Showing 42001 words to 45000 words out of 210924 words

Chapter 15 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22918

kanka Tariq ni ba ajinka bane kuma kar ka sake nemata daga yau kashe wayar tayi gamida yin k'wafa....


"D'an gajeren tsaki yayi kafin yayi dialling lambarta, saida ya kira sau uku tana ejecting kafin a na hud'u ta d'aga tana wani yamutsa fuska, hak'uri ya soma bata yana lallashinta, da k'yar ta hak'ura kafin yace " Tayi hak'uri yanzu haka Dad d'insa ya aikesa ne urgent, he can't fetch her but he promised da zaran ya gama da Dad dinsa zaizo...

"Tana kashe wayar taja tsaki a fili ta furta k'aramin d'an iska,
"Tana fitowa gate ta hangesa har lokacin na tsaye bakin titi. Murmushi tayi kafin ta k'arasa wajensa....




"A firgice ya farka daga mummunar mafarkin da yayi, rufe fuskarsa yayi da tafukan hannayensa kafin yayi addu'a, mik'ewa yayi ya lek'a barrandan Annah, zaune ya hangosu ita da Annah suna duba litattafan da aka sayo mata na makaranta daga gani zaka gane suna cikin farin ciki, don ya nuna a fuskokinsu, sauk'e ajiyan zuciya yayi yana tuno mafarkin..

_"Wai gashi nan rataye da jakarsa zai tafi, har ya soma nisa yajiyo muryar Zubaidah tana k'walla masa kira, juyowar da zaiyi yaji ta rungumesa cikin jikinta, a hankali yaji tace "Na yafe maka Jalal duniya da lahira, rungumeta sosai yayi cike da farin ciki ta rakosa har k'ofa, har ya shige mota tana masa waving tana murmushi...... "Gefe da ita kwatsam ya hango Labib Salim da kuma Tariq suna Torrik'e da makamai suna wani irin dariya.... Da sauri ya fito daga motan ya nufota saidai kafin ya k'araso ya hangi tsohon saurayinta Umar ya sureta da k'arfin gaske yasa gudu, ihu take tana kiran Jalal, saidai kafin ya k'araso mota tabi kansa...._

"A hankali ya sauke ajiyan zuciya, ya dubi 'yar k'aramar agogon dake mak'ale bangon d'akin ya nuna k'arfe 5:30 na yamma, bathroom ya shiga ya sakar ma kansa shower sabida zafin da ake sosai a garin....


"Fitowa yayi cikin shiga ta k'anan kaya, sun karb'esa sosai, hayi taje gashinsa da yasha aski da gyaran fuska Wanda ya fito da asalin kyaunsa, kallo d'aya ta masa ta d'auke kanta sanda yake nannad'e hannun rigarsa, tsuka taja a hankali take annurin fuskarta ya d'aukewa ga wani irin fad'uwar gaba data tsinci kanta dashi. D'an karasowa yayi yana satan kallonta yake gaida Annah, Hadiza ne da d'anta Kamal suka shigo.
"Kamal ya tafi da gudu ya rungume Jalal yana fad'in "Uncle Jay, rungumesa Jalal yayi yana dariya ya d'agasa sama yana masa wasa, da gefen idonta ta saci kallonsu, sosai Kamal da Jalal suka shak'u......

"Gaisawa suke da Annah amma hankalinta naga Zubaidah dake faman shirya littafan gabanta, tab'e baki Hadiza tayi kafin ta dubi Jalal da har lokacin wasa yake da Kamal kafin yab'e baki tace "
"Ni ban tab'a ganin irin wann aure ba, ace miji bashida iko da matarsa halan kai ka bata izinin komawa makaranta, ta k'arashe maganar tana duban Jalal,..
"Mik'ewa Zubaidah tayi tana binta da mugun kallo kafin tace " Ni ba matar aure bace kar ki sake kirana matar aure, daga haka ta kwashi books din ta wuce d'aki kaman zata tashi sama..... "Dariya Hadiza ta kwashe dashi harda rangad'a guda, burinta knn dama ta k'untata wa Zubaidah....
"Daga Annah har Jalal kallo suka bita dashi, Jalal ya girgiza kai kafin ya sauk'e Kamal dake kafad"ansa yabi bayan Zubaidah......



Sameena ce ๐Ÿ‘Œ๐Ÿพ
[1/23, 22:17] โ€ช+234 803 619 0581โ€ฌ: ๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜ *ZUBAIDAH*

31

*ยฉSameena Aleeyou...โœ๐Ÿพ*

_Queen Samy Novels Forum...๐Ÿ“–๐Ÿ“š_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*



"Da saurin gaske ya finciko hannunta ta fad'o jikinsa, wani irin yanayi suka shiga su duka biyun,..Yanda k'irjinta yake bugawa da sauri kuwa har cikin jikinsa yake ji.....
"K'ok'arin k'wace kanta ta shiga yi da iyakan k'arfinta tana fad'in ya cika ta,
"Kallonta yake fuskarsa a tamke kafin ya shiga jan hannunta.....
"Tirjewa take tana fad'in "Malam ka cikani nace, ni ba 'yar iska irinku bane, dalla cika ni ina zaka kaini..... Bai kuma saurarenta ba sai suranta da yayi ya azata a kafad'a had'ida toshe bakinta da hannunsa.....
"K'ok'arin ihu take kanyi tana neman hanyar k'watan kanta, Bai ajiyeta a ko ina ba sai d'akinsa.....
"Innalillahi jikin Zubaidah ne ya soma kyarma sosai, take ta shiga tuno fuskokinsu, jada baya ta soma yi tana jawo rigarta tana k'ok'arin rufe jikinta, tama kasa ihun sai mannewa jikin garu da takeyi tana cije leb'enta tana girgiza kai...

"Sanda ya zauna gefe da ita, ta yunk'ura zata tashi had'i da k'ok'arin kwand'ara ihu.....
"Rik'ota yayi ta fad'o kansa suka zube saman katifar yayi amfani da d'aya hannunsa ya toshe bakinta.... Banda kuka da kyarma da jikinta keyi bata komai....

"Duk sai yaji babu dad'i it wasn't his intention to scared her... A hankali ya rungumeta tsam cikin jikinsa kaman me rad'a haka ya soma fad'in" I'm sorry, I didn't mean to scared You, I only want us to talk, babu abinda zan maki so pls listen to what I'm gonna say.

"Jin lallausar fatarsa take tamkar garwashin wuta ne a jikinta, d'akin kuwa jinsa take tamkar cikin wuta aka jefata,..

"Jin tayi shiru yasa sa bud'e mata baki still tana rungume cikin jikinsa,.

"Jalal yaci gaba da fad'in" Zubaidah nasan bazaki tab'a yafemin ba duk da ban aikata laifin ba, but believe me I will never forgive my self either for not stopping them, I'll live with the pain.....
"Jin maganganunsa take tamkar ana zubawa kunnuwanta ruwan dalma dukda dad'i da muryarsa kedashi, toshe kunnuwanta tayi tana ci gaba da hawaye....

"A haka take fad'in" Wllhi wllhi na tsaneka na tsani ganinka, don Allah ka tafi ka k'yalemin rayuwata ka sakeni kowa yaje yayi rayuwarsa, na tsani na tuna waini Zubaidah inada auren mutumin danafi tsana a duniya a kaina,.... A hankali taci gaba da fad'in" Bazan tab'a manta wann fuskar taka ba, kai ka fara rik'oni a lokacin da nake k'ok'arin tsere ma sharrinku, lokacin da nake k'ok'arin tserewa mutuncina da martaba ta, duk bakuga wann ba sabida bakuda 'Ya'ya snn baku da k'anne dukanku, kuka k'etan haddi na ba tareda d'and'ani tausayi ba balle imani, sabida kunada masu tsaya maku, aka hanani magana snn aka aura min mutumin da yafi kowa zalunta ta a duniya, shin kuna tunanin Allah zai k'yaleku, kun lalata rayuwar yarinyar da bata ci maku ba bata sha maku ba, an dunk'ule rayuwata an jefa cikin wani 'yar takarda na kud'i an damk'a maka sabida asirin 'Ya'ansu ya rufu. Ka sani bakufi k'arfin Allah ba da Sannu zai saka min d'aya bayan d'aya...... Kuka ya kuma kufce mata ta shiga matsewa cikin garu kamar wacce ta tuna wani abu....

"Zogi da rad'ad'i zuciyarsa take masa take idanunda suka kad'a sukayi jazur, tabbas duk abinda Zubaidah ta fad'i haka ne....
"Kallonta yake yanda ta matse jikin garu tana kuka, tausayinta ya cika zuciyarsa, k'ok'arin matsowa kusanta ya soma yi, tayi saurin d'ago kai had'i da girgiza kai tana fad'in kar kayi gigin matsowa kusana, ka bud'e mun k'ofa na fice....
"Jiki a sanyaye ya mik'e yayi yanda tace.

"Da saurinta tazo zata shige yayi saurin tare k'ofar da hannunsa, d'ago kai tayi tana dubansa, gani tayi gaba d'aya fuskarsa tayi ja sosai haka nan idanunsa, gajern tsaki tayi kafin tace " Malam zan wuce.
"D'an fuzar da iska yayi kafin yace " Tambaya d'aya nake so na maki....

"Murmushin takaici tayi kafin tace " Darajar Annah kaci wllhi shiyasa ma na tsaya saurarenka, tanada mutunci tanada kirki wllhi batyi deserving d'a irinka ba, so let pass....

"Gyad'a kansa yayi kafin yace "K'warai she deserves a son better than I, Na sani. Shiyasa nake so na sake cin darajarta ki amsa min wann tambaya nawa.
"Idan na tafi zaki yafe mun...

"Kallonsa tayi gamida kauda kai gefe kafin tace " Har abada bazan tab'a yafe ma d'aya daga cikinku ba, don Allah ka tafi ka bar rayuwata and never come back...
"Sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yace " I hope one day you'll forgive me and you'll realize that I'm doing this to protect you....

"Murmushin takaici tayi kafin tace " I never need your protection snn ko gawarka ce a gabana bazan tab'a yafe maka ba...

"A hankali ya sauk'e hannunsa ya bata hanya kafin ya furta zan tafi as you wish.... Ficewa tayi cikin sauri kaman zata kifa k'asa...


"Hadiza dake lab'e taga fitowarta daga d'akin Jalal, tayi saurin k'arasa tasha gabanta tana dariya harda shewa kafin tace " Ashe a gabanmu ne kike gwada baki sonsa baku ko magana, ashe dai har turakansa kike zuwa, ayyirririr ni Dije naga Salon soyayyar zamani......
"Hararanta kawai Zubaidah keyi da idanunta da taci kuka, wani kukan ne ya kuma kufce mata, cikin kuka take fad'in nidae wllhi ba matar aure bace, kar ki sake kirana matar aure..... Daga haka ta nufi barandar Annah tana kuka.
"Hadiza tayi wani shewa kafin tace " idan baki sonsa me ya kaiki d'akinsa, dogon tsaki taja kafin ta wuce tana rangad'awa mijinta kira....


"Kan Annah ta fad'a tana kuka, har magrib Annah na lallashinta tana akin abu guda....








"Kallo yake kan faman bin layin dashi, yanayin mutanen da yake gani suna wucewa ya tabbatar masa babu kamun kai wajen.
"Juyowa Zulaihat tayi tana dubansa kaman ta gane tunanin da yake tayi d'an murmushi sanda ta saka d'an makulli tana bud'e k'ofar kafin tace " Kaga yanayin layin namu haka ko, kasan akasarin mazauna unguwar nan 'yan makaranta ne kaman ni, ka kwantar da hankalinka ka saki ranka.

"Gajeren murmushi yayi sanda tai masa nuni da saman sofa ya zauna.

"Kayi hak'uri fah gidan nawa babu wani abin tab'awa kasancewar yanzu na shigo garin. Amma barin dafa mana abu me sauk'i.
"D'an murmushi yayi kafin yace "Kar ki damu masauk'in da kika min ma na gode zuwa gobe zan tafi neman abinda ya kawo ni.

"D'an murmushi tayi kafin ta cire d'an mayafin dake jikinta, take suran jikinta cikin matsettsen d'inkinta wanda tamkar a jikinta aka d'inka ya bayyana, saurin d'auke kansa yayi daga barin dubanta, tayi wani murmushin cin nasara kafin ta soma tafiya cikin kwarkwasa ta nufi kitchen.
"Mintuna kad'an ta dafo masu indomie da soyayyen kwai.

"Gaba d'aya kasa sakewa yayi sabida kayan dake jikin Zulaihat, rabin k'irjinta a waje yake, snn da gangan take sunkuyawa komai ya bayyana, da kanta tayi serving nasa sai jansa da hira take tun yana basar da hiran nata har ya soma amsata jefi jefi...


"Amma me ya kawo ka Abuja Umar, nasan bai kamata na maka wann tambayar ba, but I don't may be I can help.

"Shiru yayi yana tunani cikin zuciyarsa, ya fad'a mata ne ko kuma kar ya fad'a mata, Wata zuciya tace ka fad'a mata k'ila tasan gidan da kazo nema.

"D'an karkad'a spoon d'in hannunta tayi saman fuskarsa tace " you there...


"Murmushi yayi kafin yace" Wani gida nake nema a cikin Abuja ko kin sani.

"Wani gida kenan, ta tambaya tana dubansa.

"Gidan Alh Kasim Dasuki.

"Murmushi Zulaihat tayi kafin tace "Ai duk garin nan babu wanda baisan gidan Alh Dasuki ba, k'ila ta'aziya kazo masu.

"Baison jan zancen Don haka kai tsaye ya gyad'a mata kansa ba tareda yace Komai ba, a fili yace zaki bani adress din gobe insha Allah.
"Ba tareda ta kawo komai ba ta gyad'a kanta kana tace " Yeah sure, for now finished your food I'll right back ta fad'i tana mik'ewa.

"Gyad'a kansa yayi a cikin ransa ya furta " JALAL, kwanan ka ya k'are your dead has arrived...


Sameena ce ๐Ÿ‘Œ๐Ÿพ
[1/23, 22:17] โ€ช+234 803 619 0581โ€ฌ: ๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜ *ZUBAIDAH*

32

*ยฉSameena Aleeyou...โœ๐Ÿพ*

_Queen Samy Novels Forum...๐Ÿ“–๐Ÿ“š_

*Dedicated To All Victims Of Rape...*



"Shiru Zulaihat tayi tana tunanin anya batayi gangancin sauk'an stranger a gidanta ba, wata zuciya tace " But You fell for him the very moment you saw him.
"D'an jimm ta kuma yi kafin zuciyarta taci gaba da ayyana mata "Anya kuwa bazata kira Tariq ta tambayesa ba tunda he's related to the Dasuki's, toh kuma idan kika kira sa fah, what about your plans for this hot guy da kike tsananin sha'awan had'a jiki dashi?.. Just let him be, ki zuba masa ido kiga gudun ruwansa snn kiyi k'ok'arin samun abinda kike nema wajensa.. Da wann tunani Zulaihat tayi murmushi kafin ta mik'e ta nufi parlor cikin wasu arnan kayan baccinta wanda suda babu dangin juna ne.


"Yanda ta barsa kishingid'e kan sofa haka ta dawo ta taddasa, kafe sa da ido tayi komai nasa ya burgeta, irin mazan da take tsananin son huld'a dasu knn, a hankali ta k'araso gamida zama hannun kujeran, d'an rank'wafowa tayi ta tsura wa labb'ansa ido, a hankali ta had'iye miyau, d'an yatsanta tasa ta shiga lailaye fatar bakinsa gamida hura masa iskan numfashinta tana wani lumshe idanu....

"Kaman a mafarki haka yaji wani bak'on Al'amari na faruwa dashi, cikin sauri ya bud'e idanunsa masu d'auke da bacci ya sauk'esu kanta, a razane da yanayin nata ya matsa k'arshen kujeran gamida kauda kai gefe don kuwa wann shiga nata ko kad'an bai dace ya kalla ba.

"D'an saita kanta tayi don tasan wnn dole tasha wuya kafin ta samesa da gani baisan hark'arba.

"Ganin ya bita da kallon tuhuma yasata saurin mik'ewa tana had'a igiyar rigarta kafin tace " Sorry I didn't mean to wake you up, dama ce maka zanyi da ka koma d'aki ka kwanta kan gado you will be more comfortable kaman kujeran ta kasa maka....

"Gajeren tsaki yayi kafin yace " Nan ma yayi min na gode, daga haka ya juya da fuskarsa gefe, ba don yana so ta basa adreshin gidan Dasuki's ba da tuni ya cika ma rigarsa iska....

"Zulaihat ta sha jinin jikinta ganin irin dizgin da yayi mata, amma dashike ba kunya bace da ita, zagayowa tayi ta gabansa snn ta soma tafiya cikin kwarkwasa ta yanda duk wani gab'a na jikinta ke motsawa. Fuska d'auke da murmushi tace mu kwan lafiya.....
"Bai iya amsa mata ba sai had'iyan miyau da yayi snn ya kasa daina kallon salon tafiyarta, a hankali ya dafe kansa sanda ta shige d'akin, wani irin yanyi maras fasaltuwa ya ziyarcesa.....



*Washe gari*

"Mami zan amsa kiran Uncle ne sabida ke, dan idan ta nine wllhi ko fuskarsa banson gani... Bata amsa sa ba sai ci gaba da had'a masa buttons d'in hannun rigarsa data ci gaba da yi.
"Tallafo fuskarta Labib yayi da hannunsa kafin yace" Are you still mad at me, com'on Mami I said I'm sorry, shikenan fine I promise you I'll try to control my temper and I'll learn how to put up with him, but he would explain to me how the heck my Dad borrows those money.... Manna mata peck yayi a kumatunta sanda ta gama hada masa aninin hannun rigar, Jacket dinsa ya d'auka suka nufo downstairs a tare, da kanta tayi serving nasa breakfast, ma'aikata sai kai komo suke, suna masu mamakin yau Labib kaman ba shi ba, da alama na cikin farin ciki don kuwa har suma ya gaisa dasu yau...
"K'arfe 8:15am daidai ya fito daga mansion din ya nufi motarsa k'irar Mercedes Benz,..


"Cak ya tsaya da motarsa ganin wani mutumi sai faman fafatawa suke da securities both masu tsaron gidansu da masu tsaron gidansu Salim dashike gidan a manne ne komai iri guda idan baka sani ba ma saika d'auka gida guda ne., Tuhumarsa suke me ya biyo dashi layin.
"Horn ya masu sukayi saurin k'arasowa suna fad'in" Sorry Sir had'i da wangame masa babban gate d'in wanda yake k'arafuna ne sanda sanda kana iya hango waje.

"Labib yace " Who's that Man Jerry?

"Sir we have no idea who he's, but we are suspecting him hes up to something, or may be someone sent him to spy on you *The Dasuki's*

A hankali yayi wata silent smile, "what if this man is after Kasim Dasuki, what if he's planning to take revenge on Alh Kasim, k'ilma wani business partner dinsa ya cuta shine ya turo wnn mutumin ya masa bincike don ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login