Showing 108001 words to 111000 words out of 210924 words

Chapter 37 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22872

I.... I just couldn't help it ne, I still can't believe my Pappy is gone...... Ta k'arashe cikin sheshshek'an kuka.....

"Rungumota Mumsy tayi kafin itama tayi bursting cikin kuka saida sukayi mai isansu kafin suka zauna bakin gado.....

"Mumsy ta rik'o hannayen Kausar kafin ta soma fad'in" Dear I know exactly how you feeling, but what you did lately was wrong, it doesn't suite you at all... Yau da Pappyn ki zai tashi yaga irin abunda kikayi bazaiji dad'i ba, snn nima banji dad'i coz I'm also suffering... Your Father was the great love of my life..... But I had to accept the fact that he's gone.... Ki kasance mai tawakkali Allah yana son masu hak'uri, snn duk wanda ya zalunceka a duniyar nan kaine a saman sa... Ki bari hukuma tayi aikinta wann ba field d'inki bane tunda they are already investigating the matter....
"Kiyi hak'uri kiyi hak'uri kinji Kausar kiyi ma mahaifinki addu'a shi kid'aine abinda yake buk'ata daga gareki a yanzu kinji daughter...... Gyad'a kanta tayi tana share hawayen idanunta da bayan hannunta kafin ta rungume Mumsy very tied kana tace " Mumsy pls stay here with me for a while.... Murmushin k'arfin hali Mumsy tayi tana shafa kanta kafin tace " I'll always be here for you sweetheart, together we will overcome this horrible tragedy.., Asmah dake tsaye bakin k'ofa ta goge hawayen da suka zubo mata, tausayin family d'inta yana ratsa ta b'argo da tsoka, she needs to be very strong, her family needs her now more than ever.....๐Ÿ˜ช

*****************

"Sai faman masifa yake shi d'aya yana huci, lek'owa ta d'an tsakiyar mota yayi ya dubi Faisal dake front seat kafin yace " Faisal are you sure you did a clean job, na fad'a maka bana so wani suspicious yayi linking d'ina da abinda ya faru, coz I've had enough already, dealing with the issue of those kids ma ya isheni, bana so na sake fad'awa wani court case coz a halin da ake ciki yanzu our company is not financially stable....

"Faisal ya d'an karkato yana kallon baya kafin yace " Boss you don't have to worry about that, let them go ahead and press the charges, sune a rana, coz basu da wani evidence against you..... Dariyar da Barr yayi ne ya katse su.... Daddy ya karkato yana dubansa alamun yana jiran amsa yaji dariyar me yake.....

"Barr yaci gaba da fad'in" Ai a halin yanzu ba shigar da k'ara bane a gabansu, su samu su wanye da masu hannun jari a company d'insu, sabida idan wasu sunyi hak'uri wasu bazasu yi hak'uri ba, Alh Tahir was a very wealthy man, yanada hannayen jari a k'asashe daban daban snn yana banking da bankuna a k'asashe daban daban a duniya, a lokacin da mukayi Business partnership with his company Attorney na Company d'insu ya bani wasu documents duk wani breakdown na business dinshi was written on that document..... So I suggest mu ringa bin k'afafun Employees d'insa da kuma shear holders na company d'insa a hankali muna nuna masu muna influencing nasu muna persuading nasu muna nuna masu cewa lallai lallai kar su yarda, Hajiya Raliya sai ta fito masu da kud'insu da sukayi asara, daga nan mujasu a jiki su zuba kud'ad'ensu a company d'inmu tunda dama we are at risk of going bankrupt, so kunga basu da wani lokacin shigar da k'ara koda ace zasu san gaskiya ma, wancan issue d'in zaiyi distracting nasu.....


"Tunda ya soma magana Alh Kasim ke binsa da kallo lallai ya yarda Barr abokin tafiya ne.... Dariya ya fashe dashi harda cire hula kafin yace " You are just an incredible Attorney , wann yayi , you should start working on that right away, kayi copying document d'in a computer ka fara spreading nashi to their Emails....
"Wata silent murmushi Barr yayi kafin yace " You don't need to tell me what I should do, You can trust me on that.... Shigar da k'ara shine babban kuskuren da Haj Raliya da d'iyarta zasuyi....



"Ganin motocin police a k'ofar company d'insu ya basu shock dukda sun san hakan ka iya faruwa.....


"Motarsu tana gama parking securities suka shiga bud'e masu.... D'aya daga cikin securities d'in na company d'insu ya soma fad'in" Sir we got some police men here, they said they are here to interrogate you Sir.. Gyad'a kai yayi kafin yace let them in....


"Tambayoyi Police suka masa gameda k'onewar company d'in abokinsa da kuma mutuwarsa, snn suka ce zasu iya dawowa any moment, Daddy yace " You are always welcome, Im willing to cooperate with you duk lokacin da kuka dawo, what I can't take shine wann ridiculous acquisition d'in da 'yar marigayi take mun, I should hve press charges against her amma sabida zaman mutunci da kuma alkhairin da ya faru tsakani na da mahaifinta shiyasa nake d'aga mata k'afa.... But next time I won't tolerate such scandal...

****************

*Police station*

" Sunyi jigum suna jiran feedback,Ansar sai faman kai komo yake yayinda Zubaidah da Annah suketa faman bin mutanen dake shige da fice da kallo...

"DPO ne ya fito tareda Ansar, suna tafe suna magana, Detective Amir shine cikon na ukun su,..

"Zubaidah kam tunda ta hango fuskar Ansar ta cika da damuwa tasan tabbas something is definitely wrong, mik'ewa tayi zata nufesu Annah tayi saurin rik'o hannunta tace " Mu jirasu a nan Daughter...

"Kallon Annah ta d'an yi fuska cike da damuwa kafin ta koma ta zauna tana mai bin umarninta, Zuciyarta bai daina bugawa da sauri da sauri ba, ita kad'ai take dunk'ule 'yan yatsunta tana bud'e su tunani kalan daban daban suka shiga zayartan kwanyarta... Har Ansar ya k'araso wajen bata sani ba saida taji salatin Annah kafin tayi saurin d'ago kanta a zabure tana dubansu.... Ganin hawaye na fita daga idanun Annah ya kuma firgita Zubaidah...

"Kuka ta fashe dashi tana fad'in" Sun kashe shi koh, nasan bazasu k'yalemu ba.... Annah ina yake I want to see him, pls take me to him....... Sosai Annah ta rik'eta tana girgiza kai itama tana hawayen take fad'in" Basu kashesa ba Zubaidah, Jalal na nan a raye.... amma sunyi masa illa sunji masa rauni.....

"D'agowa tayi tana duban Ansar wanda ke nan tasye jugum snn tace "Where is he? ...
" K'ak'aro kalamai yayi ya d"aura saman harshensa ya soma basu labarin duk abunda ya faru according to yanda ya sami labarin, snn ne yake tambayar su ko sun san Shattima, nan Annah ta fad'a masa alak'arsu da Shattima.

"Ansar ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Gobe da safe insha Allah zamu wuce gomben, a halin yanzu police are investigating the issue, na fad'a masu main suspect d'inmu Alh Kasim Dasuki ne sabida shika da grudges against Jalal, zasu tafi suyi interrogating nashi right away.... "Ya d'an ja fasali kafin ya shafi sumar sa yace " Annah to be honest with you zamanku a Suleja is risky considering the situation, kunga irin abubuwan da suketa faruwa a kwana biyun nan, Alh Kasim is capable of anything. He's a a monster, he do not have a heart, who knows what he's up to, especially yanzu da idon duniya ta masa cha, mutane sun soma gane wanene shi...

"Annah ta sauk'e ajiyan zuciya takai dubanta ga Zubaidah wacce har lokacin hawaye take da alama bata tare dasu tayi nisa wani duniyan...

"D'agowa tayi ta dubi Ansar kafin tace " Barr ina zamuje wa muke dashi cikin Abuja....

"Ansar ya d'an Saki murmushi kafin yace " Haba Annah don't talk like that zaki sa naji kaman har yanzu nida ku bamu zama d'aya ba,

"Gidana wadacecce ne, zan iya komawa chan sashen baki sai na bar maku cikin gidan kuyi zamanku har zuwa lokacin da zamu kammala Shari'an mu.... Yanzu bari na kira Hafiz ya taho da mota idan yaso sai ya d'auko su Hamma, kuma sai muje ku d'auki duk wasu kayan amfanin ku for the meantime.....
"Wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Hafiz gamida matsawa d'an gefe kad'an...



"Annah kam kallo ta bisa dashi cike da mamakin mutunci da karamci irin na Ansar, Allah sarki tausayinsa na rashin iyayensa da 'yan uwansa ya cika zuciyarta, tabbas yau da iyayensa na raye zasuyi alfahari da samun d'a kaman Ansar, Allah yaci gaba da karesa daga sharrin masu nemansa da sharri, Tabbas addu'an Alkhairi shine kurum zasuyi ma Ansar dun ko kusa bazasu iya biyansa abubuwan da yayi masu ba....



******************


"Tunda suka shigo gidan su Hadiza sai washe baki ake ana d'add'ana kujeru, Kamal ma ya tab'a wann flower vase d'in ya tab'a wancen, sai kalle kalle da d'an k'uyanci suke, Ansar ya nunnuna masu d'akuna da komai da komai, harta su kitchen su Store kayan buk'ata na abinci da sauransu, gidan nasa babu laifi ya wadace su ba tareda tak'ura ba.. Zubaidah kam kallonsu kawai take burinta bai wuce gari ya waye ta ganta a garin Gombe ba...

"Bayan ya gama nuna masu ko ina ya sauk'o downstairs ya nufi d'akin bak'i ya karkad'e ko ina ya shiga jera kayansa a wardrobe, yana cikin shirya kayan wayan Asmah ya shigo masa, " Bayan sun gaisuwa irin ta masoya ta cika sa da shagwab'a shiko sai biyeta yake yana lallashinta snn ne ya soma fad'a mata abubuwan da suke faruwa har kwaso familyn Jalal da yayi ya dawo dasu gidansa, da kuma maganar tafiyarsa Gombe a gobe idan Allah ya kai rai...


"Sosai hankalin Asmah ya tashi da jin abinda ya sami Jalal, oh when will all these end, ta furta a hankali....
"Cikin sanyin muryarsa taji yace "Soon insha Allah my Love, zamuyi auren mu cikin sabuwar duniya maras rikici da fargaba da izinin Allah......

"Haka kurum taji jikinta yayi sanyi, cikin sanyin murya tace " Allah yasa my Attorney, murmushi yayi gaimda lumshe idanu kafin yace " Ameen my Attorney, kiyi bacci I'll call da safe kafin mu wuce kinji.. ..
"Sallama sukayi kafin suka katse wayar.... ..

"Kwance take saman gado rungume da rigarsa, tunaninsa ya ringa yawo a k'irjinta, ko wani hali yake ciki...... Ta goge hawayen da ya zubo mata gamida k'ank'ame rigarsa, tayita tuno abubuwan da tayi masa a baya, ta tuna irin hak'urin da yi da ita, ta tuna irin fad'i tashin da yake don ganin rayuwarta ta inganta, ta tuna irin sadaukarwa yake kanyi duk a saboda ita.... Kai anya ta cancanci Jalal, anya bai cancanci sabuwar mace ba wacce babu wani Mahaluk'i da ya lalata mata rayuwa,.... Take taji gaba d'aya she's feeling ashamed tabbas ta yarda tana son Jalal, amma tana tunanin ranar da za'ace ta soma rayuwar aure da Jalal,...... Girgiza kai ta soma da sauri tana mai dad'a k'ank'ame hannayenta had'i da runtse idanu, don kuwa wann tunani ba komai ya haifar mata ba, sai gano fuskokin su Labib da take cikin idanunta.... A haka Annah ta shigo ta sameta, ta zauna gefe da ita ta shiga lallashinta tana nuna mata addu'a shi zaiyi masu maganin damuwarsu ba kuka ba.... Mik'ewa Zubaidah tayi ta nufi bathroom don yin alwala tabbas Allah shine maganin komai.....



"Washe gari Annah har ta tashi ta had'a masu breakfast. Ansar ya shigo cikin shiri yana fad'in" Wow daga ina wann aroma d'in ke fitowa, Murmushi Annah ta sakar masa kafin tace " Good morning, oya have a seat....

"Zama yayi d'aya daga cikin kujerun Annah ta shiga serving nasa tana jansa da hira....... "Jin yayi shiru baya amsawa yasata d'ago kai tana dubansa, k'walla ta gani tab idonsa ya k'ura ma abincin idanu....

"Kujera ta d'an jawo ta zauna chan gefe dashi kafin tace " Ansar are you alright....?

"D'an goge k'wallan idonsa yayi ya k'a'karo murmushi kafin yace " I'm fine Annah, it just that you remind me of my Mum,.... You sounds like her, and she cooks delicious food, I missed her so much, inama tana nan a yanzu nayi devoting entier life d'ina wajen kyautata mata, even though nasan bazan mata kwatankwacin sadaukarwar da ta min ba sanda nake yaro,..... I couldn't have chance to be with her, all of them ....

"Tausayinsa ya cika zuciyar Annah, wani sabon tsana Alh Kasim ya kuma wanzuwa a zuciyarta, a hankali ta soma fad'in" Ansar kai d'a na gari ne wanda ko wata mahaifiya zatayi alfahari da kai, nasan addu'an alkhairi da kake masu yana isa garesu, snn shi wanda yayi sanadinsu bazai tabbata a doron k'asa yana zalunci ba, da sannu Allah zai kawo k'arshensa....

"D'ago Kai yayi yana gyad'awa kafin yace " Hakane Annah insha Allah k'arshen Kasim Dasuki yazo snn zai girbe duk wani abinda ya shuka.......




"Hadiza dake lab'e a k'ofa jinjina kai ta soma cikin zuciyarta take fad'in" Kenan duk yanda akayi Alh Kasim nada sa hannu a mutuwar iyayen Ansar..... Murmushi ta soma a hankali cikin ranta taci gaba da fad'in" Kai haba ai biri yayi kama da mutum, shiyasa ya tsaya kai da fata ganin Zubaidah taci wann shari'a bayan ba biyansa ko tasi ake ba, idan kuwa hakane lallai zatayi amfani da wann damar,.... Ta k'arashe zancen zucin nata tana mai kai duvanta ga family pic d'in Ansar dake ajiye saman console a corridor d'in..... Jin k'aran tafiya alamun ana sauk'owa daga stirs yasata saurin saita kanta ta k'arasa cikin parlorn suka soma gaisawa da Ansar da kuma Annah, sai faman fari'a take uwa gonar auduga....

"Zubaidah ce ta sauk'o parlorn ciki shiri itama, tana sanye cikin red atampa mai touches d'in sea blue, ta d'aura sea blue hijab wanda yake daidai gwiwarta, tayi matuk'ar kyau duka she's looking pale, da gani kasan she had a sleepless night.... Annah ta sakar mata murmushi suna masu amsa sallamarta itada Ansar yayinda Hadiza ta bita da wani mugun kallo k'asa k'asa.... Bayan sun gaisa Ansar kam d'aukan abincinsa yayi ya koma cikin parlorn ya zauna yana ci, nan Hamma ma ya fito ya zauna tareda Ansar suka ci abinsu tare, sosai Ansar kejin dad'in hira da Hamma...

"K'arfe tara da wasu 'yan dak'ik'ai na safiya suka d'auki hanyan Gombe, har waje Hamma da Hadiza suka raka su gamida masu fatan alkhairi snn suka bada sak'on gaisuwarsu a isar ma Jalal...
"Ansar kuwa saida yaja kunnen danga security dake masa gadi sosai da sosai, yace ya kula da Al'amarin tsaro sosai...



. "Suna tafiya Hadiza tayi shirinta tsaf ta had'a Hamma da Kamal da kallon tashan gwaigwai na yara (cartoon) tace bari taje kasuwa ta sayo masu kayan miya na fridge ya k'are...

"D'aukan k'aramin hoton dake ajjiye saman console tayi ta b'oye cikin jakarta kafin tayi ficewarta......





Sameena ce ๐Ÿ‘Œ๐Ÿพ
[1/23, 22:26] โ€ช+234 803 619 0581โ€ฌ: ๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜ *ZUBAIDAH*

64

*ยฉSameena Aleeyou...โœ๐Ÿพ*

_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION ๐Ÿค_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*


*A Big Shout Out To All The Readers ๐Ÿ˜ป*




"Zaune yake gaban Mai Martaba, Ya tattaro nutsuwarsa gaba d'aya ya had'e waje guda, kan nan nasa duk'e a k'asa, kallo guda zaka masa ka gane ramar da yayi.....

"A hankali Mai Martaba ke karantar canzawan da Shattima yayi a 'yan kwanakin nan, yana son Shattima yana jinsa tamkar d'an da ya haifa, ko kusa baison ganinsa cikin wann yanyi... Ajiye takardun hannunsa yayi saman makeken darduman Alfarma dake malale a parlorn kafin yayi gyaran murya ya kirawo sunan Shattima da ainihin sunansa had'i da jefo masa tambayar da yasa gaban Shattima mugun fad'uwa...

"Abdullah...... Shin akwai abunda ke damunka ne.???


"Shattima ya d'an daburce yama rasa me zaice, don kuwa magana ta gaskiya bazai iya fad'awa Mai Martaba son tilon d'iyarsa yake ba, toh ma ta ina hakan zata kasance bayan har an bayar da Zahidah..... Muryar Mai Martaba ya kuma jiyowa yana fad'in" Abdullah kai d'ana ne , ka fad'a mun idan akwai abunda ke damun ka, ko tafiya Kanon ne baka shirya ba...... Ai Mai Martaba bai kai aya ba Shattima ya soma girgiza kai yana fad'in" A'a Abba dama... Ya d'an ja aya.... K'irjinsa yaci gaba da bugawa sabida k'warjinin Mai Martaba ya wuce gaban ka masa k'arya. Take dabara ta fad'o masa ya tuna kan Ya shigo an masa waya ana nemansa a asibiti patient d'insa ya farka.... Nan Ya soma fad'in"

"Abba dama...emm dama akwai wani abokina da 'yan fashi suka taresa a hanyarsa ta zuwa garin nan suka masa duka to the point of death, yanzu haka yana asibiti yana receiving treatments..... snn bashida kowa a garin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login