Showing 129001 words to 132000 words out of 210924 words
duniya banida abinda zan iya biyanka... Na ajiye maganar sarauta a gefe, ina maka magana ne a siga ta D'AN ADAM na gode na gode Abdullah....
"Cikin sauri Shattima ya katse sa ta hanyar girgiza kai yana fad'in" Abbah don Allah kayi shiru, zan jima ina jin zafin godiyar da kake min, don Allah Abbah ka daina.....
"Murmushi take tana hawaye kafin tace " Ya Shattima da gaske zan ga Hamma na, finally our family will be reunited again... Ina yake, ka kaini wajen sa pls dan Allah ka kaini.. I can't to meet him.... "Kallon soyayya kurum suke aika ma juna daga Shattiman har Zahidar....
"Cikin ransa ya furta " Damn it, I can't take, I just can't... You really crossing the line Shattima.... "Ba tareda fahimtar kowa ba ya mik'e ya fice daga tampatsetsen parlon... "Mahaifinsa ne kurum ya lura da hakan, baibi ta kansa ba donmin kuwa shima tasa yake nema ta ficcesa a wann situation d'in....
"Ummi dai yak'e ta soma tana karanto godiya ga ubangiji, sai ka rantse har cikin ranta farin ciki take....
"Daga ita Ummin har Baba Ciroma farin cikin su suka shiga nunawa tsantsa...
"Mai Martaba ya dubi Dr Madi kafin yace " Likita ai sai a sallamo min d'ana na gansa ko kuma ni naje da kaina na gansa....
"Daga Shattima har Dr Madi saida cikinsu yabada wani sauti, don basu san me zasu cewa Mai Martaba ba tunda bashida masaniya akan komai, rayuwar Jalal is different, he's dealing with alot....
"Murya na d'an rawa Dr Madi ya kuma rusunawa kafin yace " Allah Ya taimake ka.... Dama shirin sallaman nasa ake.... Toh saidai.... Saidai.... Gaba d'aya suka kafe Dr Madi da idanu.. Ummi da Baba Ciroma kuwa addu'a kurum suke cikin ransu Allah yasa ma mutuwa yayi kowa ya huta, basu gansa ba balle hankulan su ya tashi....
"Take annurin fuskar Mai Martaba ya d'auke cak, ya koma asalin sarkin sa Mai cike da madafen iko.... Jira kurum yake yaji me Dr Madi zai fad'i...
"Zahida kuwa mik'ewa tayi cikeda d'oki take fad'in" Nice zan fara sanar da Madaki wann babban Albishir, cikin sauri ta fice tana tattare alkyabban ta....
"Ganin haka yasa Shattima d'anyin gyaran Murya kafin yace " Abbah dama akwai d'an abinda ya kamata ka sani gameda Jalal...
"Mai Martaba ya jinjina kai yana duban Shattima kafin yace " Abdullah fad'i ko menene, ko menene Modibbo yake so ayi za'ayi sa da izinin Allah.. Idan gadon mulkin yake so, yanzun nan zan sauk'a na damk'a masa wann masarauta, Amma kar yace bazai dawo garemu ba....
"Shattima ya d'anyi murmushi k'arfin hali kafin yace " Allah Ya tainakeka Abbah, ko kusa ba haka bane, Jalal ba irin wad'an nan mutanen bane.... Jin Shattima ya d'anyi shiru yasa Dr Madi rusunawa kafin yace " Allah Ya baka nasara zan koma bakin aiki idan ka min izini.....
"Mai Martaba ya jinjina kai, cikin sauri Baba Ciroma yace " Ba a maka izinin tafiya ba likita bokan turai, dole ka fayyace mana ina d'anmu yake..???
"Kallon Ciroma Mai Martaba yayi kafin yace " Yaya mun masa izini....
"Har wuya Ciroma ya kawo don jira yake yaji Dr Madi yace " Lamid'o ya cika ne... "Godiya Dr Madi ya shiga yi cike da rusunawa har ya fice...
"Gaba d'aya sunyi nisa duniyar tunanin da suka tafi sai jiyo muryar Shattima sukayi sanda ya soma bawa Mai Martaba labarin tun farkon had'uwar sa da Jalal, da irin k'alubalen da shida family d'insa suke fuskanta a rayuwa.....
****************
"Annah why am I having this feeling... I don't know but Im so anxious.... Kaman wani abu zai same sa, what if he's hiding something from us, jiya jiya yace mana zai dawo gida right away da zaran an sallame sa, buuuttt.. Why the sudden change of mind..
"Annah ta d'an rik'o hannayen ta tace " Ki daina tunani haka daughter, besides kinsan halin Jalal da kafiya ma abu, he might be planning for this for a long time, nasan bazai k'yale maganar neman Dr d'in nan ba har sai ya cimma burinsa, he can do anything for you dear...
"A hankali Zubaidah ta gyad'a kanta kafin tace " I hope he'll be safe... I hope wata rana komai zai wuce ya zama tarihi....
"Rungumeta Annah tayi tana murmushi kafin tace " Soon darling, insha Allah komai yazo k'arshe....
"Hadiza dake mak'ale saman staircase tayi wani murmushi mugunta kafin tace a zuciyarta
_"Wahala bazai tab'a k'yaleki ba Zubaidah domin kuwa a cikinta aka haife ki, snn a cikinta kike rayuwa, zaki dawwama a cikin ta.... Ayi shari'ar mu gani...._ Daga haka ta kuma yin wata murmushi ta kuma yi ta juya ta nufi d'aki.....
*************
"Tofar da jinin dake bakinsa yayi kafin ya d'ago yana huci yake fad'in" No no ka gama duk abun da zakayi akaina you imbecile, but don't you dare go near my wife.... I swear if you dare hurt her I'll kill you.... Katakon hannunsa ya kuma buga wa Jalal a k'afafun sa kafin ya kuma ajjiye masa pen da paper saman cinyar sa dake d'aure gamgam da jikin kujera yace " Oya write, go ahead and sign the divorce...
"Kallon sa kawai Jalal keyi yana wani irin huci.....
"Ya kalli agogon hannunsa kafin ya sauk'a k'asan kangon yana amsa kira da wayar sa..... Bayan kaman wucewar wasu awanni ya dawo hannunsa d'auke da takarda nannad'e da snacks..
"Kujera ya janyo ya zauna gaban Jalal suna watsa ma juna mugun kallo kafin yace " Are you hungry Hero....??? Ya fad'i yana wata murmushi.... Tuntsurewa da dariya yayi kafin yace " Yeah why should I even asked, you must be starving... Ya shiga d'aura snacks d'in saman 'yar karyayyiyar kujerar data raba tsakanin su, ya warware takardan tsaf kafin ya soma ci yana fad'in" Let's eat Dude, go on have some.... Yana gyad'a kai yake fad'i..... "Dariya ya kuma fashewa dashi gamida sassauta murya yana fad'in" Oh I'm so sorry na mance ashe bazaka iya ba... Kana so na kira sweetheart d'inka so that she should feed you.... Opss this place is quite far for her..... Poor you..... " Okay okay fine if you want ni zan baka... Ya shiga tura masa cake a baki yana fad'in" Oya take it, open your mouth and eat...... Da k'arfin gaske yake danna cake d'in a bakin Jalal.....
"Fuzarwa Jalal yayi yana wani irin huci yake fad'in" You imbecile you'll pay dearly...... Tuntsirewa da dariya Umar yayi kafin ya sauk'a downstairs a tare suka hauro da wasu k'artai guda biyu.... Dubansu da kyau yayi kafin yace " Danny take care of this brat.... Make sure he's safe here, idan yunwa taci uwar sa Ya buk'aci abinci ku basa,...
"Danny ya gyad'a kai kafin yace "Yess Boss...
"Umar Ya sunkuyo daidai fuskar Jalal kafin ya soma fad'in" I brought you company Mr Hero, look ka gansu, zasu kula da kai sosai, saidai fah bazaka tab'a barin kujeran nan ba until you sign these papers... Ya d'ago takardan yana karkad'asu a fuskar Jalal... Dariya ya kuma fashewa dashi kafin yace " Enjoy your stay..... Daga haka ya nufi downstairs yana wata irin dariya.....
****************
*Prison*
" A zabure ya tashi daga mummunar mafarkin da yayi yana k'ara wanda yasa gaba d'aya sauran 'yan d'akin suka tashi...
"Labib ya k'arasa da sauri yana rik'e Tariq yana k'ok'arin calming nasa, kan su ankara sai ganin fitsari sukayi na tsoyayowa daga gadon Tariq.....
"'Yan d'akin kuwa me zasuyi banda dariya da shewa har saida ganduroba d'aya ya shigo ya daka masu tsawa....
"Labib ya jawo Tariq suka dawo gadon sa dukda fiffizgewa da Tariq d'in keyi.... Salim kuwa dafe kansa kurum yayi cikin wani irin yanayi.. Ya k'agu kwanaki hud'un nan su cika a gudanar da shari'a su fice daga wann kurkukun.....
Sameena ce ๐๐พ
[1/23, 22:28] โช+234 803 619 0581โฌ: ๐๐๐๐ *ZUBAIDAH*
73
*ยฉSameena Aleeyou...โ๐พ*
_๐KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ๐ค_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*Where is she๐๐๐ My Fadindin Aka Fadila Talba ๐.... This one's hers.... Allah k'aro baseera darling aci gaba da suburbud'o mana RAYUWA TA ๐ป๐*
"Shiru Mai Martaba yayi yana jinjina labarin da Shattima ya basu... Tausayi da soyayyar d'ansa ya cika zuciyar sa..
"Ummi kanta saida ta tausaya ma Jalal, Baba Ciroma kuwa bai furta komai ba sai tunane tunanen da ya soma, neman hanyar da zai salwantar da Lamid'o ya shiga yi tunkan ya iso wann masarauta...
"Shattima yaci gaba da fad'in" Abba a gani na tunda shari'ar kwanaki ne ya rage ayisa, ina ganin idan mun bari an gama komai zaifi zuwa cikin sauk'i don na tabbata bazamu sami kan Jalal a yanzu ba, snn abubuwa zasu masa yawa... Abbah kuma idan son samu ne a b'oye samun Lamid'o har sai lokacin da zaizo masarautar nan sabida na tabbata wa'enda sukayi sanadiyar b'acewar sa muddin suka ji labarin an same sa zasu iya yin wani abin to stop him from coming back...
"Cikin Ummi ya d'uri ruwa ji take tamkar Shattima ya gane she's behind everything, gumi ya shiga keto mata dukda manya manya Air conditioner dasuke hurawa cikin parlorn...
"Baba Ciroma kuwa cikin ransa yayi murmushi yace " Kaman ka sani yaro.. A fili kuwa cewa yayi.. " Wann shawari taka tayi Shattima, haka kurum za'ayi don guje ma sharrin abokan gaba...
"Mai Martaba ya jinjina kai kafin yace " Haka ne....
"Shattima yayi godiya kafin ya rusunar da kai yana fad'in" Abbah idan anmin izini zan dakatar da Zahidah daga sanar da Madaki sabida idan ta sani yanzu zatayi ta saka damuwan son ganin sa a ranta...
"Jinjina Kai Mai Martaba yayi kafin yace " Kayi gaskiya Abdullah mun maka izini... Allah Ya albarkaci rayuwar ka.... Ya kuma rusunawa yana godiya kafin ya fice...
"Bayan Shattima ya fice "Mai Martaba ya dubi Ummi da Baba Ciroma kana yayi gyaran murya ya soma fad'in" Alhamdulillah dukan ku biyu kuna nan, zanyi amfani da wann damar na sanar daku mun d'aga bikin yaran nan Khalifa da Zahida har sai Al'amra sun daidai ta, Yaya sai a sanar dasu Waziri maganar d'aga auren....
"Baba Ciroma ya jinjina kai kafin yace " Hakan yayi...
"Ummi kuwa kasa cewa komai tayi don kuwa she's not there gaba d'aya...
"Kusan karo suka kusan Yi da juna.. Zata fad'i yayi saurin tallafo ta.... Sun jima suna kallon juna kafin Zahida tayi k'arfin halin k'wacan kanta.... "Da sauri Shattima ya saketa kafin yace " Oh I'm I'm sorry, I didn't know you were coming.....
"D'an gyara alkyabban ta tayi kafin tace " No no its okay.... Ta d'an sa kai zata wuce Shattima ya kuma shan gabanta...
"D'ago ido tayi tana dubansa, gani tayi he's looking so pale.... Da sauri ta d'auke idanunta had'i da kauda kai gefe....
"Murya can k'asan mak'oshi yace " Muna fad'a da juna har haka ne...?? Lately you were nice to me sabida an samu Hamman ki, and now ko gaisuwa bazan samu ba.?? Remember you still my little sis no matter what happens..
"Ya Shattim pls stop making this difficult, bana so azo pick d'in da I can't take it.... Pls kaji...
"Murmushi Shattima yayi kafin yace " It won't come to that pick... But you need to keep this in mind.... Seeing you happy makes me feel happy..... Snn ganin ki cikin akasin haka yana jefa ni cikin akasin farin ciki... Yanzu da nasan ganin Hamman ki zai saka ki cikin farin ciki I won't rest until I brought him here for you and your family.... Ya k'arashe yana murmushi mai bayyan hak'wara... "Murmushi Zahida ma tayi ba tareda ta furta komai ba, cikin zuciyarta kuwa tsantsan soyayyar sa ne.....
"Shattima ya katse shirun da fad'in" Da fatan baki sanar da Madaki batun ba..
"Girgiza masa kai tayi alamun a'a kafin tace " No na samu tana bacci...
"Shattima ya jinjina kai kana yace " Good, nan ya sanar da Zahida uzirin su na rashin sanar da Madaki yanzu, itama taji dad'in haka, daga nan tambayoyi ta shiga jero ma Shattima gameda yayan ta....
"Shattima ya murmusa kafin yace " I can see someone's curious.... Ya k'arashe teasingly...
"She chuckled sann ta d'an rufe fuskar ta da tafukan hannu kana tace " I just can't wait to meet him, kana da pics d'insa pls show me, I knw he's handsome.....
"Murmushi kawai Shattima yayi kafin yace " Kar ki damu soon zaki gansa.... "Ta murmusa tace I hope so...
"Har Zahida ta shige sashen su farin ciki take ji maras misaltuwa.....
"Daga yanda Khalifa ke tsaye ya hangi Shattima yanda ya raka Zahidah da kallon soyayya, fasa shigowa yayi ya juya, a fili yake furta " That idiot is really getting on my Freaking nerves.... I've do something tun wuri... Putting him in his place... Fadawa na gaishesa na masa gadabout kota kansu baibi ba yayi ficewar sa.
*****************
"What you're very stupid, what rubbish are you talking about.... " Jirgina yayi sinking.... No no this is ridiculous, ka fad'a min abinda hankali zai kama.......
"Dafe kansa yayi gamida zama gijif cikin kujera yana sunbatu shi kad'ai.....
"Barr Munir ne ya shigo da files a hannunsa yana tafe yana magana yana duba takardun... "Turus ya tsaya ganin Alh Kasim zube cikin kujera yana maganganu shi kad'ai...
"Barr ya dafa sa yace " Mr President lafiya... Are you okay, is everything alright..???
"Da k'arfin gaske Alh Kasim yace " No no... Nothing is alright,... Jirgina jirgina ta shak'o kayan over 1million Dollars wai Captain Bala yana ce min tayi sinking...... Can you just imagine.. " No no this is not going to happen,...... "Kamasa Barr Munir yayi ya zaunar sa yana k'ok'arin calming d'insa dukda shima ya jijjiga da jin batun....
"A zabure Alh Kasim ya mik'e ya nufo waje ba tareda sanin ina ya dosa ba, Barr ya take masa baya...
"A reception suka ga ana kallon News sai nuno labarin ake da sunan Company d'insu Dasuki Holding... Fuzar da iska kurum yayi ya karkata babban riga kafin ya fice...
***************
Yau ta kama sauran kwana guda tak a koma kotu, gaba d'aya hankalin Zubaidah ya gama tashi, hankakin ta sam bai kwanta ba da rashin dawowar Jalal, kowa ya ganta zai gane hakan, idan ta kira wayar sa baya shiga, saidai text da yake turo mata cewa yana lafiya ta kwantar da hankalin ta, abin har ya soma k'ona mata rai, itafah a halin yanzu ganinsa ya fiye mata shari'an dake gaban ta, meyasa Ya Jay yak'i fahimtar hakan.... Jin muryar Ansar da Annnah a downstairs yasata saurin zura hijabi ta sauk'a....
"Ya Ansar did he call you, Ya gaya maka ina yake ne...
"Daga Ansar d'in har Annah saida ta basu tausayi, Annah ta k'arasa ta rik'ota suka zauna saman sofa.
"Ansar ya d'an girgiza kai kafin yace " Bamuyi magana ba, but he texted me, I'm quite sure he won't stop har sai ya sami Dr d'in.... Ya jaddada min he'll make it to the trial... I knw Jalal he's gonna keep his word... Ki kwantar da hankalin ki Zubaidah... Jalal is doing all this for you...
"Yanzu ko Tariq baiyi confessing ba at least munada option b... Balle ma Tariq ya tabbatar min he'll confess everything, Zai fad'i iyakacin gaskiyar sa a gaban Alk'ali, da wad'an nan hujjoji masu k'arfi muke saka ran Allah zai bamu nasara ...
"Zaro ido Annah da Zubaidah sukayi cike da farin ciki suke hamdala, Annah ta rungume Zubaidah tana fad'in" This a great news.... Alhamdulillah.... Ansar Allah ne kurum zai biyaka ladan aikin ka..
"Zaro ido waje Hadiza tayi daga yanda take lab'e kafin tace "Aiko banci ta zama ba.... Ba tareda kowa ya lura da ita ba ta samu ta sulale ta fice daga gidan.....
***********
"Just how flipping damn stupid are you..?!!! Don't you gerrit, wuya tsanani matsi tak'ura bazasu tab'a sa na rabu da Zubaidah ba... You can keep me here for good,