Showing 150001 words to 153000 words out of 210924 words

Chapter 51 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22877

ya d'auko ledar d'azu ya saya masu snacks da drinks a wani restaurant kafin su fice daga garin Jos kafin ya mik'a mata yace " Oya eat before you fall sick....

"Banza ta masa sai kallon glass d'in window take lokaci guda tana share hawayen da suke zubo mata.... "Har cikin ransa yake jin takaicin abunda take masa, but ba yanda ya iya, he just have to put up with her shits for the mean time idan dai yana so ya Mallaki Zubaidah. He has to win Zulaihat back...
"A hankali cikin wani salo na murya ya furta " When did you hate me that much.... "Shiru bata kulasa ba... Hannun sa guda ya Saki steering wheel dashi ya d'aura saman hannunta.....
"Da sauri ta janye hannunta tana watsa masa harara kafin tace " Kar ka kuskura ka sake tab'a ni, na fad'a maka wann ba Zulaihat d'in da ka sani da bane...

"Had'iyan kalamanta yayi yace a ransa "Duk kiyitayi tunda weak point naki shine so na da kike yi over...
"Bai kuma ce mata komai ba, sai maida hankalin sa da yayi ga tuk'in mota.....

*************

"Basu suke shiga garin yola ba sai wajajen k'arfe biyu na dare...
"Kai tsaye Hotel ya nufa zai kama masu masauk'i kafin safiya fir fir Zulaihat tak'i yarda.... Hararansa take tana fad'in" Wllhi kaji na rantse idan baka maidani Abuja kafin ranar shiga kotun Jalal ba wllhi zaka sha mamaki ne ... Zaka san cewa ban mance bariki a kwanyata ba...Zaka san cewa mace nake.

"Fuzar da iska yayi kafin yace a hankali "Enough of this Zulaihat....

"Ta kuma hararan sa kafin tace " Ko kuma mi.. Mi zaka mun, ko nima kashe ni zakayi kaman yanda ka saba.... "Bata kai aya ba ya rik'e arms d'inta sosai cikin daka tsawa yace " Nace ya isheki haka, naji I'm taking you back to Abuja and I won't stop you from testifying.... The only thing you need to do is to change your testimony..... Dole kibi umarni na coz from this very moment you are mine, ke tawace...

"Fizge jikinta tayi tace " Let go of me... Ni ba taka bace get this to your damn head... Daga haka tasa kai ta Bud'e marfin motar zata fice...
"Saurin fitowa shima yayi ya k'araso ya sha gabanta... Lallashinta ya shiga yi yana shan gabanta tana canza hanya.....
"A haka 'yan sanda masu patrol suka k'araso yanda suke suna fad'in" Su waye ku, me kuke yi a waje a wann lokaci....
" Umar yayi saurin rik'o hannunta kafin ya dubi 'yan sandan cikeda confidence yace " Officer barkanku da aiki d'an misunderstanding muka samu she's my wife........ "Hararansa take kafin tace " Hey don't be too fool of yourself ni ba matar ka bace... Umar Ya kuma rik'o hannunta yace " Com'on wifey.... It doesn't have to reach that point....
"D'an sanda tamkar TV suka zame masa, ya kalli wann ya kalli wancan "Da sauri yace " Kai kai just hold it right there.... Ku min bayani k'wara d'aya gamshesshiya ko mu wuce station...

"Umar na shafa baki ya k'araso jikin officer yasa hannu a pantpocket d'insa ya zaro 'yan d'ari biyar biyar kusan guda biyar ya shafa ma officer a hannu kafin yace " Mun gode officer aci gaba da aiki ...Daga haka yaja Zulaihat suka wuce mota, officer sai washe baki yake uwa gonar auduga....


"Suna shiga mota ta fizge hannun ta.... D'an kallonta yayi kafin yace " We spending the night at a hotel... Final say, na gama magana...

"Bata ce masa komai ba har ya isa wani hamshak'in hotel... Koda ya kama masu d'aki ma k'in shiga tayi dole ya fice ya kwana a mota don lallab'a ta yake ya cimma burin sa...


"Washe gari suka nufi gidan su Zulaihat.....



Sameena ce
[1/23, 22:30] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

81

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*





"Tun daga kwanar anguwar jama'a ke kallon hamshak'iyar GLK d'in data karyo kwana,.. Matasa masu zaman bakin titi banda wow basu fad'in komai.. Kai Alla Alla suke suga wanda zai fito daga motar nan....


"Ganin wani had'add'en saurayi da Zulaihat sun fito yasa su sakin baki... "D'aya yace " Kai mutumi na gaskiya daduro ya kai ma yarinyar can... D'aya yace wann daga gani irin 'ya'yan b'arayin nan ta samu zasu kwasheta...
"Kai Baaba ashe akwai kashe k'wark'wata a unguwar nan..... Ire iren chats d'in da wad'an nan matasa masu zaman banza suka rink'a yi kenan.. ( Allah ka shiryar mana da matasan mu ka saka masu kishin kawunansu da zafin nema ameen)...


"Daga wajen gate wajen flowers ya tsaya... Zulaihat ta sa kai ta shige ciki don tasan Dad d'inta bai tafi office ba...
"K'irjinta sai faman lugude yake yana dukan tara tara, ga hawaye da ya ciko mata idanu....


"Gaba d'aya family d'in suna zaune saman dinning table probably having their breakfast.... Ba sai ance maka cikin farin ciki suke ba... Ta kai duban ta ga mahaifin ta wanda keta faman saka abinci a bakin wata yarinya wanda da gani kasan k'anwar ta ce, yarinyar bazata gaza shekaru biyu ba... Murmushi da hawaye ya kufce mata..

"Kaman daga sama taji ance Aunty Zulaihat..????

"Gaba d'aya suka juya suna kallon Imtihal wacce tayi maganar..

"Zulaihta ta d'ago kai hawaye na bin k'uncinta... Da gudu Imtihal ta tafi ta rungume ta tana fad'in Anty Zulaihat kin dawo knn koh, bazaki sake tafiya ki barmu ba koh...

"Zulaihat ta d'ago fuskar k'anwarta tana ganin yanda ta girma sosai... Kan ta sami zarafin magana sai sauk'an mari taji a fuskar ta..
"Ta d'ago tana duban mahaifin ta dake faman huci kaman zaki....

"Wani iskancin kika zo min gida watsettsiya kawai...

"Dafe fuskar ta tayi tana duban mahaifinta hawaye na zuba... " Aunty ta k'araso rik'e da k'aramar d'iyar ta tana tafe hannuwa...

"Dad ka yafe ni pls.... Bata kai aya ba, ya shiga figan hannuwanta suka nufo waje... Kkcib'us sukayi da Umar dake tsaye cikin shirt d'insa mai layi layi long sleeves yayi folding hannayen rigan zuwa elbows d'insa.... Jifa da ita Dad yayi ya nufi Umar a zuciye yana fad'in" Wanene kai dan Uban ka... Who are you..??

"Har ransa yaji zafin zagin da Baban Zulaihat ya masa, ba don yana neman kota wani hanya Zulaihat ta yarda dashi ba, da ya cirewa mutumin nan rashin kunyar sa...

"Umar Ya durk'usa har k'asa yana gaida Dad...
"Ba wann na tambaye ka ba, me kukazo yi gidana..

"Umar Ya d'an sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Baba pls kar ka mana mummunar fahimta, ni nan masoyin Zulaihat ne, ya d'an juya ya kalli Zulaihat dake zuban hawaye... Kafin ya dawo ga dubansa ga Dad sann yaci gaba da fad'in" Dama dama Baba mun zo ne Zulaihat ta nemi yafiyar ka snn.... Ya d'anyi shiru.. "Dad ya katse sa da fad'in" Snn me..?
"Umar yace "Snn na na.. Ni manemin aurenta ne...


"Kwab'e babbar rigar sa Dad yayi yayiyo kan Umar Ya jawosa ya shiga lakkad'a yana fad'in" No zaku nuna wa Bariki, 'Yan k'wal uba, tun kafin a aifi uban ka nayi nawa barikin... Shege maras kunya ka kwaso k'afa uwa mutumin arziki... Wann fuska taka da k'yar idan tana sallah..... Da anganka fulb'e sak amma wann ido naka da gani kaci uwar duniyan ci....

"Zulaihat har k'asa ta tsuguna tana kuka sosai take bawa Dad hak'uri.... Ya juyo kanta yana runtumo mata wasu manya manyan ashariya yana fad'in sai kin gane kuren ki yau... Tiyo d'in bayi ma flowers ya d'auka yayi kanta.... A tamanin Umar Ya k'aras ya kare ta Dad yayita lapta masa....
"Dad yana fad'in" Ka matsa min ko na kar ka.... "Da k'arfin gaske Umar Ya finciki tiyo d'in daidai sanda mak'ota suka soma shigowa don dama sun san gidan Alh Saleh Bushasha haka ne take faruwa idan matarsa ta sami rahoton an gansa a hotel, yaran sa kam ai ya zame masu jiki.... Wnn bak'in dalili na d'aya daga cikin abinda yasa Zulaihat ta shiga duniya....

"Umar yaci gaba da fad'in" Ina son Zulaihat ina sonta kuma dole ka aura min ita ko kak'i ko kaso ko mu tafi wani wajan daban muyi aure.... She's here to repent her mistakes, why is it so hard for you to forgive her... What kind of parent are you... Shin bazaka gode ma Allah ba, ya shiryar maka da d'iyar ka.... Ya sassauta murya kafin yaci gaba da fad'in" Haba Baba alot people suna neman nasu yaran su shiriya basu shiriya ba, pls don't be so selfish, give your a chance to start again... She's only human, she made mistakes.... Don Allah ka yafe mata ka aura mana juna....

"Duk rashin kunyar Alh Bushasha da rashin ganin girman mutane, yau saida Ya kasa tanka wa Umar, mutane kuwa sai jin dad'i suke suna jinjina wa wann saurayi, ga wa'enda suka san Zulaihat cewa suke tayi sa'an miji ta huta da fitanan gidan.....

"Aunty kuwa tab'e baki tayi tace " Mijina idan ka cika d'an halas ka aura wa Zulai wann saurayin.... Ba ita ta iya samo miji a bariki ba, ka duba yanda rankatatap anguwar nan aka fito akai mana chaa, suka baka kunya... Wllhi ka aura mata shi kowa ya huta... Jarabebbiya mai halin uwar ta.....

"Alh Bushasha ya kad'a kai kafin yace " Kinyi gaskiya, dama bansan wani munafuncin da iyayi bane ya dawo da ita muna zaman zaman mu....

"Ya juyo ya kalli Umar yace bata sadaki, mik'a mata a hannunta.... "D'ago kai tayi cike da al'ajabi tana duban Mahaifinta.... "Umar Ya gyad'a mata kai alamun kar taji tsoro...

"Alh Bushasha ya kalli Almajiran dake lek'owa ta gate yace " Kai kira mini Sallau Mai goro da Mal Tanimu Allah yasa basu tafi kasuwa ba..... Yaran suka tafi a guje...

"Alh Sallau da Mal Tanimu sun sha mamakin kiran da Mak'ocin nasu ya masu don ko ba zaman mutunci suke ba......

"Bayan sun hallara Alh Bushasha yace "Toh kune shaidu, dama a musulnce bayan sadaki alwali sai shaidu shknn aure ya d'auru.... Sun sha mamakin jin wann furuci nasa, don basu san da dawowar Zulaihat ba..... Take aka d'aura auren Zulaihat da Umar kan sadaki Naira 1000 don kuwa iyakacinta knn a jikinsa sai wasu 'yan canji da ba'a rasawa....


"Zulaihat bata tab'a tunanin abin na mahaifinta ya kai haka ba, tabbas she should just stop deceiving her self thinking ko asiri akai wa mahaifinta Zunzurutun halin sa ne... "Ubangiji ka bamu iyaye na gari, da 'ya'yaye na gari ameen....
"Kai ita ko a film bata tab'a karo da irin wann aure nata ba.... Abu kaman almara gashi ta zamo matar Umar wai....

"Bayan d'aura aure zata shiga cikin gidan yace " Ina zakije... Ta d'ago tana kallon mahaifin ta... Girgiza kai yayi kafin yace " Ai barikiji na fad'a maki kwabo kwabo wann nawa bakya gani, me zaki shigar min gida kiyi.... Maza wuce ki bisa can maki, kuma baki gama ganin rayuwa ba... Zatayi magana ya nufota yana neman abun raruma yace " Fita fice min daga gida annoba kawai.... Wnn yarinya farin k"afa ne dake da uwarki tunda na rabu daku nake samun nasara,... Hankad'ata yayi Umar yayi saurin tareta ta fad'o jikinsa... Alh Bushasha harda karkad'e hannu alamun an zubar da datti kafin ya maida sakatar gidan sa ya kulle....


"D'ago ido mai zuban hawaye tayi tana duban Umar, da sauri ya rungume ta yana fad'in" It's okay, you have me kinji, i'll never leave your side... I'll always be here kinji... Kasa ce masa komai tayi sai kuka da take yi da iya k'arfin ta... A haka ya Bud'e Mota ya saka ta.... Ya dawo driver seat ya zauna ya soma tuk'i suka fice daga layin.... Kai tsaye Hotel d'in suka koma....


"Bai bari tayi tafiya da k'afafunta ba, cak ya d'auke ta Ya nufi building d'in da ita,.... He's just acting like an Angel, duk wanda ya gansu dole ya rantse Zulaihat tayi dacen mai sonta...

"Ya kwantar da ita a d'aki ya masu placing order snn ya dawo ya shiga riritata tamkar k'wai... Gaba d'aya ya dad'a dulmiyar da k'wak'walwar Zulaihat, sabuwar soyayyar sa ya ringa gina mata a zuciyar ta.... Har ta kawo point d'in da tabbas Zulaihat ta yarda Umar nadama yayi tunda duk ya mata wad'an nan abubuwan... K'arshe sakewa dashi tayi suka wuni suna zallan soyayya a d'akin hotel d'in nan.... Sallah ne kurum yake raba su....

"Kanta na kwance bisa k'irjinsa yana shafa gashin kanta lokaci guda yana hango fuskar masoyiyar sa Zubaidah wacce he's doing all this ne to get her.... Jiyo muryar Zulaihat yayi tana fad'in" Mine toh yanzu baka tsoron Tariq ya mutu, Allah fa zai kama ka...

"Murmushi Umar yayi ya dago ta zaune ya manna mata kiss a kumatu kafin yace " Bazai mutu ba insha Allah sweet, ki daina saka damuwa ma ranki, you'll testify and Jalal would be out of jell, nima na tausaya masu shida Zubaidah they've been through alot, they deserves to be happy just like us.... In spite of everything we went through daga k'arshe mun kasance tare... So suma zasu kasnce tare...

"Murmushi tayi ta rungume sa kafin tace " I love you mine... Bai amsa ta ba sai squeezing nata da ya soma yi, zuciyar sa na raya masa tamkar Zubaidah ce a tare dashi....

"Haka suka kwana suka wuni suna faranta ran juna... Kwanan su biyu a garin Yola kafin suka kamo hanyar Abuja da sassafe....

******************

"Inaso naje Abuja da kaina Abdullah, na kasa samun sukuni har sai na gansa..
"Inaso satin da zamu shiga komai ya zama Ready, snn banaso kowa yasan wann batu, kama daga mutanen cikin gida har na waje... Ga dukkan alamu mugun mu yana tare damu, snn baya fata Modibbo ya dawo gare mu...
"Abdullahi wann magana daga ni ne sai kai babu third party saiko Uban gijin mu.....

"Shattima ya gyad'a kai kafin yace " Insha Allah komai zai zama ready Abbah, I'll have everything under control, albarkanku da addu'o'in ku bazasu fad'i k'asa ba Albarkacin fiyayyen halitta Abbah...

"Mai Martaba ya gyad'a kai kana yace " Tashi kaje Allah Ya maka albarka...

"Shattima ya kuma rusunar da kai kafin yace " Ameen Abbah snn ya mik'e a ladabce ya fice....


***************


"Suna zazzaune a parlor suna kallon labaru a tashar Aljazira malam Liti yayi sallam... Mumsy ta amsa masa gamida masa izini...


"Mal Liti ya rusuna kafin ya gaida Mummy Kausar da Asmah suka gaidas kafin yace " Hajiya dama wasu bak'in turawa ne kukayi....

"Mumsy tace bak'in turawa Mal Liti...

"Mal liti ya gyad'a kai yace k'warai kuwa Haj ba bak'ak"en faata bane..

"Mumsy tace "Toh Mal liti, bismillah a shigo dasu... Da sauri Mal Liti ya wuce masu iso...


"Ga mamakin su ba kowa bane illa Mr Felix Delecolina abokin kasuwancin Pappy na k'asar Holland kafin su dawo Nigeria da kuma Attorney Hamood, tsohon lauyan kampanin Pappy shima tun suna k'asar Holland.....


"Innah ta dubesu Shek'ek'e kafin tace "Aure Ummaru.. " Bata tab'a kiransa da sunar sa ba sai yau...
"Zulaihat ta durk'usa tana gaida Innah, bata amsa ba sai ci gaba da tafe hannaye da take tana fad'in" Na shiga uku ni Fulera, shiknn Baba Wuro kace na aifo ka ma kadangarun bariki.....

"Umar Ya fuzar da iska kafin ya kamo Zulaihat dake durk'ushe k'irjinta na bugawa yace " Muje sweet I'll take care of this.... TTad'ago ido zatayi magana yace " kiyi shiru ki shiga d'aki ki kwanta ki huta, Sai na shigo.... Da kansa ya kwantar da ita kafin Ya dawo wajen Innah suka soma toya tasu wainar...

"Firfir Innah tak'i amsar Zulaihat, fad'i take "Yanzu Baba Wuro duk 'yan mata masu mutunci da suke k'aunar ka ka rasa wacce zaka d'auko ka kawo min a matsayin surkuwa sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login