Showing 207001 words to 210000 words out of 210924 words
Da gudu ta shige d'aki had'i da turo k'ofa, ta runtse idanun ta hawayen farin ciki na zubo mata....
"Sosai Mumsy ta sa masa Albarka had'i da masa fatan Alkhairi... kafin ta mik'e ta nufi d'akin Kausar don jin nata ra'ayin...
"Tun daga looks d'in da Mumsy ta gani tattare da Kausar tasan itama tana son Ansar, hakan yayi ma Mumsy dad'i.. Saidai tayi masu fatan kasancewa cikin farin ciki, ji take kaman tafi ko wata uwa sa'a....
"Mumsy da kanta ta shirya Kausar ta sauk'a downstairs wajen Ansar....
*************
"Bayan kwana biyu suka tattara suka koma Gombe... Har liyafa maiji da lafia aka had'a masu...
"A ranar kuma Baba Ciroma ya soma magana, tunda Ummi taji haka, jikinta ya sare, jin yau Baba Ciroma zai shigo fadah yasata sarewa gaba d'aya... Abu mafi mata sauk'i shine tayi confessing laifin ta...
"Cikin parlorn Abbah yayi tsit Ummi ake saurare...
"Sosai jikkunan su yayi sanyi.... Daskarewa kurum Jalal yayi yana sauraren Ummi, kai ba Jalal kawai ba gaba d'aya kasa gaskata abinda kunnuwar su ke jiye masu suke...
"Duk k'arfin hali irin na Abbah saida hawaye suka shiga gangara masa....
"Kuka Zahidah keyi kaman ranta zai fita...
"Cikin kuka ta k'araso gaban mahaifiyar ta tana jijjigata take fad'in" Ummi why, why Ummi..... Meyasa kika zama Monster, Ummi meyasa kika zama SANDIN K'UNCIN MU, why Ummi..... Ummi don Allah kice min abubuwan da kike fad'i ba gaskiya bane...
"Ummi ta rik'e Zahidah tana kuka sosai take fad'in" Daughter I was a monster, a betrayal.... I don't deserve any of you..... Amma ba yin kaina bane, shawarin Baba Ciroma ne da kuma sharrin shed'an snn wllhi tllhi babu hannu na a kisan Daada..... "Abu guda da nasan nayi shine salwantar da Lamid'o..
"Ku yafe min don Allah..... Modibbo ku yafe min, Abbah ku yafe min....
"Jijiyoyin jikin Jalal sukayi rud'u rud'u, hawaye masu zafi suka ci gaba da bin k'uncin sa....
"Ummi jiki a sanyaye ta matso kusa da Jalal yayi saurin matsawa baya...... Tana mai ci gaba da kuka take rok'on sa gafara...
"Kaman daga sama sai jiyo muryar Abbah tayi yana fad'in" Kilishi kin cuce ni, kin zalunce mu nida d'ana, kar kiyi gigin tab'a min d'a da wannan k'azantacciyar hannun naki..... "Keda Ciroma bansan me zan ce maku... Amma ku sani Allah yana nan kuma yafiku, da sannu zaku girbe abinda kuka shuka.... Ku sani Zakaran da Allah Ya nufa da cara ko ana muzuru ko ana shaho toh fah sai yayi.... Kun rabani da farin cikin rayuwata Suhaima.... Kilishi kin cika butulu.... Ki sani ni Aliyu na gama zaman aure dake.... Ki tattara ki koma masarautar ku..... Zan rubuta sak'o na tura, duk irin mugayen abubuwan da kika aikata..
"Ummi tasa hannu aka tana kuka.... Zubaidah da Annah ma sosai suke kuka..
"Annah ta rungumo Jalal tana fad'in" I'm here son, I'm here for you, let it out... Yi kukan ka... Ai Jalal kaman jira yake nan ya kwantar da kansa jikin Annah ya shiga kuka da duka zuciyar sa.... Tabbas an zalunce su... Zahidah ma k'arasawa tayi ga Zubaidah ta kwanta cikin jikinta tana kuka sosai...
"Jiki a sanyaye Khalifa ya shigo yana kuka sosai... K'arasawa yayi gaban Mai Martaba yayi irin zaman rak'umi, cikin tsananin kuka yake fad'in" Abbah, Baba Ciroma babu, he confessed everything before he died..... Abbah ya fad'i komai duk mugayen ayyukan da yayi kafin ya mutu, Abbah ka yafe wa mahaifi na ko zai sassaucin Ubangiji..... Khalifa ya kifa kansa yana kuka sosai....
"Tsit kake ji sai sautin kuka, ...
"Mai Martaba ya kifa kansa kurum hawaye na kwarara masa... Tabbas matar sa da d'an uwansa sun masa zalunci mafi muni a duniya...
"Shattima ne yayi k'arfin halin rik'o Khalifa ya fice dashi don yasan Abbah bazai iya koda kallon sa ba....
"Wann rana haka Fadah ta wuni babu walwala....
"Su Baba Waziri mahaifin Shattima da sauran masu sarautun gargajiya su suka tsaya akan komai har aka kai Baba Ciroma makwancin sa... Mai Martaba kam ranar haka ya wuni babu lafiya...
"Jalal ma bai gane yanda yake ba, for second Zubaidah bata bar side d'insa ba, dukda Zubaidan ma ba jin dad'in jikin ta take ba, but she needs to be very strong for her husband, he needs her now more than ever....
"Zahidah ma sosai abin yayi affecting nata, Annah ita ta tsaya sosai akan Zahidah, sosai take bata duk wani kulawa da d'a yake nema wajen iyaye...
"Zahidah ta rik'e hannun Annah kafin tace " Annah why my mother, why she??? I thought lokacin da aka sami Hamma Modibbo bak'in ciki ya k'are mana, but I was wrong Annah.... Why Annah..???
"Rungumeta Annah tayi kafin tace " Wannan shine rayuwar sweetheart, Allah yakan jarabce mu ta yanda bamuyi tsammani ba, the most important shine kar mu rasa imanin mu, Allah yafimu sanin meyasa Al'amra suke faruwa haka...
"Kiyi hak'uri sweetheart ki karb'i k'addaran ki hannu bibbiyu sai kiga Allah Ya sawwak'a maki... And if you need anything don't forget that I'll be right here okay.....
"Rungumeta Zahidah tayi tana matsan hawaye.....
"A haka Jalal ya shigo ya same su, cike da tausayawa yake kallon Zahidah... Ganin sa yasata mik'ewa da sauri... Da gudu ta tafi ta rungume sa tana kuka take fad'in " Brother...... "Sosai ya rungume ta yana fad'in" it's okay Sis we are here, we are all here for you kinji...
"Gyad'a masa kai tayi tana hawaye, Jalal ya kuma hugging d'inta tausayin ta na ratsa zuciyar sa.....
***********
"A haka har akayi kwana Uku, Ummi da Jakadiya b'ab'ewa sukayi, gashi Jakadiya ma an koreta daga masarautar.... Haka ta tagayyara a titi...
"Ummi kuwa sam masarautar Katagum suka k'i karb'an ta, dama Mai Martaba sarkin Katagum ne ya had'a auren....
"Haka ta koma gaban iyayen ta cikin k'unci... Gashi ba wani k'arfi bane dasu, ta saba rayuwa cikin daula da sarauta da jin dad'i... Abubuwa sun sauya ma Ummi, idan ka ganta sai ka tausaya mata... Dama mahaifin ta irin masu Almajiran zauren nan ne... Haka Ummi ta koma tuk'a tuwo tukunya lamba Arba'in... Duk d'an farin fatar ya tauye ta koma abin tausayi, ga tarin kunyar abunda ta aikata....
"Jalal da Zahidah sun tafi masarautar Zazzau sunyi kwanaki biyu, masarautar Mahaifiyar sa, sosai sukaji dad'in zuwan sa, dukda Kakan sa saekin Zazzau mai rasuwa baya nan, amma sosai 'yan uwan sa sukaji dad'in zuwan sa, tarban girma da karramawa akai masu.... Basu samu damar zuwa da Zubaidah ba sabida lalurar dake jikin ta... Inama zai bari tayi tafiya, bayan yanda yake ji da cikin jikin tan nan, wani rirtata yake kaman ya maidata ciki....
"Sosai ya dank'a amanarta hannun Annah...
"Kwana hud'u sukayi suka dawo Gombe... A hanya Zahidah ta kawo wani shawari wanda Jalal yaji dad'in hakan sosai wanda idan hakan ta kasance shi zaifi kowa farin ciki, sosai ya jinjina ma k'anwar tasa da wann dogon mazari da hange da tayi...
"Sanda suka proposing buk'atar su ma Annah da Mai Martaba sosai Annah taji kunya, Kai yaran nan basu kyauta mata ba, haka ta ringa fad'i cikin zuciyar ta.. Shi kuwa Abbah sosai yaji dad'in hakan.. Kaman yaran nasa sun shiga zuciyar sa don ya jima da k'yasa hakan lol....
"Abunku da manya kuma masu sarauta ba wani d'aukan lokaci za'ayi ba... Cikin lokuta k'ank'ani aka soma gudanar da komai, sanda Jalal yayi waya yake sanar da Ansar nan shima ya sanar dashi an saka auren su da Kausar sosai Jalal yaji dad'in hakan ya jero masu addu'o'i..
*Ranar Biki*
"Babban biki akayi a fadah abin sai wanda ya gani.. Su Unman Shattima ba'a sama ba'a k'asa, ji take kaman k'awarta Suhaima ce ta dawo masarautar... Fuskoki suka cika da annuri, Algaita da Tambura sun bugu a wann rana... Shi kansa Abbah abin saida ya tuno masa da Suhaimar sa... Wani dad'i yake ji cikin Zuciyar sa maras misaltuwa...
"Bayan biki da kad'an Annah ta nace saidai a dawo da Ummi tunda tayi nadama, snn wanda yayi sanadiyar mutuwar Suhaima shima tasa ta k'are... Ba don Abbah yaso ba saida rabin ransa Jalal ya saka baki snn ya amince...
"Annah da kanta ta tafi masarautar Katagum don yin bikon Ummi, wayyo zo kaga yanda ake bawa Annah tsaro... Ummi sosai tayi farin ciki, tabbas Jalal dasu Annah alkhairi ne a gare ta... Amma kam tanajin kunyar had'a idanu da Jalal musamman dataji shine musabbabin komawar ta...
"Annah ta rik'e Fadah kowa nata ne, Ummi kanta 'yar kallo ta zamto a masarautar.. Fadah tayi albarka tayi dad'i sai Allah son barka...
"Bayan wasu kwanaki Khalifa ya sami Shattima ya basa hak'urin duk wasu abubuwan da ya masa a baya snn ya k'arada, zai tafi wani k'asa k'arin karatu, tabbas kunyar abinda mahaifin sa yayi bazai barsa yaci gaba da zama a masarautar ba.... Shattima ka rik'e amanar Zahidah domin da kai tafi dacewa.. Allah yaso saduwar mu Bro... Rungume sa Shattima yayi cike da alhini... Haka sukayi sallama da Khaifah....
**********
*Prison*
Boris ya kalli Labib yana sosa hab'arsa yana wata kafiran murmushi kafin yace " What do we have here.... "Ina alk'awarin mu dakai cewa zaka fitar dani, baka fitar dani ba baka bani kud'i ba gashi ka dawo... Koda yake kun tsiyance gaba d'aya... And yanzu ni kuma zan amshi kud'i na... Boys get them... Ya fad'i yana duban muk'arraban sa.... "Salim na jada baya Labib ma na jada baya.... Basu ankara ba suka soma sauk'e masu na jaki, sauran 'yan prison sai tafi suke suna zuga su....
"Labib da yaji duka yayi duka yace " Ku dakata wllhi nabada kud'inku ma wancan mutumin ya cinye, ku tambaya kuji lawyer ne.... Ya k'arashe yana nuna Barr Munir...
"Ai kuwa nan suka yi kan Barr suka soma lakkad'a tamkar an turo su... Garin duka suka jefo sa daga saman bene....
"Kankace me sun gudu sun watse, k'ashin bayan Barr ya kareraye... Haka ya dinga ihu yana fad'in" I don't feel my legs, my don't feel my hands, what's happening to me.... Aka zo aka kwashe sa sai ihu yake... Babu hannu babu k'afafu sai kansa ne kurum mai motsawa.....
*Sameena Aleeyou Mrs*
[7:22AM, 2/9/2018] βͺ+234 809 781 2439β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
100
*π*
*Β©Sameena Aleeyou... βπΎ*
_πKAINUWA WRITERS ASSOCIATION π€_
*Gaisuwa a gareku Aysha Mrs Muhammad and Zeenert ππ€*
"Kwanci tashi babu wuya wajen mai sama, satuttuka sun shud'e hakan nan watanni sun shud'e, anyi bikin Ansar da Kasaur sannan Shattima da Zahidah....
"Rayuwa tayi das'i sai godiyan Allah... Da k'yar Madaki ta amince da dawowar Ummi, dukda haka bata wani sake da ita ba, komai Annah ce akan gaba, sosai Annah ta rik'e masarautar, wani sabon rayuwa mai dad'in gaske suka tsinci kawunan su ciki.
"Tsakanin Annah da Ummi an rasa waye yafi bawa Zubaidah da jaririn cikin ta kulawa.. Sosai suke kula da ita, harta Madaki ba'a barta a baya ba... Masha Allah Zubaidah ta zamto shalele, kowa burin sa ya kyautata mata, baga mijin ta ba baga siraka nan ta ba..
"Hamma da Kamal sosai ake basu kulawa, Hamma a kullum cikin lissafin kwanaki ko ince watannin da suka rage ma Hadiza yake... Allah sarki soyayya dai gamo ne na jini.....
*********
"Zaune take saman carpet cikin nata ya turo sosai, k'afafun ta sun d'an hahhau.... Nad'e hannayen rigar sulken sa yayi ya shiga matse mata k'afafun yanai mata sannu..
"A hankali ta bud'e idanun ta ta sauk'e su saman kyakkyawan fuskar sa...
"Murmushi ya sakar mata kafin yace " Sannu Baby wifey... Do you need anything....??
"D'an murmushi ta masa kafin tace " Of course my Hero...
"Da sauri ya mik'e yana tambayar ta me take so...
"Far da idanu tayi kafin tace " I love you, a hankali....
"Zama yayi gefen ta yana murmushi kafin yace " And I love you too Baby Wifey.... You and our unborn Champion or princess..... Murmushi ta sakar masa kafin ya had'e lips d'insu waje guda.....
**********
"Zaune take saman kujera a d'akin Goggo, gashesshiyar masara ne a hannun ta take kan faman ci, da alama ta shiga watar haihuwar ta.....
"Da sallama ya turo k'ofar d'akin ya shigo.... Murmushi ta sakar masa tanai masa sannu..
"Murmushin shima ya mata kafin ya zauna daga can gefe yanai mata sannu...
"Ledan hannun sa ya bud'e ya ciro d'an wani k'wali ya mik'a mata...
"Kallon sa tayi ta kalli kwalin kafin tace " What's this... Another gift... Hey it's not my birthday..
"Murmushi yayi baice komai ba... "
"Tana Bud'ewa taga kayan Baby ne unisex masu kyau da tsada... "Kallo take kan faman bin kayan dashi baki sake kafin tace " Hey this is way too expensive... Haba Imam...... "Shiiihhh yayi saurin katse ta kafin yace " It's not yours ai, na Baby ne... His first welcome gift....
"Murmushi tayi soyayyar Imam na dad'a shiga zuciyar ta... Kafin ta soma masa godiya yayi saurin mik'ewa ya ajiye mata sauran kayan ya fice wajen Goggo...
"Hawaye masu zafi suka shiga kwararo ma Zulaihat.... Murmushi tayi had'i da rungume kayan cikin jikin ta...
"Bayan kwana biyu labor ya tashi ma Zulaihat.... Goggo da Imam basu bar side d'inta ba har saida ta haifo d'anta k'ato namiji kyakkyawan gaske...
"Sanda Imam ya rungumi d'an cikin k'irjin sa a hankali ya furta "Welcome to the world Son had'i da sumbatar sa a goshi....
"Hawaye suka sauk'o mata... Kowa a asibitin mamakin yanda Imam ke son d'an sa da matar sa yake, duk a zaton su matar sa ne da d'an sa...
"Tana asibitin ta sami labarin harbin Umar da akayi sabida escape a prison da ya tashi yi... Sosai tayi kuka tana kallon jaririn ta... "Haka Imam yayita k'arfafa mata gwiwa yana rarrashin ta, amma kam kuka ya zama mata dole......
"Duk kulawan da ya kamata mai jego ta samu Imam da Goggo suna bata..... A haka har tayi wata guda da satittuka... Nan ne suka shirya suka nufi Yola gaba d'aya harda Goggo...
"Sun sha mamakin samun mahaifin Zulaihat cikin tsananin ciwo, haka ya ringa kuka yana bama Zulaihat hak'urin duk wani abinda ya mata a baya.. Anty ma haka tayita bata hak'uri suna neman yafiyar ta, don kuwa tabbas abubuwan da suka same su a rayuwa hakkin Zulaihat ne..
"Zulaihat ma ta basu labarin irin rayuwar da ta shiga tareda Umar, ta kuma nemi yafiyar mahaifin ta.. Anty ta karb'i jinjirin ta mai suna Muhammad tana gani... Sosai yaron ya shiga ransu.... Haka Dad da Anty sukayita godiya ma Goggo da Imam....
"Bayan tayi arba'in aka sha bikin su tareda Imam...Ba yanda Anty batayi ba a bar mata Muhammad sai ya kwana biyu a kawo sa... Dashike nono bai dami yaron sosai ba... Fir Imam yak'i ko kunya babu, wai zaiyi kewan d'an sa...
"Imam ya rik'e hannayen ta kafin yace " Alhamdulillah, yau burina ya cika, Allah Ya cika min burina, ya mallaka min matar da nake mafarkin kasancewa tareda ita....
"Ta d'an murmusa had'i da sunkuyar da kai idanunta suka kawo ruwa ... A hankali ta soma furta, Imam you don't deserve me, you deserve someone more than me.... You're Young and fresh blood, while on the other hand I... I'm... Saurin rungumo ta yayi kafin yace " Shiiish " Kar na sake jin wann maganar