Showing 201001 words to 204000 words out of 210924 words

Chapter 68 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22869

da kazo kana rok'on mu gafara, idan mu munji tausayin ka mun yafe maka, ina Allahn sauran mutanen da ka zalunta, shin su sun yafe maka, shin matayen da ka maidasu zawrawan dole ka rabasu da mazajen su shin su sun yafe maka, 'ya'yayen da ka rabasu da iyayen su ka maidasu marayun dole shin su sun yafe maka, .... Snn Alh Kasim idan har da gaske kake kayi nadaman duk abubuwan da kayi a kotu zakayi wann bayanan a gaban Alk'ali, justice must be served.... Kaje gida sai mun had'u a kotu.. Allah Ya yafe mu gaba d'aya...

"Hawaye na bin idanun Alh Kasim ya juyo yana nuna Hadiza yana fad'in" Kece sila, kece kika soma cewa zaki iya rufe bakin Zubaidah idan an baki kud'i...... Ya k'arashe yana tari sosai...

"Hadiza cike da borin kunya take waige waige tana fad'in" Ni, ni, sharri zaka min, wato kaga k'arshen ka yazo shine bari ka bini da sharri bayan wanda ka mun... Wlhi k'aryar ka tasha k'arya....

"Kallon mamaki suka bita dashi had'i da girgiza kai kafin suka shige cikin gidan suka barta nan tsaye kan Alh Kasim sai banbami da masifa na borin kunya take masa... Taga abin bazai ficce ta ba ta ciro wayar ta cikin jaka, ta lasto lambar Hajiya Farha,..

"Su mummy suna nan gida hankali tashe don babu wanda yace yaga fitar Alh Kasim sai ganin wayar Hadiza tayi na shigo mata, har ta mance tanada layin Hadiza...


"Da masifa Hadiza ta soma mata tana fad'in toh wllhi tallhi ki rabani da wann shegen mijin naki, don munafunci bayan k'ulleliyar da ya k'ulla min shine zai kuma biyowa ya d'aura min laifi yaga bashida hanyar tsira, toh wllhi idan yayi gigin d'auran laifi wllhi har kuma bazaku tsira ba....
Tayi tsaki ta kashe wayar kafin ta nufi cikin gidan, facal facal, sai faman huci take ita ala dole an d'aura mata sharri...



"Hankali tashe su Hajiya Farha suka fito suka nemi tasi suka nufo k'ofar gidan Ansar suka kwashi Alh Kasim....

"Koda Hadiza ta shigo cikin gidan babu Wanda ya d'ago mata zancen...
"Kana ganin yanayin ta kasan dai babu gaskiya a tattare da ita...

"A haka kwanakin komawa kotu suka cika....

********

*January 21st,* rana ce da tayi daidai da ranar komawa kotu, jama'a ne ta ko ta ina sun cika haraban kotun... Jama'a ne cike a wajen musamman mata matasa kai harda wanda suka d'an data, ko wacce ta rik'e babban takarda a hannun ta mai d'auke da rubutun Justice for Zubaidah, rubutun anyi su ne da manyan haruffa, basu fasa nanata abinda ke rubuce jikin takardun su ba tamkar masu biya karatu.....

"Sanda aka zo wucewa dasu Salim sai k'ara sautin muryoyin su suke, .
"Hajiya Farha itace mai tura keken Alh Kasim yayinda Mamy ke tsaye gefen ta...

Sanda su Zubaidah suka iso kuwa gaba d'aya waje ya dad'a kacamewa, sai ka rantse Prinyanka Chopra ne ko kuma Salina Gomez ce ta shigo taro sabida yanda hankulan mutane yayi kansu gaba d'aya itada Jalal, sai kakkare ta yake sabida yanda mutane ke tururuwan zuwa kallon ta, tamkar wata celebrity haka ta koma, bai yi niyan Guard su zo kotun ba dole yayi waya ma Chief security d'insa yace ya turo masu guards, ...

"Journalist kuwa kaman anyi ruwan su....


"Bayan wasu mintoci aka hallara a d'akin gudanar da shari'a....


*Toh fah readers..... Here we are.. #FinalTrial let's see su waye zasuyi nasara... ๐Ÿ˜„**

*Sameena Aleeyou Mrs*
๐ŸŒ’๐ŸŒ’๐ŸŒ’๐ŸŒ’ *ZUBAIDAH*


97

*ยฉSameena Aleeyou... โœ๐Ÿพ*


_*Dedicated To All Victims Of Rape...*_



_๐ŸŒˆKainuwa Writers Association wannan Shafi naku NE, Allah k'ara hazak'a d'aukaka da baseera... Ana tare๐Ÿค ๐Ÿ˜_

*Anty Batul Jattko*
*Aysha Sada Machika (Commander)*
*Aisha Machika*
*Fauxy MB*
*Anty Fauzah*
*Ummy Ontop*
*Ayshat Hamzat*
*Maryam Ahmad Paki (Inlaw)*
*Mrs Mansoor*
*Anty Napy Saulawa*
*Nafisa Isa*
*Beebhalo*
*Fadeela Talba*
*Maimouna Maradi*
*Jiddah*
*Jiddah cool*
*Ummy Abdoul*
*Meenat Yakasai*
*Ummu Nabil*
*Halima MK*
*Sa'adat Alk'ali*
*Maryam Ishaq*
*Maryam Gozaki*
*Miss Ayush*
*Jamila Isma'il*
*Aysha S Bayero*
*Memcy Ata*



"Zahida rik'e da hannun Kamal ta bud'e bayan BMW d'in Shattima wa Kamal ya shige yana mai cike da murnan za'a je Wonderland, ya cikata da surutu yana tambayanta Anty Zahidah pls nidai zan shiga Water splash pls kar ki hanani...
"No Kamal you might catch cold, and it's risk for kids like you kaji Champ.... D'an turo baki yayi kafin yace " Okay fine but zan sha ice-cream, pls don't say I'll catch cold..
"Murmushi tayi ta shafi kansa kafin tace " Of course zaka sha ice cream harma da Pizza.... D'an turo baki yayi kafin yace " I don't like pizza I prefer Shawarma...
"D'aga masa babban yatsa tayi tana murmushi kafin tace " Hey same team, Team Shawarma,.. Tsalle ya d'an yi yana murna harda mik'a mata hannu suka tafa yana fad'in yaji dadi team din su d'aya...
"Shattima ne ya k'araso yana danna wayar sa yake fad'in" Team pizza...
"Zahida ta juyo tana duban sa tana murmushi yayi kyau cikin shigar sa ta k'anan kaya kafin tace " Mun maka wayo mu biyu kai d'aya... Ehen kuma mutum dole yaci irin namu...
"Shattima ya k'araso yana saka phone d'insa cikin aljihu kafin yace " Aima dole na tunda Gimbiya tana so...
"Murmushi kurum tayi cike da so da k'aunar sa..
"Shattima ya k'ura mata idanu yana kallon ta yanda tayi kyau sosai kafin yace " My lady, you look spectacular...

"Murmushi tayi kafin ta d'an rausayar da idanu tace " Godiya nake My Champion... Murmushin shima yayi kafin ya bud'e mata frontseat yace " Shall we??... Gyad'a masa kai tayi kafin ta shige nan suka d'auki hanyar Wonderland.... Fuskokin su cike da murmushi

*********
*National High Court*

"Kotun ta cika mak'il harda mutanen da bakayi zato ba, hannun Zubaidah rik'e cikin na Jalal, tunda aka shigo dasu Labib take jin kanta na juyawa, lokaci guda kanta ya sara ya soma mata ciwo, daurewa kawai take amma kam tabbas bata jin dad'i wanda ta alak'anta hakan da cink'oson mutanen da ta shiga ne ya janyo mata hakan ko kuma ganin su Labib....

"Jalal ya d'an dad'a rungumota daidai lokacin da aka shigo da Umar, idonsa k'yam akansu..

"Jalal yace " Baby idan bazaki iya zama a nan ba Annah ta kaiki wancan parlorn ku zauna...

"Murmushi ta sakar masa kafin tace " No Hubby zan iya.... Murmushi ya kuma mata kafin ya mik'a hannun ta ma Annah suka zauna waje guda daidai lokacin da Alk'ali ya shigo gaba d'aya kotu ta mik'e, aka buk'aci su Jalal Labib da kuma Salim da su k'araso cikin akurkin tuhuma....


"Kotu fah tayi tsit k'irajai sai bugu suke yayinda idaniya suka sauya launi....

"Confession d'in Labib aka soma gabatarwa a gaban Judge....
"Tunda aka soma karanto confession d'in idaniya suka shiga zubda hawaye.... Babu kaman Mamy da Mummy, Alh Kasim kam jigum kawai yayi saman wheelchair d'insa yayinda Barr Munir ya kifa kansa kurum yana saurare...

"Idanun Jalal sukayi ja suka kad'a yayinda hawaye yaci gaba da zuba daga idanun Zubaidah, Annah na rik'e da yatsun hannun ta gam, itama hawayen ne ke zubo mata....

"Sanda Salim yaji musabbabin abinda yasa Labib ya kawo masu shawarin su bi Zubaidah su mata fyad'e tsalle yayi ya kai mai naushi a hanci yana kuka da idanun sa yake fad'in" I knew it, I knew you always loved her, you loved Kausar...... I knew you did it to ruin me...... I hate you Labib....

SILENCEEEEE... Don't speak without permission..

"Alk'ali ya fad'i had'i da buga benchi.....

"Mumsy tayi saurin rungumo Kausar dake faman k'unshe bakin ta hawaye na zubo mata,....
"Ansar ya sauk'e idanun sa akan Kausar yana mai jin zafin hawayen da take..

"Kotu tayi stit kafin Labib yaci gaba da fad'in" I'm not denying my guilt your Honor but I promise you, I didn't force any of them to rape her.... All I know.... All I know is that I got Jalal drunk.... Nasan na bawa Jalal k'waya ya sha hankalin sa ya gushe to fulfill my mission..... Bai kai aya ba Jalal dake faman huci yayi wata tsalle yakai mai naushi a hanci yana fad'in" You miserable coward... I knew it, nasan aikin ka ne bansha wani abu alcoholic ba a wancan daren... You'll rot behind bars and pay for your dirty crimes....
"A can mazaunin su Zubaidah kuwa runtse idanun ta kawai take sabida wani irin yunk'urin aman da take ji..... Sanda Jalal ya soma kai duka ma Labib daidai lokacin data shiga k'waza amai.... Hankalin Annah ya tashi sosai..... Lokaci guda hankalin Jalal yayi kansu yana rik'e da kwalan rigar Labib.... A daidai lokacin kuma ran Alk'ali yayi mugun b'aci....

"Cike da b'acin rai yake buga benchi kafin yace " All of you should get out of here... Get out, we breaking for 15minutes.....

"Gaba d'aya dole kowa ya fice...

"Annah ta rik'o hannun Zubaidah lokaci guda Jalal ya k'araso ya rik'eta sosai yana fad'in" Baby are you sick ne... " Ya rik'eta sosai kanta na k'asa bata iya furta masa komai ba... Duban Annah yayi kafin yace " I'll take her to the restroom....
"Annah ta gyad'a masa kai kurum tanai ma Zubaidah sannu...


"Har restroom d'in ya rakata ya wanke mata baki da fuska kafin yace " Zubaidah you can't go back in there... Ki zauna tareda Annah a wancan parlorn...

"Girgiza masa kai tayi tana goge goshinta lokaci guda yana taimaka mata kafin tace " No Ya Jay... Zan iya naji sauk'i, I just want to see them been sentenced to Jail even if I'll vomit again.... I wanna see them confessing their crimes... Ina so ihun su da dariyan su ya b'ace min daga cikin kunnuwa na da confession d'insu da zasuyi... Ta k'arashe tana kwantar da kai cikin k'irjin sa.

"Sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin ya matse ta cikin jikinsa had'i da rungume ta gaba d'aya....


"Zulaihat ta hangi su Annah dasu Mumsy suna zazzaune waje guda kafin a koma ga shari'a ta d'an dubi Imam kafin tace " Bara naje mu gaisa.
"Murmushi ya sakar mata had'i da gyad'a kansa kafin yace " Kina so na maki rakiya..?

"D'an murmushi tayi kafin tace " A'a haba dai babu damuwa zan iya zuwa...
"Imam ya murmusa kafin yace " Kin san bakida lafiya kinyi insisting muzo ne shiyasa muka zo, but you supposed to be at home getting some rest.

"Murmushi ta kuma kafin tace " I promise you I'll be fine insha Allah... Snn Umar na tare da jami'an tsaro so he can't do anything insha Allah...

"Gyad'a mata kai yayi yana murmushi kafin ta wuce....

***********

*15minutes later*


"Shari'a taci gaba.....

"Labib yaci gaba da fad'in" Your Honor na bawa Jalal k'waya ne don hankalin sa ya gushe na cimma buri na, sabida nasan tabbas Jalal na cikin hankalin sa bazai bari mu aikata laifin ba.... Idonsa ya kawo ruwa sanda yaci gaba da fad'in" Jalal's innocent your Honor, bai aikata laifin ba bai aikata ba, on the contrary he was only trying to protect her from us, tun lokacin da muka d'aura idanun mu akanta, tunda naga abokai na suna da interest akanta nasan zan iya amfani da damar nayi ruining Salim da Uncle d'ina.....

"Alk'ali ya sunkuya yayi rubutu kafin ya d'ago ya dubi Salim yace " Salim kaji confession d'in da d'an uwan ka yayi... "Ka yarda ka amince ka aikata laifin...??

"Idanun Salim suka ci gaba da zuban hawaye... Jalal kallon sa kawai yake da idanun sa da suka kad'a sukayi jazir...

"Kai muke saurare Malam Salim" Alk'ali ya kuma fad'i...

"Salim Ya soma girgiza kai hawaye na bin k'uncin sa kafin yaci gaba da bayanin yanda mahaifin sa Kasim Dasuki da kuma Uncle d'insa Barr Munir suka shirya yanda zasu lak'aba ma Jalal laifin shi kad'ansa...... Yasa bayan hannu ya goge hawayen da suka zubo masa kafin yaci gaba da fad'in" But your Honor you heard him right, da bakin sa Labib ya fad'i sabida biyan buk'atar sa ya jamu yayi mana jagora snn shine mai laifi a nan, shi yafi cancan ta a hukunta sa, ciki harda mutuwan Tariq da kuma b'ata mana rayuwa da yayi.....
"Labib ya zabura yana kallon sa kafin yace " Shut your mouth you idiot.... Did I drag you by force,????

"Silence...!!!!!
"Don't speak without permission.... " Alk'ali ya fad'i had'i da buga benchi kafin yaci gaba da fad'in" Just answer the question did you commit the crime..??
"I don't care if you were forced or not, just go straight to the point and answer my question, ka aikata laifin...???

"Salim yana hawaye.... "Zubaidah kallon sa kawai take da idanun ta da suka jik'e tana jiran taji amsar sa, kotu tayi tsit gaba d'aya all eyes on Salim....

"Saida ya had'iyi wata miyau kafin ya soma gyad'a kansa yana mai ci gaba da hawaye yake fad'in" Yes yes your Honor, I admit..... I... I took all responsibilities of my actions and declared my self Guilty.....!!!!!.

"Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya Zubaidah tayi lokaci guda suka had'a idanu ita da Jalal suna masu kallon juna, idanun ta sharkaf da hawaye yayinda Jalal ya k'ak'aro murmushi saman face d'insa ya sakar mata ....


"Alk'ali ya bawa Dr dama shima ya fad'i duk iyaka abinda ya sani har kud'i da Alh Kasim ya basa da kuma b'acewa da yayi aka neme sa aka rasa duk a dalilin Alh Kasim....

"Alk'ali yayi rubutu kafin ya buk'aci Alh Kasim da Barr Munir su fito gaban Kotu.....


"Barr Munir ya gyad'a kansa hawayen nadama suna k'ok'arin bin k'uncin sa sanda yaci gaba da fad'in" Yes your Honor, naci mutuncin shari'a I'm nothing but a miserable coward, an incompetent Attorney who deserve to rot in jail...... I was always there helping Alh Kasim with his evil missions.... Da taimako na yake gudanar da duk bak'ak'en mugayen laifukan da ya aikata...... Duk mutanen da Alh Kasim ya ha'inta ya salwantar da rayukan su da dukiyar su saida Barr Munir ya fad'i a gaban Judge....

"Kotu ta kacame da kuka... Sosai Kausar take kuka itada mahaifiyar ta sanda suka ji Alh Kasim shine sanadin mutuwar Alh Tahir Marafah da kuma Amir da Asmah....

"Ansar wani irin hawaye mai zafin gaske ne ke bin k'uncin sa ya yunk'ura ya cakamo wuyan Alh Kasim yana kuka sosai yake fad'in" I'll kill you.... You Animal..... Jalal yayi saurin rik'osa sanda Alk'ali ya buga benchi...
"Fizga Ansar yake yana fad'in" You'll spend the rest of your miserable life behind bars...

"Ai Jalal yana janye Ansar Labib yayi kan Alh Kasim yana fad'in" I knew it, I knew it was you.... You were behind my fathers death Kasim Dasuki I'll kill you with my bear hands... Ya mak'ure Alh Kasim yana k'ok'arin aika sa lahira.... Saida aka taru aka janye Labib....

"Kai jama'a gaba d'aya kotu ta rikice saida aka kuma breaking for some minutes...

"Gaba d'aya su Mummy da Mamy kuka suke kaman ransu zai fice, wann wani irin Al'amari ne haka.... Duk wanda yake cikin d'akin shari'an nan saida ya girgiza da jin irin laifukan da Alh Kasim ya tapka.....

"Bayan wasu mintoci bayan an dawo Alk'ali ya buk'aci Hadiza ta fito gaban kotu don kuwa Barr Munir ya fad'i komai yanda ta taimaka masu suka cimma burin su, duk wani shirin da su Ansar suke ita ke kai masu rahoto, har zoben Salim data tsinta ta kaimasu da kuma checks na bogi da suka bata, bai b'oye komai ba....

"Hadiza ta fito gaban kotu hannayen ta duka biyu aka ta durk'usa saman gwiwoyin ta tana kuka tana rok'on a yafe mata wllhi sharrin shed'an ne..... Bata musa laifukan ta ba tsaf tayi confessing itama tana mai cizgan kukan nadama...

"Mamaki da Al'ajabi ya cika zukatan su......

"Bayan Hadiza Umar ne aka fito dashi gaban kotu hannayen sa d'aure cikin cuffs....
"Shima confessing laifukan sa yayi yana mai kukan nadama da rasa iyayen sa duka biyu da yayi duk a dalilin son zuciya da rashin d'aukan k'addara irin nasa.... Har kisan Tariq da yayi bai musa ba....

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login