Showing 141001 words to 144000 words out of 210924 words
" Audullahi niko inaso na tsaya a nan na d'an kama ruwa...
"Shattima ya d'anyi slow ya kalli agogon jikin motar ta nuna k'arfe shida da wasu 'yan dak'ik'ai, cike da gurmamawa Shattima yace " Baba ai da ka bari mun shiga Tilden Fulani tunda mun kusa shiga amma nan wajen is very risk ba'a faye tsayawa ba, iyanin sai muyi sallahn mangaribar mu....
"Baba Ciroma ya cika yayi fam, take ya soma bore yana fad'in" Aikin banza aikin wofi, nine Aliyu (Mai Martaba) zai had'ani da yaro a tafiya kuma na fad'i abu ace baza'a yisa ba, sarauta ce Allah ne me badata, kuma da Allah yaso da yanzu nine a kujeran nan ba Aliyu ba, ina binsa da umarnin sa sauda k'afa dukda k'anina ne amma bazan lamunci wulak'anci da raini daga yara 'ya'ayan ciki na ba.....
"Cak Shattima yaja yayi burki cike da mamaki, me Ya kawo wadann maganganun....
"Baba Ciroma yaci gaba da fad'in bud'e min na fita d'an k'wal uba.....
"Murya har na rawa Shattima ya shiga basa hak'uri had'i da bud'e lock.... Aiko Baba Ciroma na fita wasu mutane da sanduna da gorori suka nufo su suka shiga dukar motar da iyaka k'arfin su....
"Dukda fasa masa glass d'in mota da sukayi bai hanasa danna giya da k'arfin gaske ba yayi rivers lokaci guda..... Bada son ransa bane ya bar Baba Ciroma dole ya tafi ya nemo masu d'auki kafin ayi kan me uwa dawabi ba wan ba k'anin karatun arne... Tunda baya dasu kad'an sun wuce checkpoint na Sojoji.
"Dukan Baba Ciroma suke da iyaka k'arfin su yana fad'in" Ba shi bane ba ku saurara ba shi bane ba, wllhi shine wanda ya gudu, na rantse maku ni na biya kud'in" Kar ku kashe ni kuyi min rai....
"K'auyawan nan kuwa sai raptama masa sanda suke suna fad'in" Aradun Allah k'arya kake, yace mana zai ajjiye ka a nan wajen mu gama da kai, ku buge shi.... Rititim suka ci gaba da aza masa sanda .... Banda k'alu innalillahi da Baba Ciroma ke iya fad'i baya komai.... Tun yana iya motsi har ya bar motsawa... Daidai nan su Shattima da sojojin checkpoint suka k'araso... Aiko nan suka gudu suka shige daji.... Ruwa ruwa aka kwashi Baba Ciroma aka shige dashi mota suka nufo dashi Babban asibitin Bauchi Abubakar Tafawa Balewa University Teaching Hospital Bauchi.... Cikin sauri aka karb'i Baba Ciroma a emergency rai a hannun Allah.....
*****************
"Tunda ta dawo gida tayi jigum ko abinci ta kasa ci, wunin ranar guda haka tayisa babu cin abinci... Goggo ta lura da hakan, don kuwa duk barkwancin Zulaihat yau kam shiru ta b'ace....
"Imam ne ya shigo gidan dawowar sa knn daga makaranta don yau ya jima yana lectures bai sami zarafin yin tasi ba, sabida tutorials da ya gudanar ma 'yan ajin su....
"Ya sha mamaki ganin yau basa zaune saman tabarman da ya saba dawowa yana iske su... Kai tsaye d'aki ya wuce ya ajiye littafan sa kafin ya canza kaya ya nufo d'akin Goggo.
"Zulaihat bata a parlor sai Goggo dake faman saita radio...
"A'a Imamu an dawo Goggo ta tambaya tana murmushi...
"Imam ya k'arasa yana fad'in" Eh 'yar tsohuwa Allah yayi sun sake ni na dawo... Goggo ta murmusa tace toh bismillah maza kazo kaci abinci yau mutumin ka akayi d'an Wake... Imam dai murmusawa kurum yayi amma hankalinsa yafi karkata ta ina zai hango Zulaihat...
"Goggo ta katse sa da fad'in" Lafiya dai koh... D'an jim yayi kafin yace " Goggo Zulaihat fah..
"Goggo ta d'an rage murya kafin tace " Tana ciki yau haka nan ta wuni, k'ila bata jin dad'i ne, maza ka shiga ka tambaye ta nasan zata fad'a maka...
"Bata jin dad'i ya fad'i fuskar sa fal damuwa... Mik'ewa yayi ya nufi uwar d'akin goggo yana fad'in barin duba ta kana yayi knocking a k'ofa....
"Da sauri ta shiga goge hawayen idanunta kafin ta d'auko mayafi ta rufa snn ta basa izinin shigowa...
"Tun daga ganin yanayin ta yasan babu lafiya... K'arfin hali ta shiga yi tana k'ok'arin d'aura murmushi saman fuskar ta tace " Student yau baka dawo da wuri ba, you got us worried ...
"Tsareta da idanu yayi kafin yace " Meke damun ki, ..."Far da idanu tayi tana masa hararan wasa kafin tace " Ban gane ba, I'm fine..
"Imam ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " you look so weird, snn goggo tace min yau haka kika wuni, ... By now kinsan na sanki sosai... So just tell me what's up with you...
"Zulaihat ta share hawayen da taji sun ciko mata idanu.. " Cikin zuciyar ta take fad'in" I can't share it with you Imam, I can't tell anyone, I'm so scared.....
"Imam yayi shiru yana karantar ta, a hankali yace " Ko ana maki wani abinda baki so ne...
"Girgiza kai tayi kafin tace " Never, kawai.... Kawai... I'm just missing home ne, even though my momma died I still want to see my father again, dukda watsar da rayuwata da yayi, I wanna see him again and ask for his forgiveness, nasan ba laifin sa bane, laifin evil step-mom d'ina ne.....
"Tausayin ta Ya cika zuciyar Imam, cikin sanyin murya ya shiga lallashin ta yana nuna mata insha Allah zai kaita har Adamawa wajen mahaifin ta...
"Murmushin yak'e kurum tayi cikin zuciyarta kuwa baubuwa ne da dama suka mata cunk'us... Don kuwa babban abin takaicin ta shine ta kasa yakishe soyayyar Umar cikin zuciyar ta....
************
"Ya jima yana tsaye a waje babu Kausar babu alamun ta... Sai faman d'aga kai yake yana hangen benen gidan...
"Asmah ta kuma suban ta a karo na biyu tace don girman Allah Kausar kije ki sallame sa wllhi ba tafiya zaiyi ba idan bakije bar, kinga babu yanda Mal Liti baiyi dashi ba, yak'i tafiya...
"Mik'ewa Kausar tayi a fusace kafin tace " This is the worse mistake of his life... Wllhi sai yayi nadamar tako k'afarsa gidan nan..... Da k'arfin gaske ta fizgi k'ofa ta fice...
Sameena ce ๐๐พ
[1/23, 22:29] โช+234 803 619 0581โฌ: ๐๐๐๐ *ZUBAIDAH*
77
*ยฉSameena Aleeyou...โ๐พ*
_๐KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ๐ค_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*This chapter is your Meemah darling ๐๐น*
"Tun daga nesa zuciyar ta ke tafarfasa, babu komai cikinta illa tsana da k'yamar sa.
"Hasken tangama tangaman security lights da ya k'awata gidan ya haske mata fuska... Wani sanyi ya ziyarci ran Salim. Murmushi ya soma dukda tsantsan fushi dake hangowa kwance saman fuskar ta.... Baki na rawa ya soma fad'in" Sweetheart I missed you...
"What the heck brought you here...?? Kausar ta katse sa da fad'in haka cike da masifa sai faman huci take...
"Salim Ya d'an juya idanunsa gamida shafan sumar sa kafin yace " Kausar you and I need to talk.... But before then ki bari na maki ta'aziyan rashin da mukayi na Pappy snn ki shigar dani na gaida Mumsy na mata ta'aziya.... "Bai kai aya ba yaji sauk'ar mari a face d'insa...
"Rik'e da k'uncinsa yake duban ta yanda take huci, fararen sleepy eyes d'inta sun koma jajazir sabida tsananin b'acin rai... Sharewa yayi kafin yace "I'm sorry.... "Takaicin duniyar nan ya cika Kausar.... Bai k'arasa magana ba ta shiga nuna masa hanya tana fad'in" Get out... Get out of here, you really have no shame, how dare show your face here after all the damages you and your family caused to my family .....
"Girgiza kai Salim Ya soma yana fad'in" No Kausar dan Allah ki saurare ni.. I knw I hurt you, I tore your heart into thousand pieces.... Do you think I'm not also suffering, rubuta maki takardan saki da nayi yafi komai jefani cikin tashin hankali, Kausar I can't do without you, pls have pity on me... Don't turn your back on me.... Nasan kema kina sona I know you does...
"You miserable liar, you never loved me.... Just get out of here already... Ka fita kafin na kira maka 'yan sanda, you rachet criminal... Muryar ta Ya soma shaking hawaye ya soma zuba mata sanda taci gaba da fad'in" You destroyed my life.... You ruined it completely, you nothing but a disaster.... I hate you I hate you Salim Dasuki so very much... Ta k'arasa ta shiga dukan sa a k'irjinsa da duka hannayen ta biyu tana kuka take fad'in" Ka fice ka bar mana gida get out... You disgusting I hate you... "Hannayen ta Ya shiga k'ok'arin rik'ewa yana fad'in" Enough Kausar, Calm down for heaven's sake... Fizgewa take tana fad'in "Let me go you rachet rapist, why can't you just admit already ....
" Da k'arfi ya rik'e hannayen ta idanunsa sun kad'a sunyi ja sosai kafin yace " Yes I admit I raped her, but you know what.. I did not anticipate that to happen.... I was forced to go there by Labib....... Da k'arfin gaske ta fincike tana dubansa da wani irin tsana da k'yama.. Ta shiga ja da baya da baya... Tana girgiza kai...
" Dafe kansa yayi kafin ya soma fad'in" Kausar listen to me, my love..... Kan ya ankara sai jiyo k'aranta yayi ta bugu da baya k'arafun da aka gewaye wasu manya manyan flowers dasu.... A sittin yayi kanta yana k'walla mata kira....
"Mumsy da Asmah a tamanin suka nufo downstairs dan sunji k'aran da Kausar tayi da kuma muryar Salim na kiranta..... "Gaba d'aya Mumsy kam ma bata san da zuwar Salim ba ..
"Rik'eta Salim yayi yana jijjigata yana fad'in" pls ki tashi Kausar pls kinji my love.... Jinin da yaga yana bin k'afafunta ya jefa sa cikin tsananin tashin hankali..... " Mumsy Murya na rawa ta soma fad'in" Me kai mata, what did you do to my daughter... Girgirza kai kurum Salim yake yana fad'in" No Mumsy I didn't do anything.... We really need to take her to a Doctor..... " Jawota Mumsy tayi da k'arfin gaske tana fad'in" Let go of my daughter, kar ka sake tab'a min 'ya kai ba mijin ta bane..... Daidai nan Asmah ta k'araso da 'yar 406 d'insu da ta masu saura a gidan tace " Mumsy mu tafi asibiti. The baby.... Cikin sauri Mumsy ta rungumota suka shige mota sai cije baki Kausar take har lokacin idanunta a lumshe...
"Mumsy murya a dake ta juyo ta dubi Salim tace " Duk abinda ya sami 'Yata I'll have you arrested.... Daga haka Mal liti ya bud'e masu gate cikin tsananin tashin hankali, sai tuhumar kansa yake me yasa ya bud'e ma Salim gate, yasan ba don Hajiya tana cikin tashin hankali ba da tai masa fad'an hakan...
"Kasa gaskgata abinda kunnuwar sa suka ji masa yayi, knn Kausar ciki ne da ita, she's pregnant, murmushin da baisan daga ina ba ta b'alle masa a fili yace " I'll be come a father... Ya kasa rufe bakinsa... Cikin sauri ya nufi motar sa Benz 4matic E350.... Da mugun gudu ya shiga bin bayan su.... Ta mirror Asmah ta hangi Salim. Cikin sauri ta d'au wayar ta ta shiga neman layin Ansar bai d'agawa.... Jin bai d'aga ba yasata neman layin Detective Amir don ranar Ansar yayi amfani da wayar ta Ya kira DT Amir.... Amir na d'auka ta soma magana cikin sauri..
"Hello DT, this is Barr. Asma'u, Barr. Kumo's fiancee... pls we need security, a guy's been harassing my sister ... Snn kawai akwai matsala DT yanzu haka muna hanyar asibiti I can't text you location coz I'm driving... Pls help us with some cops...
"Cikin sauri Amir ya mik'e yana kallon Ansar da Hafiz WA'enda ke jiran fitowar Jalal kafin yace " Okay Barr try to text me the location as soon as possible I'll be there in some minutes..... Daga haka ficewa yayi ko gaya masu Ansar beyi ba ya nufi ride d'insa ...
****************
"Ansar ya dubi Jalal kafin yace " Da nasan wajen Tariq zakaje wllhi da ban k'yaleka ba, Jalal ya kamata ka rage wann zuciyar taka, kullum ina fad'a maka haka... Yanzu kaka babban case d'in dake gaban mu, ...
"Waima ba wann ba, ina ka shiga ne kam tun bayan sallaman ka daga asibiti...
"Jalal ya fuzar da iska kafin yace " I was kidnapped...
"Kaman daga sama haka Ansar yaji batun.. Ya maimaita.. " You were kidnapped, by who..???
"Gyad'a kansa yayi kafin yace " That Jerk kidnapped me from the hospital, nan ya labarta ma Ansar duk abinda ya faru....
"Cike da mamaki Ansar yake kallon Jalal... Girgiza kai yayi kafin yace " I don't get you man, you mean to say you went through all this... "Com'on Jalal why didn't you report right away.....
"Hannayen sa duka biyu ya d'aura saman table d'in dake gaban su kafin yace " That idiot is capable of murder, I don't want him to hurt either of my family , and he also threatens to kill Zubaidah idan nayi wani abu foolish... I just had to obey his rules.... Ka gane Ansar bana so su san wann zancen keep it between us... Idan ka fad'a masu hankalin su zai dad'a tashi, what worries me now shine ni ina kulle a nan snn wancan scumbag d'in yana yawo a tsakanin Al'umma I'm afraid he might does something to my wife.... Ansar you need to look after them more than ever for me now....
"Ansar ya shafi kansa kafin yace " Kanaga bazamu filing complaint ba...
"Girgiza kai Jalal yayi kafin yace "No point of doing that, kar ka mance already ina cikin babban Case a yanzu haka, no one will believe me, snn banida wani prove, ko kuma iyakacin shaidar ku saidai kuce nayita maku waya ina texting naku ina ce maku neman Dr naje... So ka gani babu prove.. "Yanzu yaushene suka ce za'a yi transferring d'ina to prison.
"Ansar ya fuzar da iska kafin yace " D'azu daga prosecution office muke, the prosecutor suggested that you'll be transpiring to prison by next week muddin ba'a sami wani genuine evidence ba cewa you're not guilty....
"Jalal ya fuzar da iska kafin yace " How's Zubaidah..
"D'an girgiza kai Ansar yayi kafin yace" You knew the answer though, don't ask me of that again.....
"Murmushi k'arfin hali Jalal yayi kafin yace " Okay fine bazan k'ara ba.... Ansar d'inma murmushi yayi kafin ya mik 'e yace "Zakiya magana da Hafiz... Gyad'a kai Jalal yayi without saying a word.... *
"Suna isa asibiti likitoci suka amsheta, babu yanda Mumsy batayi Salim Ya bar Asibitin nan ba yak'i, rok'onta yake pls ta barsa yasan condition d'in da babyn sa ke ciki.... Wani takaici ya kuma cika Mumsy ganin ta abinda ke cikin Kausar yake bata lafiyar d'iyar ta ba... Mumsy ta tsoratasa da fad'in" Zasuyi Filing restraining order against him, amma inaa Salim bai saduda ya tafi ba.... Ana a haka DT Amir ya k'araso asibitin. Baiyi mamakin ganin Salim ba don yasan shine tsohon mijin Kausar..
"DT Amir babu yanda baiyi da Salim ya tafi ba fir yak'i tafiya, k'arshe ma sai cewa yayi, idan son Kausar yake gwarama ya daina don tasa ce har abada... Amir ya harzuk'a ya cakumo Salim.... Da k'arfin gaske ya fitar dashi daga reception d'in.
"Su Mumsy da Asmah suka shige cikin d'akin sanda Dr ya lek'o yace suna iya shigowa...
"Kwance suka hangeta saman gadon hawaye na Bin k'uncinta hannayen ta d'aure saman cikinta, cikin kuka take fad'in " My baby, I lost my child, I'll never forgive Salim.... Kuka sosai ya kufce mata...
"Mumsy da Asmah suka k'arasa suka rungume ta suna sharan hawaye.. Lallashinta suka shiga yi ta hanyar k'arfafa mata gwiwa..
"Kausar ta goge hawayen ta kafin tace " Dan Allah kar ku barshi yazo yanda nake wllhi na tsane sa..
"Mumsy ta shafi kanta tace " it's okay sweetheart bazai zo ba, Detective Amir ya kore sa, he won't border you again..
"A