Showing 18001 words to 21000 words out of 210924 words

Chapter 7 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22859

har muzo mu gine gida kalan nasu....... Hadiza tayi shewa ta miƙa wa Iyalle hannu suka tafe kafin tacr" Ƙawata shiyasa nake sonki yanzu bari kiga da zafi zafi ake dukan ƙarfe. Yawwa ƙawata cewsr Iyalle maza lalumo nawa kasoɓ ki bani ke ai tanzu kin zama hajiya.
"Hadiza ta zaro kuɗi ta danƙawa Iyalle kafin ta fice.



"Yanda Iyalle ta tsara mata kuwa hakan akayi, Hamma Habibu yasha kuka shaɓe shaɓe harda majina, tabbas yasan iyayensa bazasu taɓa yafe masa ba ya kasa riƙe masu amanar tilon ƙanwarsa, Hadiza harda hawayen munafunci take basa baki, kayi haƙuri Habibu ina nan tare da kai snn duk wanda yayi wann abu wa Zubaidah bazmu taɓa barinsa ba ko ɗan uban waye, sai an bi mana kadinmu, maza shirya muje asibitin, babu musu ya shirya suka nufi asibiti.


""Labib ne ya soma ƙarasowa yanda Jalal ke zaune kafin su Salim.suka karaso, murya kalan na masu nadama suka soma magana dashi, ko kallo basu ishesa ba ƙarshe ma tashi yayi ya bar masu wajen, ya ɗau aƙwashin ko yau ya koma Abuja bazai ci gaba da zama da Dasuki family ba, ya koyi darussa a rayuwa snn zai tashi ya nemi abun kansa duk wuya duk rintsi.

**************************

*Gombe Fada*


Wata matashiyar mata ce zaune saman Kujeru na alfarma, a shekare bazata gaza shekaru 40 ba, tana sanye cikin kaya na alfarma, fuskan nan nata ko kaɗan babu annuri, ido ta kafe hoton jariri dake manne a tangamemen parlron dashi, wani katutun baƙin cini ya kuma tokare mata maƙoshi, Idan akwai abinda tafi tsana a rayuwarta toh wann tangamemwn hoton ne wanda yake kaman ruhin mijinta Mai marta sarkin Gombe MODIBBO ALIYU MU'ALLAYIƊI.




Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:11] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

13

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...📖📚_


"Gimbiya Zahida ce ta shigo parlorn cikin shiga shiga ta alfarma Alkebba fara ƙal sai ɗauke ido yake, daka ganta basai ance maka ga jinin sarauta ba, gefe da mahaifiyarta ta zauna fuskarta ɗauke da murmurshi kana tace" Barka da Hantsi Ummi na, da fatan kin tashi lafiya.
"Murmushi matar data kira da Ummi tayi kafin ta shafi gefen fuskar Zahida tace " Barka ɗiyar saraki jikar saraki da fatan kin wayi gari lafiya.
"Murmushi bai bayyana haƙwara Zahida tayi kafin ta riƙo hannun Ummi tace " Ummi kina sani naji kamar watarana zanyi sarauta idan kina koɗa ni haka.
"Ummi ta jawo Zahida cikin jikinta ta rungume kafin tace" Mai Martaba baida wani ɗa ko jika a doron ƙasa face ke, baida gudan jininsa a duniyan nan face ke ƴar lele na, meyasa kike tunani wataran bazaki mulki garin nan ba.
"Rausayar daidanu Zahida tayi kafin tace" Ummi a ina kika taɓa jin mace tayi sarauta a ƙasar nan, burina dai kawai shine na auri saraki nima don gaskiya idan ba jinin sarauta ba bazan yi aure ba.
" Ummi tayi wani dariya mai cike da ma'anoni idanunta suka sauƙa kan tangamemen hoton jaririn dake manne a tampatsetsen parlor kafin tace" Maza tashi muje mu gaida kakarki kafin ta fara mita.
"Babu musu Zahida ta miƙe Ummi na riƙe da hannunta bayi guda biyu ne ciki harda Jakadiya suka take masu baya snn suka nufi sashen "Madaki wato mahaifiyar mai Martaba.......



"Tunda ta buɗe ido tayi ido huɗu da lkitan ta ringa mimmiƙewa tana wani irin ƙara haɗi da ƙanƙame jikinta dukda azaban ciwon da takeji, babu yanda likita baiyi ba ya dubata amma abu yaci tura, kai duk wani mutum idan ya shigo muddin na mijini ne to ta rinƙa figita kenan tana wanu irin kuka mai wani irin sauti tana ƙanƙanme jikinta.....
"Daga can nesa ya tsaya yana kallonta sanda aka kira nurses sukai mata alluran bacci, wani irin tausayinta ne ya cika zuciyarsa, take yaji bazai iya kallon wann hali na ƙunci da wahala da take ciki ba, kaman wanda kwai ya fashe ma a ciki haka ya fito reception.

"Zama yayi a reception yana kallon Hamma Habibu dake ta faman share hawayen da ya wanke fuskarda gaba ɗaya, Jalal ya kuma jin tausayin waɗan nan bayin Allah sanda yaga Hamma Habibu ya kama wuyar rigarsa yana sharan majina dashi a hankali ya ƙarasa ga Hamma Habibu gamida da dafe kafaɗansa Habibu ya ɗago rinannun idanunsa da suka jiƙe da hawayr yana kallon Jalal kana ya soma faɗin"
"Bata da kowa sai ni, iyayenmu sun rasu sun bar min amanarta, gashi na kasa cika masu burinsu, na kasa riƙe amanar tilon ƙanwata, idan ta mutu bazan taɓa yafr ws kaina ba.... Kuka mai ƙarfi ya kufce masa sanda yake dukan kansa da duka hannayensa biyu yana faɗin" Bani da amfani, gaskiyar Hadiza ne banida amfani, banida amfanin komai.... Kalmar da ya ringa nanataw knn yana dukan kansa da ƙarfin gaske.
"Jalal da tuni hawaye sun ciko idanunsa, tausayin Zubaidah da Hamman ta ya cika zuciyar sa, Allaj sarki ashe marainiya ce babu uwa babu uba babu dangi sai Hamman ta wanda yake irin mitanen nanne masu maysalar ƙwaƙwalwa. Abu mai kaman wuya ne ke sa Jalal kuks, zai iya cewa tun yana yaro kai koda yakr yarinta duk tsananin abu bai yin kuka amma wann karan sai ji yayi ya kasa controlling kansa, tuni idanunsa sunyi jazur haka nan farin fatar sa ta koma ja, tsanar aminan sa ne ya cika zuciyar sa haɗi da tausayin Zubaidah da rayuwar da zata fuskanta...

"Annah ce ta bawa Jalal kuɗi ya sayo allura don babu wanda ake buƙata za'a mata a asibitin, cikin sauri ya amsa ya nufi waje, Annah ta karaso ga Hammah Habibu tana basa baki cike da tausayawa.


"A daidai ƙofa ya haɗu dasu, sun ɓadda kama basu ɗauko luxurious cars ɗinsu ba, Daddy ne sai Barr Munir... "Cikin sauri Jalal yayi niyyan wucewa Barr Munir yayi alama wa Gurd ɗinsu guda ɗaya da hannu, kan kace me an janye Jalal zuwa cikin wata mota mai baƙar glass.
"Fuzgewa Jalal ya shiga yu da iya ƙarfinsa daidai lokacin da Barr Munir da Daddy suka shigo, banda harara babu abinda Jalal ke masu, a hasale yake faɗin" Me kuke yi a nan marassa imani.
"Daddy yayi wata murmushi kafin yace" Relax boy, dont di anything foolish, magana ɗaya zuwa biyu zamuyi da kai, if you cooperate fine ka tsira, idan kuma ka ƙi..... Wata murmushi yayi jafin ya kalli Barrister.
"Barrister yayi gyaran murya kafin yace" Jalal, shin kana da shaida cewa su Salim su suka raping yarinyar nan, shin idan kana tunanin idan kayi gigin sbigar da ƙara kai zaka tsira ne, bazaka tsira ba , tunda dukanku kuna wajen sanda incidence ɗin ya faru, tabbas yarinyar ta ganku gaba ɗaya, babu mai cire ka cikin wnn mess ɗin, she'll admit dukanku ne kukayi raping nata, snn boy ina gani daga idanunka you are madly in love with her....."Da mamki kurum Jalal ke kallonsa.
"Barr yayi wata murmushi kafin yaxi gaba da zayanno kalamai masu ɓadda tunanin mutum irin nasu na lawyoyi " Ka sake tunani da kyau yaro, idan kayi confessing laifinku zaka tafi prison for the rest of your life don bakada mai tsaya maka, kar ka mance ƙasar nan idan kana da kuɗi babu mai ja da kai, su salim will be free kai ɗaya za'a bar cikin wann mess ɗin don kaine talaka, and poor mum ɗinka da bata da kowa saiki, ƙunci zai kasheta, snn wann yarinya bazaka taɓa kasancewa da ita ba, wataƙila itama depression ya kasheta, kaga ashe tainakon da kayi niyyan yi baiyi rana ba.
"Jalal ya zuciye tamkar zai jai mai naushi yake faɗin" Stop involving me a cikin mess ɗinsu, ban aikata ba n no one will force me to confrss something I never did, not even you Alhj Kasim.
"Murmushi sukayi su duka biyi, kafin Barr yace" I like your courage boy, amma dai ka duba maganar da nayi maka, and abu na karshe idan kana so kayi saving life ɗin yarinya ka aureta....
"Mun riga mun gama magana da likita gibe za'ayi discharging nata kai tsaye kuma Abuja zamu wuce gaba ɗaya including her and her family. So dabara ya rage naka Jalal, ka sani kai za'a bari a rana don mun sami amincewar uwar goyonta da likitan ta, kaga baka da shaida... Daga haka suka buɗe masa marfin mota ya fice jikin sa a sanyaƴe.
"Wai shin haka duniya ta koma, wai shin shi talaka bashida ikon gudanar da rayuwarsa yanda yake so, shin mutane haka suka zama, abin duniya ya gama rufe idanun kowa, kaico irin wann rayuewa da muke cikinta a yau.....


Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:11] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

14

*©Sameena Aleeyou....✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...📖📚_


" Jiki a sanyaye ya tare mai mashin yana tambayarsa ina zai sami chemist mafi kusa don ba sanin garin yayi ba, basu wani tafiya mai nisa ba suka samu, nan ya sai alluran ya koma asibiti.
"To his greatest surprise wulgawan motar compnayn *Dasuki Hodlings* ya gani, kuma tabbas ɗazu cikin ta su Daddy suka zo. Toh me ya dawo dasu tambayar da yayi ma kansa kenn, sann babu mai basa amsar wann tambayar nasa yasa ya nufi asibitin kai tsaye.

"Shaye da mamaki Jalal ke kallon su Mommy da Mami, Annah ce ta hango shi tsaye ya kafe su da idanu,
"Jalal ƙaraso mana , Allah dai yasa an sami alluran, Annah ta faɗi daidau lokacin da gaba ɗaya suka maida kallonsu ƙofa, Mami Momy da kuma Yaya Hadiza.
"Momy ce ta miƙe gamida karɓan alluran hannun Jalal wanda ya koma tamkar gunki bai gama shan mamakin ɗan adam ba saida yaji momy na faɗin" Jalal abokan ka sun wuce sun barka har ina masu faɗan ina suka bari ka, ashe kai kam taimako ka tsaya... Da mugun mamaki kurum yaje binta da kallo sanda taci gaba da faɗin "
" Allah sarki Jalal yaron arziki, Allah dai ya biyaka kaida mahaifiyarka, irin wann raimako da kukayi ai mu ya kamata mu ringa yin irinsa, ta maida duvanta ga Annah daketa faman murmushi kafin tace" Habs Annah ai irin haka da wuri ake faɗi sai mubada kalan namu gudumawar, ƴanmatan da kaddara da tsautsayi na fyaɗe a auka masu haƙiƙa suna buƙatar taimako da kulawa don haka ne ma Alhj ya yanke shawarin taimaka masu itada familynta, gobe insha Allah zamu tafi Abuja baki ɗaya don hakan ne kurum zai mantar da ita wann mummunar ƙaddara da sameta, zamanta a nan zai ringa tuna mata abin, snn cannin wajen zama zai mantar da ita komai.
"Mami dai kallon Mommy kawai tayi tana mamakin yanda halin momy da Daddyn Salim yazo daidai, banda lugude da ƙirjinta keyi bata komai sau kallo, dan kuwa saida mijinta ya mata kashedi babu ruwanta a wann zalunci, toh ya zata yu tuɓda ɗanta na ciki, data rasa tilon ɗanta gwara ta biye masu kida hakan ka iya kawo matsala ga aurenta.

"Annah da yaya Hadiza godiya suka shiga, yaya Hadiza harda share hawayen munafunci tuni ta kaɗo kan Hamma Habibu yazo yayi godiya, bai kawo komai a ransa ba ya ringa masu godiya...


"Takaici da tausayi ya hanasa ci gaba da tsayƴwa a wajen, tuni ya fice zuwa farfajiayan asibitin.... Ƙasar wata bishiya a samu ya zauna gamida haɗe kansa da gwiwarsa, maganganun Alhj Kasim da Barr suka shiga dawo masa,
"Kalaman da yafi nanatawa shine *"You are in love with her, Ka aureta shine maka mafita...*
"Girgiza kai ya soma tamkar zararre, ko ɗaya ko kaɗan baijin abinda yake ji game da ita So ne ,shi bai taɓa yin soyayya ba balle yasan yaya take, abunda ya sani shine yana jinta tamkar ƙanwarsa snn yana tsananin tausayinta, snn ya ɗau alwashin tamaika mata har iya rayuwarsa.... A gigice ya miƙe ya nufi cikin asibitin sanda yajiyo wani irin karan da ta saki.....


" Mami dai jigum tayi a mota har suka isa gida, tana shiga parlon su ta tarar da Daddyn Labib zaune yana karanta jarida da alama isowarta yake jira.
"Kamar wacce ƙwai ya fashe ma a ciki ta nufesa tanai masa sannu da gida, ko kallo bata ishe sa ba baƙƙe ya tanka ta. Sanin bazai mata magana ba yasata nufi sama.
"Daidai step na biyu taji ya kira sunanta, cak ta tsaya ba tare da ta jiyo ba.
"Saboda kin raina ni shine saida kika biƴewa Yaya da matar sa kuka je ha'intar waɗan nan bayin Allahn ko, kina cikin hankalinki kuwa Salma, na saka maki doka ki take......."Kamar me shirin kuka ta soma faɗin" Haba haba Jamil, me kake tunani, na bari inaji ina gani tilon ɗan nawa ya tafi gidan yari, bazan iya rasa sa ba idan kai baka damu dashi ba...."Mikewa yayi gamida ajjiye jaridar dake hannunsa kafin yace " Shi ya janyo ma kansa, shi ya saka kansa a ciki don haka babu hanuna a kare shi, kuma a yau na isa Abuja zan miƙa sa ma hukuma....."Ihun da Mami ta saki ne ya kaɗo hankulan sauran mutanen dake gida, kuka take kan rusawa tana fadin " Ita babu mai kai mata ɗata kurkuku....

"Alhj Kasim da Hajiya Farha a tare suja shigo, Mami ta karasa gabansu tana kuka take roƙon Daddy, Yaya dan Allh ka masa magana cewa yayi zai miƙa Labib ga hukuma, Yaya ka taimaka min ka hana sa....."Momy ta riƙo Mami tana lallashinta suka nufi upstirs....

"Wani mugun kallo Alhj Kasim ke waysa wa ƙanin nasa kafin yace" Jamilu wato baka daina maganar nan ba koh, bari kaji na faɗa maka dukda cewa kai ka haifi Labib baka isa ka min iko akansa ba, bari kaji na sake faɗa maka in case u forgotten "Wllhi wllhi babu mahaluƙin da ya isa ya shigar da ɗana prison muddin Naira na aiki a kasar nan, Jamil ga fili ga doki idan kayi shirin yin faɗa dani yayan ka. Kayi abunda kaga dama tunda yanzu har ni nake faɗa kake faɗa.... "Daga haka yasa kai ya fice fuuuu...
"Kallo Alhj Jamil yabi ɗan uwan nasa dashi, jikinsa yayi sanyi tabbas bazai so yaga rugujewar family ɗinsu ba hankali ya sulale gamida zama bisa sofa haɗi da zare faran tabarau na ƙarin ƙarfin gani dake idanunsa.....




*Washe gari*

"Tunda aka sallame ta bara ɗago ido ta kalli kowa ba, snn bata san duniyar take ko akasin haka ba, iyakacin abinda take tunawa shine dariyar su da shewan su sanda zasu rabata da mutuncin ta, haka nan idan ta buɗe idanun ta fuskokinsu take gani, motsi kaɗan idan tayi takan ji zafi zogo haɗi raɗaɗi daga ƙasanta, hakiƙa a galin yanzu tafu shiga sahun marassa ganjali, don kuwa tabbas bata san yanda hankalin nata yake ba, iyaka abinda ta sani shine duk na mijin da yazo kusa da ita takan fita hayyacinta takan koma tamkar mai ciwin hauka....




*Abuja*

"Batasan a ina take ba, itadai buɗe ido tayi ta ganta a wani gida na daban, mafarki take waɗann samaruka sun nufota da wuƙa tana ihu tana gudu, gabanta kuma Umar ne ya buɗe hannu alamun ta ƙaraso garesa, fuskarsa kaman ba nasa ba ashe shima wuƙar ne a hannu sa.. Da tsoro ta isa gareshi yana ƙoƙarin burma mata wuƙar knn ɗaya daga cikin samarukan nan ya ture Umar ya rungumeta.........
"A gigice ta saki wani irin ƙara gamida taƙurewa waje guda, .. Hadiza ce ta shigo gamida jan dogon tsaki jin Zubaidah na kiran sunan Umar,......Yaya na kazo ka ceceni kashe ni zasuyi,
"Ruwa cikin kopi Hadiza ta ɗebo gamida sheƙa mata..... Babu shiri ta buɗe ido firgit, ta yunƙura zata tashi taɓi zafi, hannunta dake ɗaure da bendeji yanda ta gurɗe taji ya shiga mata zogi alamun ta fama, a gigice ta fito daga ɗakin tana kallon yanagin yanda take, wani ƙara ta saki gamida durƙusawa waje...




"Labib dake tsaye ta windown ɗakinsa yake hangota, wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Salim.....



Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:12] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

15

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...📖📚_


"Hello guy kana ina ne? Daga ɗaya ɓangaren Salim ya amsa
"Gidan su Kausar, what akwai wani abu ne.
"Okay mu haɗu a company things are getting outta control...
"Dont get u buddy, wau meke faruwa ne.
"Gajeren tsaki Labib yayu kafin yace" Salim its about that girl....
"You mean the Cow girl.
"Dama wacce yarinya nake maka magana aside from her, ka gane Uncle cant tackle this issue alone, we need to talk kafin abubuwa su caɓe wann matan yayan nata zata zame mana sabon matsala, nu banma san meyasa Uncle ya kwaso su ya taho dasu ba,..... "
"Miƙewa Salim yayi kana yace "Okay fine ka kira Taruq kace masa mu haɗu a company.. Daga haka yayi hanging.
"Fuzar da iska yayi gamida furta "Dmn dammit..!!!!
'Daidai nan Kausar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login