Showing 9001 words to 12000 words out of 210924 words

Chapter 4 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22858

dukda kyawun hallita da suke dashi... Babu shiri ta kaɗa saniyarta ta soma tafiya don gani take kaman zasu dawo.
"A daidai bakin kwalta ta haɗu da Ummaru, ganin yanayinta yasa shi ɗan razana, don gaba ɗaya a figice take.
" Surbajo na yaya dai lafiya ya tambaya yana ƙoƙarin kota maya saniyar, ɗan langaɓe kai tayi cike da yarinta take faɗin" Ba kaine kaƙi zuwa ba gashi ruwa ya min duka.
"Ɗan murmushi Ummaru yayi dama yasan hakan ka iya kasancewa. Haƙuri ya soma bata yana lallashinta har ta haƙura kafin ya sako zancen tafoyar da zaiyi nan da kwana biyu.
"Take idanun Zubaidah suka yi raurau, ƙwalla ya ciko idanunta, kaman me shirin kuka take faɗin" Yanzu shikenan tafiya zakayi ka barni...." Nan da nan yaji babu daɗi rausayinta ya cikasa, sandar hannunta ya karɓa kafin yace" Zubaidah ɗago ki kalleni, da ƙyar ta iya ɗagowa tana dubansa, Ummaru yaci gaba da faɗin" Ba jimawa zanyi ba sayi guda kacal zanyi, Shanu zamu kao chan jihar Lagos, na maki alƙawarin bazan wuce sati gudan nan ba. "Turi baki ta kumayi cikin harshenta na fullanci take faɗin" Nide da ka bar wann tofiya mu zauna kawai abinmu. "Umar yayi murmushi yana jin daɗin zance da ita yarintarta da ƙuriciyarta na birgesa, "
"Kinga kuɗin aurenmu zanje nemowa, ko bakiso ayi auren ne....."Tuni tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta dashi alamun kunya, mirmushi kawai yayi kana suka ci gaba da tafiyansu suna hiransu gwanin ban sha'awa..



***************************
"Hankalin Annah ya gaza kwanciya, haka kurum take jin mummunar faɗuwan gaba, tana jin gwara ta kasance da Jalal ɗinta don kuwa ziciyarta tana raya mata mummunan tunani sarara, tasan tabbas taje Dukku da yawa daga danginta zasu gujeta, don haka bazata je wajensu ba ko taje, toh wajen wa zataje ta tambayi kanta, take tunanin ƙawarta Inna Wuro ya faɗo mata hakan kuwa za'ayi don tabbas su Lado sukayi ido huɗu da Jalal zasu iya ganesa kuma zasu faɗa masa komai.. Babu shiri Annah ta hau shiri ta nufi Dukku.


"Yaya Hadiza ce zaune saman tabarma sai karyan loman tuwo take tana jefawa baki kaman bata taɓa cin abinci ba, dama wann ɗabi'arta ce idan tana cin abinci kai kace wani zai wabce ne, jin sallamar aminiyarta Iyalle yasata saurin wurga kwanon tuwon bayan ƙyaure, nan ta shiga shage miyar kukan jikin rigarga kafin ta amsa sallaman Iyalle, tsegege Iyalle ke kallonta kafin ta taɓe baki tace" Meye kike ɓoye mun.
"Hadiza ta haɗe gira tace ban gane ba, kaman yaya me zan ɓoge maki, abinci na ida ci yanzun nan.....
"Taɓe baki Iyalle tayi kafin tace" Umhm ƙawata kenan sekace bansanki ba, keni ba wann ba labari nazo maki dashi na arziki da ɗumi ɗuminta. Tuni Hadiza ta kaɗe bujenta ta gyara zama, ina saurarenki.
" Iyalle ta zauna da ƙyar kafin ta ciro gudan ƴan dubu dubu cikin pose ɗinta ta goga su idanun Hadiza......
" Aiko baki sake Hadiza ke faɗin" Ƙawata ina kikayi babban kamu haka, " Iyalle ta murmusa kafin tace" umhm toh ki zauna a nan ke anayi banda ke.
"Ban gane anayi vanda ni ba, cewar Hadiza,
" Iyalle ta gyara zama kafin tace" Albishirinki idan kinson waɗan nan bugun habujan kema kina iya samu.
"Hadiza anji zancen arziki tuni ta miƙe ƙafafu tana faɗin ƙawata ina daurafenki wazaiƙi masu gidan rana ai sede bai samu ba.
" Iyalle ta mutmusa kafin tace" Ai kindaiji labarin zuwan su Alhj Dasuki da Alhj Marafa me neman kujeran shugaban ƙasa,.... Hadiza ta gyaɗa kai da sauri kafin tace" Ai ancema layin anguwan ba'abi duk sojojine a wajen suke tsaro. Wai idan muyum yabi wajen ke ko ƙwaronr yabi wajen sai an harbe sa
" Iyalle tace" Toh barikiji na faɗa maki sojoji dai suna tsaron anguwar amma basu hana mutane zuwa ba, ke yau na taƙaice maki ƙofar gidan tamkar kasuwa , a nan aka raba mana dubu biyar biyar duk wanda yaje babu babba babu yaro, inaga dai da ingin buga kuɗi ma suka taho don kuɗin baya ƙarewa.
" Haba idanun Hadiza sukayi wulli wulli taji kuɗi tuni ta wawuro ƙafar silipers ɗinta tana faɗin " Ƙawata tashi ki rakani, ... " Iyalle ta sheƙe da dariya kafin ta jawo Hadiza ta zaunar kana tace" Ƙawata ai kin makara na yau kam an gama. Hadiza rai ɓace take faɗin amma ƙawata baki kyauta min ba, ai aminta batace haka ba, ni duk yanda naga kaya mai kyau kafin wata dilalliya a garin nan ta sani sai na sanar dake ...."
" Iyalle tayi dariya kafin tace" Nima yau na sani da ƙyar su Dije suka yarda suka tafi dani kinsan suke aiki a gidan, toh a daƙilin haka na samu, sann da naji sunce suna neman ƙarin ma'aikata sabida hidiman da zasuyi na bikin ƴaƴansu nace bara na sanar dake kema ki samu, kinga sai ki tafi da wnn aljanar ƙanwar mijin taki tunda naga ta iya kala kalan abinci ko yaya kikace.
" Hadiza harza buga tsalle don murna kafin tace" Kai gaskiga ƙawata kin burge, kin kyauta min, aiko dolenta ma taje kinga nayi riba biyu ga kuɗinta ga nawa...... Dariya sukayi gamida tafe hannaye suka ci gaba da hiransu, kafin Iyalle ta tafi akan sai sun Haɗu.......




" Momyn Salim ce keta faman kaikomo yayinda ma'aikata suke take mata baya sai nuna yanda take so wajen da za'ayi event ɗin tsarin ya kasance, mussaman suka taho da masu tsara wajen daga Abuja, Annah ta dubi momy tace" Hajiya idan babu wani aikin zan wuce masauƙi. Momy ta murmusa kafin tace" Haba Annah ai gwara ki zauna a nan, ni banyi zaton jikin naki zai sakeki ki samu zuwa ba, snn wann biki fah na Salim ne kinga kuwa ai yakamata a soma komai dake.
" Annah ta murmusa kafin tace toh shikenan Hajiya yanda kikace.



"Isowan su Zubaidah kenan cikin kataparen gidan, daga ita har Yaya Hadiza kallo suka bi gidan dashi ko a mafarki basu taɓa shigowa gida irinsa ba, nan da nan Iyalle ta gabatar dasu ma Dije, Dije sai wani yauƙi take tana masu tambayoyin ƙaƙa uwaka ta haifeka irin ta smi matsayin nan, da ƙyar da roƙo dai ta yarda ta amince ta kaisu gaban momy a matsayin extra ma'aikata da aka ɗauka. Daga nan kitchen suka wuce suka soma aiki babu kama ƙafan yaro.



Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:09] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

09

*©Sameena Aleeyou....✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...📖📚_


"Balele nifa kaga irin abinda bana so muzo muna ƙoƙarin kutsawa da ƙyar ɓa don Zubaidah na wajen nan ba wlhi babu abinda zai kawo ni, Cewar Umar dake tsaye gefen Balele suna ƙoƙarin kutsawa cikin gidan da ƙyar.
"Ko saurarensa Balele beyi ba sai fizgo hannunsa da ya samu yayi suka shige daga kansu kuwa aka kulle gate.

"Can gefe suka samu suka zauna sai kalle kalle suke irin ƙyale kyalen dake a wann gida, darene amma tamkar rana sabida yanda wutan lantarki ya gewaye ko ina, mutane sai kai komo ake.


"Momy da Mamin Labib ne tafe suna haƴewa bene yanda baƙinsu suke yayinda Zubaidah ke take masu baya hannunta ɗauke da tray, sai kalle kalle take tana mamakin dama akwai gidaje masu kyau da tsari irin wann a garinsu, kai idan aka ce zata taɓa shiga gida irin haka a rayuwarta zata musa.
"Suna Mami ta mata umarni ta ajiye. Nan tabi umarnin Mami ta ajiye ta nufi ƙasa, nan ne fah ta ɓata a hanya, don kuwa wann girma gida dole ma mutum ya ɓata musamman irinta da bata taɓa shiga irin gidan ba.
"Hanyar da ta miƙe dama nan tabi, sai wage waige take, gashi abinda yafi bata mamaki shine wann hanyar yayi shiru da yawa, anya nan suka biyo dasu Hajiya kuwa, haka dai taci gaba da tafiya har ta hangi stirs da sauri tayi wajen ta soma sauƙowa.....
" Bata ankara ba saiji tayi ta bugi jikin mutum, kallon kallo suka shiga yima juna, haka kueum taji gabanta yayi mugun faduwa snn ta rasa a ina tasan wann fuska, shi kuwa Jalal kasa daina kallonta yayi, haka kurum yaji ya tsinci kansa cikin farin ciki,.... Murya na rawa ta soma basa haƙuri.
"Dan Allah kayi haƙuri wllhi bansan da mutum bane, kayi haƙuri kaji yallaɓai kar ka sa sojojinku su harbeni......" Jalal kam dariya taso basa ganin duk yanda ta daburce, is Okay is Okay... Ya faɗi fuskarsa ɗauke da murmushi kafin yace zo ki wuce, da sauri ta raɓa ta gefensa ta nufi downstirs,
"Har ta kusa sauƙa Jalal yace" Emm ina zakije.
" Cikin sauri tace dashi sashen ma'aikata. Ɗan murmushi yayi mai bayyana dimpls ɗinsa kafin yace" I think Ƴou miss the way, kallonsa tayi ba tareda tace komai ba don kyaun halittarsa na firgita ta tamjar ba mutum ba haka take dubansa musamman da yayi murmishi.
"Ganin tayi sakare tana dubansa yasa yin wani murmushin kafin yace "muje na nuna maki, babu musu tabi bayansa, har ƙofan da zai fitar da kai BQ ya fito da ita,.... Da sauri ta nufi ƙofan ba tareda tace dashi komai ba, "Jiyo daddaɗan muryarsa tayi yana faɗin" Baki min godiya ba.
"Ɗan juyowa tayi gamida masa godiya cikin harshen fillanci, Shima murmushin yayi ya amsa mata cikin harshen fillanci... Jin yayi mata fillanci yasata ficewa da sauri tana ƙunshe dariyan da yazo bakinta da hannunta don kuwa da kalman tsokana ta masa godiya shima kuma da hakan ya amsa. Itakam tafi bashi balarabe ko bature kwata kwata bata kawo bafilatani bane.... Har ta isa kitchen murmushi take....
" Wani uwar harara Hadiza ta watsa mata kafin tace" Ke murmushin me kike, snn meyasa kika jima daga kai abu kinsan aiki na jiranki. Kinje kin saki baki da hanci kina masu kallon ƙurillan da kika saba koh.
" A'a emm dama..... bata gama faɗin abinda zata faɗa ba Hadiza ta jawota da niyan jibganta.... Sauran ma'aikata sai ƴan gulmammaki suke, Annah ce ta shigo dama itace incharge na ma'aikatan tunda ta taho, da sauri ta ƙwaci Zubaidah daga hannun Hadiza tace" Haba baiwar Allah, ko me ta maki ai bai kamata kina dukan budurwa kaman wann ba, Hadiza dai bata ce komai ba sai hararan Zubaidah da take.
"Annah ta kalli Zubaidah gamida sakar mata murmushi kafin tace " Ɗauko karas ɗin chan kin fere min babu musu Zubaidah tayi yanda tace cike da girmamawa. Haka kurum Annah taji yarinyar ya burgeta ta shiga ranta lokaci guda...


" Tun shigowarsa ɗakin yake murmushi ya kasa ce masu komai sai murmushi. Salim dake tsaye cikin closet ɗinsa na shiryawa ango to be, ya kalli Jalal ta jikin mirror kaɗin yace" Whats up with you Buddy, you seems very happy, Murmushi Jalal ya kumayi gamida zama tsakanin Tariq da Labib da suke kan buga PS5..... Ɗaura hannayensa yayi bisa kafaɗunsu yana duban Salim dake tsaye closet kafin yace" Guys I just saw her, I saw her......
" Da mamaki suke kallonsa har suna haɗa baki wajen cewa" sawWho"???
" Kaman wanda ya tuna abu, murmushi yayi ya miƙe ya nufi ƙaramin fridge ɗin dake ɗakin ya ɗauko kwalban wine ya tsiyaya a cup ya kurɓa, Labib ya dara kafin yace" Guy wacece ka gani.
" Jalal yayi murmushi ya kuma kurɓan wine ɗin kafin yace "Never mind its just my imagination... "Dariya kawai sukayi sanda Salim ya ƙarasa shirinsa suka fito gaba ɗayansu suka nufi filin event wanda aka tsara shi kai kace a turai ne, .....
"Isowar su Kausar kenan fili ya kacame, Salim ya shagala da kallonta don kuwa tayi kyau har ta gaji, wata arniyar silver gown ta saka kai komai nata silver ne sai ta fito tamkar wata me zuwa gasar sarauniyar kyau.
"Idon Labib ya sauƙa kan Asmah wacce itama tasha gayunta cikin red gown tayi ɗauri irin na yayi da royal blue vail a kanta tayi kyau matuƙa, duk haɗuwan da suke bata taɓa masa kyau irin ta yau ba.
"Taro yayi taro nan da nan aka soma gudanar da Event.


"Zubaidah sai leƙe take ta windon kitchen tanason fita taga amaryar don taji anyi annoucing isowarta. Ta ɗan saci kallon yaya Hadiza kana tace" Yaya don Allah naje na kalli amaryar.....Wani uwar harara Hadiza ta watsa mata kafin tace" Bazakije ba don uwarki, shegiya me shegen son kallon tsiya, wann abu duk a kunnen Annah ya faru. Ɗan girgiza kai tayi dukda batasan alaƙan dake tsakanin Hadiza da Zubaidah ba ta tabbata Zubaidah tana shan wuya wajen Hadiza, ƙarasowa cikin tangamemen Kitchen ɗin Annah tayi ta dubi Zubaidah dake ɗaman leƙe ta window tace" Zubaidah kina son kallo ne.
" Da sauri Zubaidah ta juyo ta dubi Annah gamida kallon yaya Hadiza data sakar mata harara. Annah tayi murmushi don kuwa taga irin kallon da Hadiza tayima Zubaidah..... Baki na rawa Zubaidah tace " a'a Annah ban ƙarasa haɗa waɗan nan parantan ba.
"Annah ta murmusa kafin tace kar ki damu zo muje ki kalla, juyawa Annah tayi ta dubi Elizabeth ɗaya daga cikin ma'aikatan da suka taho dasu daga Abuja masu uniform kana tace" Elizabeth continue with the plates arrangement" Elizabeth ta amsa da Okay Ma.
"Duk sunsha mamakin jin Annah na turanci harta Zubaidah saida tayi mamakin jin Annah tana turanci... "Hannunta Annah ta riƙe suka nufi farfajiyan gidan yanda ake gudnar da shagalin.

"Tun fitowarsu idanun Jalal ya sauƙa kansu, yasha mamaki sosai ganin Annah tare da Zubaida riƙe da hanun juna har suna magana. Toh dama Annah tasanta ne, toh a ina tasan ta??? Kasa samo amsar tambayoyin nasa yayi.
"Salim dake rawa da bride to be ɗinsa idanunsa suka sauƙa kan Zubaidah, kallon ta yake da mamaki, a hankali ya furta *"Cow Girl"* me take yi a nan.???
" Ɗan sunkuyowa yayi saitin kunnen Kausar kana yace" Sweetheart barin je wajen su Labib I'll back in some minutes.
" Kausar ta murmusa kafin tace" No prblm Dear take ur time. Satan idon mutane yayu gamida manna mata kiss a kumatu...."Zari ido waje Kausar tayi tana dubansa, harda wani kashe mata ido guda kafin ya wuce.
" Asmah ta taso da sauri tana dariya, a daidai saitin kunnen Kausar take faɗin " Girl I saw that, lallai wann angi naki za'a sha fama, nide kar aje ana kiran mumsy da Papy suzo su kawo.ɗauki, Hararan wasa Kausar ta watsa mata gamida riƙo hannayen Asmah suka soma yin rawan a tare.....


"Salim yana ƙarasowa table ɗinsu ya samu zancen cow girl suke dun babu wanda yasan sunanta cikn su, as usual Jalal yana warning nasu. Caraf idanun Jalal suka haɗu dana Annah, alama ta masa da hannu kan yazo.
"Su Salim suka dubesa suna murmushi ƙasa ƙasa suke faɗin yaje ƙila Annah tasnta ne. Zubaidah kuwa tana ganinsu a tare a haka, ta tunosu ta tuno yanda ta gansu bakin rafi, faɗuwar gaba ta tsinci kanta dashi..... Tana cikin tunanin ta jiyo nuryar Annah tana faɗin" Zubaidah barin yi magana da yarona, gyaɗa mata kai kawai Zubaidh tayi ba tare da tace komai ba, har lokacin ƙirjinta na bugawa musamman da Labib ya ɗago mata hannu tare da kashe mata ido guda.

"Ɗan matsawa gefe Annah tayi itada Jalal tana masa magana amma idonsa da hankalinsa gaba ɗaya suna kan Zubaidah......
" Daga yanda suke zaune can baya shida Balele ya hangeta sai faman rarraba ido take, ya kuma duban Jalal daya kafe ta da idanu, yaga sanda suka sakar wa junansu murmushi..." Take gabansa yayi mugun faɗuwa Da sauri ya miƙe ya nufi yanda take.
" Saida ta razana da ganin Umar don batayi zaton zata gansa a nan ba.... Juyawa yayi sukayi ido huɗu da Jalal, Jalal yayi saurin kauda nasa kan gefe.
" Fuska a tamke tana gaishesa ko amsawa baiyi ba ya soma faɗin" Wanene wancan saurayin da kike masa murmushi.
"Ido ta zari tana dubansa kafin tayi magana a zuciye yake faɗin" Naga irin kallon da yake maki, ke bakisan yaran masu kuɗin nan ba koh, waima har yanzu aikin uwar me kike da bazaki tafi gida ba,..." Kasa cemasa komai tayi sai kallon data busa dashi, kishinsa yayi yawa bacin bata ga laifin datayi a nan ba ko ƙwara.... " Umar ya kuma hasaƙa ganin tai masa biris,...." Bata gama tunanin da take ba ta jiyo muryarsa naci gaba da faɗin" Wani gulmar ne ma ya fito dake nan keda kike aiki a kitchen, Okay dama kallon maza kikazo yi, fine kici gaba. Yayi maki kyau, ni zan wuce lagos gobe da asubahin fari. Idan kinga dama ki bar wajen nan as soon as u can. Daga haka bai kuma cewa komai ba ya wuce fuuuu, Ko sallama da Balele bai samu zarafin yi ba ya fice abinsa.



" Labib ya dubi Salim da Tariq kafin yace guys ku kwantar da hankalinku ni nasan maganin Jalal, kan wann ƙazamar talakan yarinyar zai nemi raina mana hankali, muna buƙatan jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login