Showing 132001 words to 135000 words out of 210924 words

Chapter 45 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22874

but I swear.... Na rantse da wanda ya halicce ni bazan saki Zubaidah ba, she's mine, tawa ce.... And the moment I step out of this damn chair..... Your hell will start right here on earth .... "

"Da k'arfin gaske Umar Ya matse bakinsa yana huci yake fad'in" Shut the fuck up you idiot.. You took away what is rightfully mine .... "If you fricking think you leaving this place alive kayi kuskure.... Coz this place is your hell..... Ya mik'e yana yarfe hannunsa kafin yace " Apparently the heroin is tomorrow right... Yayi wata murmushi kafin yace " I'll be there snn zan kawo maka ita nan na kashe ka in front of her..... And finally zamu kasance tare in our new world..... Ya k'arashe cikin tuntsurewa da dariya...

"Huci kawai Jalal keyi yana jijjiga kujeran yake fad'in" You're despicable, I swear to you I'll kill whoever messes with my Wife.....

"Kira Umar Ya shiga doka ma Danny.... Da sauri Danny ya hauro sama yana amsa kiran uban gidan san...


"Bindiga Umar Ya mik'a masa kafin yace " Make sure he didn't escape, if he tries to do anything stupid shoot him without thinking twice..... Daga haka ficewa yayi ko sauraren Danny bai tsaya yi ba....


"Sunajin yanda ya kwashi motar sa da bala'in gudu... Ni kuwa Samee nace _fast and furious, maza Allah hadaka da Paul Walker 😂_

***************

"Tunda ya fice su Danny suka sami sarari sukayita d'irkan giyan su kota kan Jalal basu bi ba...
"Shi kuwa Jalal d'an fashashen kwalban da ya samu yake kan faman yanka d'aurin da aka masa yake ta baya ba tareda sanin su ba... Gaba d'aya ya yayyanke hannunsa, dukda zogi da azaba da yake ji bai fasa ba, he really need to get out of this place before that idiot does something drastic to his wife.....

**************


"Kausar ta tsare Asmah da idanu har saida Asmah ta soma zargin anya wann kallo na lafiya..?
"Dafe kafad'un Kausar tayi kafin tace " Sistu jikin ne? Ko akwai abinda kike so ne...?
"Shiru Kausar ta mata ba tareda ta furta komai ba..
"Sauk'e ajiyan zuciya Asmah tayi kafin ta kwashi books d'inta ta nufi k'ofa tana fad'in "I'll be downstairs if you need anything... "Ji tayi Kausar ta rik'e hannunta guda. A hankali Asmah ta jiyo tana duban ta kafin tace " Sistu idan kina son wani ne pls tell me, ko wani abin ci kike kwadayi I'll prepare it for you right away....

"Murmushi Kausar tayi kafin tace "Really.... Okay fine na gode, amma ni yanzu tambayar ki zanyi.. Why are you hiding things from me now....

"Galala Asmah ta d'an kalleta kafin tace " Hiding things, com'on Kausar me zan b'oye maki.... I'm only worried about you ne.

"Of course you hiding something, keda Mumsy, you don't want me to find out.... "D'an girgiza kai Asmah tayi kafin tace " For crying out loud stop being so paranoid Kausar.... Kinga bakida k'oshin lafia ki kwanta, I'll prepare something delicious for you..

"I perfectly well know you Asmah, idan kina b'oye min wani abu na sani, idan akwai wanda yasanki better than I do toh Ansar ne... Amma tunda kince ba haka bane bara na fad'a maki abinda kuke b'oye min.. Baku so nasan I'm crying Salim's child ko ba haka bane....

"Gaban Asmah ya fad'i, ta d'ago tana duban Kausar... "Murmushi Kausar ta sakar mata kafin tace " Nasan I'm pregnant tun sanda na soma ciwon nan, and this is exactly 2mnths without me having my days... "So tell me what were you afraid of, huh..? Tsoro kuke kar na zubar da cikin ko me..??

"Asmah ta d'anyi shiru kafin tace " Kausar nasan halinki snn nasan right now you are so devastated ko baki nuna mana ba, we all knw how much you hate Salim and his family muddin kika san kinada ciki you might freak-out and komai ka iya faruwa... Amma na sha mamakin ganin kin sani bakiyi komai akai ba....

"Murmushi Kausar tayi kafin tace " No one can escape his destiny sistu.... Mu kuma kalan namu jarabawan knn, Salim ruins my life but that doesn't mean zan kashe abinda ke ciki na ko na k'yamci abinda ke ciki na bisa laifin mahaifin sa,, Zan so d'ana with all my heart, tasa bayan hannu tana share hawayen ta had'i da murmushi k'arfin hali kafin tace " Children are great treasure, they are blessing ... Muryar ta Ya soma rawa sanda taci gaba da fad'in" I'll give my child a different story, he must not know about his Dad, bazai san mahaifinsa na gidan yari ba da wann bak'in laifi da ya aikata.... Hawaye ya kufce mata sanda taci gaba da fad'in" Tell me Asmah am I making the right decision ... Ki fad'a mun 'yar uwa... "Rungumeta Asmah tayi kuka ya kufce mata ba tareda ta iya furta komai ba...
"Mumsy dake tsaye bakin k'ofa k'arasowa tayi ta had'asu duka biyu ta rungume tana fad'in" Alhamdulillah, Allah na gode maka daka blessing d'ina da 'ya'ayan albarka.... Allah Ya maku albarka sweethearts, always remember that I'm here for you kunji Angels...

"Suka d'ago suna kallon Mumsy had'i da share mata hawayen ta.. "Mumsy ta rik'e hannun Asmah tace " Koda bani na haifeki ba ina jinki tamkar 'yar dana haifa a ciki na, you've always been there for my family, I owed you alot my niece.... " Da sauri Asmah tasa hannu ta toshe bakin Mumsy tana girgiza kai take fad'in" Mumsy don't say those things pls kinji, haihuwata ne kurum bakiyi ba but you've done more than enough for me... Murmushi sukayi gaba d'aya kafin Mumsy ta kuma bud'e masu hannu tace oya family hug.... Gaba d'aya suka rungume juna fuskokin su d'auke da annuri...

************

"Alh Kasim ya bigi kujeran dake gaban sa da k'arfin gaske kafin ya dubi Barr yace get me Faisal.... Cikin sauri Barr ya matsa gefe ya shiga dialing lambar Faisal....

"Check d'in bogi ya kuma rubutawa ya mik'a ma Hadiza, ta washe baki tana murna... Daga nan ta mik'e ta fice cikin sauri gudu gudu, sai waige waige take kar a ganta...


"Alh Kasim ya kuma watsa wa Alh Maina wata uwar harara kafin yace " You better stop your Son, don wllhi kaji na rantse idan yayi confessing I'll ruin you just like I did to Tahir Marafa, shida yake da arziki balle kai...

"Alh Maina ya shiga girgiza kai yana tattare naman goshin sa yake fad'in" No no I can't lose my only son.... I need to stop him right away..

"Alh Kasim ya tab'e baki kafin yace " Da yafi maka, don wllhi d'ana Salim Ya tafi jell for years akan shi I'll make your life a living hell, .... Daga haka mik'ewa yayi ya fice suka had'u da Faisal a wani waiting....

"Kallon Faisal ido cikin ido yayi kafin yace " Gobe ne or never, idan ba'a gama shari'ar nan a gobe ba na baka go ahead ka kashe Attorney Kumo... Ka kashe sa har lahira...
"Ficewa yayi sabida wayan da aka masa yanada clients da zasu soma maganar sayan hannun jari don kuwa kampanin sa is going bankrupt.....

***********

"Cikin sa'a Allah Ya basa dama ya yanke igiyan dake d'aure da hannayen sa da k'yar... Cige baki yayi sabida zogi da hannayen sa ke masa, a hankali ya soma warware na k'afafun sa, har ya kwance su tsaf..... Sad'af sad'af ya mik'e yana d'ingisawa da k'yar....



Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:28] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

74

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*


"A hankali yake takawa lokaci guda yana d'an cije leb'e sabida zogi da rad'ad'i da wounds d'insa ke masa..
"Can ya hangi su Danny sai sharan bacci suke ga kwalaben barasa har kusan guda uku a gaban su.. "Jalal yaci gaba da sauk'owa daga benen cikin dabara . Danny ne ya d'anyi juyi yana sunbatu yana gyara zaman bindigar a saman k'irjinsa.
"Jalal yayi saurin durk'usawa ya b'oye jikin rub'ebb'iyar katon staircase d'in.. "Jin Danny yayi shiru yaci gaba da baccin sa yasa sa mik'ewa yaci gaba da sauk'owa cikin dabara..

"Ga sanyi da ya gauraye gari ga duhun dare ga rigar sa gaba d'aya jini ya b'ata, uwa uba bai san ina ne wajen ba.... "Cikin dabara ya k'arasa ya d'auki jacket d'in dake lank'aye jikin wata katako ya soma k'ok'arin barin wajen ganin d'aya gardin na mutsu mutsu alamun zai tashi...


"Da dabara da taimakon Allah Jalal ya samu ya fice daga wann kango na gini... Tafiya yake yana jan k'afarsa da k'yar ba tareda sanin ina ya dosa ba, don kuwa ga dukkan alamu wann gini a k'ungurumin daji yake, ko alamun kwalta bai hanga ba balle yayi tunanin ganin ginannakin mutane.
"Saida yayi tafiya mai nisa kafin ya zauna k'asar wata bishiya ya shiga treating wounds d'insa. Yage gefen hannun rigar sa yayi ya shiga d'aure yanda jini ke zuba. Ya d'ago jacket d'in da yana dubawa ko Allah zaisa ya sami waya a cikin ta...
"Fuzar da iska yayi gamida dafe kansa ganin babu waya a ciki saiko wata garin hoda.. Sosai yaji takaicin hakan, saidai ganin damuwa bazata ficce sa ba yasa sa mik'ewa ya gabatar da taimama kafin ya soma sallah....

*************

"Firgit ta farka daga mummunar mafarkin da tayi tana mai ambaton Allah.
"Ta jawo igiyan wutan side lamp ta kunna kafin ta jawo wayar ta dake gefe da lamp d'in ta danna don duba lokaci.
"K'arfe 2 da wasu mintoci agogon wayar nata ya nuna..... "Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya tayi kafin ta karanto addu'a ta shafa... Ta jima tana zaune saman gadon tayi jigum zuciyar ta naci gaba da yankewa.... "Da sauri ta soma girgiza kai tana fad'in" It's only a dream, My Ya Jay na lafiya, babu abinda zai samesa da izinin Allah.. Domin kawar ma kanta tunanin mik'ewa tayi ta nufi bathroom ta d'auro alwala ta tada sallah... Haka ta ringa nafilfili tana kai kukan ta wajen Rabbil Izza...
"Ba ita ta koma bacci ba sai wajajen uku da rabi na talatainin dare... Da asubahi kuwa har kusan makara tayi don saida Annah ta lek'o ta tasheta don gaba d'aya ba wani samun nitsettsen bacci tayi ba...
"Gaba d'aya jikinta ya gama sanewa tun kan su tafi kotun. Bata da burin da ya wuce tayi tozali da Jalal...

**************

*National High Court Abuja*

"Tun daga waje zai tabbatar maka babban shari'a za'a gudanar.
"Motar prison ta paka nan aka soma fito dasu hannayen su rufe cikin handcuffs.. Su Mummy Mamy da kuma Mum d'in Tariq gaba d'aya suka nufi 'ya'yan nasu suna masu fashewa da kuka ganin yanda suka canza lokaci guda tamkar ba su ba, 'Ya'yan hutu masu ji da gata.... So suke sukai hannu su tab'asu amma inaa Cops sun hana, sai faman kakkare su suke suna fad'in" No touching..

"Journalist kuwa tamkar anyi ruwan su haka sukayi chaaa suna wurgo ma duk wanda suka gane nada alak'a da Shari'ar..

"Gaba d'aya su Mummy dasu Alh Kasim suka d'unguma suka bi bayan su Salim wanda keta faman juyowa yana fad'in" Daddy pls... Uncle Mummy pls ku fitar dani a wajen nan.... I can't go back to jell....

"Mata matasa kuwa harma da manyan mata sune suka cika bakin kotun kowa da k'atoton takarda a hannunta an rubuta *JUSTICE FOR ZUBAIDAH* da manyan harrufa, sun d'add'aga sama suna fad'i tamkar masu biya karatu....

"Zubaidah dake zaune a reception k'irjinta yaci gaba da fad'uwa... Gefe da ita Annah ne, sai Hamman ta Habibu daga b'angaren dama, daga can wani kujeran kuwa Ansar ne da Hafiz sai faman tattaunawa suke k'asa k'asa. Hadiza bata zo ba tana can gida tareda Kamal...

"Fuskokin su ta hango ana shigowa dasu, tun daga nesa suma suka hangesu, banda mugun kallo babu abinda suke watsa masu, musamman Labib wanda yake a tsakiya.... Kafe su da idanu Zubaidah ma tayi, ihun su da shewan su ya shiga yawo a kunnuwan ta da kwanyar ta, dariyar su take ji sosai cikin kunnuwan ta, fuskokinsu take hangowa sanda Tariq da Salim suka Bank'are ta Labib ya keta mata riga daga sama har k'asa...... "Wani irin k'ara ta Saki lokaci guda gamida toshe kunnuwan ta had'i da runtse idanu da k'arfi..
"Annah tayi saurin rik'eta sosai tana mai karanto mata addu 'o'i.... "Ansar da Hafiz suka k'araso cikin sauri suna fad'i wa Annah kodai Zubaidah ta zauna da Hamman ta a can waiting d'in ne, tunda ganin su Labib na jefata cikin tashin hankali....

"Annah da Hamma duk sukayi na'am da hakan.. "D'ago kai Zubaidah tayi tana girgizawa kafin tace " No no Annah Ina so najisu suna confessing inaso ihun su da shewan su ya b'ace min ta hanyar jiyo muryoyin su suna confessing, I wanna see them been sentenced to jell... All of them. I want it to come to an end.... Ta k'arashe tana goge hawayen idanun ta....
"D'ago ido da zatayi sukayi ido hud'u da Labib idanun sa cikin burin d'aukan fansa... Da sauri ta dubi Annah tace "Annah mu koma ta can pls kinji.... Babu musu Annah ta rik'o hannun ta suka nufi tacan gefen...

"Labib ya bud'e murya yace " You miserable liar.... Tell them you're lying ... I swear you won't get away with this.... I'll make you pay.. All of you will pay...... "A zuciye Ansar ya k'arasa yana fad'in" Shut your trap you criminal.... Barr Munir yayi saurin tasowa Ya sha gaban Ansar yana fad'in" Don't talk to my client you good for nothing.. "Hafiz ne ya rik'o Ansar yana janye sa..

***********

"Alk'ali yana isowa aka bud'e d'akin shari'a.....

"Kowa ya nemi waje ya zauna, sanda Alk'ali ya shigo gaba d'aya aka mik'e don girmamawa, saida ya zauna bisa kujeran sa kafin kowa ya koma ya zauna...
"Ba tareda b'ata lokaci ba aka soma gudanar da shari'a..

"Gaba d'aya hankalinta baya wajen, idanun ta naga k'ofa, gani take tamkar zai bud'e ya shigo... Why isn't he here yet, what took him so long... Why did he leave me all alone by my self .. He should be here by now. He promised to be with me in this very day. "Cikin zuciyarta taci gaba da fad'in" I need you, I'm so restless, I can do it without you , I'm so scared, zasu k'aryata ni kaman yanda suka saba... You're my strength pls don't let me down..... Pleaseee...... Ta k'arashe zancen zucin nata tana mai runtse idanu...


*************

"Fadan k'arshe mai motar ya sauk'e sa kafin yace " Bawan Allah na maka iyaka k'ok'arina tunda na d'aukoka tun daga Toro har fadan k'arshe babu sisin kwabo...

"Jalal ya jinjina kai kafin yace " Ka taimake ni bawan Allah. Nasan kamin kayi iyaka k'ok'arin ka amma don Allah ka cikita ladan ka ka shigar dani Abuja, insha Allah zan biyaka kud'ad'en ka..
"Mai vectra ya jinjina kai kafin yace "Shiknn muje tunda kace zaka biyani kud'ina... "Ci gaba yayi da tuk'i yana satan kallon Jalal cikin rashin yarda dashi, sabida yanayi da yake ciki, ga dukkan alamu idan ba d'an fashi bane, toh kuwa d'an dambe ne... Da wann tunani ya ringa palpala gudu don gujema binciken jami'an tsaro...

**************

"Gaba d'aya kotu tayi tsit tana saurarn amsar da Tariq zai bada..
"Alk'ali ya kuma gyaran murya yace " Malam Tariq shin ka yarda ka amince ka amsa laifin da Malama Zubaidah take tuhumar ka dashi... "Did you commit the Crime..

"D'agowa Tariq yayi sukayi ido hud'u da Alh Kasim .... "Wani kallo Alh Kasim ya jefa masa gamida sakin murmushi.... Tariq ya kuma duban mahaifin sa da cike da tausayawa... Suka kuma yin ido hud'u da Ansar..... Ya kuma juyawa ya kalli Zubaidah.......

" Girgiza Kai Tariq yayi idanunsa tabb k'walla kafin yace " I deny it your Honor I'm not guilty.....
"Runtse idanunta tayi hawaye masu zafi suka sauk'o mata.... Da sauri Annah ta rungume ta ba tareda ta iya furta komai ba jiki a mace...

"Alh Kasim dasu Salim kuwa hak'waran su kasa rufuwa yayi sabida farin ciki..

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login