Showing 165001 words to 168000 words out of 210924 words

Chapter 56 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22900

ka kuma kashe mun rayuwa..... Ko sauraren ta beyi ba... Ya Bud'e k'ofa ya fice...


"Kai tsaye apartment d'insa suka nufa, Jalal yace Inspector na tabbata bazamu same sa a nan ba, ka bari mu d'auki hanyar Akwanga...
"Inspector yayi murmushi kafin yace " Jalal this is my job ko baka yarda da profession d'ina bane....

"Jalal ya d'an ji babu dad'i kafin ya girgiza kai yace " A'a ko d'aya Inspector, ina dai fad'a maka ne abinda nake da tabbaci akai...
"Inspector ya gyad'a kai kafin yace mu fara zuwa nan...


"Zulaihat na zaune a d'aki taci kukan ta har ta gaji, taji ana bubbuga k'ofa, da sauri ta fito da niyyan yima Umar rashin mituncin da bai tab'a zato ba... "Ganin Jalal da polisawa yasa ta soma ja da baya...

"Jalal a zuciye yace " Ina mahaukacin mijin nan naki... Ina yakeee..!!
"Inspector ya rik'o Jalal yanai masa nuni da cuffs d'in hannun sa yace " Jalal idan bazaka nitsa hankalin ka ba, zan kuma d'aure hannayen mu...

"Jalal ya fuzar da iska kurum yana huci....

"Inspector ya dubi Zulaihat dake faman shaking yace ina yake.??

"Murya na rawa tace " Yayya baya nan , ya fita aiki...

"Inspector ya murmusa kafin yace " Ke kuwa ko kishi bakiji ne, idan kina kishin kanki ya kamata ki fad'a mana gaskiya, don mijin ki Ya kira mu Ya sanar damu Zubaidah na hannun shi, and that means he's also responsible for the death of DT Amir Kaita and Barr Asm'u Marafa.....

"Kaman sauk'an aradu haka Zulaihat taji zancen... Cikin wani irin murya take fad'in" Yanzu kuna so kuce min rashin imanin Umar har ya kai ya kashe mutane har biyu, .... Innah da fitowar ta knn ta soma ganin k'asa na juya mata, bata iya k'arasa fitowa ba, ta sulale a k'asa.

"Zulaihat ta fashe da kuka kafin tace " Officer wllhi bansan yanda yake ba, ban sani ba tun daren jiya ya fice... Ta k'arashe tana durk'ushewa a wajen tana wani irin kuka.....

"Jalal ya kalli Inspector yace " Kaji koh, pls ka k'yaleni na tafi ni nasan yanda wann Jerk d'in zai kaita, who knows me zai mata Inspector, he's insane he's capable of anything .... Ya k'arashe yana mai soma tafiya cikin sauri...

"Inspector ya rik'o hannun sa kafin yace " Bazaka d'auki doka a hannun ka ba, snn zuwa nan da ka ga muyi zamu k'ara report d'in a cikin case d'in ne... Wanted ake neman sa yanzu, ...... Inspector baikai aya ba, Sargent ya k'araso ya sara ma inspector cike da rusunawa ya dank'a ma Jalal wayar sa da ake kira....

"Jalal ya kalli screen d'in ya d'ago ya kalli Inspector kafin yace " Speaking of the Devil.... Saurin d'agawa yayi ya soma fad'in" You Animal ina ka kaimin mata, ina matata....

"Inspector ya masa alama kan yyasaa handsfree, Jalal yayi yanda Inspector yace "
"Umar yaci gaba da fad'in" You coward idan kana son matar ka be a man for once and stop being coward... Let's see how much you love her.... I'll send you location, kazo kai kad'ai and don't bring cops with you.... Let's see idan da gaske kana sonta and you can protect her.... D'iff ya kashe wayar....


"Jalal ya wani fincika yana dafe kansa yake fad'in" That imbecile I'll destroy him... Daidai lokacin da k'aran text ya shigo.... A tare suka karanta, Inspector ya kalli Sargent yace ya kira mota guda na police....
"Jalal ya shiga girgiza kai yana fad'in" No no inspector, rayuwar matata na cikin had'ari... Who knows what that Bastard could have done to her.... Zanje ni kad'ai kaman yanda ya buk'ata na dawo da ita.... Ya k'arashe yana mai soma tafiya...


"Inspector yayi saurin rik'esa kafin yace " Already hukuma na neman sa, Trap ya had'a maka sabida kaje kai kad'ai, amma a bisa a haka, ga motata ka tafi da ita mu kuma zamu biyo ka da wata motar daban..
"Jalal ya gyad'a kai ya amshi motar inspector ya kwashe ta a tamanin ya bar wajen...
"Inspector ya masa fatan tsarin Allah, snn ya gargad'esa sosai, he should be careful, kar ya d'auki doka a hannun sa....
"Daga nan Inspector ya danna intercom d'insa ya sanar suna buk'atar hilox ASAP.....


"Zulaihat tana shiga gida taci karo da Innah zube a k'asa tamkar bata numfashi, rud'ewa tayi tama rasa wanne zatayi gaba d'aya sai kuka,.. No d'in Ambulance ta shiga dialing hannayen ta suna rawa.

************

"Tsayuwa tayi k'ofar Bankin don ba wai ta iya bud'ewa bane.... Sai kalle Kalle take tana raba idanu, mutane kuwa sai kai komon su suke.
"Fuskar nan nata sai k'yallin Vaseline take.... "Hadiza fah abu ya dameta taga mutane sai shige da fice suke, babu wanda yabi takan ta... "K'arshe dai security d'aya ne da tun shigowar ta yake lura da ita ya k'araso yanda take yace " Lafiya hajiya..???

"Jin yayi mata hausa ba kaman masu tsaron gate d'in nan da suka ta shek'o mata turanci ba yasata washe baki ta soma gaidasa harda rusunawar ta... Ba tareda b'ata lokaci ba ta ciro checks d'inta har kusan guda uku tana nuna masa kan cewa kud'ad'en ta tazo amsa...

"Security ya k'are ma checks d'in kallo cike da mamakin yawan kud'ad'en dake jiki kafin ya soma tafiya yace ta biyo sa...
"Hadiza ta kuma washe baki ta rusuna tanai masa godiya suka nufi cikin Banki....



"Yana huci yayi saitin ta da bakin bindiga yana fad'in " Take off I said, take off those clothes, kar ki bari na cire maki da kaina don wllhi you'll regret....

"Kuka take tana girgiza masa kai take fad'in " Dan Allah kar ka min haka, kar ka zama d'aya daga cikin su, kar ka bari bak'in tarihin ya maimaita kansa...... " Kaji tausayi na don Allah.....

"Zaki min shiru ko sai na fasa kanki, munafuka kawai, wasu 'yan iska ma wa'enda basu sha wuya akan ki ba sun same ki a bulus balle ni.... Ki cire kayan ki nace, snn ki fad'a min yaya kike so abun ya kasance" Fast and furious ko kuma Slow and Gentle..... Talk ya k'arashe yana dad'a pointing nata da bakin bindiga.....

"Girgiza masa kai kawai take, ta duk'unk'une wuyar rigar ta gaba d'aya sai faman rawa da jikinta keyi....


"Yana hararan ta Ya shiga b'abb'alle boturan rigar sa yana fad'in " Wllhi yau sai Jalal ya ganki kwance cikin jikina idan yaso ya mutu.....

"Girgiza kai kawai take tana fad'in" No... No pls.. Don't do this, I beg of you, have mercy......

" Kallon wajen yayi tabbas this is the location, a tamanin ko k'arasa parking motar beyi ba ya fice ya nufi tsohuwar ginin mai tarin d'akuna yana tunanin ta ina zai dosa.... Kaman daga sama ya jiyo ihun ta sanda Umar ke k'ok'arin fincikar rigar ta......

"Wani irin wawan tsalle Jalal yayi ya nufi yanda ya jiyo sautin ta.... Da wata irin gudu.....

"K'afar sa yasa ya daki k'ofar saida ta b'alle.... Innalillahi Umar Ya hanga na kokawa da Zubaidah yana neman rabata da suturan ta.... Wani irin kukan kura yayi fatar sa ta koma jazir haka idanun saw... Take wani irin zufa ya karyo made.... " Dunk'ule hannayen sa yayi har kanajin k'aran Lank'washewar k'ashi da wata irin tsalle ya isa ya kwantar dashi da naushi yana masa wata iirin duka ko ta ina ba tareda ya iya furta komai ba......

"Kuka Zubaidah taci gaba da yi tana k'ank'ame jikinta tana kallon yanda Jalal ke dukan Umar, bata tab'a ganin sa cikin irin wann yanayi ba... Yana yi hawaye na fita idanun sa....
"Jefar da Umar da zaiyi ya jefa sa saman bindiga....

"D'aukar bindigan yayi da sauri yana dafe gefen cikin sa ga jini na bin bakinsa da hancin sa ya shiga pointing bindigar a kan Zubaidah yana kallon Jalal yake fad'in " I'll kill her........

*******

"Tun daga costumers care, kowa ya kalli check d'in sai ya mik'a ma d'an uwansa.... Maganganu suke kanyi ta harshen turanci suna kallon Hadiza...
"Sai faman cika take tana wani batsewa Acn Banki na ratsa ta, tana jin ta tayi kud'i, idan ta kalle su saidai ta tab'e baki tace " Ku gama turancin munafuncin ku kud'ina ne dai dole ku fito mun dasu... Gashi har alk'awari tayi ma security d'in da ya rakota cewa zata sammasa wani abu da zaran ta fito... _Nasan su o'o ma sun sa rai a kud'in Hadiza... ๐Ÿคฃ_...

"D'aya ya mik'e ya bada check d'in a counter... Suma kalla sukayi cike da mamaki kafin suka kira accountant d'in Dasuki Holding suka sanar dashi right away....


"Jim kad'an ya iso wajen ya karb'i checks d'in yana gani, wann ba signing d'in Alh Kasim bane, this is fake, irin masu satan check ne suje a kwaikwayi signature d'in mutum a maka a jiki... Da sauri ya dubesu yace " Call securities right away, don't let her escape.. Daga haka ya nufi ofishin Manager...


"Waya akayi Dasuki Holding, Alh Kasim yace atafau baisan zancen ba suyi arresting d'inta.... Accountant yace an gama...

"Alh Kasim ya kalli Barr suka fashe da dariya kafin yace " We got rid of her. Ba ita mayyan kud'i ba, ina zamu iya kyautan wad'an nan kud'ad'e in spite of halin da muke ciki na had'arin kariyan arziki, taje can su k'are da 'yan sanda pressing charges zanyi nasan bazata tab'a yarda 'yan uwanta su sani ba, asirin ta zai tonu.... Suka kuma fashewa da dariya....


"Put that gun down you idiot.... Jalal ya fad'i yana ware hannayen sa yana wani irin huci.... Daidai lokacin da motar 'yan sanda suka k'araso... "

"You coward police ka kira... Cewar Umar lokaci guda hankalin sa yayi kan k'aran takalman cops... Jalal yayi anfani da d'an damar yayi tsalle ya janye Zubaidah, Tasss..!!! Umar Ya kai harbi sai a kafad'ar Jalal... Zubaidah ta k'walla uban k'ara, gamgam Jalal ya rik'eta da hannu guda...

"Umar Ya dira ta window 'yan sanda suka bisa a guje, suna masu dakatar dashi ko suyi harbi, ina gudu yake yana juyowa suna musayen wuta da cops, nan suka same sa a gefen bayar sa ta k'asa, gudu yaci gaba da yi yana cijewa ya shige ciyayi....


"Sosai Jalal ya rungume Zubaidah dake kuka da duka zuciyar ta yana fad'in" its over baby insha Allah, I'm here, I'm here baby... Police zasu kama sa and he will pay for everything he's done.... "Kuka kawai take tana dad'a kwanciya cikin jikinsa, shi kuwa sai cijewa yake yana matse idanun sa sabida rad'ad'i da bullet d'in take masa a cikin jikin sa....

"Nan da nan aka kawo ambulance aka d'auke su, journalist kuwa kaman anyi ruwan su, bama kasan wa ya gayyace su ba...




"Hadiza ta were idanu sanda 'yar sanda guda d'aya ta shiga janta tana fad'in" Get up, tashi nace b'arauniya kawai...

"Hadiza ta had'e giran sama da k'asa tana fad'in" Me na maki, kud'i na nazo karb'a.. Ta fad'i tana karkad'e Ghana most go d'inta na jdan kud'i,.
"D'ayar ta kuma jawo ta tana fad'in tashi kafin na sauk'e maki kulkin nan saman k'afarki, munafuka inama kikayi kalan amsar wad'an nan kud'ad'e ta fad'i tana d'aura wa Hadiza handcuffs...

"Hadiza ta soma kuruwa tana fad'in" Wllh ita ba b'arauniya bace, inaa ko kulata basuyi ba, suka wuce da ita bayan motar 'yansanda......


"Jet d'insu tayi landing a babban filin jirgin saman Abuja, kai tsaye Mansion d'in sa suka wuce dake Aso Rock, idan kaga Mai Martaba bazaka shaida shi cewa sarki bane, don kuwa gaba d'aya ya b'adda kamanni, jampa yasa da hula, k'uruciyar sa da kamannin su da Jalal sai ya fito sosai....



"Hon. Gali ya buga table kafin yace " Don't take me for a fool Alh Kasim, kowa yasan halin da company d'inka ke ciki, irin zaluncin da kayi Allah bazai barka ba, nayi danasanin zuba dukiyata a wann k'azancecciyar company d'in naka... I won't allow you to ruin me, zan cire dukiya ta, I mean everything that I invested here, single scent bazan bari ba.... Yayi Wata murmushi kafin yace " If I were you zan fara tunanin ta yanda zan fito da kud'ad'en nan kafin wata mai kamawa... Ya kuma yin murmushi kafin yace " Hon Gali nake, ko a house ka tambaya kaji wanene Gali.... Daga haka ya gyara babbar rigar sa ya fice...

"Barr da Alh Kasim suka kalli Juna....


"Tsaki ya buga kafin ya danna wayar gaban sa ya kira sakatariyar sa yace " Jade get me all pending matters right away... Daga haka ya katse wayar yana huci...

"Barr ya kafe sa da ido kafin yace " What do we do now...

"Tsaki Alh Kasim ya kuma danna wayar yace " Jade check my skedule with the CEO Modibbo Cooperation.... Daga haka ya kuma katse wayar....



Sameena ce ๐Ÿ‘Œ๐Ÿพ
[1/23, 22:31] โ€ช+234 803 619 0581โ€ฌ: ๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜ *ZUBAIDAH*

87


*ยฉSameena Aleeyou...โœ๐Ÿพ*


_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION ๐Ÿค_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*



"Kasa samun layin Ambulance tayi gaba d'aya hankalin ta Ya kai mak'ura wajen tashi, ta rasa waye zata kira ya taimaka mata ga Innah dai kwance take lifeless a k'asa..
"Tsoron ta guda kar Innah ta mace mata a nan...
"Kuka take sosai tana nadaman auren Umar wanda bata tab'a yin irin sa ba... Tunanin Imam ya fad'o mata, kai anya zata iya kiran sa, toh waye zata kira idan bata kirasa ba, batada kowa a garin nan bayan shi...
"Hannun ta na rawa ta shiga neman layin Imam tana mai Allah wadai da hali irin nata...


"Suna zaune a Caf shida abokin sa wayar Zulaihat ya shigo wayar sa, mik'ewa tsaye yayi yana kallon wayar shaye da mamaki...
"Anas ya kalle sa yace " Lafiya ko sarkin nacin nan ne har ya shiga...

"Imam ya girgiza kai ba tareda yace komai ba ya d'aga wayar k'irjinsa na bugawa da sauri...
"Cikin wani irin murya mai cike da kuka ya niyo Zulaihat tana fad'in" Imam ka taimaka min pls kar ta mace min a nan, don Allah kazo bro... I need you pls.... Daga haka yaji ta katse wayar tana ci gaba da kuka...

"Cak yayi tsaye yana bin wayar da kallo ba tareda ya fahimce ta ba..

"Anas ya tsare sa da idanu yana karantar sa...

"Imam yayi saurin d'aukan car keys d'insa ya tattari folder d'insa da wayar sa yana shirin tafiya..

"Anas ya rik'osa yace " Guy wai meke faruwa ne, ina zaka je..

"Imam ya zaro kud'i a aljihun sa ya ajiye saman table kafin yace " Friend zamuyi waya, I really need to go, Zulaihat ta kirani tana kuka ban gane kanta ba, but koma meye nasan babu lafiya...

"Uban tsaki Anas ya buga kafin yace " Amma you are very stupid wllhi, dama kan wann yarinyar ne kake wann rawar jikin, wllhi na ma zaci Goggo ne zaka ce babu lafiya... Ya kuma yin tsaki kafin yace " Babu yanda zakaje wllhi, Kadai san Dr Habu d'aukan attendance yake ...

"Imam ya d'an dafe kansa kafin yace " Anas zamuyi maganar idan na dawo, Ka bani hanya pls...

"Anas ya saki baki yana kallon Imam yanda ya ture sa gefe ya wuce cikin sauri....
"Tab'e baki yayi yace " Kaje Allah sa ta tsinka ruhin ka gaba d'aya bama zuciya ba, maras zuciya kawai....

**************

"Har aka isa station Hadiza bata daina kuruwa tana rantse rantse cewa ita ba b'arauniya bace.
"Ko sauraren ta basuyi ba suka tura k'eyar ta cikin cell.

"Wata gabjejiyar mata dake zaune a gefe tace " Idan baki mana shiru ba zaki gane kuren ki...
"Hadiza dake cike fam da haushi batasan sanda ta soma surfa wa matar nan zagi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login