Showing 33001 words to 36000 words out of 210924 words
"Makarantar primary da Annah ta sami aikin kula da yara suka tafi yanda za'a sama wa Kamalu gurbin karatu,....
"Zaune take a maidaidaicin parlorn Annah yau har TV ta kunna tana kallo, lokaci guda tunanin Umar ya fad'o mata, ko wani hali yake ciki, shin a yanzu zai iya amincewa da soyayyar ta, take taji hawaye na neman kufce mata, koda shike zuban hawaye ya zame mata jiki......
"Ya jima yana tsaye yana kallonta, sai yanzu ya samu daman k'are mata kallo gaba d'aya, dukda ba farin sani ya mata a da ba yasan ta rame sosai, sabida damuwar dake k'unshe cikin zuciyarta. tausayinta na dad'a fizagarsa.
"Jikinta ne ya bata ana kallonta, aiko tana d'ago ido suka yi ido hud'u. Yana sanye cikin k'anan kaya red shirt da black jeans wanda ya fito da tsantsar farin fatarsa da kyawun halittarsa..... Ai tuni jikinta ya soma kyarma kaman mazari, a guje ta mik'e zata shige d'aki saidai tuni Jalal ya rik'ota ta fad'o jikinsa, k'ank'ame jikinta tayi tana k'k'arin k'walla ihu yasa hannu ya rufe bakinta, dukda yaji a jikinsa sosai kasancewar yanda jikinsu ya manne dana juna, don rabonsa da kusantar wata mace tun bayan had'uwarsa da Zubaidah,.....
"A hankali yake kallonta yana girgiza mata kai alamun tayi shiru, ...
"Batayi shirun ba sai ihu take dukda hannunsa na rufe saman bakinta, bata fasa kai masa duka da duka hannayenta biyu ba..
"Dad'a matseta yayi sosai cikin jikinsa suna jin bugun zuciyar junansu kafin ya soma fad'in" Dan Allah kiyi shiru kiyi hak'uri ki saurareni, babu abinda zan maki.....
"Jin kukan nata ya tsagaita yasa sa bud'e mata baki gamida sakinta a hankali..
"Aiko tuni ta matsa can gefe ta shiga jan rigarta tana rufe illahirin jikinta dashi.... "Cikeda tsiwa take fad'in" Malam ka fice kafin na maka ihu.....
"D'an fuzar da iska yayi kafin ya durk'usa a gabanta, nan da nan ta shiga ja da baya har ta isa k'arshen garu...
"Jalal ya k'urawa yatsun k'afanta ido wanda yasata saurin lullub'e k'afarta.
"Kauda kansa gefe yayi kafin yace " Meyasa kike tskrona...
"Jin tambayar tayi gatsau, d'ago rinannun idanunta tayi tana watsa masa kallon k'yama da tsantsar tsana, lokaci guda kuma taji ta kasa jure kallon nasa, Kauda kanta gefe tayi kafin tace " Sabida na tsaneka, na tsani ganin ka, sabida kai d'aya ne daga cikin mutanen danafi tsanar su fiye da komai a duniya, nafi tsanarka fiye da yanda na tsani shed'an. Kuma wllhi wllhi sai ka sake ni sabida ni Zubaidah matar wani ne akwai baikonsa akaina kafin ku bayyana a rayuwarmu, kafin ku canza mana farin cikinmu zuwa bak'in ciki, idan baka sake ni ba, toh ni ina iya tafiya na bar maku gidan.......
"Hannu yasa duka biyu ya shafi sumarsa gamida fuzar da iska" Ya jima kaman bazaice komai ba har ta cire ran bazaiyi magana ba ta jiyo muryarsa cike da taushi yana fad'in" Zubaidah bazan sake ki ba koda ace ba auren soyayya mukayi ba, dukda nida ke bamu son junanmu amma k'addara ta had'a.......... " Baikai aya ba ya jiyo siriryar muryarta cikeda tsiwa tana fad'in" No k'addara bai had'ani da kai ba, sabida ni ba matar aure bace, lokaci na d'ibar wa kaina kuma lokacin na cikawa zanyi tafiyata ba tareda neman shawarin d'aya daga cikinku ba not even my Hammah.
"Kallonta kawai yake yanda take maganar, lallai tanada courage sosai, girgiza kansa yayi dukda bata dubansa kafin yace " Ba sai kin tafi ba Zubaidah, ni zan taf har sai rananar da kika sami gurbi na yafe min a cikin zuciyarki. Amma akwai abu guda da ni Jalal nake so ki sani,......" D'ago ido tayi ta dubesa kafin ta kauda kai gefe.
"Jalal yaci gaba da fad 'in" Wllhi wllhi na rantse da mahallici na ban aikata ba......... " Da sauri tasa hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta gamida k'walla k'ara, don kuwa komai ya shiga dawo mata, bata manta wann farin fuskar nasa wanda a idanunta bak'kk'irin yake lokacin da ya soma rik'ota........" Ganin ya kasa controlling d'inta yasa mik'ewa da sauri, tuni ta shiga d'aukan duk abinda ke gefenta tana jifa masa tana fad'in ya fita ta tsanesa....
"Dole Jalal ya fice zuciyarsa cike da tausayinta, Lallai dole su nemi taimakon likitita dole su nemi taimakon *Therapist* dan kuwa abin yayi affecting Zubaidah sosai.......
*********************
*K'asar Gombe*
"Gimbiya Zahida ce kwance saman tapkeken gadonta na alfarma, waya manne a kunnenta da alama da k'awarta take wayan..
" Kai Kausar friend amma nai maki murna, Allah Ya baku zaman lafiya keda angonki Salim.
"Daga d'aya b'angaren Kausar ta murmusa kafin tace " Na gode " Princess Heeda, nidai babban farin cikin da zanyi shine ki halarci bikina...
"Zahida ta d'an ware ido had'i da yin murmushi kafin tace " Friend I can't promise you that, sabida na fad'a maki yanda mahaifina Mai martaba yake, bai barina ina zuwa bikin k'awaye koda a cikin Gombe ne balle har wani gari, idan kinga naje biki toh shakka babu bukin dangine a cikin fada. ..
"Kausar ta d'an juya idanu fuskarta d'auke da murmushi kafin tace " Pls try and ask him nasan shima me yuwa zaizo d'aurin aure, tunda shine babban mutum a gari, kinga fah dukanmu daga gari guda muke, pls Heeda ki kwatanta tambayarsa, Ummi tasa baki, pls pls pls.......
"Zahida ta murmusa kawai dan kuwa duk yanda zatayi bayni wa Kausar bazata gane ba.Dan haka ta amince zata gwada tambayarsa......
"Ummi ce ta turo k'ofar ta shigo bayan Zahida ta gama wayar......
Sameena ce ππΎ
[1/23, 22:15] βͺ+234 803 619 0581β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
25
*Β©Sameena Aleeyou... βπΎ*
_Queen Samy Novels Forum... ππ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Zahida ta fad'ad'a murmushinta sanda Ummi ta zauna gefenta.
"Ummi barka da shigowa ta fad'i tana duban mahaifiyar nata.
"Murmushi mai cike da k'asaita Ummi tayi kafin ta shafi gefen fuskar d'iyar tata tace " Barka Princess, who were talking to on the phone, you seems very happy.
"Zahida tayi murmushi kafin tace " Ummi zaki iya tuna wata k'awata da nace maki we met on facebook.
"Ummi ta d'an juya idanunta kafin tace " K'warai na tuna, ba kince 'yar gidan Tahir Marafa Dukku ba, me neman takaran kujeran shugaban k'asa.
"Zahida tayi saurin gyad'a kanta kana tace " Eh ita fah Ummi, she's getting married in couple of weeks, so..... So.... Ta d'anyi shiru don tunanin abinda take shirin fad'i.
"Ummi ta rik'o hannayenta cikin nata kafin tace" uhum go ahead.
"Dama Ummi tunani nake ko Mai martaba zai barni naje...
"D'an kallonta Ummi tayi gamida sauk'e ajiyan zuciya don kuwa tasan abu ne mai kamar wuya.
"Girgiza kai tayi kafin tace " Zahida kinsan halin mahaifinki, kinsan irin kula da tsaron da yake baki bazai yarda ki tafi wani gari biki ba, bikinma na k'awa duka nasan shima na iya zuwa d'aurin aure amma kinsan bazai barki ba, don haka Karma kisa wa ranki abinda ba samu zakiyi ba. Idan ban manta ba rabonki da yin tafiya mai tsawo tun azumi da muka tafi harami don gudanar da Umra,.
"Zahida fuska a turb'une tace " Ummi ina son sarauta amma ko kad"an banson wann kulle da ake wa matan sarauta, ni shiyasa nafi so ni nazama sarauniyar komai saida iko na, and that's when da zan ringa barin matan babban gida suna fita kaman sauran mata.... "Ganin magaifiyar Tata ta zuba mata ido tana dubanta yasata gyara zama kafin ta jeho wa Ummi tambaya.
"Wai Ummi meyasa Abba nashi kullen yayi tsamari, har yau bai barni naci gaba da karatu ba snn yak'i ya min maganar aure har yanzu. Haba we are in a 21st century fah, ai an daina irin wann sarautar, naga k'awata Mardiya Saraki d'iyar sarkin Katsina kwatakwata Babanta bai masu irin wnn kullen ita da k'annenta, Wllhi Ummi they are leaving their lives like ordinary people..... Amma miyasa Abba yake haka.
"Dafata Ummi tayi kafin ta Kai Dubanta ga hoton jaririn dake ajiye gefen bedside d'in Zahida tace " Meyasa kike ajjiye da wnn hoton.
"Zahida tayi murmushi gamida shafa hoton da hannunta tace " *Hamma Lamid'o Modibbo* saida gaban Ummi yabada damm jin an ambaci sunansa.
"Zahida taci gaba da fad'in" Ummi wllhi wataran nakanji inama ace nima inada d'an uwa ko 'yar uwa, jiya na gani cikin d'akin Madaki na d'auko na kawo shi d'akina, ....
"Ummi tayi kicin kicin da fuska, wai har yaushene iyalanta zasu daina tuna Modibbo Lamid'o, a zahiri baya taredasu amma tabbas a bad'ini yana tare dasu, she wants to get rid of him completely.
"Murmushin da baikai wuya Ummi tayi kafin ta rungumo Zahida tace " Gimbiya Zahida, ke kad'ai kin ishe mu a gidan nan, muna sonki fiye da komai, a dalilin sonki da yawa da mahaifinki ke maki yake maki wann kullen. Dalili na biyu kuwa. Ta sake duban hoton Modibbo kafin tace " Tun lokacin da mahaifinki ya rasa Modibbo yake fatan sake samun magajj, shiyasa koda aka haifeki yake kafaffa da rayuwarki don gani yake kaman kema na iya rasaki.
"Murmushi Zahida ta d'anyj zuciyarta cike da tahsayin mahaifinta, mik'ewa tayi kana tace " Ummi barinje wajen madaki na mata alk'awarin zan shiga tayata hira. Kai Ummi ta gyad' mata kafin tace "A sauk'a lafiya Gimbiya.....
"Zahida ta dubi Jakadiya dake tsaye bakin k'ofa da sauri Jakadiya ta rusuna ta shiga mata kirari, ba tareda tabi takan Jakadiya ba tayi shigewarta don kuwa tak'i jinin matar gaba d'aya.....
"Jakadiya ta shigo gamida duban Ummi cikin ladabi, mikewa Ummi tayi kafin tace "Ki sameni a d'akina, wucewa tayi ba tareda ta tsaya jin me jakadiya zatace ba sabida k'unan da zuciyarta ya shigayi tunda ta kula Zahida gudar jininta ma son wnn maceccen yaron take.
"Tafe take a hanyar da zai sadaka da Babban gwani da kuma b'angaren Madaki kakarta. Kaman daga sama ta hangesa sai sauri yake.
"Murmushi yayi sanda shima ya hangeta, maida masa martanin murmushin nasa tayi kafin tace " Yaya Shatima form where?
"My Lady!!!!! Ya fad'i had'i do sadda kansa k'asa lokacin da yake k'arasowa.
"Kai Ta Shatima ni dan Allah ka daina bani wann girman haka.
"Shatima yayi murmushi kafin yace "Be abunda kike so ba kenn ko kin daina son sarautar ne? Ya k'arashe maganar tensely.
"D'an murmushi tayi kafin tace " kaima kasan bazan daina so ba don ajini na yake kawai dai zan canza tsarin sarautar ne idan na hau....
"Shatima yayi murmushi mai bayyana hak'wara kafin yace " Haka ne Your majesty, gaba daya suka dara kafin yace " Zahida you'll never change, will you?
"Abokina dai yanada aiki.....
"Nan da nan Zahida tayi kicin kicin da fuska tace " Wllhi Karma ka fara, bakasan yanda na tsani wann abokin naka ba......
"Shatima na dariya yace "Au kema kinsan Khalifah jinin sarauta ne, kuma kince bazakiyi aure ba sai saraki toh kinga ai daidain ki knn....
ππΎ
[1/23, 22:15] βͺ+234 803 619 0581β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
26
*Β©Sameena Aleeyou... βπΎ*
_Queen Samy Novels Forum... ππ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
_Dear Lovers kuci gaba da manejin gajerun posts pls, wllhi this days I'm fully occupied ne, will continue adjusting insha Allah .... Luv you allπ_
"Tafiya Zahida ta soma yi ba tareda ta masa sallama ba, .
"Da sauri Shatima yasha gabanta yana murmushi, Harara ta kuma galla masa a karo na biyu kafin tace " Ya Shatima Allah zamu b'ata.
"Still fuskarsa d'auke da murmushi yace " Allah huci ran Gimbiya kuma k'anwata, kiyi hak'uri na daina.
"D'an kallonsa tayi dole tayi murmushi don kuwa bata iya juran dad's da Shattima,
"Idan Gimbiya ta barni zan k'arasa Babban gwani wajen mai Martaba. Ya fad'i yana sadda kai k'asa.
"Murmushi tayi mai fito da asalin kyaunta kafin tace " Saurin me kake ne haka wai.
"Shattima ya d'ago Taliesin hanunsa gamida girgiza su yace " Wllhi kin gani tun jiya Mai Martaba yake expecting wad'an nan takardun ban kai masa ba, gashi aike na zaiyi zuwa Abuja cikin satin nan da zaran ya kammala sa hannu a takardun.
"Jin ya ambaci Abuja yasa Zahida ware idanu, inama Mai Martaba zai bari ta tafi tareda Shattima, sanin abune ba mai yuwuwa ba yasata d'anyi murmushi kafin tace " Ya Shattima kuma yaushe zaka dawo idan ka tafi, ...
"Business trip ne Princess bansan yaushe zan dawo ba gaskiya amma probably bazan wuce sati uku ba.
"Zahida ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace " Shiknn Allah Ya bada sa'a. Murmushi yayi kana ya amsa da ameen snn suka jera suna tafe, har cikin ransu suna k'aunan juna matsayin yaya da k'anwa.
"Shattima d'a ne ga mai girma Waziri, Mai Martaba ya aminta da Shattima sosai sabida hankali da kamala da Shattima kedashi, shiyasa tunda Shattima ya kawo girma ya kammala karatun degree d'insa Mai Martaba ya d'aura sa kan duk wani hidima na kasuwancinsa. Wanda yawan shigowa cikin gidan da mu'amala da ahalin gidan yasa suka sami shak'uwa sosai da Gimbiya Zahida......
********************
"Balele ya kallesa a karo na biyu kafin ya sauk'e ajiyan zuciya yace " Umar kayiwa ka cire yarinyar nan a zuciyarka, bata sonka ta sami madadinka, da ace tana sonka da ta dawo gareka, amma bata dawo ba bata waiwayeka ba, ka k'yaleta tunda ba itace autar mata ba, ka zab'a cikin 'yammatan da suke sonka ka Aura, amma har yaushe zaka bari tunanin mace ya maida ka haka.....
"Umar ya jefa d'an k'aramin dutsen dake hannunsa cikin rapin, kallon wajen yake yana tuna kalan soyayyan da suka sha da Zubaidah a wann waje, yana tuna nan shine wajen had'uwarsu, amma Zubaidah ta mance komai taci amanarsa....
"Kauda kansa gefe yayi kafin yace " Balele kasan irin son da nake ma Zubaidah, kasan itace farin ciki na a wann rayuwar, bazan iya auren wata mace ba face ita, ko kad'an ban tab'a kawo Zubaidah zata iya min abu makamancin haka ba, amma babu komai zan manta ta, zan manta da duk wani abu da ya shafeta, zan tafi na bar wajen nan, zanyi nesa da garin nan, zan fara daga farko a can yanda babu wanda yasanni...... "Ya k'arashe maganar yana nannad'e handkachip d'in da tab'a basa a hannunsa...
"Balele ya dafa kafad'ansa yace " K'warai abokina zaka iya aiki a wani garin ba nan ba da sannu Allah zai cire maka ita gaba d'aya daga cikin zuciyarka, Allah yayi maka jagora.... Bai iya cewa amin ba sai mik'ewa da yayi, a tare suka bar wajen suka nufi cikin gari shida Balele....
*Abuja*
*Dasuki Holding of companies*
_At the conference meeting_
"Da mugun mamaki Alhj Jamil yake bin documents d'in da shakka babu sa hannunsa ne akai, yaushe a ina ya amso wad'an nan kud'ad'e, dafe kansa yayi da hannayensa biyu yana karanto innalillahi.
"Daddy ya kuma tura masa takardun in a furious tune yake fad'in" Why why Jamil, Where do you expect us to get that kind of money, you are nothing but a disaster to business..... Shiru Alhj Jamil yayi bai iya cewa komai ba,
"Sauran shearHolders suka soma maganganu k'asa k'asa.
"Alhj Maina mahaifin Tariq yace " A gaskiya inada kusan 5% a wann company and idan aka samu Bankruptcy zaiyi affecting d'ina sosai don Banki ba yarda zata yi ba WA'adin da ta bada yana cika zata mallake company d'in gaba d'aya, snn Banki ba d'aya ba kuma Bankunan k'asashen waje, so gaskiya inaga zan cire shears d'ina, anyone from the shear holders wanna join me, Ya k'arashe maganar da alaman tambaya.
"Nan masu k'anan shears da manyan shears suka soma k'orafi suma.
"Alhj Kasim da Barr Munir suka shiga basu baki suna nuna masu lallai bazasu bari wann company mai tarin albarka ta ruguje ba.
"Wakilin Alhj Tahir Marafa yayi gyaran murya kafin yace" *Marafah Construction Company* zata saka hannun jarinta, zata ciro 50% daga company d'inta ta saka a Dasuki Holdings, take Daddy ya washe baki farin ciki ya lullub'e sa suka had'a idanu shida Barr Munir, plan d'insu ta tafi daidai... Da haka aka k'arashe meeting Alhj Kasim ya shaida masu lallai shida k'aninsa zasuyi yanda zasuyi su biya wad'ancan kud'ad'en...
"A b'angaren Alh Jamil kuwa k'rjinsa ne ya shiga masa zogi