Showing 21001 words to 24000 words out of 210924 words

Chapter 8 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22857

ƙaraso riƙe ƙaramar tray a hannun ta... Da mamaki take binsa da kallo ganin ya miƙe ya ɗauki car keys ɗinsa.

"Ajiye tray ɗin tayi saman tabƙe kafin ta bisa da kallo.
"Ɗan murmushi yayi kafin yace" Sweetheart I'm so sorry but I really need to go.
"Ɓata fuska sosai Kausar tayi kafin tace" I dont get u, you mean you leaving right now, haba Salim wai meke damunka ne, this days you acting very strange, tun jiya fah ka dawo bakazo ka ganni ba as your fiancee na ɗauka ma da zaran ka iso zaka zo ka ganni, ko waya mukayi da kai bana gane kanka kwana biyun nan, tell ne pls is something bordering you???
"Ƙaƙaro murmushi yayi gamida ƙarasowa daf da ita hannayenta ya riƙe kafin yace" Sweetheart don't let those ideas to ur head pls. Babu abinda ke faruwa sai zallan soyayyar ki, Daddy ne ya kirani and its urgent, you know how business men are, always busy,
"Hannunsa Kausar ta kalla bataga zobensa ba, ɗago ido ta kuma yi tana masa kallon tuhuma kafun tace "And where is your ring.
"Ƙirjinsa yabada rasss, cikin sauri ya saita kansa kafin yace " Em na cire shi lukacin da zanyi wanka but ina zuwa guda zan saka.
"Cikin rashin gamsuwa da excuse ɗinsa tace " But that ring is a promise bazaka taɓa cire shi ko yaya,
"Ɗan fuzar da iska yayi sanda wayarsa ta soma ƙara, da sauri ya saka a silent kafin ya kalleta yace " For Allah's sake Kausar its just a ring, besides mu a nan ƙasar ba auren zobe muke ba, its obvious kin saba ɗabi'un turawan yamma, but its diff here kin gane, whats important is that I love you with all of my heart and I mean it, Ɗan kallan agogon hannunsa yayi kafin yace" Daddy is waiting for me, I'll give you a call, luv u take care daga haka ya fice sai sauri yake kaman zai kifa...
"Kallo ta bisa dashi har ya fice......
"Cikin gida Kausar ta wuce jiki a sanyaye, haka kurum take ji wani abu na shirin faruwa tsakaninta da Salim.




"Ƙura ma Yaya Hadiza ido tayi tana binta da kallon mamaki, she couldn't believe what shes hearing, hawayae na bin ƙuncinta ta sa bayan hannunta maras ciwon ta ɗan goge kafin ta soma faɗin"
"Meyasa, meyasa kika ɗauko ni daga mahaifata kika kawo nan wajen, meyasa baki bari na mutu ba, meyasa baki bari an bisneni gefen iyaye na ba, meyasa kika rabo ni da garin masoyi na, shin kina tunanin zanci gaba da rayuwa ne, shin kina tunanin ni Zubaida har akwai sauran rayuwa a gaba na, babu ita. Mutuwa a wnn lokacin yafiye mun komai....
"Tsawan da Hadiza ta daka mata ya jawo hankalin su Momy da Annah gaba ɗaya suka nufo sashen da aka sauƙe su Zubaidah. Janta Hadiza ta shiga yi tana faɗin babu yanda zaki tafi a nan zaki tsaya a nan zaki ci gaba da rayuwa.......
"A zuciye Zubaidah ta fizge hannunta daga riƙon da Hadiza ta mata, babu alamun tsoro a tattare da ita take kallonta, cikin ɗaga murya take faɗin"
"Is this all you can do for me, iyakacin abunda zaki iya min kenn? Ki amimce ki biyo waɗanda suka lalata min rayuwa suka durƙusar da rayuwar yarinyar da bata ci masu ba bata sha ba, shin idan kece Zubaidah hakan ta faru dake shin yaya zakiji,..
"For years kina azabtar dani kina wulaƙanta Hamma na sabida lalura na rayuwa da yake dashi, daidai da rana guda ban taɓa saɓa maki ba, shin abinda zaki saka min dashi knn....
"Da mugun mamaki Hadiza ke kallon Zubaidah ta canza gaba ɗaya ta koma tamkar ba ita ba lokaci guda, Huci ta soma tana bƙrin kunya....
"Ɗaga mata hannu Zubaidah tayi kafin taci gaba da faɗin" Kin kula.dani tun ina yarinya Allah saka maki da alkhairi da abubuwan da kika min, Allah ya biyaki na sani nida Hamma na duk muna ƙarƙashin kulawarki ne, Allah ya biyaki. Amma ki sani mutuwata a yanzu tafiye mun komai..... Da ɗingishi ta juya ta koma cikin ɗakin gamida rufe ƙofar.....
"Bugun duniya Hadiza tayi Zubaidah taƙi buɗewa. "Taƙurewa tayi can ƙuryan ɗakin tana kuka mai tsuma rai.

"Momy jiki a sanyaye ta koma sashen ta yayinda Annah ke tsaye a wajen tamkar gunki, abu guda da Zubaidah ta faɗi yayi muguɓ ɗaga mata hankali, *Kika kawoni wajen waɗanda suka lalata min rayuw* kalmar da Annah tayita nanatawa kenn, abinda ya ƙulle mata kai ta kasa fahimta. Jiki a sanyaye ta wuce ɓangarensu tana tunanin lamarin......

"Daga yanda yake tsaye ya gama jin komai yaga komai a gabansa komai ya faru, Zuciyarsa taci gaba da zogi da raɗaɗi, shin haka zai tsaya yanaji yana gani rayuwarta ta ƙarasa lalacewa,..."A fili ya furta no, no no cikin sauri ya juya ya nufi gate ya fice......




"A ƙofar *Dasuki Holding* suka haɗu su duka uku. Salim ne ya soma fitowa daga motarsa kafin su Labib da Tariq suka fito dama tare suke Labib ya biya ya ɗauki Tariq, Securities ne suka ƙaraso suka karɓi keys ɗin motocinsu suka ƙarasa da motocin parking space snn su kuma suka shige cikin companƴ ɗin wanda yake ko ta ina glass ne tamkar a turai kake.



"Guys gaskiya nifa na fara nadamar abinda mukayi don wllhi my Dad is totally mad at me, cewar Tariq yayinda suke ƙoƙarin shigewa cikin lift, Salim ya ɗanyi gajeren tsaki kafin yace nima dai abin ya soma damuna don Kausar ta fara tunanin I'm hidding something from het. Tsaki Labib yayi sanda suka isa floor ɗin Daddy kafin ya juyo ya dubesu yace" Thats precisely why we are here, to talk with our parents, they shouldnt have brought that girl here in the first place. Gaba ɗaya suka kaɗa kansu suka ce haka ne.
"Duk yanda suka wuce gaushe su ake *The Dasuki's* ba yara masu ji da kansu da ƙarfin arzikin iyayensu......


"Sakatariyan Daddy ta ɗan dubesu cike da rusunawa tace " Am sorry but Mr president is at the middle of a meeting right now, you cant see him now....
"Dmmit!!!!! Labib ya faɗi da karfi gamida buga tabƙe ɗinta wanda yasata zabura.
"kwanto da kansa saitin fuskarta yayi fuska a tamke yake faɗin " If you dont want to get self fired then go in right a way, and tell him we wanna see him right now.
"Da sauri ta miƙe kafin tace Ok ok sir right a way sir,ta wuce ta nufi Conference hall .....


"Ana tsakiya da meeting sakayariyar sa ta kawo masa saƙon, fuzsr da iska yayi cikin ransa yace " Those boys wunt kill me, excusing kansa yayi kana yayi alama ma Lauyan sa Barr Munir kan cewa ya biyo bayansa, babu musu Barr ya miƙe yabi bayansa...



"Babban parlon dake cikin Office ɗin suka ƙarasa, shigarsu yayi daidai da banko ƙofar wanda hakan ya ja hankalinsu gaba ɗaya suka kalli ƙofan. Cikin wani irin yanayi suke dubansa.
"Barr yayi saurin faɗin " How dare you barge in here, ku talakawa really have no manners.
"Daddy ya girgiza kai kafin yaci it is not his fault, I have to make it clear to those stupids securities that this filthy jark isnt my son, he cant just come in here inti this very company.....

"Alhj Kasim we need to talk for the sake of these spoiled brats ya ƙarashe maganar yana nuna su Salim da tuni sun sha jinin jikinsu....


Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:12] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

16

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum....📖📚_


"Kallon mamaki suka bisa dashi, Alhj Kasim ya dubesu kafin yace "Excuse us, Labib ya kalli Uncle ɗin nasa kaman me son yin magana sai kuma yabi bayansu ya fice.
"Jalal ya dubi Barr Munir dake zaune saman ɗaya daga cikin royal chairs ɗin da aka ƙawata parlorn dasu kafin yace" Kaifa Barr aren't gonna excuse us...."Dakatar dashi Alhj Kasim yayi ta hanyar ɗaga masa hannu kafin yace " Boy ko me zaka faɗa min ka faɗa min gaban lawyer na, nida shi babu wani shamaƙi a tsakanin mu so just go ahead and talk.

"Ƙarasowa cikin parlorn yayi gamida zama bisa kujera mai kallon na Alhj Kasim tuni idanunsa sun rine zuciyarsa ta shiga masa zafi sabida abinda zai faɗi, bashi da wani choice rather than it..."Barr ne ya katse masa shirunsa da faɗin " Jalal we don't have the whole day, Mr President is a busy man so kayi abinda ya kawo ka.

"Fuzar da iska yayi kafin ya ɗago ido ƴana dubansu kana yace" *Zan aureta* daga nan shiru yayi bai kuma cewa komai ba, sai faman murza hannunsa yake jijiyoyin jikinsa sunyi ruɗuruɗu haka nan idanun sa sun koma jawur....


"Surprisedly suke kallonsa...
"Fari'a ne ya cika fuskokinsu mission ɗinsu goes well wann na ɗaya daga cikin dalilin da yasa suka taho dasu, don sun san muddin Jalal ya aureta toh magana ta ruhu har abada babu abinda zai kuma tono ta.
" Kafaɗan Jalal Alhj Kasim ya shiga bubbugawa a hankali kafin yace" Now you proved to us you are capable of helping her, da kayi gigin kai report da shine ka cuceta ka kuma cuci kanka, don bazaku taɓa kancewa tare ba, you'll endup in jell and ita kuma she might commit suicide ko depression ya karta gaba ɗaya, and ƴour poor mother will loose her only son, Jalal you did the best thing.

"Har lokacin dai Jalal bai ce masu komai sai kallon gefe da yake yi.
"Alhj Kasim yayi ma Barr ido, check Brr ya ɗauko ya rubata mar kuɗi kafin ya miƙa masa yace" Ka je ka nemi hida sai ku yare gaba ɗayanku a can....." Bai gama rufe baki ba Jalal ya miƙe yana masa mugun kallo kafin yace" Bana son komai daga gareku, auren Zubaidah sji kaɗai na tambayeku sabida a halin yanzu ku kuke iko da ita tunda kuke iko da wicked sister inlaw ɗinta......

"Murmushin bossawa sukayi baki ɗaya kafin Alhj Kasim ya dubi Barr ya masa ido, Kallo suka bi Jalal dashi wanda tuni ya fice....

"A first parlor ya hangu su Salim suna zazzaune, Harara yabisu dashi ɗaya bayan ɗaya, Labib ne ya miƙe da sauri ya nufesa, saidai kafin ya iskesa ya tura sliding door ɗin ya fice.....


"Alhj Jamil da Alhj Maina Dad ɗin Tariq suka ƙaraso parlorn after the meeting don jin me ake ciki, Alhj Kasim yace kar su damu he can take care if everything.... "Kallonsa dai kawai sukayi amma sunsan Alhj Kasim zai iya yin komai to get rid of his problems.
"Alhj Jamil ya ajiye masa wasu documents saman table ɗinsa kafin yace
" Yaya our company its at risk of going bankrupt, we might loose some of our employees sabida fake golds da aka fitar zuwa NewZeeland,...
"A zabure ya miƙe yana kallon ƙanin nasa, tunu ya cire hular kansa ya shiga fifita duk da sanyin AC ɗin dake parlorn "
"Jamil yaya akayi suka gane Zinaren bogi ne, Jamil we can't go bankrupt you need to do something.... Gaba ɗaya kaman zaucecce yake maganar, Waya ya ɗaga ya kira sakatariyarsa yace ta masa scheduling meeting da *Marafa Group Of Companies* Barr da Alhj Jamil sai kallonsa suke yanda ya zauce lokaci guda.
"Kallon Alhj Jamil ya kumayi kafin yace " Ka kira duk wani bankin da ka sani ka karɓo aron kuɗi kafin business venture ɗinmu da Marafa group of companies ya bunƙasa, we cant loose our company brother, do as I said pls,...
"Alhj Jamil ya dubesa da mamaki kafin yace" Yaya bashin banki fah kake magana, kasan....." Bai ƙarasa rufe baki ba Alhj Kasim yace " Haba Jamil so kake mu rasa company ɗinmu, ko billion nawa ne kasa hannu ka karɓa idan yaso daga baya sai mu wanye dasu, amma yaya kake gani yau udan baba ya taso yaga company ɗin da yasha wuya akansa ƴaƴan sa his very own children sun kasa maintaining, pls brother just do as I said for the sake of our company, for the sake of *Dasuki Holdings* Fuzar da iska Alhj Jamiƙ yayi kafin ya riƙo hannun ɗan uwan nasa yace " Yaya zanyi yanda kace, daga haka ya miƙe ya nufi Office ɗinsa.....

"Yana ficewa Alhj Kasim da Barr Munir suka kwashe da dariya harda tafe hannu,.
"Barr yace " Mr president baka da kyau, Alhj Kasim ya murmusa yana karkaɗa pen kafin yace" Let him borrow the Money, with that I'll ruin him completely dariya suka kuma yi hadi da tafe hannu...


¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤

*A Dukku fah*

"Inna wai har yau babu wanda zaice min ha yanda Zubaidah take, ya kuma tambaya a karo na biyu.
"Ajiye rariyan tankaɗen dake hannunta tayi fuska a tamke kafin tace" Baba Wuro (Haka take kiran Umar) Har sau nawa zan faɗa maka nima bani da taƙamammen masniyar yanda suka tafi, iyakacin jitajitan danaji cikin gari shi na faɗa maka, Zubaidah bada kanta tayi ma ɗaya daga cikin yaran masu kuɗin nan da suka zo, bayan sun gama lalatan su, suka tattara suka bisu garinsu wasu ma cewa suke da maƙudan kuɗi suka sayesu.....
"Girgiza kai ya shiga yi idanunsa jazur yake faɗin" Inna ni nasan ƙarya ake mata sharri ne, Zubadah na bazata taɓa bada kanta ma wani ba, bazata taɓa bin masu kuɗi ta barni ba, nasan tana sona......" Baffah ne ya fito daga kewaye ya tarar suna zancen....
"Ajiye butar hanunsa yayi gamida zubar da ruwan dake bakinsa kafin ya juyo yana ma Umar mugun kallo kana yace " Wato har yanzu bazaka daina maganar wann yarinyar ba ko, toh idan baka sani ba ka sani, maganar da mahaifiyarka ta faɗa maka gaskiya ne, idan da ba gaskiya bane ai da sun mana sallama kafin su tafi musamman ita Zubaidar tunda akwai baikon ta akan ka...


"Idanuwansa suka ciko ƙwalla, da sauri ya miƙe ya shige ɗaki gamida kulle kansa, da gaske ne Zubaidah ta barsa sabida wani, take ya yuna sanda tayi aikin wuni guda gidan Alhj Dasuki, ya tuna irin kallon da wani saurayi ne kyau yake mata, ya tuna yanda itama ta masa murmushi, tabbas ko wata mace zata iya barin masoyinta akan wann saurayin sabkda ya haɗa komai na rayuwa, ka kuɗi ga kyau,....."Share hawayen da suka zubo masa yayi yana jin zuciyarsa na masa ƙuna, bazai iya barin Zubaidah ba, bazai iya rayuwa babu ita ba, dole ya fice ya neme ta dole ya dawo da ita gareshi don kuwa tabbas Zubaidah *Mallakin sa* ne......


"Iyalle ta dubi ƙanwarta shafa wacce ke mutuwar son Umar amma besan tanayi ba, tayi murmushi kafin tace" Shafah ki kwantar da hankalinki Ummaru kaman kin samu an gama, ni nan da kike gani ni na kitsa wa Hadiza yanda zata yi, bacin haka ina taga kwanyar yin wnn tunani, ni dai abinda nake so dake kisan yanda zaki saye zuciyarsa tunda naga har kusan mutuwa nikayi sanda yakai baikon Zubaidah.
"Shafa tayi wani murmushin jin dɗi, don yanzu jinta take tamkar sarauniyar mata tunda Zubaidah ta tafi kafin tace" Ai wllhi bakiji wani daɗin da nake ji ba, yanzu kika tabbatar min ke ɗin yayata ce, Umar kuma dole yaso ni tunda wancan me kama da aljanai ɗin tayi gaba.. Dariya suka kuma yi a tare harda kashe hannu....



*Gombe, Fada*

" Abba barka da war haka , cewar Zahida yayinda take ƙarasawa kusan mahaifin nata,
"Murmushi yayi mai fitar da ƙwarjininsa kafin yace "Barka Gimbiya ƙarasi mana, ya matsa mata gefe da tumtim ɗin da yaɗan kishingiɗa akai ta ƙaraso gamida zama daf dashi. Hannayenta ya riƙo gamida sunbatar su kafin yace" Allah ya miki albarka ɗiyata. Murmushi tayi tana mai kallon mahaifin nata wanda a kullum cikin tausayin sa take sabida damuwan da bar yau ya kasa mance ta sama da shekaru ashirin da huɗu.
"Ɗan gyaran murya Zahida tagi kafin ta kalli tapkeken hoton jaririn da duk wani parlor a gidan akwai hoton kafin tace " Abba meyasa baza a cire hotunan ba tunda naga ɗaga maku hankula yake musamman kai da Madaki, snn ya mutu Abba inaga ajiye hotonsa a parlor haka babu wani alfanu
"Girgiza mata kai yayi idanunsa naga hoton kafin yace "Zahida Yayanki bai mutu ba, ni inaji a cikin jikina bai mutu ba, nasan watarana Allah zai haɗani dashi, ina ganinsa kullum cikin mafarkina, snn Suhaima tana faɗa min cikin mafarki na ɗanmu yanada rai, snn ta bar min amanarsa duk randa na hafu dashi......."Baki Zahida ta saki tana kallon mahaifinta wanda ba don jinin sarauta dake yawo a jikinsa ba da sai tace tabbas kwanyarsa ta kusan samin matsala, a hankali ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login