Showing 60001 words to 63000 words out of 210924 words
Salim yayi raping yarinyar nan, ke ai kinsan hukuncin fyad'e tunda fannin da kike knn a kotu...
"Gyad'a kanta Asmah tayi kafin tace " But this is different cousin the victim married the rapist, batayi magana ba bata nemi hakkinta ba, she chooses to be with her rapist then fine let them be, kar ki zama mak d'aukam zantukan mutane don shaidan fyad'e babban Al'amari news kotu, sabida fyad'e babban laifi ne, pls Kausar ki nutsu a gidan aurenki , me kike tunani idan aka sake ki a yanzu Me zaki ce wasu Mumsy da Pappy, bayan farin cikin da kika sasu kina son jefa su cikin bak'in ciki ne,.....
"Kausar dai shiru tayi sai k'walla da suka ciko idanunta, Asmah cike da tausayawa ta kuma rik'o yatsun hannun 'yar uwar tata kafin taci gaba da fad'in " Reconcile, talk to your husband fix everything together okay, I know it might be difficult but pls do it for the sake of your marriage kinji...
"Ba tareda tace komai ba ta rungume Asmah tana hawaye....
"Mummy na zaune a parlor tana kallon tashan labarai Barr Munir ya shigo kaman an jehosa,...
"D'an zabura tayi kafin tace " Brother lafiya ka shigo min parlor haka, you gave me a fright....
"Shafa sank'onsa yayi kafin ya shiga zagaye parlorn, a tamanin Mummy ta mik'e ganin yanayin nasa sosai ya razanata,
"Wai meke faruwa ne?? Ta kuma tambaya.
"Zama yayi bisa sofa kafin yace "Farha Ina Kausar??
"Tana sashensu, cewar Mummy
"Ki kirata kuzo muyi magana, ya fad'i yana matse k'wallan idonsa...
"Wai meke faruwa ne, Mummy ta kuma tambaya sanda muryarta ya soma shaking.... Ka fada min meke faruwa Ta Munir na rok'i arzikinka....
"Tasowa yayi daga kujeran da yake ya dawo kujeran da take zaune ya rik'e hannayenta yace " Calm down pls Farha, idan baki kwantar da hankalinki ba bazan iya fad'a maki ba,.... Shiru tayi tana k'unshe bakinta da kuka ke neman b'alle mata, k'walla kira yayi wa Jane dake kitchen d'in Mummy kafin yace ta kira masa Kausar.. Nan da nan Jane ta wuce kiran Kausar....
"A tare suka shigo parlorn itada Asmah, Sai faman cin magani take ba don Asmah ta matsa mata ba ma da ba zuwa zatayi ba..
"Gaisar da Uncle Munir sukayi kaman yanda Salim ke kiransa, Sun sha jinin jikinsu da ganin yanayin Mummy,
"Barr yace su Zauna magana zasuyi akan Salim.... K'irjinsu yabada Rass ..!!!
"Mummy cike da damuwa take fad'in me ya sami Salim... Ka fad'a min Munir...
Sameena ce
[1/23, 22:20] βͺ+234 803 619 0581β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
41
*Β©Sameena Aleeyou...βπΎ*
_Queen Samy Novels Forum...ππ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Shiru parlorn yayi suna sauraren Barr Munir, banda bugun k'irajensu baka jin komai, ...
"Saida ya kuma goge k'wallan idonsa kafin ya soma fad'in" Salim.... Salim was trying to commit suicide, he shot himself...... Ai baikai aya ba Mummy ta saki wani irin k'ara....
"Kausar ma toshe bakinta tayi tana k'unshe kukanta ta fad'a jikin Asmah wacce itama tashin hankalin ne ya ziyarce ta...
"Cikin tsananin kuka Mummy ta rik'o yayanta Barr Munir take fad'in" No.. No Munir this is ridiculous, tell me ba gaskiya bane, Oh my baby boy me yake nema a duniyar nan bai samu ba har yake yunk'urin kashe kansa... Mik'ewa ta kuma yi tana fad'in" Take me to him Munir, I really want to see my boy, ...
"Mik'ewa Kausar ma tayi idanunta sharkaf da hawaye take fad'in" I'll go with you mummy...
"Barr ya d'an dubeta kafin yace " Inaganin Kausar ki zauna a gida, don zuwan naki ka iya haifar da wani abin, sabida magana ta gaskiya A DALILIN KI ne yake yunk'urin kashe kansa.... Gaba d'aya suka zaro ido harda Mummy, Asmah tasa hannu a k'irji ta dafe..
"Barr yaci gaba da fad'in" Salim was trying to kill himself because of you Kausar, That filthy girl called you and told you k'aryar data saba, wanda DAGA TAIMAKO abin nasu ya koma sharri, a dalilin yunk'urin raba aurenku da kike k'ok'arin yi shi yasa Salim yanke shawaran kashe kansa Don bazai iya rayuwa babu ke ba, yana sonki yanda baki tsammani, don haka inaga ki zauna a gida kawai shi yafi... Hannunsa Mummy ta shiga janyo hannun Barr duk da jin zancen nasa yayi matuk'ar girgiza ta bai hanata watsa wa Kausar mugun kallo ba don tasan komai ka iya faruwa tunda an jima ana b'oyewa Kausar da iyayenta, ficewa sukayi itada Munir cikin sauri....
"Bud'e baki tayi zatayi wa Asmah magana sai kuka, Asmah ta rungumota tana lallashi, jin dirin motar Barr yasata d'ago kai a zabure tana fad'in" Asmau mu bisu kar su b'ace mana, I really want to see Salim, take me to him pls... Ta k'arashe maganar cikin fashewa da kuka....
"Gyad'a kanta kawai Asmah tayi kafin ta rik'o hannunta suka fice suka nufi mota....
"Mai taxi yana ajiyesu tasa kai zata shige, saurin rik'o hannunta yayi kafin yace " I'll be waiting for you here har ki gama classes d'in naki..
"Da mugun mamaki take duban yanda ya rik'e mata hannu ga mutane nata faman kai komo, gaba d'aya jinta a tsarge take, gani take kaman kowa su yake kallo, ..
"A hankali tace " Give me back back my hand.. Tana maganar tana kallon mutane a tsarge, d'an matsowa kusanta yayi yana murmushi kafin yace " Sai kin min alk'awarin zaki amince nazo d'aukanki snn zaki soma Therapy class d'inki as well...
"Jin hannunsa cikin nata yana haifar mata da wani irin yanayi don haka da sauri ta gyad'a kanta kana tace " Eh naji na amince but that doesn't mean you'll be fetching me up everyday.... "
"Murmushi ya kumayi wanda ya jima baiyi irinsa ba har saida fararen hak'waransa suka bayyana he couldn't believe wai yau Zubaidah ke masa magana haka cikin sanyin murya har tana cewa ta amince da buk'atarsa...
"D'an sakin hannunta yayi kafin yace " I'll get you later, take care....
"Ba tare da tace komai ba cike da k'osawa tayi shigewarta, k'irjinta na bugawa da sauri da sauri, sai faman dunk'ule hannunta da ya rik'e take, don ji take kaman har yanzu hannayensu na cikin na juna....
*Dasuki Hospital*
"Daddy yana hango Mummy ya tafi ya rungumeta, kuka mai k'arfi ya kuma b'ark'e mata tana fad'in" Kasim our son, our only son, tell me he can go through this.... Zaunar da ita Daddy yayi yana calming d'inta, Labib dake tsaye tare da Tariq yayi saurin taro ruwa a dispense ya mik'awa Mummy yana fad'in "Have some water Aunt,
"Karb'a tayi tana kallon Labib d'in kafin tace " Tell me your brother will get out of here soon...
"Durk'usawa yayi gaban kujeran da take zaune ya rik'e hannayenta kana yace " Insha Allah Aunt, very soon, I know my cousin is a fighter he can get through this, ki kwantar da hankalinki pls Aunt, Yasa hannu ya amshi ruwan ya Kai bakinta kafin yace " Drink your water..
"Gyad'a masa kai tayi ta shiga kwankwad'an ruwan...
"Nurses ne suka Bud'e k'ofar kana suka soma turo sa kan gado mai tayu.... Ai tuni sukayi kansa gaba d'aya hakan yayi daidai da isowar su Kausar.
"Da sauri ta k'arasa jikin gadon tana kiran sunansa, Nurses kuwa sai faman tattaresu suke don har lokacin bai farfad'o ba snn ga oxygen saman hancinsa...
"Intensive care aka saka sa snn aka hana kowa shiga, saidai suna hangensa ta glass..
"Mummy tamkar baud'eddiya haka ta koma, saida Mum d'in Tariq ta iso kafin ta d'an sami nutsuwa...
"Suna zazzaune gaba d'aya a reception, gaba d'aya Kausar jinta take a tsarge ganin kowa da kalan kallon da yake mata, she felt guilty for what happened, Asmah ta lura da haka taja 'yar uwarta ta kwantar bisa kafad'a coz she knows exactly how she feels.
"Asmah bani wayarki ban fito da tawa ba, Kausar ta fad'i cikin rawar murya ,
"Mik'a mata Asmah tayi ba tareda tace komai ba..
"Mumsy da Pappy suna bisa dinning table suna breakfast lokaci guda suna firan d'iyar tasu da sukayi kewarta wayar Mumsy ya soma ringing, d'agawa tayi tana murmushi take duban mijin nata kana tace "Kaga muna zancenta ga wayar Asmah, k'ila tana can gidan nata..
"Murmushi kawai pappy yayi gamida sipping coffee d'insa sanda Mumsy ke amsa wayar...
"Jin muryar Kausar ce ba Asmah gashi cikin wani irin ta yanayi yasa hankalin Hajiya Raliya tashi wanda yasa Alh Tahir ajiye mug d'in hannunsa babu shiri...
"Wani asibiti kuke, okay gamu nan zuwa, Mumsy ta fad'i kafin ta kashe wayar tana duban mijin nata wanda shima ita yake duba..
"Meke faruwa, waye a asibiti, Pappy ya tambaya sounding curious...
"A daburce ta soma fad'in" Wai Salim ne babu lafiya yana intensive care, Pappy our daughter need us tashi muje pls, oh my poor baby kuka take sanda take min magana...
"Subhanallah d'auko min wayata a sama barince Lawan ya fito da mota, cikin sauri Mumsy ta amsa kafin ta nufi upstairs.....
***********
"Wani farinciki maras misaltuwa yake ji haka kurum wanda shi kansa baisan dalili ba, ni kuwa Sameena nace (Jalal keep on saying taimakonta kake..... you are into the girl irin totally d'in nan..... π)
"Shiryawa yayi tsaf cikin k'anan kaya, Ash shirt da brown chinos, yayi kyau sosai dukda raunin dake jikinsa bai hana kyaun halittarsa fitowa ba. A gurguje yayi sallama wa Annah ya sanar da ita zai d'auko Zubaidah snn daga chan zasu wuce gidan Dr Khaleesat therapist wacce zasu na therapy classes da Zubaidah, sosai Annah taji dad'i ganin abubuwa sun soma canzawa tsakanin Jalal da Zubaidah...
"Tana fitowa daga gate d'in makarantar ta hangesa tsaye kasan wata bishiya, haka kurum taji mugun fad'uwar gaba, d'an saita kanta tayi kafin ta soma tafiya cikin tsanaki...
"Tun daga nesa yake murmushi kumatunsa saielotsawa suke, har ta k'araso yanda yake ta tsaya daga can gefe, fuskar nan tana tamau babu alamun fari'a...
"Yasan bazata masa magana d'an kallonta yayi kafin yace " Shall we..
"Ba tareda ta kallesa ba ta soma tafiya.
"So how's your first day at school, ya tambaya sanda suka k'arasa bakin hanya..
"Shiru kaman bazata amsa ba sai kuma tace "Lafia a tak'aice...
" Har suka shige tasi d'in bata kuma cewa komai bar, shima shirun yayi har suka isa gidan Dr Khaleesat....
"Bayan sun sauk'a a tasi d'in ne ta bisa da kallo alamun tambaya.
"Yasan hakan zata kansance kai tsaye yace " D'aya class d'in zakiyi a nan...
"Tab'e baki tayi gamida kauda kai gefe kafin tace " Niba mahaukaciya bane babu therapy d'in da zanyi...
"D'an shiru yayi yana kallonta kafin yace " You promised me.
"Kallonsa tayi yanda yayi maganar cikin sigan tausayi, d'an jimm tayi kafin tace " Eh ai sabida ka amince min zaka tafi shiyasa nima na amince " Gyad'a kansa yayi dukda fad'uwar gaban da yaji, yasan ya mata alk'awarin barin rayuwarta amma baijin zai iya cikawa, he leave her all alone.
"D'an ware madaidaitan idanunsa yayi wanda basu faye girma sosai ba sai tsawo da shape me kyau kafin yace " Fine naji na amince mu k'arasa, bata kuma cewa komai ba ta soma binsa a baya..
"Bayan sunyi knocking mai gadi ya bud m'e masu ya tambayesu ko Dr tasan da zuwansu, Jalal ya shaida masa ta sani snn ya buk'aci ya sake masu iso, ba tareda b'ata lokaci ba aka masu izinin shigowa...
"Masuk'i aka masu a parlour, mintoci kad'an wata mata 'yar gayu ta fito at her early 40's, da murmushinta ta k'araso tana masu sannu da zuwa, Da gani tanada barkwanci.
"Bayan sun gaisa ne Jalal yace shine wanda ya tura mata sak'o ta mail d'inta tace suzo gida su sameta....
"Murmushi Dr Khaleesat tayi kafin tace " Ai tun daga ganinku na ganeku Jalal, ta kalli Zubaidah lokaci guda tana karantar ta yanda ta zauna can gefe Jalal na wani kujera na daban.
"Kan kace me an cika gabansu da drinks, Dr Khaleesat ta kalli Zubaidah ta kalli Jalal kafin tayi murmushi tace " Mr Mrs Jalal ya kuka zauna kujera daban, kallon juna sukayi a tare babu wanda ya iya cewa komai, Dr tayi murmushi sanda take mik'awa Zubaidah cup na drink kafin tace " Kina tsoronsa ko??
"Kallon mamaki Zubaidah ta mata, Dr ta kuma yin murmushi kafin ta dubi Jalal tace " Mr Jay ka d'an jira mu a wancan waiting parlour d'in, ba tarda b'ata lokaci ba Jalal yayi yanda tace.
"Kafe Zubaidah dake faman juya Cup d'in hannunta da ido tayi kafin tace "Feel at home kinji, gidan nan be'azuwa ba'aci komai ba, so ina jinki, tsoron mijin naki kike...
"Sai snn Zubaidah ta dubeta kafin tace " Ni ba tsoronsa nake ji ba, tsanarsa nayi , snn ba mijina bane don ya kusa tafiya ya bar min rayuwata, ...
"Dr ta murmusa kafin tace "Nasan bashi kad'ai ba duk wani namiji ma kin tsana, Zubaidah ta gyad'a kanta kafin tace " Hamma na ne kawai ban tsana ba,
"Jinjina Kai Dr tayi kafin tace " But what makes you hate them, kallonta tayi kaman bazatayi magana ba sai kuma tasa hannau tana share idonta alamun hawaye sun zubo mata, Dr ta d'auko tissue paper kana ta goge mata hawayen kafin tace "I know it hurts, it's very hard to start again, but you have to fight your Devastation, don't let it get into you, only then you'll live again... Ta d'an ja fasali kafin taci gaba da fad'in" First kiyi k'ok'ari kisami soyayyar kanki, ki k'aunaci kanki snn kisa a ranki Allah ba yak'i ki bane ya baki irin wann jarabawan, no it's a trial, it could happen to anyone, second be happy with the people around you, people that shows you love and compassion, don't ever push them away, don't let them go, such people are blessing from Allah. Snn duk mutanen da kika Allah Ya ciresu daga rayuwarki you are not meant to be with them, because sometimes absence of some people makes us something in life...
"Tunda ta fara magana Zubaidah ta nutsu ta bata hankali sosai, maganganun Dr Khaleesat ya haifar mata da tunanin da bata tab'a yin irinsa ba.
"Hira Dr ta ringa jan Zubaidah dashi tana mata tambayoyi gameda rayuwarta, d'an lokaci k'ank'ani taji ta sake da Dr Khaleesat, daga bisani Dr tacee" Toh Zubaidah ni a yanzu k'awarki ce kuma aminiyar shawarin ki, snn pls I need you to be honest with me, no hiding things okay......
"Murmushi Zubaidah tayi gamida gyad'a mata kai don shakka babu taji relief a d'an wann hiran da sukayi da Dr Khaleesat.
"Bayan sun gama da Zubaidah ta nemi ganin Jalal shi kad'ai shima, nan ta d'anyi briefing nasa yanda sukayi snn ta basu Time d'in da zasu na zuwa, sosai Jalal yayi godiya wa Dr ya tambayeta yanayin biyan kud'in.
"D'an murmushi tayi kafin tace " Ta jima tana wann taimaka wa mata 'yan uwan ta da mummunar k'addara ta fyad'e ta auka masu, she's not doing it for money, snn labarin Zubaidah ya banbanta da wanda taci karo dasu a baya, don haka she really wants be part of her Story....
"Godiya sosai ya mata gamida jinjina mata, tabbas da za'a sami mutane irin Dr Khaleesat da Al'ummah taci gaba sosai,... Allah ka yawaita mana irinsu ameen...