Showing 102001 words to 105000 words out of 210924 words

Chapter 35 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22894

da case d'in Zubaidah, at first nak'i yarda masu sabida nasan halin Kasim Dasuki, nasan shi waye, he's the reason why I lost everything... A d'an tak'aice ya basu labarin grudges d'insa da Alh Kasim....

"Mamaki ya cika su....
. "Zubaidah na hawaye ta soma fad'in" If that's the case the Dasukis must be watching us, precisely sun gane we are somehow allied with the Marafah's, and nayi imani duk wanda suka san munyi alak'a dasu wajen karyasu toh sai sun gama dasu...... Kuka sosai ya kufce mata sanda taci gaba da fad'in" It's because of me, ni ZUBAIDAH everyone has to suffer saboda ni, maybe da ban yi magana ba things will different.... why me..why....
"Da sauri Jalal ya k'arasa ya rik 'e hannayenta kana yace " This is non of your fault, the Dasukis are to blame, sune sila, and they must all pay for each and single crimes they had committed.... Share hawayen nan I don't wanna see them.... Gyad'a masa kai kawai tayi tana share hawayen....

"Jalal ya k'arasa wajen Ansar yana fad'in" So what would we do now Attorney, kanaga tafiyar nan namu zata yuwu kuwa, Asmah needs you now, ya kamata ayi zaman nan har kwana uku dakai, snn now I'm afraid to leave my family all alone, ina jin tsoron kar wani abu ya samesu, looks like Alh Kasim is desperate, he's willing to do anything to take his out of prison, he's capable of anything.....

"Ansar ya dafasa yace " You're quite right Jalal, but that doesn't mean zamu k'yalesa yaci gaba da ta'addanci da kashe innocent souls.... Snn kasan Prosecution office ne suka tura Detectives d'in don gudanar da bincike, bazai yuwu a d'aga masu rana ba, snn you the only one that knows the place, so you really have to go, don't worry about your family, nida Hafiz muna nan we would look after them insha Allah. You have my word...

"Gyad'a kansa Jalal yayi kafin yace " I trust you Attorney, Allah Ya bamu sa'a ya d'aura mu kan azzalumai...

"Ansar ya amsa da Ameen thumma ameen, wayarsa ya latsa lambar Detective Amir kana yace " Detective bamu ganku ba...

"Daga d'aya b'angaren Detective yace " Mun riga mun wuce Attorney, you also should be on your way, coz we want to do this as soon as possible...

"Ansar ya amsa da okay Detective, yeah right, sure... Bayan ya katse wayar ya dubi Jalal yace " Jalal you need to get going sun riga Sun d'auki hanya, and the prosecutor yana expecting report d'in before our up coming trail, kar ka mance maganan Dr d'in, do anything you can reach him, we will be on touch....

"Gyad'a kansa kawai Jalal yayi amma har cikin ransa tunani yake Allah yasa kud'in jikinsa su ishesa.....


"Sallama suka kumayi da Annah da Zubaidah Ansar ya kaisa har tasha....


***********************


"Isowarsa garin kenan sai wani cincin magani yake, tsaki ya kuma ja a karo na babu adadi ganin jikin mahaifin nasa ba har yanda Balele yake fad'i masa bane a waya, .
"Inna ta ajiye masa damun fura a gabansa tana fad'in" Kashi abunci ka kwaso hanya....

"Kauda kai gefe yayi ya kuma jan tsaki a hankali gamida watsa wa Baffah dake kwance kan tabarman azara wata uwar harara.... Inna ta kuma nanata masa a karo na uku....

"A hasale ya katseta da fad'in" Inna nace maki bansha bansha ko dole ne...

"Jiki har na b'ari Inna ta d'aga k'waryan tana fad'in kayi hak'uri Baba Wuro, aradu bansan ka daina chi bane.... Yayi gajeren tsaki kafin yace " Tashi tashi ki kamasa mu kaisa asibiti....

"Babu musu Inna ta soma cicciban mijinta, ko kallo basu ishe Umar ba yayi ficewarsa waje yana karkad'a key d'in mota...



"Bayan sun isa garin da location d'in da incidence d'in ya faru suka soma kasancewar gari ya soma duhu.... Nan da nan Detectives suka soma aune aunensu harda tape suna d'aukan wajen a hotuna.....

"Ganin wajen ya tuno masa komai, yasa sa tuna wancan bak'in daren, d'ya bayan d'aya haka abubuwan suka ringa dawo masa kwanyarsa....


"Detective Amir suna gama abunda zasuyi suka dau hanyar Abuja a lokacin, Jalal kuwa baici ta barin gari ba, he really need to find that Doctor....

*******************

"Admitting Baffah akayi Umar sai wani foffozewa yeke irin shi ga shegen nan, Likita na masa bayanin ciwon uban nasa ko kulasa beyiba yayi ficewarsa yana fad'in is non of my business, you can discuss that with his wife, nayi iya abunda zan iya tunda na biya charges d'in.....


... "Danno kan da zaiyi ya hangi fuskar Jalal ya tunk'aro ward d'in" Cikin sauri ya lab'e har saida Jalal ya wuce. .

"A hankali ya furta what is that jerk doing here.... " Shi kad'ansa ya saki wata murmushi a hankali kafin yace " I'm pretty sure ka kawo kanka kabarinka...


*Mannage this guys 😍😘*

Sameena ce πŸ‘ŒπŸΎ
[1/23, 22:25] β€ͺ+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

61


*©Sameena Aleeyou...✍🏾*


_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🀝_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*





"Jalal ya dubi likitan dake gabansa cike damuwa yace " Yanzu Dr bakasan yanda zan samesa ba, baka san ina ya koma ba. .

"Dr ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Dr Hashim ya kwana biyu da barin asibitin nan kai garinma entirely, and a iya sanina ba gwamnati bane ta canza masa wajen aiki, wayan gari akayi aka rasa sa, he disappeared just like that.

"Hannu yasa cikin gashin kansa yana cukurkud'asu kafin yace " I knew it, they will do anything in their powers to hide that imbecile so called Dr... Damn it....

"Dr ya dubesa kafin yace " You alright...?

"D'an kallon Dr yayi kafin yace " Oh yeah yeah I'm fine... Anyway na gode k'warai Dr pls idan kaji wani abu gameda wancan Dr d'in pls let me know right away....

"Dr Madi ya gyad'a kansa kafin sukayi exchanging phone number da Jalal... Har bakin asibiti ya rako Jalal kafin ya koma.....



"Tunani ya soma yi where would he stay to spend the night, gashi babu wadateccen kud'i a jikinsa balle ya kama room a hotel, gashi shi ba sanin kowa yayi ba... Agogon hannunsa ya duba kafin ya furta Shattima a hankali...

"Wayan Shattima ya shiga nema.. Saida tayi ringing har kusan sau uku kafin aka d'aga...

"Daga d'aya b'angaren da murna Shattima ya d'aga suka soma gaisawa da hiran yaushe rabo.... A gurguje Jalal ya fad'awa Shattima gashi a yankinsu...

"Shattima harda wani d'an ihu da tsallen murna kafin yace " I'll come and get you bro..

"Murmushi Jalal yayi kafin yace " No.. No no you don't have to that zanzo da kaina, idan na iso sai na kiraka..

"Shattima yayi yayi yazo ya d'aukesa Jalal yak'i amincewa, dole ya hak'ura aka bi ra'ayin Jalal.....



"Daga bayan bishiyar da ya lab'e ya gama jin hiran Jalal snn ya gane ina ya dosa.... Shi kad'ai ya fashe da dariya kafin ya shiga neman layin Balele.

"Balele yana d'agawa ko gaisawa basuyi ba Umar yace " Kana Tasha ne..??

"D'an tsaki Balele yayi kafin yace " Toh idan ina tashan me zan maka, don har yanzu fushi yake da Umar....

"Gajeren tsaki yayi kafin yace " Ka fad'a mun mana bana son wulak'anci...

"A tak'aice yace masa " A'a bana nan...

"Okay su Boris fah kanaga zan samesu....

"Da mamaki Balele yake fad'in" Yau kuma kaine da neman su Boris me zasu maka...

"Cikin sauri yace " A'a no babu komai kawai so nake mu d'an gaisa don yau yau zan wuce kasan bazan iya kwanan garin nan ba...

"Balele ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Ummaru kayi hattara da duniya, itafah wann rayuwa da kake ganinta wllhi ba komai bace " Gaba d'aya ka canza ka koma wani abu daban, kar ka mance a da kaine mai mun nasiha nabi duniya da iyaye a Sannu amma yanz...... Cikin hasala ya katse sa da fad'in" A'a a'a don't you dare scold me, who the heck you think you are to lecture my authority... Ina ragar maka ne for old time sake.. Mtsw useless kawai.... Daga haka ya katse wayar....



"Yasan probably Jalal bai isa bakin tasha ba tunda a acab'a zaijeshi.... Da d'an banzan gudu ya kwashi motar sa ya nufi tasha wajen aikinsa a da...

"Bai jima yana neman su Boris ba ya samesu a lungun da suke zama suna shan kayan maye, basu sha mamakin ganin canzawan sa ba tunda ance ya tafi bulaguro... Haba nan fah su Boris suka shiga masa fadanci, shi kuma sai d'dd'aga kai yake uwa namijin k'adangare.....


"Umar ya ciro kud'ad'e ya mik'a masu kafin yaci gaba da fad'in" Kuna jina zaku gansa wani d'an dogo baida jiki sosai, fari ne sosai mai yalwan suma.... I want you guys to Finish him up....KILL HIM...

"Qazaza na tangad'i yake fad'in" ka mana bayanin yanda zamu gane da yaren da muke fahimta....

"Umar ya d'an tank'wafo yana waige waige kafin yace " Ina nufin ku kashesa har lahira.... Dariya suka tuntsure dashi kafin suka ce an gama, masu gidan rana kawai zaka k'ara mana, babu musu ya k'irgo kud'i ya kuma basu, don idandai akan ya sami Zubaidah ne ta zama MALLAKIN SA babu abinda bazai yi ba...

"Daga nan ko asibiti bai koma ba ya d'auki hanyar Abuja cikin palpala gudu abinka da lafiyayyar mota, zuciyarsa fari k'al ya kusa mallakan Zubaidar sa, the love of his life.....

*******************

"Bai sha wahalan samu motar da zata fitar dashi zuwa cikin garin Gombe ba, saidai matafiyar basu da yawa...


"Sunyi nisa sosai kafin daga nesa suka hango Danger ana dakatar dasu.... Driver ya soma salati yana k'ok'arin sake starry, Jalal dake front seat shima salatin yake yana tambayar driver meke faruwa.

"Bawan Allah ai inaga mazan daji ne.... Daidai sanda suka bugi motar da sanda suna fad'in" Tsaya tsaya ko uwarka ta haifi wata ....

"Mazan Daji Jalal ya nanata a hankali... Finfincike marfin motar sukayi idanunsu a rurrufe ga sanduna da dangin su adda a hannunsu suke fad'in" Ku fito, ku fito akace....


"Tsegege Jalal ke kallonsu yana mamakin wann irin rashin imanin ganin harda mata cikin motar suke fad'in" A kwanta a k'asa.... Ai kaine d'an iska bazaka kwanta ba ko, cewar d'aya daga cikinsu... Jawosa suka shiga yi suka sauk'a jeji dashi yana fad'in" Ina zaku kaini, ku karb'a abunda kuke so, me zaku mun..... Tummm yaji sauk'an murtuk'ek'iyar sanda a gefen kansa take jini ya watsu ya kwanta a k'asa....


"Driver da sauran 'yan motan harda budurwarsu wacce da ita aka had'a plan d'in suka kwashe da dariya suka koma garin Dukku, don dama k'arya suka masa bazai sami motar Gombe a lokacin ba.

"Dukansa suke kaman Allah ne ya aiko su, tun yana 'yan k'ara yana rik'e cikinsa har ya daina, sai ka rantse hatsi suke bugewa yanda suke runtuma masa sanda da iya k'arfinsu.... Tun yana d'an motsa yatsun sa har ya daina.....

"D'an mirginar dashi sukayi tabbas baya numfashi nan suka fashe da dariya suka shiga jawosa a k'asa har k'ark'ashin wata bishiya snn suka k'yalesa.....


********************

"Shattima ya kira wayar Jalal yafi abunda yafi, gashi dai tana ringing amma ba'a d'agawa, hankalinsa ya tashi sosai ganin dare ya soma ja....

"Tsakar gida ya fito yaci gaba da trying layin still shiru, ba'a d'agawa.....

"Ameera ce ta hangosa daga kitchen taje dafa indomie ta k'araso tsakar gidan tana fad'in "Yaya wai Aunty Zahidah kake nema ne haka.....

"Harara ya b'alla mata kafin yace " Ke wai ni sa'anki ne, k'arama dake sai sa ido, yaushe ma na soma wann wasan dake.....

. "Ameera ta turo baki tace " Au gani dai nayi munada little secret d'inmu nida kai ko kana so na fad'awa Umma, ta d'an soma jada baya tana dariya take fad'in" Ranar da Aunty Zahidah tazo kuka sha kukan soyayya...... Tsalle d'aya yayi ya capko ta kafin yace " Haba little deal d'inmu ne wancan ai.... Yasan halin Ameera da shegen zuba uwa kurna yanzu saita yad'a sa har kunnen Khalifa... Umma ce ta fito daga sashen Baba Waziri ta hangesu tasan wata suke k'ullawa tunda ta gansu haka....


"K'arasowa tayi tana tana watsa musu kallo kafin tace " Uban me ku kuma kuke k'ullawa....

. "Ameera ta washe baki tace indomie nake dafa mana ai kema zakici ko Umma...... Rufe mun baki Umma ta katse ta kafin tace " Ni zakuyi ma Boko, yaushe aka haifeki Ameera, wato ya k'ulla maki munafuncin da zaki fad'a ko, ai dai kam idan aka ganku ku biyu cikin shiri da juna wata kuke k'ullawa tunda sam bakwa zama inuwa guda....

"Shattima yace " Umma Ameera fah only sis d'ita ce, idan kinga ina scolding nata so nake ta zama good girl, right little...?? Ya k'arashe yana duban Ameera da har ta soma sakin layi tana fad'in" Eh mana ai Umma ta zaci waya kake da Aunty Zahida tunda tace ka mance..... Jawo Ameera yayi yana faman toshe bakinta....

"Umma ta fizgota tace " Munafuki barta ta fad'a, ta shiga tafe hannaye tana sallalami take fad'in" Auho wato Shattima har kuka ka soma yi sabida mace, Na shiga uku ni Amina, ban haifi lusari ba..... Ta soma k'ok'arin fuzge wayan tana fad'in"Bani naga uban da kake kira....



"Ran Shattima idan yayi dubu ya b'aci, har ransa masifar Umma na damunsa, mik'a mata wayan yayi yana fad'in" Haba Umma ni shikenan bazan girma ba a idanunki, fah yanda kike d'aukan Ameera haka kike d'auka na, toh gashi ki gani abokina da nake baki labari shi nake kira, yace mun yana hanya kuma har yanzu bai iso ba,... Gashi see it your self... Ya k'arashe maganar yana bata wayar fuska a murtuk'e ya wuce d'aki.....

"Baki Umma ta sake kana tace " Kafi shanu d'aurewa...

. "Ameera ma baki a ture ta wuce d'aki tana fad'in" Umma wllhi yanzu shiknn kinsa zai fasa bani kyautar da ya min alk'awari....


"Tab'e baki Umma tayi ta rakasu da kallo ta soma tafiya tana fad'in" Can ta matse maku, kunfi kusa.......



**************************

"Bacci take had'e da wasu irin mafarkai marassa kan gado, idan tayi mafarkin saita farka a firgice, idan tayi addu'a sai ta samu komai ya lafa mata, hankalinta yafi karkata kan son sanin halin da Jalal yake ciki, tunda sukayi waya yace zaije ya nemi Dr d'in basu sake waya ba, haka kurum tunanin sa ya haifar mata da fad'uwan gaba mai tsanani... Mik'ewa tayi ta d'au wayanta ta shiga neman layinsa dukda dare da ya. ja..

"Haka wayar ta ringa ringing babu response, hankalinta taji ya tashi sosai, haka kurum jikinta ya bata something is going on with him, she has a feeling he's in danger....... Tsawa akayi kasancewar hadari da ya had'u sosai..... Kecewan ruwan yayi daidai da kecewar kukanta.........

"Babu shiri Annah ta bud'e ido firgit ta hangi Zubaidah dake k'ank'ame da jikinta tana kuka....

"Mik'ewa Annah tayi ta kunna tocila tana fad'in subhanallahi lafiya Zubaidah, meke faruwa.....

"Cikin kuka take fad'in" Annah bai d'auki wayata ba, what if something bad happens to him, what if he's life is in danger, what if he doesn't come back to me, what if that was the last goodbye what if bazan sake ganinsa ba.......

"Gaba d'aya gwiwoyin Annah taji sun sake sunyi sanyi, but she needs to be strong, d'an rungumo Zubaidah tayi kafin tace " Ki kwantar da hankalinkk Zubaidah Jalal yana lafiya da izinin Allah, and he will surely come back to us, he's doing this

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login