Showing 120001 words to 123000 words out of 210924 words

Chapter 41 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22915

irin kuka mai tsuma zuciya.... Hugging d'inta yayi very tied har saida yaji wajen ciwonsa na masa zogi kafin ya soma fad'in " Take care okay, just take care of yourself, always remember that you are my world, I love you ultimately kinji sweetheart.... Kar ki mance ko bamu sake had'uwa ba, don't give up kinji..... Ya k'arashe cikin rawar murya.....

"Kuka ta kuma fashewa dashi tana girgiza kai.... Fuskokinsu sunyi jajazir had'e karan hancinsu waje guda yayi ido a lumshe ya aika mata da light kiss kafin yace " I wish you success in your exams, and.. And when ever you thought of me, just say a word zaki ganni a gabanki... Ya k'arashe cikin sigan zolaya....

"Murya na rawa take fad'in" I won't let you down insha Allah, zan tsaya nayi exams d'ina da kyau kaji snn kullum zan rik'a maka addu'a.... Murmushi yayi mai bayyan dimples d'insa kafin yace " I know you will.... Oya come here, kukan nan ya isa haka....Suka kuma hugging juna, sun jima a haka kafin Ansar yayi knocking a k'ofa.....

"Jalal ya kuma damk'a wa Ansar amanar family d'insa kafin suka tafi cikin tsananin kewa da alhini da soyayyan junan su... A ranar haka Jalal ya wuni cikin damuwa da kewar iyalan sa dukda Shattima yana nan tare dashi wuni guda, yanzu Mai Martaba har hutu ya bawa Shattima sabida abokin sa dake asibiti.....

*************


"Dandatson mutanen da ya gani cike a k'ofar gidansu ya tabbatar masa cewa gaskiya ne mahaifinsa ya rasu.... Tun daga nesa mutane ke masa gaisuwa, kan ya isa cikin gida kuwa labari ya riske Innah, wani sabon kuka ya kuma b'alle mata musamman da ta tuna Ummaru shine sanadin ciwon mijin ta....

"Koda ya shigo ciki haka Mata suka ringa masa ta'aziya, wasu kuwa k'us k'us suka ringa yi suna Allah wadai irin arzikin sa wanda yayisu dare guda, wasu ma Allah wadai da haihuwan d'a irinsa suke, don kuwa labarin duniya baya b'uya, maganganu sunyita fitowa iri da kala bayan tafiyar sa....

"Innah ciki ciki ta amsa masa gaisuwar sa snn bayaga gaisuwa babu magana data kuma had'a su, haka ya fito waje ana karb'an gaisuwar dashi ba don yaso ba....

*************

"Wajajen yamma lis suka iso garin Abuja, Su Hadiza sai nan dasu ake sabida jinta take cikin kud'i, shari'a kawai take jira ayi ta tattari d'anta su gudu koda k'asar waje ne.... _(Allah sarki jahilci babu dad'i, da ta san cewa Check d'in bogi Alh Kasim ya bata da bata tsaya b'ata lokacin ta ba..)_

"A wann dare haka Zubaidah ta kwana cikin kewar mijinta, shima Jalal d'in hakan ne ta kasance dashi, ya tuno baccinsu a saman wann gado nasa, Ya tuna beautiful moments da suka kasance ciki, tabbas da ace zata zauna a wann asibiti har ya warke tabbas da ba zaiga jimawar sa ba ....

"Kwana uku aka gama makokin Baffah, Dole Umar Ya tikasta ma Inna saidai ta biyosa su tafi a cewar sa babu mai kula da ita, Innah ta k'ek'ashe k'asa tace fir bazata bisa ba, yaje chan ya k'arata da rayuwar sa... Magiya Umar Ya ringa mata yana nuna mata yayi nadamar duk wasu abubuwab da ya aikata a baya, kafin Innah ta d'an soma sauk'owa daga dokin fushinta, da sharad'in idan ta gama takaba zata bisa.... "Aifah fir Umar yak'i saidai ta bishi yanzu yanzu idan yaso tayi takaban nata a chan...
"Baiko bari tayi sallama da mak'ota ba ya d'auko Innah suka nufo Abuja....


**************

"Hankali kwance take rubuta jarabawarta, kusan kullum sai sunyi waya da Jalal, Ansar da Annah suke kaita su d'aukota, wata rana Ansar da Hamma wata rana kuwa Annah ita kad'ai...

"A kwana a tashi babu wuya wajen Rabbil Izza yau saura satittuka da basufi hud'u ba a koma kotu, ta ko wani b'angare suna k'ok'arin suga Sun had'a evidence d'in da zai kare su ya basu nasara a kotu....

"Yau tunda Ansar ya dawo gida ya had'a uban tagumi yanata faman research, Annah ta sauk'o parlorn k'asan ta samesa, tambayar sa tayi koda abinda ke damunsa, shiru kurum Ansar yayi don yama rasa da wanne zai soma mata.... Jin Annah ta sauk'a k'asa yasa Hadiza sad'ad'owa a hankali ta mak'ale jikin staircase...

"Ansar ya dubi Annah da kyau kafin ya sauk'ar da nannauyan ajiyan zuciya yace " Annah we are running out of time, komai ka iya faruwa a kotu, muddin bamu sami likitan da yayi treating Zubaidah ba Kotu bazata amince da mu ba, snn zata bayar da belin su Salim, yanzu haka daga Prosecution office nake, Prosecutors ya tabbatar min this is the only way for us to win, sai ko kuma su Labib sunyi confessing laifinsu... Annah I'm completely lost, I don't wanna fail Zubaidah and Jalal, in the next three weeks za'a sallami Jalal, what if I couldn't make it...... Ya soma girgiza kai shi kad'ai....


"Annah ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace " Ansar muna da hop guda d'aya, Tariq, Tariq zai iya confessing gaskiya, sabida a yanda naji yak'i bada had'in kai wa Barr Munir, snn su kansu The Dasukis and the Maina'a are not in good terms, so na tabbata they will go against each other k'arshe......

"Shiru Ansar yayi yana nazari kafin ya fuzar da iska yace " I must see Tariq , ina so nasan meye ke cikin mind d'insa, dukda nasan confession d'insa abune mai wuya don Alh bazai bari ba, he'll threaten his parents, I know that imbecile is capable of anything.... Amma insha Allah I'll do all my best, I won't rest until I see Kasim Dasuki spending his last day behind bars....

"Mik'ewa yayi yana duba agogon hannunsa kafin yace " Yanzu zan tura Hafiz Dukku, idan ma ministry of health zamuje duk zamuje a binciko mana that miserable Dr, amma kafin nan zan tafi prison na ga Tariq.....


"Annah ta gyad'a masa kai kafin tace " Allah Ya baka nasara Ansar, Allah d'aura mu bisa azzalumai..... Ameen Annahn mu... Ya amsa da fad'in haka kafin ya fice........


"Ya jima yana zaune wajen ganawa da mutane, har ya cire ran Tariq bazai fito ba sai gashi ya fito cikin uniform d'insa na prisoners, Ya jima yana k'arewa Ansar kallo kafin ya k'araso yanda yake.....

"Ansar ya sakar masa murmushi kafin yace " Bismillah zauna.... Babu musu Tariq ya zauna ba tareda ya furta koda kalma guda ba......

"Ansar yayi gyaran murya ya soma magana, still Tariq bai ce masa komai ba sai k'ura ma waje guda idanu da yayi...... Duk iya k'ok'arin Ansar na ganin Tariq ya masa magana Tariq bai yi ba, tunda ya zauna a wajen tamkar dutse baice k'ala ba, hakan ne take kasancewa dashi a duk lokacin da wani ya kawo masa visit..... Daga can Mum ta hangi Ansar zaune da Tariq k'irjinta ya yanke ya fad'i... Gudu gudu ta fice ta shiga neman layin mijinta wanda basa tare a yanzu.....


"Ba don yaso ba ya d'aya wayar nata cikin hasala, yana zaune cikin office d'insa dake Dasuki Holding..... "Cikin daburcewa take sanar dashi taga Lauyan Zubaidah da Tariq, ..... Ai bata kai aya ba Dad ya mik'e cikin tsananin tashin hankalk, don kuwa Dr ya sanar dashi Tariq ya sami minor tab'in hankali na rashin magana a dalilin accident d'in da yayi, Ya sami internal bleeding wanda duka sun masa aiki sun cire jinin, zai kwashi watanni kafin ya dawo normal....

"A guje Alh Maina ya nufo lift suka yi kicibus da Alh Kasim.... Take ya labarta masa abinda ke faruwa.....


"Cike da tashin hankali Alh Kasim ya shiga neman Faisal, a tare suka fice gaba d'aya daga company d'in cikin tsananin tashin hankali....
"Waya Alh Kasim yayi ma Barr Munir yace maza ya nufi prison and stop Ansar from talking to Tariq..... Shi kad'ai Ya ringa bubbuga car seat yana sunbatai kaman tab'abb'e.....


"Tun daga nesa Barr yake gudu kaman zai kifa da k'asa ya cakumo Ansar saida ya Mike tsaye babu shiri kafin ya soma fad'in" How dare you talk to my client you idiot.... Ansar ya fincike wuyar rigar sa daga rik'on da Barr Munir ya masa yana fad'in" Let go of me you good for nothing..... Nan hankulan gandurobobi ya dawo kansu suka soma k'ok'arin rabasu....

"Barr Munir yaci gaba da fad'in" Don't you ever let this imbecile come near my clients again or I'll press charges......

"Go ahead Attorney, ka shigar da k'ara idan ka isa, let me remind you this, wllhi Allah bazai barku ba, dukkan ku sai kun girbe abinda kuka shuka......


"Munir yana murmushi da gefen bakinsa yake fad'in " We shall see young Attorney..... Ficewa Ansar yayi daga wajen ganin tuni Tariq ya koma ciki....



"Barr Munir yaja gefe kafin yayi dialing lambar Faisal yace " Get your boys ready he's on his way right now..... Daga haka ya katse wayar yana wata mayaudariya murmushi.....





Sameena ce ๐Ÿ‘Œ๐Ÿพ
[1/23, 22:27] โ€ช+234 803 619 0581โ€ฌ: ๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜ *ZUBAIDAH*

69

*ยฉSameena Aleeyou...โœ๐Ÿพ*

_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION ๐Ÿค_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*





"Gudu yake kan falfalawa bisa kwalta ba tareda sanin wasu na biye dashi ba, saida yayi nisa sosai ya iso yanda babu mutane sosai kafin ya lura motar bayansa binsa suke.... A hankali ya soma rage speed yana k'ok'arin ciro wayarsa kwatsam sai ganin mota yayi ta sha gabansa.....
"Cikin sauri Ansar ya danna birki yana karanto innalillahi wa inna ilahirraji'un....
"Fuskokin su rurrufe da mask suka fito suna pointing d'insa da bindiga d'ayan ya jawosa ya fidda sa yana fad'in" Move.... "Ansar gaba d'aya ya rasa gane meke faruwa... Cikin dakewar murya yake fad'in" Me kuke nema a wajena.... Bai kai aya ba d'ayan ya danna kansa cikin mota yana fad'in" Shut up idiot... Da sauri suka saka masa Blindfold suka rufe masa idanu.... "D'ayan yace " Tony get his ride, Okay Boss Tony ya amsa kafin ya nufi motar Ansar.... "Cikin mintuna k'alilan suka bar wajen da gudun gaske uwa masu shirin tashi sama....

"What do you want from me, where the heck are you taking me to...??? Ansar ya tambaya cike da confidence...

"Shut your mouth you idiot, waya baka daman magana...? Cewar d'aya daga cikin su....
"Dukda idanunsa suna rufe yasan tabbas sun kwashi tafiya mai nisa....


"Suna isowa haka suka ringa hankad'asa suna fad'in" Move....
"Hannayen sa a d'dd'aure suka yasar dashi gaban Alh Kasim.....

"Murmushi Alh Kasim yayi kafin yace " Ku bud'e masa idanu, babu musu sukayi yanda yace...


"Ansar ya d'ago idanunsa da suka masa nauyi yana duban wajen da aka kawo sa da kuma mutumin dake make saman kujera a gabansa..... " Wani huci kawai yake ya yunk'ura zai kai capka wa Alh Kasim yana fad'in" You worthless imbecile....... "Da sauri d'aya daga cikin boys d'insa ya zaunar da Ansar ta hanyar kai mai naushi a ciki... "Babu yanda Ansar ya iya coz sun d'dd'aure mai hannu....


"Alh Kasim ya d'aga masu hannu alamun su k'yalesa... Takowa yayi har gaban Ansar kafin yace " ANSAR MA'ARUF KUMO, Am I right.... "Wani fincika Ansar ya kuma yi, komai ya shiga dawo masa, rasa family d'insa da kalan k'uncin rayuwa da Alh Kasim yayi sanadin shigar sa ciki.... Da kakkausar murya yake fad'in" Don't you dare call my fathers name again you miserable coward....

"Murmushi Alh Kasim yayi kafin yace " Gaskiya ne you're really his son... Saida ya d'an d'au lokaci kafin yaci gaba da fad'in" Attorney na kiraka nan ne mu samu peace nida kai..... "Hararansa kawai Ansar keyi ba tareda ya iya furta komai ba sai jini dake fitowa daga hancinsa.... "Yana huci ya soma fad'in" K'arya kake Alh Kasim bazaka tab'a samun peace da kowa ba, snn bazaka tab'a samun kwanciyar hankali ba until you paid for your damn crimes, you are a murderer, nasan ka kawo ni nan ne don ka kashe ni, go ahead and fulfill your mission, don na rantse idan ina numfashi sai ka tafi jell, and you'll spend the rest of your damn life there... Bai kai aya ba Alh Kasim ya wanka masa wata marin da saida jini ya tsattu daga bakinsa.....

"D'agowa Ansar yayi dukda galabaitan da yayi bakinsa bai mutu ba, yaci gaba da fad'in" I was even surprised da naga baka kashe ni ba tuntuni, coz you're not human, you're an Animal, a heartless being who doesn't...... Tasss...! Kake ji Alh Kasim ya kuma d'aukesa da Wata mari..... Kamo hab'an Ansar yayi yana huci yayinda Ansar d'inma ke huci .. Alh Kasim yaci gaba da fad'in" How dare you, you little brat, na gama da mahaifin ka ma balle kai, da ina son na ganka a mace da tuni ka mutu, but I don't wanna ruin my plans, I'm asking you nicely and politely withdraw the case, vanished disappeared get lost.... Zan baka duk wani dukiyar mahaifin ka da Ya rasa su a dalilina, zan baka huge amount of money ka tafi wani k'asar and start a fresh there...... Bai kai aya ba Ansar wanda zuciyar sa take kan faman tafarfasa ya tsatta masa miyau a fuskar sa... Cikin karaji yake fad'in"
"You are unbelievable Kasim Dasuki, you're the worst creature I've ever seen.. How dare you, har kanada gots da zaka kalli cikin idona ka gaya mun wad'annan magan ganu, you're an insane, tell me zaka iya dawo mun da mahaifiyata zaka iya dawo mun da mahaifi na, can you bring me back my two siblings.... Telllll meeee can youuuuu.....??? Ya k'arashe cikin wani irin murya mai firgitarwa idanunsa sunyi jazir sai zuban ruwa suke.... "Ansar yaci gaba da fad'in" Of course you can't... " Ba kowa bane irinka mai son kansa da son abun duniya, snn shari'ar Zubaidah bazan yi watsi dashi ba har sai mun kai bango, Allah zai had'a mu a kotu ranar da idon marassa gaskiya zai raina fata...... "Alh Kasim ya kuma d'auke sa da mari me kayu kafin yace cikin karaji... " You'll live to regret this Attorney, you've no clue who you really messing with, ... Ya kuma yin murmushi kafin yace " I'll see you in court Attorney, let's see who would win... Daga haka ya juya ya kalli boys d'insa kafin yace " Get him outta here..... Daga haka motarsa shima ya nufa....


"Kaman yanda suka d'auko Ansar ido a rufe haka suka fiddashi daga wajen, can gefen kwalta suka ajjiye mai motar sa snn suka jefar dashi gefen motar...

"Ya jima yana durk'ushe a wajen yana share jinin hancinsa kafin ya tashi da k'yar ya nufi motar, ko kad'an baiso su Annah su gane abinda ya same sa don kuwa hankulan su tashi zaiyi, don haka kai tsaye gidan su Hafiz Ya wuce......

**************

"Alhamdulillah, Zubaidah ta k'are jarabawar ta saidai fatan samun nasara, sosai kowa yayi mata murna ciki harda Hadiza dukda na ciki na ciki, hakan tayi daidai da saura sati biyu cif a koma kotu, snn washe gari ake saka ran sallaman Jalal daga asibiti, wani dad'i take ji maras misaltuwa, ji take she's ever ready to show her husband how she loves him, tabbas yanzu kam ta gama yarda she's into him irin totally d'in nan, fatan ta Ya dawo su gina rayuwar su snn mak'iyan su su sami abinda ya dace dasu, they will insha Allah finally have peace, .... Ita kad'ai take murmushi tana aikin gyara masa d'akin sa, a haka Annah ta shigo ta tadda ta suka ci gaba da aikin tare suna hira cikin annashuwa da jin dad'i gwanin ban Sha'awa.....


"Innah ki kwantar da hankalin ki tafiyar nan ba jinawa zanyi ba sann na fad'a maki oga na idan ban je ba zaiyi fushi dani, kinji ki kwantar da hankalin ki.....

"Innah ta sauk'e ajiyar zuciya kafin tace " Toh shiknn Baba Wuro, Amma kai shiknn bazaka ajiye iyali ba wacce zata ke dafa mana irin abincin da muka saba ci, kaga nidai ban saba da irin wad'an nan abinci na turawa ba, snn kaima ka girma da yawa ya kamata ka ajiye iyali nima naga 'yan jikoki nah......


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login