyad'a masa kai kurum suka fito a tare...
"Cincirindon mutane sun hanasu wucewa especially journalist, kowa yanason jin ta bakin su, kowa yana son jin a ina aka kwana a shari'a... "Zubaidah tana sako k'afafunta akai mata chaaa, journalist sai faman d'aukan hoto suke suna mik'a abin magana suna jefo mata tambayoyi.... "Annah kuwa sai kakkare ta take har suka wuce 'yan matakalan da basu wuce biyar ba wanda ake bi takansu a shiga cikin kotun...
"Hafiz yayi saurin k'arasawa motar sa ya bud'e masu yana fad'in" Su k'araso nan..
"Suna hango Ansar sukayi masa chaaa, kowa naso Ansar ya amsa tambayar sa...
"Ansar yayi gyaran murya ya soma magana cikin dakewar zuciya sai faman d'aukar sa ake da cameras " This is not yet over.. We will insha Allah prove to the whole world the kind of people they are.. Most especially Kasim Dasuki.. Da yardan Allah wann shine shari'a ta k'arshe da za'a danne mana gaskiyar mu.. We will patiently wait for the next trial to come.... Sannu sannu bata hana zuwa, rana dubu na b'arawo snn rana guda ta mai kaya... Daga haka yasa kai ya wuce, suna kuma binsa suna jefa masa tambayoyi...
"Barr Munir suka hango dasu Alh Kasim tuni sukayi wajen su suna son jin ta bakin su... Su Labib kuwa tuni an bud'e masu Luxurious Cars d'insu sun wuce ciki... Tariq ma motar mahaifin sa ya wuce.....
"Tun daga nesa jikinsa ya gama yin sanyi, mutane sun soma watsewa a bakin kotun, daga can ya hangi Ansar dafe jikin mota, ya kifa kansa... Yanayin da yaga Ansar ya tabbatar masa akwai matsala.. A hanakali ya k'arasa har k'asar bishiyar da Ansar ke tsaye...
"Kaman daga sama Ansar yaji hannun mutum saman kafad'arsa...
"Da mugun mamaki ya d'ago yana kallon Jalal,... Tsaki yayi gamida fincikan marfin mota zai shige... "Jalal yayi saurin rik'o hannun sa kafin yace " Wait Ansar, tell me how did it go, where is Zubaidah, how's she, ka fad'a mun tayi nasara, tell me su Labib are already sentenced to jell...
"Huci kawai Ansar yake yana watsa ma Jalal mugun kallo kafin yace " Let go of me Jalal, and old don't ask me that again..
"Jalal ya girgiza kai kafin yace " No Ansar, you need to tell me everything, kar ka mance na bar amanar family na a hannun ka.
"Ansar yayi wata murmushin takaici kafin yace " Where is the Doctor, ina yake..???
"Jalal ya d'an shafi kansa kafin yace " Ansar it's a long story, yanzu haka my life is in danger, but I managed to escape just to protect Zubaidah... Pls tell me how did the Heroin go..???
"Ansar ya sauk'e deep breath kafin yayi briefing Jalal duk yanda ta kasance...
"Huci kawai Jalal yake yi yana tuno irin Pain d'in da Zubaidah take ciki a yanzu haka.... Fizge keys d'in Ansar yayi kafin ya shige motar yayi mata key sai huci yake tamkar zaki....
"Ansar ya bisa da kallo ba tareda ya iya furta komai ba...
"Jalal ya kwasa a guje tamkar mai barin k'asa... Ansar yabi bayan motar da kallo still speechless...
"Umar dake chan gefen kwalta da motar sa, yana ganin fitowar Jalal cikin mota a guje ya furta, "You imbecile you can't runaway from me.. "Bastard".... A guje yabi bayan Jalal don kar ya b'ace masa...
"Faisal ma dake chan gefen titi yana jiran fitowar Attorney Kumo ya cika umarnin uban gidan sa, nan yaga ba Ansar bane a cikin motar... Tsaki ya buga gamida buga kan motar a lokaci guda, cikin sauri Ya tada motar sa da niyyan barin wajen kafin a soma zargin sa....
"Gudu yake kan falfalwa saman kwalta tamkar mai shirin tashi sama, bai tsaya ko ina ba sai k'ofar gidan su Tariq,.
"Isowar su Tariq gida knn Dad d'insa Ya sauk'a yana zuge gate yayinda Tariq ke zaune cikin motar tamkar mutum mutumi...
"Yana gama parking Ya isa jikin motar ya fincike marfin da k'arfin gaske ya fizgo Tariq waje.... Jansa yake a k'asa har Ya isa jikin motar ya bud'e marfin motar ya jefa sa ciki yana huci.....
"Dad da fitowar sa knn daga gidan zai zauna a mazaunin driver Ya shigar da motar sai ganin k'ofar motar yayi a bud'e snn babu Tariq, .... Hankali tashe ya hangi mota wacce basai ance wa'enda ke ciki ne suka masa kidnapping d'a ba, cikin sauri ya shiga jiran security number yana sanar dasu lambar motar.....
"Suna fitowa daga Layin su Tariq Umar Ya shiga bin bayan su..
"Zulaihat wacce tun daga kotu take biye da Umar tace da mai mashin d'in yabi bayan wancan motar...
"Tariq ya d'ago yana duban Jalal kafin yace " Jalal what this is all about??
"Bai tankasa ba sai gudun da yake faman falfalawa idanunsa sunyi jazir haka fatar jikin sa, kana iya hango jijiyoyin jikinsa yanda duk suka tattashi sukayi kore shar... "Shiru Tariq yayi bai kuma cewa komai ba...
"Saida ya kusan barin gari kafin ya shige wani bend ya paka motar... Daga can ta waje Umar Ya paka tasa ride d'in ya nufi cikin kwanar da sand'a.... Zulaihat ma ta sauk'a daga babur d'in ta gyara lik'abin dake fuskar ta, tabi bayansa cikin sand'a da dabara........
"Bud'e marfin motar yayi yasa duka hannayen sa biyu ya finciko Tariq waje had'i da kai mai naushi a ciki.... "Tariq ya kama cikin sa yana fad'in" Jalal friend why all this...
"Kamo hab'arsa Jalal yayi ya damk'e da k'arfin gaske yana fad'in" Don't don't you dare call me friend, you nothing but a disgusting being, now tell me why didn't you tell the truth to the judge why.. Why Tariq.... I thought you not like them, I thought kayi nadama kaman yanda kace, I thought bazaka k'aryata Zubaidah a kotu kaman yanda sukayi ba... But I was wrong, you're just like them, you're even worse than them..... Fincikewa Tariq yayi yana hawaye yake fad'in" Yeah I'm worse than them, I was a coward and so selfish.... But I did it to save my family, I have no choice than to lie.... If I confess Kasim Dasuki will destroy my father... Jalal believe me I did that to protect my father... Kana tunanin abun baya cina a rai ne, kana tunanin inada wata rayuwa da zanji dad'inta a nan gaba, .... " Dukansu biyu hawaye suke daga Tariq d'in har Jalal d'in... Tariq yaci gaba da fad'in" Babu ita Jalal, babu sauran rayuwa mai dad'i a gareni, I'm life is a complete nightmare, it started from that Night, daren da Ya kasance mafi muni a rayuwata, Jalal I regretted every single thing that I did, I wish I wasn't born, I lost you my best friend, I lost my mother, and my Dad bansan makomar rayuwar da zai shiga ba randa ya wayi gari babu ni, don nasan nawa tazo k'arshe, Jalal bazan iya ci gaba da rayuwa ba.... Dan Allah ka kashe ni na huta..... Ya k'arashe yana zuba gwiwoyin sa a k'asa yana jijjiga Jalal....
"Jalal na k'ok'arin maida hawayen sa yake fincikewa daga rik'on da Tariq ya masa, a hankali ya furta, you can't manipulate me again, I've had enough already, ... Friend or should I call you foe alike kaida saura abokan naka, I hate you all, I despised you all..... And I won't rest till I see you all behind bars.... Daga haka ya janye k'afarsa ya shige mota ya bar Tariq a nan yana k'walla masa kira da iya k'arfinsa, Jalal d'inma d'ingisawa yake don ba wai Ya gama warkewa bane, da mugun gudu Ya kwashi motar ya bar wajen.....
"Daga yanda yake lab'e ya fito ya cakume Tariq ya shiga kai mai naushi ta ko ina yana fad'in" You Criminal, I'll kill you, ... Tariq k'ok'arin k'watan kansa ya shiga amma ina baza a had'a mai lafiya da wanda bai jima da tashi daga jinya ba ...... Tun Tariq na motsawa har takai ga ya kasa motsa koda d'an yatsan sa ne... Dukan sa kawai Umar yake yana fad'in " Kun shiga tsakani na da ita, you'll all get what you deserve...... Ya kuma d'ago Tariq ya buga sa da jikin wani dutse take jini ya b'alle ya soma kwarara.... "Ganin haka yasa Umar soma jada baya....
Sameena ce
[1/23, 22:28] βͺ+234 803 619 0581β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
75
*Β©Sameena Aleeyou...βπΎ*
_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION π€_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*MU SHAA KARATU π* *Novel group this spectacular chapter is yours guys ππ .... I laughed so hard jiya ππ€£πππ kai bansan Alh Kasim nada tarin mak'iya ba snn Jalal da Zubaidah nada tarin masoya har haka ba.... Nonetheless habibtys Sameena hearts each and single soul that belongs to that forum β€πΉππ*
"Da baya da baya Umar Ya ringa ja ganin Tariq baya alaman numfashi...
"Zulaihat kuwa tsoro da firgici ne ya cika ta, k'unshe bakinta tayi da k'arfin gaske tana girgiza kai hawaye na fita daga idanun ta.
"A guje suka hangi motar ta fice daga kwanar.... "Kallo 'yan sandan suka bi motar dashi tabbas itace motar da mahaifin Tariq yayi reporting. Detective Amir ya d'anyi Jim kafin yace a zuciyar sa " That car is Barr. kumo's... Mi yayi a nan, knn shi ya kidnapping Tariq.... "Da sauri Ya shiga girgiza kai cikin rashin yarda da abinda zuciyar sa ke gaya masa...."Da sauri yace da driver d'in ya shiga bend d'in...
"Basu tarar da kowa a wajen ba, can gefen d'an wani dutse suka hangi Tariq, cikin sauri suka k'arasa yanda yake..... Da sauri suka nemi taimakon Ambulance... Suna masu ci gaba da gwaje gwaje...
**************
"Tana zaune a farfajiyan gidan gefen furannin da suka k'awata d'an madaidaicin gidan... Ko sauraren mota batayi ba don gaba d'aya tayi nisa duniyar tunani, daga ciki ma fitowa waje tayi to be alone....
"Ya jima yana kallon ta daga yanda yake tsaye bak'in cikin dake zuciyar sa ta yaye lokaci guda.... A hankali ya soma takawa har ya iso yanda take...
"Jikinta ya bata na wajen, yanayin da take tsintar kanta a duk lokacin da suka keb'e shi take ji..... " Juyowa tayi a d'an zabure.... Cak ta tsaya tana dubansa sanda sukayi ido hud'u.... "Sun jima suna kallon juna a haka kafin Zubaidah tayi saurin juyawa tana maida k'wallan da ya ciko mata idanu,... "Da sauri Jalal ya rungume ta ta baya... Ya d'ora hab'arsa saman kafad'ar ta had'i da lumshe idanu...
"Kasa katab'us tayi sai lumshe idanun ta da tayi siraran hawaye suka sauk'o..... "Cikin wani irin murya mai cike da rauni tace " Ya Jay pls let go...... "Dad'a matse ta yayi sosai hannayensa saman marar ta kafin ya soma fad'in" Baby I missed you, so very much.... I'm so sorry, I knw it hurts.... But believe me sweetheart it was never my intention to let you down.....
"Kukan da take matsewa ya kufce mata.... K'ok'arin b'anb'are hannayen sa take a jikinta amma ta kasa...
"K'aran motar police ya gauraye street d'in..... Gaba d'aya daga Jalal d'in har Zubaidah basu ji ba, don kuwa juyar da ita yayi kana yayi hugging nata sosai cikin jikin sa, duk jinin ciwon dake hannayen sa sun b'ata mata jiki.... "Har su Annah su Ansar Hafiz Hamma da kuma Hadiza suka fito daga cikin gidan Jalal da Zubaidah na rungume da juna...
"Detective Amir ne da wani Sargent suka shigo cikin gidan.... Ansar yayi saurin k'arasawa yana mik'a hannu ma Detective yake fad'in" DT how may I help you...... Sai sann Zubaidah da Jalal suka Saki juna...
"Kallo suka soma binsu dashi Jalal Ya k'arasa da sauri yayi hugging Annah had'i da mik'a ma Hamma hannu sukayi masabaha.... Daga nan ya k'araso wajen su Detective dasu Ansar...
"Shiru sukayi sanda Jalal ya k'araso.... Kallo kurum suke binsa dashi ganin rigar sa duk bushesshen jini ya b'ata... Jalal d'in ma kallo yake binsu dashi kafin yace " Detective Attorneys lafiya..? What is going on here..???
"Daga Ansar har Hafiz kasa cewa komai sukayi.
"Det Amir ya d'an zura hannayen sa a aljihu kafin yace " Jalal I'm sorry but you need to come with us to the station.... Earlier Alh Maina reported that his son was abducted.... Ya bada lambar motar Barr Kumo a matsayin suspect,........ "Tun kan yayi shiru Jalal ya soma girgiza kai yana fad'in" No no..... He was asking to kill him, he was even begging, ..... But I swear I didn't, I did not kill him..... Gaba d'aya ido suka zuba masa.... Su Zubaidah kuwa tuni suka k'araso fuskokin su fal tsoro..