Showing 123001 words to 126000 words out of 210924 words
"Take annurin fuskar Umar Ya d'auke cak don kuwa ba komai yake hangowa ba illa fuskar Zubaidah, all he was dreaming about shine ta haifa masa yara, Ya gina masu rayuwar su su biyu, but they ruined everything, all his plans...... Saida Innah ta buga kujeran da yake zaune akai kafin ya dawo hayyacin sa , gamida sauk'e nannauyiyan ajiyan zuciya....
"Innah ta girgiza kai kafin tace " Baka daina tunanin ta ba koh, na sanin tunanin Zubaidah bazai tab'a barinka kayi aure ba, har yaushe ne zaka gane Zubaidah ba taka bace, bazata tab'a zama taka ba, ka rungumi k'addara Ka nemi wata ka Aura, ga 'yammata kyawawa a gari sai....... Innah bata kai aya ba ya katse ta cikin tsananin d'aga murya yake fad'in" Noo no, she's mine, she supposed to be here with me, tawa ce ni kad'ai, nasan she still loves me, har yanzu nasan tana so na, and I'll take her back coz she belongs to nobody but me, me alone....... "Baki kurum Innah ta saki tana kallon sa tamkar zautacce, anya bai sami Tab'in hankali ba, itafah batama gane sunbatun da yake yi ba, tabass dai akan Zubaidah ne, _oh ni Fulera anya bazan bar barikin nan ba na koma gida na nema ma yaron nan magani ba kafin haukar tasa tayi tsamari.... "_ ta fad'i haka cikin zuciyar ta...
"D'an fuzar da iska yayi gamida tattare naman gishin sa kafin yace " Am am kiyi hak'uri Innah, yasa hannu a pantpocket d'in sa ya ciro kud'i kafin ya ajiyesu saman center table yace " Innah GA wann, tafiyar nawa bazai wuce sati guda ba, I'm quite sure wnn zai isheki, munyi magana da wani company masu bada contract na ma"aikata zasu turo yarinya guda wacce zatana kula dake, har girki ma zata ke maki, idan tuwon kike buk'ata ma zata maki.....
"Kallonsa kurum Innah take zuciyarta na raya mata d'anta ba kansa d'aya ba, k'ila shaye shaye ya soma, bacin haka miye wani constras (Contract) ." Magana ta soma masa ta harshen fillanci nan ya fayyace mata duk abinda yake nufi....
"Agogon hannunsa ya kalla kafin ya nufi upstairs ya tattaro abin buk'atar sa ya kuma yima Innah sallama don baiso ya makara kafin ya fice, Ya nufi Mercedes d'insa GLK 350 ,Da d'an banzan gudu ya fice daga gidan kaman mai shirin tashi sama..... Yana cikin driving kiran Alh Kasim ya shigo masa...
"D'agawa yayi gamida sawa a speaker kafin ya soma amsa wayar.
"Daga d'aya b'angaren Alh Kasim yace " Da fatan ka isa garin Gombe.....
"Murmushi rainin hankali Umar yayi kafin yace " Me kake ci na baka ke zuba Alh Kasim, ka kwantar da hankalin ka kaman tsumma a randa, Jalal will not show up in the Heroine, you have my word...
"Alh Kasim yayi wata murmushi kafin yace " Make sure you get the job done..... "Katse wayar Umar yayi lokaci guda yana hango fuskar Jalal.. A hankali ya furta " You must leave her for good, you Trap....
******************
"Sanye yake cikin bak'ar shirt wanda ya d'an kama jikinsa kad'an, farar fatar sa ta dad'a haskawa sosai, nininke kayan sa yake kanyi yana jerasu cikin luggage d'insa, fuskar sa fal fari'a kama daga kan likitoci yayi kan nurses kai har zuwa kan masu shara da goge goge na asibitin sun shaida irin farin cikin da Jalal ke ciki a yau, gobe War haka yana tare da princess d'insa by God willing..... Shattima da Ummah ne sukayi sallama a k'ofa .... "Da fari'ar sa ya Mike ya isa k'ofar yana masu iso....
"Sosai Ummah taji dad'in ganin yanda Jalal ya warke sosai, gaisawa suka soma yi gaba d'aya , Jalal da Ummah sun sake sosai tamkar sun jima da sanin juna... "Shattima ya jawo luggage d'in yana ci gaba da shiryawa yake fad'in" Patient you should have leave this to me ai, nazo na k'arasa ladana..... " Murmushi kawai Jalal yayi kafin ya dafi kafad'an Shattima yace " Bro you have done enough, Allah NE kurum zai biyaku all, banada bakin maku godiya...... " Ae ae pls don't even start patient, Ummah kinjisa koh zai soma.....
"Tab'e baki Ummah tayi tana kakkab'e slippers d'in Jalal wanda yake d'an zagayawa dashi take fad'in" Ni maza kuzo ku nemo min Dr Madi d'in idan za'a iya sallaman yau ai gwara a yi, don na dama masa fura na tarba.... Ta k'arashe maganar tana saka takalman cikin leda....
"Gaba d'aya saida Jalal da Shattima suka dara.... Shattima yace " Ummah kin manta Dr Madi yaje duba Mai Martaba kinsan baiji dad'i ba....
"Jinjina kai tayi kafin tace haka kuwa akayi, d'azu kafin Baba Waziri ya fice fada ya fad'a min, kunsan kwanyar nawa abubuwa sun masa yawa, ko damuwarka da Ameera sun isheni.....
"Shattima ya d'an tab'e fuska ba tareda yace komai ba... Jalal kuwa haka kurum ya tsinci kansa da fad'uwan gaba.... Tabbas yasan Dr Madi shine likitan Mai Martaba a iya zaman su, don kuwa shine case din Jalal ke hannunsa...
"Fatan samin lafiya Jalal yayi ma Mai Martaba duk suka amsa da Ameen, snn ya k'ara da gobe insha Allah kafin mu wuce gida sai mu biya na mik'a nawa gaisuwan.....
"Jinjina kai kurum Shattima yayi amma harga Allah baison duk wani abunda zai kaisa fada a halin yanzu, avoiding komai na fada yake sabida guje ma ganin Zahida musamman da yanzu ya rage saura sati biyu kacal bikinta da Khalifah, Umma kanta ta gane haka.... Ganin change d'in da ya wanzu a fuskokin su yasa jikin Jalal yin sanyi... Bai kuma tada maganar ba saida suka zo tafiya, Bayan Ummah ta fice yake tambayar shattima dalilin sudden change d'in... Shattima ya d'anyi jimm kafin yace " We would talk about it bro, zan dawo da dare... Cike da tausayawa Jalal ya gyad'a kai don yasan dole it must be something serious...
"Sun d'an jima a wajen Jalal kafin suka wuce don dama anguwa Shattima zai sauk'e Ummah suka biya ta wajen Jalal.....
****************
"Dr Madi ya kuma kallon tabon dake shimfid'e gefen kafad'ar Mai Martaba wanda bai tab'a gani ba sai yau, Ya tuna exactly tabon dake kafad'ar Jalal kenn ta bayan sa, Ya tuna Mai Martaba da Jalal have same blood group... Kai they have something in common aside from that akwai genetic signs da suke dashi......" Gyaran muryar da Mai Martaba yayi ne yasa Dr Madi saita kansa kafin yace " Ayimin afuwa Rankashidad'e..... "D'an murmushi Mai Martaba yayi kafin yace " Dr knn yaya jinin nawa ya sauk'a....
"Saida Dr Madi ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Allah Ya taimake ka jinin ka ya sauk'a amma lallai idan son samu ka rage yawan damuwar da kake,..
"Mai Martaba ya jinjina kai sanda Dr Madi yake gyara masa zamar rigar sa 'yar shara..
"D'an gyaran murya Dr Madi yayi kafin yace " Allah Ya taimake ka ina son sanin wata irin damuwa ce haka take damun ka, Ayimin afuwa idan na wuce hurumi na....
"Maiartaba yayi k'asaitaccen murmushi kafin yace " Likita sam baka wuce hurumin ka ba, tsakani na da kai ya wuce haka, Ko Dr Mansoor na K'asar Egypt bai kaika kusanci dani ba, na yarda da kai d'ari bisa d'ari kamar yanda na yarda da d'ana Shattima...
. "Dr Madi ya murmusa cike da k'arfin gwiwa kafin yace " Godiya nake Allah Ya taimake ka...
"Mai Martaba ya gyad'a kai lokaci guda yana kallon hoton jinjirin dake mak'ale a d'akin kafin ya soma fad'in" Shine damuwata, shine ke hanani bacci duk ranar dana tuna banga gawarsa da idanu na ba, ina ganinsa cikin barci na ya zama bababban saurayi magidanci, inama ace zan kuma saka sa a idanu na, inama zan gansa na mallaka masa duk wani abinda na Mallaka........ "Dr Madi dai kai dubansa yayi ga hoton da Mai Martaba keta magana dashi.... Gabansan ya yanke ya fad'i, a fili ya furta JALULDEEN, gyad'a kai ya shiga yi yana kallon Mai Martaba yake fad'in" Allah Ya taimake ka, shine wllhi shine, your long lost Son is here, wllhi Shine Jalal, wllhi yanada Tambari irin wanda kake dashi a kafad'ar ka...... Babu shiri yaga Mai Martaba na mik'ewa tsaye ba tareda ya iya furta koda kalma guda ba........
"Ummi dake tsaye jikin labule cikinta yabada wani irin k'ara wanda idan ba sa'a ba mutanen dake waje ka iya jiyowa, girgiza kai ta soma tamkar zararriya kafin ta fice da saurin gaske gudu gudu..
"Ward d'in Amenity tayi tsit tamkar babu kowa, Ya jawo abin rufe hanci wanda likitoci ke amfani dashi ya rufe bakinsa da hancinsa, gyara zaman labcoat d'in dake jikinsa yayi kafin ya shige d'akin da aka tabbatar masa shine na Jalal......
"Ya tada iqaman sallah knn yaji bindiga a kunkuminsa,... Umar Ya kwanto da kansa saitin kunnen Jalal kafin Ya soma fad'in" If you misbehave I'll kill you right here, now let's get going.. Kunkuminsa ya rik'e tamkar likita suka soma tafiya....
*Tom readers... Dan Dan Dan..... Kai I won't say a word..Just Find out in the next page.... π*
Queen Samy ce
[1/23, 22:27] βͺ+234 803 619 0581β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
70
*Β©Sameena Aleeyou...βπΎ*
_πKAINUWA WRITERS ASSOCIATION π€_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
_Ina kike darling Aunty Fauzah ... Wann shafi naki ne ke kad'ai tol... Allah Ya bar mana ke sweetheart πβ€π_
"Gudu gudu sauri sauri Ummi ta nufi sashenta, Uwar d'aki ta shige ta zube saman gado tana maida numfashi da k'yar.. Abubuwan da suka faru shekaru ishirin da d'oriya baya suka shiga dawo mata.... Lamid'o Modibbo, Lamid'o na raye..... Girgiza kai ta soma ita kad'ai ta soma sunbatu... " Kai dukda nasan nice na hana a k'ashesa amma an tabbatar min Lamid'o bazai tab'a dawowa ba, in fact yayi nisa da masarautar nan..... " A haka Jakadiya ta iso cikin sauri ta tadda Ummi....
"Cike da rusunawa Jakadiya take fad'in" Allah Ya taimake ki da fatan lafiya na tadda ki..
"Ummi jiki na rawa take girgiza kai tana furta " Jakadiya ina so na had'u da yaya Ciroma duk yanda za'ayi....
"Jakadiya ta zaro ido waje don kuwa ba komai ne ya fad'o mata ba illa bak'in aikin da suka aikata shekarun baya......"Ummi ta katse mata tunanin cikin daka tsawa.... "
"Da sauri Jakadiya ta saita kanta kafin tayi saurin rusunawa tana fad'in" Tuba nake Allah Ya taimake ki, zan tafi yanzun nan babu b'ata lokaci..... Daga haka ta nufi k'ofa har tana tuntub'e.... Doka mata kira Ummi ta kuma yi wanda yasata dawowa babu shiri ta zube saman tiles...
"Zagaya d'akin Ummi take tana huci, komai na shirin rincab'e mata a lokacin da take cikin tsananin farin ciki na aurar da d'iyarta... Kai dole tasan yanda zatayi ta hana Lamid'o dawowa rayuwarta, dole Ciroma yasan yanda zaiyi su b'atar da wann zance idan ba haka ba kuwa wllhi wllhi Zahida bazata auri Khalifa ba......
"Sunkuyo da kai tayi tana duban jakadiya kafin tace " Jakadiya kin tabbata kin jefar da Lamid'o yanda babu wani d'an wann masarauta da zai tsince sa....
"Cikin Jakadiya yabada wani irin k'ugi.... Tambayarki nake " Ummi ta kuma daka mata wata tsawan...
"Jakadiya ta shiga gyad'a Kai tana fad'in" Allah Ya taimakeki na rantse da girman zati nayi yanda kika umarce ni, da hannaye na jefar da Lamid'o gaba jeji baya jeji, dajin da idan kuraye da zakanya basu cinyesa ba toh kuwa tabbas saidai fulanin daji masu kiwo su tsince sa.....
"Ummi ta goge gumin da ya keto mata kafin tace " Jakadiya Lamid'o yana gap da dawowa wann masarauta, Jakadiya bansan yaya zanyi ba muddin asiri na ya tonu..... " Jakadiya ta mik'e da sauri ta tallafi uwar gijiyan nata ta zaunar ta saman gado tana mata kalamai masu taushi duka tashin hankalin data tsinta kanta ciki, don kuwa tasan tabbas k'wai ta fashe za"a yanke mata hukunci mafi tsauri ita kuwa Fulani Kilishi iyakaci a maidata masarautar su da takardan saki.....
"Takarda da alk'alami Ummi ta d'auka tayi rubutu kafin ta aiki Jakadiya ta isar da sak'on zuwa hannun Baba Ciroma tunda shine silan komai.....
**************
"Dr Madi ya girgiza da ganin yanayin Mai Martaba... "K'irjinsa ya rik'e ba tareda ya iya furta komai ba.... " Sai yanzu yake ganin kuskurensa na sanar da Mai Martaba wann batu despite his health condition, ba son ransa bane he just couldn't help it ne shi kansa..... " Zubewa a k'asa Mai Martaba yayi yana rik'e da k'irjinsa....
"Cikin tsananin tashin hankali Dr Madi ya shiga k'ok'arin ceto rayuwar Mai Martaba in any way possible..... Waya yayi asibiti ba tareda b'ata lokaci ba, ....." Yana cikin danna k'irjinsa Baba Ciroma da Kahlifah suka shigo.... "Cakumo Dr Madi Baba Ciroma yayi yana fad'in" Me ka masa me kayima d'an uwana, if anything bad happens to him I'll have you arrested..... "Jakadiya dake daga waje ta jiyo maganganun Baba Ciroma a tamanin ta nufi sashen Ummi ta sanar da ita, babu shiri Ummi ta fito cikin tsananin tashin hankali.....
**************
"Tunda suka shiga motar ya kunna Ac d'in motar take numfashin Jalal yaji yana tafiya shi kuwa Umar already hancinsa da bakinsa a rufe suke... Jim kad'an Jalal ya rasa a yanda yake.... " Gudu kawai Umar ke faman falfalwa bisa kwalta.....
"A hankali ya soma tari yana yunk'urin bud'e idanunsa.... " Zabura yayi zai mik'e yajisa a d'aure gamgam jikin kujera, tundaga hannayen sa har zuwa k'afafunsa a d'aure suke, snn anyi sealing bakinsa da k'atuwar sellotape....
"Kallo ya shiga k'are ma wajen da idanunsa, kangon waje ne snn da alama cikin daji ne, don baka jiyo komai sai sautin kukan tsuntsaye..... Ya jima a haka kafin Ogan ya shigo cikin tafiya ta k'asaita, hannunsa rik'e da kwalban wine sai tangad'i yake tamkar zai kifa k'asa..... " Banda wani irin mugun kallo da Jalal ke watsa masa baya komai, baki a rufe babu halin magana. ...
"K'arasowa Umar yayi gaban Jalal yana k'are masa kallo kafin ya fashe da wata irin dariya yana nuna sa da kwalban wine d'in yake dariya kaman tababb'e.... Lokaci guda ya daina dariya fuskar sa ta koma tamau babu d'igon annuri balle imani..
"Hannu yasa ya dafi kafad'un Jalal cikin muryar maye ya soma fad'in" Jalal the Hero... Let's see if you can protect your wife again..... Opss na mance " She's never yours and she's never going to be yours.... Zaka rabu da ita a yau d'in nan like it or not Buddy...... "
"Zabura Jalal yayi yana yunk'urin yin magana, babu hali, gaba d'aya jijiyo jikinsa sun tattashi... Huci kawai yake yana watsa wa Umar kallon tsana......
"Dariya Umar Ya kuma fashewa dashi kafin ya ciro wayarsa ya shiga video d'in Jalal yana fad'in" You know you look good here, this is exactly where you belongs...... Oya d'ago kanka da kyau so that na nuna ma matarka kafin na kashe ka..... "Ya kuma fashewa da dariya kafin ya shiga juye ma Jalal wine d'in a jikinsa yana fad'in" Nasan kayi missing d'insa coz yanzu ka daina sha, kar ka damu I've alot here, I'll bury you with 10 bottles kaje can kayita sha..... Ya k'arashe yana wata muguwar dariya.....
"Saida ya gama yima Jalal wulak'anci iri da kala kafin ya jawo kujera ya zauna gaban Jalal suna facing juna "
"Bayan wucewar wasu dak'ik'ai Umar Ya soma fad'in" It will be very simple if you cooperate, abu d'aya zakayi and you'll be set free.... So your time starts now.... Ya k'arashe yana duba agogon hannunsa kafin yasa hannu ya d'aye selotape d'in dake manne a bakin Jalal....
**************
"Alluran bacci Dr Madi dole yayi ma Mai Martaba kafin ya shiga basu hak'uri yana fad'in" Su kwantar da hankalin su idan Allah yaso babu abunda zai faru, da zaran ya sami bacci ya farka shiknn...... Yana cikin bayani wayar Shattima ya shigo masa...
"Gani sukayi ya mik'e cikin tsananin tashin hankali sanda yake amsa wayar, a daburce ya furta " Jalal ya b'ace, innalillahi wa Inna'ilahirraji'un... Ganin nan zuwa, I'll be there right away..... Katse wayan yayi ya shiga bama su Ummi hak'uri yana fad'in" Suyi hak'uri but he really needs to go, don an nemi patient d'insa an rasa.... Daga Ummi har Baba Ciroma hakan ba k'aramin dad'i yayi masu ba, don kuwa yanzu zasu san makomar data dace da