Showing 87001 words to 90000 words out of 210924 words

Chapter 30 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22873

"Khalifa yayi wata k'asaiteccen murmushi kafin yace " Ko kuma kana tunanin Gimbiya Zahidar ka ta kusa zama Mallaki na a ranar da za'a nad'ani sarautar Yariman masarautar nan...

"Galala Shattima ke kallonsa kana yayi murmushi yace " Zahida ta fah kace.

"KKhalifa ya gyad'a kai yace " K'warai kuwa kowa yasan irin shak'iwar dake tsakaninku tamkar yaya da k'anwa, a ranar data zama matata zan saka maka katangar k'arfe tsakaninku tunda de kai ba muharraminta bane..

"Murmushi kawai Shattima yayi sanda yake d'ale doki had'i da yin gajeren tsaki kafin yace muje da Allah, dan wllhi muka k'ara minti biyu bamu fita ba zan fasa fita kilisan nan....


"D'ale doki Khalifa yayi yana mai ci gaba da fad'in jikina na bani nine sarki mai jiran gado.

"Shattima baice komai ba sai tunanin da yake yawan yi a 'yan kwanakin wanda ya rasa ma waye zai soma fad'i gashi abun ya damesa sosai...

*Manage this 'yan uwa zaku jini later insha Allah... 😘😍*
[1/23, 22:23] β€ͺ+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZIBAIDAH*

54


*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...πŸ“–πŸ“š_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*



"Kai tsaye gida ya wuce bayan sun sauk'a daga dawakin.

"Parlron Ummansa ya shige ya tarar babu kowa sai TV dake faman aiki.
"Zama yayi gijif cikin sofa gamida turo hulansa gaban goshi ya lumshe idanunsa,
"Umma ce ta fito tana k'wala kira wa Ameera k'anwar Shattima.... A'ah Shattima yaushe ka shigo, Umma tace sanda take zama cikin d'aya Daga cikin kujerun.

"D'an mik'ewa yayi ya zauna sosai kafin yace " Ummah barka da gida.

"Tsaresa tayi da idanu don ta lura da canzawansa kwana biyu.
"Bud'e murya Umma tayi kafin tace " Kai wai lafiyanka kwana biyu kake neman zama lusari, gaba d'aya ka canza kaman bakai ba, idan akan auren yarinyar nan Zahidah da Khalifa ne, na fad'a maka ka cire ta a ranka, Zahidah ba matarka bace sanin kanka Baba Ciroma ba barin wani zaiyi ya auri Zahidah ba tunda ya k'wallafa ma wann d'an nasa mai wuya kaman marken lema....

"Tunda ta soma magana Shattima ke kallonta, Umma dai bazata Tab'a canzawa ba, wnn masifa nata ya rasa taxation da ita...

"D'an jim yayi kafin yace " Umma am I that obvious??

"Wani uwar harara ta kuma watsa Masa kafin tace " Bana son iskanci Karma ka soma min turancin rashin kunya ka bud'e baki ka fad'a min abunda ke damunka baka da wacce ta wuce ni mahaifiyarka...

"Shattima ya kuma sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Ummah ba tunanin Zahidah nake ba, besides na cire Zahidah a raina tuntuni tunda yau wata uku cif ya rage aurenta da Khalifa childhood friend d'ina, abinda ke damuna wani abu ne daban snn tun da akayi maganar aurenta take avoiding d'ina, Umma bazan iya jure rashin maganarta a gareni ba..

"Shek'ek"e ta kallesa kafin tace " Au ka yarda ka bari wani ya aureta, ka yarda ka badakai a aura mata wanda bata so...

"Kllonta kawai Shattima keyi cike da mamakin halin Umma saikace ba itace yanzu take masa fad'an ya cire Zahidah a ransa ba..

"D'an fitowa yayi daga cikin kujeran ya turo gaba kafin yace " Umma ba wann ba, wani tambaya nake so na maki..

"Ina jinka menene?? Ta fad'i tana karyan goro.

"Tab'e fuska yayi yana dubanta kafin yace " Umma wai Don Allah ke ba tsohuwa ba sai cin goro, bakisan illansa ba koh..

"Tab'e baki tayi gamida ci gaba da taunar goronta tana fad'in" Idan ka gama iyayinka da felek'en sai ka sanar dani Likita bokan turai, kai wannan da likitanci ka karanta da kad"ifirin naka da yauk'in yafi haka..

"Shafa kansa yayi gamida bata hak'uri.


"Saida ya cire hular kansa ya ajiye saman hannun kujera kafin yace " Umma kince mun matar Mai Martaba ta fari d'iyar sarkin Zazzau k'awarki ce kafin Allah Ya mata rasuwa...


"Cak ta tsaya da taunar goron da take tana dubansa, k'walla ya ciko idanunta,...

"Shattima yaci gaba da fad'in" Umma wai meye asalin labarin mutuwarsu itada jaririnta Modibbo,..

"Umma ta goge hawayen idanunta kafin ta soma fad'in" Dadda (sunan da ake kiran marigayiya matar mai martaba a masarautar)d'iya ce ga sarkin Zazzau wanda yake sonta sama da sauran 'ya'yansa, zata girme mun a shekare sabida lokacin da aka auro ta masarautan nan ba'a ma soma maganar aurena ba, auren soyayya na saurayi da budurwa sukayi da Mai Martaba, a lokacin da akai masa wankan nad'in sarauta a lokacin aka Aura masa ita..

"Sun d'au lokaci sosai Allah bai basu haihuwa ba, don har akayi aurena da mahaifinka shiru babu labari, Nida Matar Ciroma k'anin Mai Martaba a jere muka haifeku kaida Khalifa amma har lokacin shiru matar Mai Martaba bata haihu ba, kasan babban gida da k'anan maganganu musamman ganin K'aninsa ya haihu shi bai haihu ba, ..

"Mahaifiyar Modibbo da kanta ta rok'i Mai Martaba ya k'ara aure, snn ita da kanta ta zab'awa Mai Martaba yarinyar da zai Aura, ko ya sani a masarautar nan baya son auren amma sabida Mahaifiyar Modibbo da kuma Mahaifiyarsa shi kansa Mai Martaban suna so yasa sa amincewa, nan aka auro mahaifiyar Zahida a lokacin bata fi shekaru goma Sha biyar ba zuwa sha shida, ashe tun lokacin da akayi auren Mai Martaba da Ummin Zahida Dadda nada juna biyu babu wanda ya sani.... Bayan biki da kad'an cikinta ya bayyana, nan fah kulawa ya tattara ya koma kanta gaba d'aya, Mai Martaba har mancewa yayi yayi amarya, Madaki mahaifiyar Mai Martaba nan itama kulawarta ya k'arau sosai akan Dadda, wann dalili ya sanya Ummin Zahida cikin tsananin bak'in ciki ga k'uruciya da yarinta, a lokacin har saida suka sami sab'ani sosai da Mai Martaba, Dadda matar arziki 'yar Babban gida ita ta gyara komai, suka ci gaba da zamansu lafiya, taci gaba da rainon cikinta, wata tara cif ta haihu, haihuwar da ba'a tab'a irinsa ba a masarautar nan, anyi biki na haihuwarsa wanda ba'a tab'a irinsa ba yanda yaro yaci sunan Modibbo Lamid'o....... Kukan Umma ya tsananta.. Shattima ya tashi daga kujeran da yake ya dawo gefenta ya zauna gamida rik'o kafad'unta...

"Goge hawayen tayi kafin taci gaba da fad'in Daren da akayi suna da kwana bakwai daren data zama bak'in dare a wann masarauta daren da ya sauya farin cikin wann masarauta zuwa bak'in ciki, daren da har yau ya kafa tarihi a masarautar nan, daren da aka masa lakabi da BAK'IN DARE, a wann dare aka wayi gari aka tarar da gawan Dadda snn aka nemi Yarima Modibbo aka rasa......


"Kuka sosai Umma keyi har saida Shattima yaji dama bai d'ago maganar ba, da k'yar ya samu ya lallashi Umma tayi shiru. Mik'ewa yayi ya fice ya nufi d'akin sa yana tunanin al"amarin " What if Modibbo is still alive, what if..... K'irjinsa ta shiga bugawa da sauri da sauri, What if Jalal is Yarima Modibbo, But.... How's this be possible....? No way Jalal has his own family , mahaifiyarsa tana nan da rai, ta yaya ma zai soma fad'in wann abu, da Mai Martaba zai soma ko kuwa da Jalal zai soma.... Toh wai ma how did he come up with all this, dafe kansa yayi gamida zama bisa sofa, yana addu'an Allah Ya bayyana Modibbo a duk yanda yake matuk'ar yana raye...


*****************

"Hamma ne ya fita ya amsa sallamar da ake, ganin mutum cikin bak'ak'en kaya black suit yasa sa komawa cikin gida da gudo yana neman abun d'auka, can ya hangi muciya wajen wanke wanke ai nan ya rarumo muciyar nan ya nufo waje a guje...... Zubaidah dake kwasan shanya a sittin ta biyo bayansa tana tambayarsa lafiya...., Annah ma fitowarta kenn daga bayi ta ajiye butar hannunta tabi bayansu cikin sauri.

"Hamma kam fad'i yake " Turoka sukayi koh, wai zaka gane kuranka..... Da iya k'arfinsa ya nufi bawan Allahn nan, Zubaidah tayi ta maza ta k'wace muciyar hannun Hamma tana fad'in" A'a a'a Hamma....

"Barr Ansar Kumo dafe kansa yayi yana jiran ta Allah ta samesa...

"Zubaidah ta shiga jan Hamma yana fizgewa yana fad'in" Ki barni na gama dasu ki barni dasu Zubaidah, sunga babu Jalal suna tunanin zamu bari su ci zarafinki...

"Gida ta shige dashi yayinda Annah ta k'arasa ga Barr Kumo tana fad'in" Lafiya bawan Alla, idan Dasuki ne suka turo ka tun wuri gwara ka tafi kafin mu kira maka 'yansanda...

"Kallonta Barr Kumo yayi kafin ya sauk'e nannauyiyan ajiyan zuciya yace " Sannu Hajiya.... Em by the way sunana Barr Ansar Kumo, ni lauya ne daga k'ungiyar kare rajin hakkin bil adama musamman Mata da k'anan Yara....

"Cike da rashin hamsuwa Annah ke kallonsa don tasan Dasuki's zasu iya turo sa,... Zubaidah ce ta fito Hadiza na biye da ita....

"Barr Kumo ya dubi Zubaidah data masa k'uri yace " Kar ku damu banazo nan bane don cutar daku sai don taimaka maku ......
Katsesa Hadiza tayi da fad'in" Malam ka dubeka kasha bak'in kaya uwa d'an fashi kai ai da ganinka ma babu alheri a tare da kai, .. Hararan da Annah ta narka mata yasata yin shiru....

. "Girgiza kai Zubaidah ta soma kafin tace " Malam ka fad'a mana gaskiyan wanda ya turo ka wajenmu nasan sai ankai k"orafi kungiyarku snn kuke ba wa mutum d'auki, mu kuwa bamu kai ba don bamu da hanya, nasan su suka turo ka don fad'ar damu a kotu, Kayi wa Allah ka tafi ka k'yalemu, ka tuna idan hakan ya faru akan d'yarka yaya zakaji. Don Allah kar ka taimaka masu su ci gaba da zalunci...

"Tausayinta ya cika zuciyar Barr Ansar, sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yace " Kinyi gaskiya Zubaidah snn labarinki ya zama media circus, yasa hannu ya ciro jarida cikin 'yar jakan dake hannunsa ya nuna mata kafin yace " Kin gani, a halin yanzu labarin ki is everywhere a cikin k'asar nan, people are curious to know more about you, Zubaidah ni na kawo kaina nan da ra'ayina ba tareda taimakon wata k'ungiya ba....... Idonsa ya kad'a yayi ja sosai sanda yaci gaba da fad'in" Those Despicable are hiding behind their shadows, they must pay for each and single crimes they had committed....

"Gaba d'aya suka bisa da kallon mamaki sanda yasa bayan hannunsa ya goge hawayen da suka zubo masa.
"Annah jiki a sanyaye tace mu shiga daga ciki.....


"Daga yanda Faisal ya paka motarsa ya danna wayarsa, bugu biyu Alh Kasim ya d'aga " Ina saurarenka Faisal..

"Sir no doubt they've got an attorney.......

"Mik'ewa tsaye yayi yana fad"in what.!!!!!
"No way they can't find a lawyer, abinda nake so da kai follow him and see who's helping them, Faisal bana so a sami failure make sure kayi clean aiki... Yeah I trust you..... Daga haka ya katse wayar yana safa da marwa shi kad'ansa a parlour....


"Yanda Alh Kasim ya umurcesa haka yayi..... Har suka shigo cikin Abuja Barr Kumo baisan ana biye dashi ba. A k'ofar gidansa dake unguwar APO yayi parking ganin Asmah cikin tasi tana jiran isowarsa....

"Fitowa tayi daga tasi d'in sanda shima ya fito daga motarsa suka sakar ma juna murmushi. A hankali tace " My chewing gum how does go.

"Murmushi Barr Ansar yayi kafin yace " My silly girlfriend na fad'a maki ni nafi k'arfin your chewing gum saidai your super glue. D'an hararansa Asmah tayi kafin tace " I'm not your girlfriend you know....

"Murmushi yayi kafin ya kuma cewa we can't talk here mu d'an shiga daga ciki, hararansa ta d'anyi kafin tace " I hope su mommin ka na ciki...


"K'walla ya kuma ciko idanunsa sanda ya soma tafiya ba tare da yace mata komai ba, d'an girgiza kai kawai tayi tabi bayansa tana fad'in" Ansar bazaka daina wann hali naka ba, a da nayi zaton ko wani abu ke damunka amma yanzu kam na gane tsaf halinka ne....

"Gida ne apartment me kyaun gaske, saidai tun daga waje Asmah ta gane kaman shi kad'ai yake rayuwa a gidan, parlorn sa tsaf yasha furnished sai picture wanda ba sai ance maka na family d'insa bane, saidai duk hotunan yana yaro ne Wanda bai wuce shekaru sha biyu ba, harda 'yan k'annensa mace da namiji guda biyu....
"Drinks ya kawo ya ajiye mata ta dubesa da kyau kana tace " Attorney kasan dai bazan sha komai a nan ba tunda da alama 'yan gidanku basa nan.....

"Mik'ewa tsaye yayi in a furious tune yake fad'in " Yeah basa nan kuma bazasu tab'a dawowa ba, I'm all alone, I've no family, ya k'arasa ya d'auko hoto guda d'aya yana nuna mata yake fad'in" Kinsan dalilin da yasa farko nak'i amince wa buk'atarki, kinsan dalilin da yasa nace maki " I didn't want to have anything to do with that Despicable Kasim Dasuki...????

"Zaro ido kawai Asmah take tana girgiza kai, Ansar yaci gaba da fad'in" That Bastard is the reason why I'm all alone now, that imbecile destroyed my Family,
"My Father was an international Business Man, Kasim Dasuki ya yaudaresa ya saka kud'ad'ensa gaba d'aya a company d'insu, back then bana zama a k'asar nan, ina can Qatar da Grandmother d'ina, My Dad my Mum and my two siblings were living here in Nigeria, rana d'aya heart attack ya kama mahaifina sabida karyasa da Kasim Dasuki yayi, Dad d'ina ya shigar da k'ara baiyi nasara ba, sabida Kasim Dasuki is very powerful Man, Mum d'ina tayi jinyarsa ya soma, babu yanda banso naga Mahaifina ba amma babu kud'in da zanzo Nigeria, Grandma d'ina da take jinya itama a can Qatar depression na ciwon mahaifina ya mata yawa, kwana kad'an Allah yayi mata cikawa, ni kad'aina no family no relatives ga k'arancin shekaru haka da taimakon bayin Allah na k'warai aka kai grandma makwancinta, Dad d'ina yana riskan labarin shima Allah Ya masa cikawa, .... Kukansa ya k'aru sanda yaci gaba da fad'in" I couldn't have chance to say goodbye to my Dad, Mum d'ina ta d'aukaka k'ara dare d'aya gidansu tayi gobara k'urumus, da Mamata da k'anne na guda biyu all died a gobaran. Ban tashi sani ba sai lokacin da na saka k"afata a k'asar nan, bayan shekaru masu yawa, bayan all the hardships I gone through ni kad'aina a k'asar Qatar, aikatau babu kalan wanda banyi ba, har na sami kud'in jirgi na dawo, na tarar da wann bak'ar labari wanda nasan ba aikin kowa bane illa aikinsa sabida Mum d'ina ta d'aukaka k'ara shiyasa ya halak'asu. Wann shine dalilina na zama lawyer to bring Justice to the society,...... Zama yayi bisa sofa hawaye na bin k'uncinsa,
"Tausayinsa ya cika zuciyar Asmah batasan sanda hawaye ya shiga gangara mata ba. Hanki ta ciro cikin jakarta ta mik'a masa, ya karb'a ya goge hawayen kana yace " Thank you....

"Har Asmah ta isa layinsu jikinta a mace yake da jin labarin Barr Ansar, ta k'ofar baya ta shige hide....



"Faisal da sai lokacin ya karya kan motarsa ya danna wayar uban gidansa kana yace " Sir the Marafa's are the ones helping them....

"Murmushi Alh Kasim yayi kafin yace " Alh Tahir Marafa dabinmu da kai bata k'are ba, I'll prove to that no one messes with the Dasuki's.......

"Wayan Barr Munir ya kira kafin yace " Ka bincika wanene wann lawyer d'in nasu his profession at work and his family.... Sai naji feeback, do that fast attorney we don't have much time, kwana d'aya jal ya rage mana a shiga kotu....


"K'asar akwatin ta ta bud'e ta ciro zoben tana murmushi, tasan wann ba k'aramin amfani zai masu ba tunda za'a shiga kotu, tasan Alh Kasim Dasuki zai biyata mak'udan kud'i ta gudu ita da d'anta taje ta sami miji mai hankalk tsaranta ba wann susu shashan ba..... Wata dariya Hadiza ta kuma fashewa dashi kafin ta sunce bakin zaninta ta d'aure zoben, mayafin ta ta shiga yafawa.....



Sameena ce πŸ‘ŒπŸΎπŸ‘ŒπŸΎ
[1/23, 22:23] β€ͺ+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

55

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...πŸ“–πŸ“š_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login