Showing 78001 words to 81000 words out of 210924 words
with a towel sabida zafin jikin ya sauk'a.....
"Kaman jira Hadiza take nan tayi karaf tace " Ni Dije zanga yanda za'a canza wann kaya mutanen da ko kwana d'akj guda basu tab'a yi ba shine za'a ce ya sake mata ka...... "Aya ta saka ma zancen nata ganin wani irin muguwar kallon da Jalal ya watsa mata.... "Babu wanda yace k'ala sai Dr Khaleesat data kuma duban Jalal tace " you should change your clothes too before you fall sick, kai nasan kaima baka da lafiya, zan maka prescribing magani kaima, don I'm pretty sure ciwon soyayya kuke.... Gaba d'aya suka murmusa harda Hamma wanda ke durk'ushe yana rik'e da hannun k'anwarsa.
"Toh ni zan wuce and pls a guje duk wani abinda zai b'ata mata rai for now.... Dr Khaleesat bata Kai aya ba Hamma ya dubi Hadiza yace " Kinji koh Hadiza likita tace kar a b'ata mata rai dan Allah kar ki mata masifa kinji.....
"Kallon fuskokin mutanen wajen Hadiza tayi kafin ta kafesa da wani mugun harara tace " Da shike nice uwar 'yan bala"i koh, dan na nuna damuwata akanta ashe nayi laifi.... Banji ba ban gani ba balle kuce nace.... Ta buga wani uban tsaki gamida ficewa fuuuu....
"Gaba d'aya suka bita da kallo, Hamma ya mik'e yana dariya wanda shi a tunaninsa murmushi yake ya dubi Dr yace " Kar ki damu haka take, haka take... Zan je na mata magana, ya k'arashe maganar yana nuni da k'ofa, ...
"D'an murmushi kawai Dr tayi gamida gyad'a kanta... Annah kuwa kaman ta nitse sabida takaicin Hadiza, sallama suka kuma yi da Jalal kafin Annah tayi ma Dr rakiya....
"Tsura mata dogayen idanunsa wanda basu faye girma ba yayi yana tunanin ta yanda zai soma canza mata kaya, .
"Mik'ewa yayi jiki babu laka ya nufi drawer d'in da yake tunani nata ne kafin ya bud'e, kayanta ya gani a shirye tsaf a ciki.... D'an fuzar da iska yayi kafin ya ciro wasu kayan. Ya dawo yanda take...
"Ya jima yana durk'ushe gaban gadon yana dubanta, fuzar da iska ya kumayi kafin yasa hannu ya yaye bargon,... K'irjinsa ya shiga bugawa da sauri da sauri sanda yake k'ok'arin rabata da rigar jikinta.... Abubuwan da suka faru a wancan daren suka shiga dawo masa, fuskokinsu yake hangowa sanda suke keta mata rigarta.... "Da k'arfin gaske ya runtse duka idanunsa biyu... Kasa cire mata rigar yayi sai mik'ewa tsaye da yayi cikin sauri ya nufo parlor, a k"ofa suka had'u da Annah sai rawan sanyi yake.... Kan ta sami zarafin magana yayi saurin mik'a mata kayan Zubaidah dake hannunsa yace "Barin duba su Shattima..... Ya k'areshe maganar cikin rawar murya irin ta maras lafiya....
"Kallonsa Annah tayi kafin tace " Ah sun tafi ai, sunce zakuyi waya.... "Baka da lafiya ne, she added..
"D'an jim yayi kafin yace" I'll be fine Annah just take care of her, I'll be in my room idan kina nema na..
"D'an gyad'a kai kawai tayi ta bisa da kallo cike da tausayawa har ya fice..
"Layin Shattima ya soma kira yajita a kashe, nan ya kira na Usman, .
"Usman ya sanar dashi Shattima ke da journey gobe da sassafe, zaije sa Kaduna and daga chan maybe ya wuce Gombe...
"Jalal ya kuma tak'urewa cikin bargo kafin yace " I feel bad you know, I couldn't have chance to thank you... Zan sake kiransa gobe da safe insha Allah... Na gode na gode sosai Usman " You guys are incredible Allah Ya bar zumunci...
"Haba Jalal ka daina fad'im haka pls, that's what brothers are for.. I'll see you tomorrow Allah k'ara rufa asiri...
"Ameen Jalal ya amsa dashi sukayi sallama kafin yayi hanging up...
"Washe gari tunda ya tashi tun safe bai fita ko k'ofa ba dukda jikin nasa ya masa dama dama breakfast ma har d'aki Annah ta kai masa, lokaci zuwa lokaci yake tambayar ko Zubaidah ta tashi..
"
"Wajajen k'arfe sha biyu da rabi goshin azahar ya fito ya nufi d'akin Annah...
**************
*Dasuki Holding*
"Zaune yake yana juyi saman kujeran nasa waya mak'ale a kunnensa ba sai ance maka da sahibarsa yake wayan ba, banda uwar harara babu abunda Labib ke watsa masa....
"Salim yaci gaba da fad'in" are you serious sweetheart, wait how comes bansan kina shirin had'a mana spectacular dinner ba.
"Murmushi yayi sanda ta basa answer kafin yace " Okay kice k'aramar biki zaki kuma had'a mana, okay zan fad'a wasu Daddy right away tunda duka suna nan har Pappy... Ohh my Baby can't wait to see you, kar dai kiyi aiki sosai ki gaji kinji Baby na... Ya kuma yin want murmushi mai sauti yana juyi bisa kujeran kafin yace " Okay my darling kisses to you.....
"Har ya k'arashe wayar Labib bai daina danna masa harara ba...
"Mik'ewa Salim yayi yana gyara suit d'insa ba tareda ya dubi Labib ba yake fad'in" Kausar is inviting us all for dinner tonight zanje na fad'awa su Daddy right away su Mummy ma will be there,... Bai damu da rashin ansa sa da Labib beyiba idan da sabo ya saba da halin d'an uwan nasa...
"Har ya kai k'ofa ya juyo yace " Pls ka kira Tariq ka fad'a masa though his family is invited too, amma dai pls ka fad'a masa idan yaso sai ya zama kaman farewell party d'insa...
"Bai amsa sa ba sai faman kad'a biro da yake, yana ficewa yaja tsuka gamida furta " Useless..
Sameena ce ππΎ
[1/23, 22:22] βͺ+234 803 619 0581β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
50
*Β©Sameena Aleeyou...βπΎ*
_Queen Samy Novels Forum...ππ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*I've received your messages masoyan k'warai wllhi lisaffo sunayenku ma aiki ne sabida yawanku.. Nonetheless ina sonku irin totally d'inan Alkhairin Allah Ya kaimaku duk yanda kuke...ππβ€*
"Ya jima yana tsaye bakin k'ofa hannunsa a Hard'e kan k'irjinsa, kallon siraran hawayen da suke bin k'uncinta yake...
"Jikinta ne ya bata da kwai mutum a wajen snn wann k'amshin nasa bai barin hancinta da sauri ta d'ago kai tana dubansa,... Fuskan nan nasa a mirtuk'e babu alamun Fari'a, yana sanye cikin inner red Mai V-neck had'i da lallausar wando Wanda da kad'an ya wuce gwiwarsa....
"Cikin sauri ta kauda kai gefe don bata juran kallonsa...
"Taku kad'an yayi ya k'araso cikin parlorn.... Cak ya tsaya a gabanta cikin dakakkiyar murya ya soma fad'in"
"Why... Me yasaki yin haka, .... "K'ara sautin muryar yayi cikin tsananin fad'a yake fad'in" Tell me why, what... What if I couldn't find you, what if I couldn't protect you.... Do you even realize the kind of trouble you almost got your self into huhhh..?? Do you think you the only suffering..?
"D'agota yayi sanda kukanta ya k'aru ya rik'e arms d'inta da k'arfin gaske suna fuskanta juna yaci gaba da fad'in" Look into my eyes and tell me what the heck did I do to you this time around...
"Bud'e jik'akk'un idanunta da suke sharkaf da hawaye tayi ta sauk'esu kan farin fuskarsa da ya turning red, siriryar jijiyar goshinsa ta fito sosai, siraran dogayen idanunsa sun firfito waje, sirirn hancinsa wanda bai faye tsawo ba k'ofofin sun bubbud'e, his cute pink lips keeps blowing kaman ya shafa lipstick....
"Ta tuna yanayin data gansu da Tariq zuciyarta ya shiga mata zogi da rad'ad'i..
"Da k'arfin gaske cikin tsananin kuka take fad'in" Eh gwara na tafi ko ina ne, 'cause you all the same, you... Are... Just... Like... Them... You all raped me... Snn I saw you with him hugging each other probably planning something again ...
"Are you going to deny it, huhh.. Ka fad'a mun Me kuke shiryawa akaina, ka fad'a mun kuna shirya yanda zaku...... ENOUGH.!!!!!! YA daka mata wata tsawan da saida hawaye ya fita daga idanunsa.... Annah dake kitchen saida ta yarda ludayi....
"Ita kanta Zubaidah shaking ta soma tana kallonsa bata tab'a ganinsa cikin irin wann yanayi ba....
"Ido cikin ido yake dubanta in a furious tune yaci gaba da fad'in" I love you.... I love you ultimately more than you might think. And you know I'm not asking you to love me back.. All I want is protect you and to keep you safe koda hakan zai zama ajalina.... I don't care anymore if you don't believe me..... Daga haka ya juya ya fice daga parlorn cikin sauri.......
"A bakin k'ofa suka had'u da Annah, bata sami zarafin masa magana ba ganin yanyain nasa, ta jima bataga irin wnn yanayi a tattare da d'an nata ba, ... "Cikin sauri ya nufi d'akinsa. Kallo Annah ta bisa dashi har ya shige. Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya tayi ta shiga parlon tana addu'an Allah Ya kawo k'arshen wann Al'amari.....
"Har lokacin kuka Zubaidah take, lallashi ya zame ma Annah jiki...
"Yana shiga d'akinsa wandosa ya canza zuwa ta jeans kafin ya fice.
"Suna jin ficewarsa ko sallama bai masu ba.
"Zubaidah ta kuma shigewa jikin Annah hawaye na fita idanunta, tausayin kanta ya kuma kamata, for the first time dataji babu Dad'i abinda tayiwa Jalal, Kalman *I love you and I'm not asking you to love me back* ta ringa nanatawa cikin zuciyarta, wani hawayen na kwarara mata musamman idan ta tuno abunda Umar da Zulaihat suka mata....
*******************
*Police Department Headquarter Wuse2 Abuja*
"D'aga idanunsa yayi ya kuma karantawa, zuciyarsa tana Dad'a basa k'arfin gwiwa akan abinda yayi niyya, kai tsaye ya kutsa kai ciki, tuni ya nemi ganin IG, ba'a basa daman ganin sa ba, ya jima yana jiran neman ganinsa bai samu ba har saida IG ya fito daga meeting, haka kurum yaji yana son ganin Jalal, nan aka masa izini.....
"Kai tsaye bayan sun gama gaisawa IG ya tambayesa "How may I help you young man.
"Without any hesitation Jalal yace " Sir I came to confess...
"Kalllonsa yayi da kyau kafin ya kuma tambayarsa, kai tsaye Jalal ya kuma nanata masa... In details Ya fad'i komai bai b'oye ba mai d'aukan rahoto bisa computer Ya rubuce komai.
"Inspector yasha mamakin abun sosai, don kuwa babban mutum a k'asa irin Kasim Dasuki bai zaci zai yi haka ba, koda yake mutane for their children babu abunda bazasuyi ba...
"Kallon Jalal yayi da kyau kafin yace " Mr Jalal I've heard your confession and zamu rik'e Ka a nan, but before muyi arresting sauran sai ita victim d'in tayi magana you understand what I mean say tayi filing complaint..
"Intercom ya danna kafin wani Sargent ya shigo ya fita da Jalal...
"Annah tasan halin d'an nata idan yayi fushi tasan kalan zuciyan Jalal, sai iya shafe sati ba tareda sun gansa ba, lambarsa ta shiga nema,
"Sargent d'in da ya d'auka ne ya sanar da ita Jalal na police station. Ai tuni Annah ta mik'e tsaye tana tambayarsa me ya kai d'anta police station, Kai tsaye Sargent d'in ya mik'a ma Jalal wayan...
"Cikeda tashin hankali ta soma magana, Jalal, me kayi aka kama ka, me ya faru......
"A hankali yace " Annah ki kwantar da hankalinki ni na kai kaina, I confessed everything,
"Annah ta nanata a fili daidai sanda ta juya taga Zubaidah ta mata k'uri alamun tana saurarenta... Da sauri ta k'araso tana fad"im Annah Dan Allah barin masa magana, tana maganan cikin rawan murya zuciyarta cike da takaicin kanta don kuwa ita tayi provoking d'insa.....
"Pls come back home, dan Allah ka dawo I promise bazan sake ba, kaji but pls don't leave me all alone by my self..... Abunda yaji knn cikin kunnuwarsa wanda ya kasa gasgatawa.
"Damk'e wayar yayi sosai kafin ya soma fad'in" I'm doing this for us to live in peace, all I want from you is to talk, don't remain silent, File a complaint against your enemies, don't let them get away with it, kiyi magana kiyi magana, talk kinji babu rufarufa from this very moment, let the whole world know the truth, let us get what we deserve, kinji... Pls talk.
"Kaman na ganinta haka take nodding kanta tana hawaye take fad'in" I'll talk Right away, I'll speak up, kaji, you'll be safe and you'll be free..... Kuka ya kuma kufce mata, Annah ce ta karb'i wayan ta tambayesa station d'in da yake......
****************
"A hankali ta turo k'ofar d'akin har lokacin zuba kaya yake cikin luggage d'insa, dafasa mum tayi kafin tace " Tariq da gaske tafiya zakayi ka barmu, Tariq you are our only son bazan iya jure rashinka ba.....
"D'an jefar da rigar hannunsa yayi ya d'ago yana dubanta kafin yace " Oh com'on Mum do we have to talk about it again, bazan iya ci gaba da rayuwa a nan bar, I need a change of environment Mum, I need to forget everything that happened here, I need to start a fresh....
"D'an goge hawayen idanunta tayi kafin tace " Zan ringa visiting d'in ko yaushe, ..
"Murmushi yayi gamida hugging d'inta da hannu d'aya cikin arms d'insa kafin yace " Bazaki iya visiting d'ina ko yaushe ba, munyi nisa, Moscow da nan akwai nisa sosai Mum, all I can say you'll always remain here.... Ya k'arashe yana nuni da k'irjinsa ma'ana heart d"insa... Murmushi ta sakar masa itama ta rungume sa sosai... Sa hannu yayi ya share mata hawayen idanunta...
"Tayasa arranging kayan taci gaba dayi, sunayi suna hiran sanyin da zai tarar a Moscow, nan ta tambayesa ko zaije dinner d'in da Kausar ta had'a anjima..
"D'an jimm yayi kafin yace " I'm not so sure coz flight d'ina da safe ne so banson nazo ban tashi da wuri ba...
"Shafa kansa tayi tana fad'in" No excuse you are going, at least kayi sallama da kowa.... Zaiyi magana ta d'aura hannu bisa lips d"insa tace" Final you are going na gama magana....
"Murmushi yayi kana yace " Alright Mum just because you insist, that's my boy ta fad'i sanda take zipping jakar....
"Around 7:00pm ya nufo stirs d'in Mum don jin kota shirya su tafi tare, wayan da yake jiyowa daga d'akinta yasa gabansa ya yanke ya fad'i.
"Mum taci gaba da fad'in" Haba Barr Munir na fad'a maka zanzo zanzo , idan Tariq ya tafi ma mun huta had'uwa a hotel coz gobe zai tafi, tayi wani dariya kafin taci gaba da fad'in" Haba kar ka damu alak'armu bazata Tab'a yankewa ba don bazan tab'a bari Alh Maina ya sani ba.....
"Bibbiyu Tariq ya soma gani, ya kasa gasgata abubuwan da ya gama ji, cikin sauri ya juya ya sauk'a k'asa, kai tsaye motar sa ya nufa ya fice a guje, fuskar Barr Munir kawai yake hangowa, shi kad'ai yake huci yake fad'in" I'll kill that Bastard with my very own hands.........
*At the company*
" Salim Ya kuma duban Labib kafin yace " Hey stop being so stubborn, dalla ka tashi mu tafi, kaifa mugun D'angelo iska ne, you wai uwar Me zaka tsaya yi ko anan zaka kwana ne.
"Da wutsiyar Ido Labib ya kallesa kafin yace " Do I always have to explain my self, nace maka bazanje ba fine, ka tafi mana abunka...
"Rufe laptop d'in gaban Labib Salim yayi yana wata murmushi yake fad'in" Hey your crush is gonna be there too, Asmah I'm pretty sure tana chanma probably helping Kausar, com'on don't be stubborn tashi muje.....
"Hararansa kawai Labib yayi kafin ya mik'e yana zungurin k'eyarsa yace " You such a jerk you know....
'Dariya Salim yayi yana fad'in whatever.... Dariya kawai Labib d'inma yayi kafin suka nufi lift suka sauk'o k'asa.
"Dukansu motar Salim suka shige, Labin yayabawa wani security car keys d'insa yace ya kaimasa gida....
"Suna fitowa k"ofar company d'in motocin police , cike da tashin hankali suke bin polisawan da kallo, guda d'aya ne ya fito ya nufi motarsu... Tuni suka bud'e motar..
"Cike da gadara Labib yake fad'in" Lafiyanku wa kuke nema snn bakusan nan company bane,