Showing 186001 words to 189000 words out of 226732 words
tsayuwa gami da ɗan dubansa.
"Daga ni har kai, mun yarda da kaddara mai kyau da marar kyau saboda mu din musulmai ne. Kamar yanda na ji batun aurenmu da kai daga sama, haka Allah Ya bani ikon karɓar lamarin matsayin kaddarata kuma mai kyau. Ko ba komai na shaida kana da ɗabi'u masu kyau daidai gwargwado. Hakanan iyayena da suka haɗa ni da kai, na tabbatar ba za su cutar da ni ba har abada. Bana so na ƙara yin gangancin saɓa umarninsu."
Tana kaiwa nan ta sunkuyar da kai don ba ta kaunar kallon da yake jifanta da shi da ta kasa ganewa.
"Ba wannan na tambayeki ba. Tambayar da na maki, kenan ba...Shikenan dai. Hakan ma is good."
Ya fasa nanata tambayar, sai ya share. Can kuma ya kara magana.
"Ku mata kun fi kaunar wadanda za su tsaya su na furtamaku kalaman so a baki alhalin idan aka yi auren ba lallai su iya tafiyar da lamuranku yanda ake so ba. Ina da tabbacin har da wannan a bahagon tunaninki."
"Me ya kawo batun so? Ai bana jin akwai shi a tsakaninmu. Ba ka san cewa ko ba aure ana yin so ba?"
Ya ji zafin kalamanta don haka shima ya shirya ramuwa.
"Shiyasa ki ka kasa hakuri da auren da babu so?"
Ta dubeshi, wani murmushi ya ke ganin ya ci galaba ta fusata. Ta kasa haɗiye maganar da ke cinta, ta maida mishi martani nan take.
"Yanzu ai gashinan zan yi. Ko ba komai a rayuwa ana koyon darasi, da auren so da wanda ma babu soyayyar, duk darasi ne a gareni. Na kuma gani. Idan a baya na yi na soyayyar, yanzu na hakura zan jarraba wanda babu soyayyar na ji yanda ake ji. Ko itama tana dauwama ko aa."
Tana kaiwa nan ta soma tafiya da zummar barin wurin, ya riƙo hannunta ta dawo baya. Ta juya da sauri gami da kokarin janyewa amma ina karfin ba ɗaya ba.
"Ka cikani tunda dai ka riga ka san cewa haramun ne."
Idanunsa tuni sun kaɗa. Shi Ramlat ke nufi da ba ta so ko me?
"Idan wasa ki ke yi, bai miki kyau ba. Ina miki rantsuwa da Allah, ko yankar naman jikin Hussein za ki dinga yi kullum kina gasawa tsabar ƙiyayya, sai kin zauna da ni muddin aka ɗaura aurenmu. Idan kika ga kin fita daga gidana, to ki sa a ranki, ƙasa ce za ta zama makwancinki a ranar. Babu fitar yaji ko kuma saki. Kar ki shigo gidana da makami, zan miki tanadin kala-kala sai wanda kika zaɓa. Zan iya mutuwa, amma har abada kar ki ji a ranki za ki shigo gidana kuma na rabu da ke. Har abada Ramlat."
Ta dubeshi da idanunta da suka cicciko, ba karamin fusata ya yi da zantukanta ba. Jikinta ya yi sanyi, ya saki hannunta ya faɗa motar gami da rufewa da karfi. Ta ci gaba da tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta bar harabar wurin zuwa ciki.
[3/17, 9:18 AM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA HAMSIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1018053716?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=H1vXb7%2FW6A2U5P8fFwbtuiA8loSGt%2B%2BNft8tDKy3EJM810crtMGUnxqUIIutxZI04rTU84moV3sLlZ4ErYDW%2BHsUJ6yuYaxKr9kgvrgaa2%2BsQQrAwLvUCmdmO42m8ACV
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
57)
Kiciɓus ta yi da Alhassan dake fitowa, ta yi saurin sunne kai kamar mai jin kunya. Shi kuwa a fisge da suka hada ido ya gane kamar ranta a ɓace yake.
"Har ka fito?"
Ta furta cikin dakiya, ya dan yi dariya.
"Na fito Amarsu, zan wuce. Gobe dai zan koma Adamawa sai ranar daurin aure in sha Allah."
"Allah Ya tsare hanya. A gaidamin su Aunty Kausar da Fatima."
"Zasu ji in sha Allahu."
Daga nan suka yi sallama ta shige ciki shi kuma ya nufi wurin motar yana ta tunani. Koda ya shiga, ya dubi Hussein da ya ɗago kai daga saman sitiyari.
"Lafiya? Na ganka wani iri kamar yanda itama Ramlatun na lura da damuwa a fuskarta. Meyafaru?"
"Nothing."
Ya amsa a gajarce sadda ya tayar da motar suka bar harabar gidan. AlHassan bai kara magana ba banda baki da ya taɓe. Sai da suka yi nisa ne kafin ya ji ya kamata ya ce wani abu ko da shawara ce sanin halin mutumin.
"Idan mutum yana son mace, kwantar da kai ya ke yi ya nemi soyayyarta. Mace ba ta son gadara ko taƙama, mace kulawa ta ke so da kuma a nunamata soyayya a fili kuma a gaban kowa. Ban san me ya haɗaku da Ramlatu ba, amma na kalli abin a mahangar ba ka taɓa soyayya ba, asalima matan ke binka a baya kana yanƙwana su. Idan har ka ce ta wannan hanyar za ka siye zuciyar Ramlatu, abun zai ba ka wuya daga kai har ita. Kar ka yi wasa da damarka."
Hussein tun soma maganar ɗan uwansa, bai katse shi ba, kamar yanda kunnuwansa ba su bar sauraronsa ba. Sai da ya kai karshe ne ya ɗan yamutse fuska.
"Su matan ba za su iya hakuri da kowace kulawa ta biyo bayan aure ba? Dole burinsu tun su na waje a nunamusu?"
Abin ya ba AlHassan dariya.
"Ka taɓa ganin inda aka yi cinikin biri a sama? Ko kuwa su matan kana tunanin sun san gaibu da nan take za su karanci halayyar mutane irinku? Su ba wannan a gabansu, su dai su gani a ƙas. Kuma dama ai amfanin taɗin kenan, a fahimci juna a kuma ga ko za'a iya zama a jure halayyar juna. Na tabbatarmaka idan ka ci gaba da tafiya a wannan shan ƙamshin naka da rashin maida hankali, za ka sha wuya a hannun Ramlatu bayan aurenku."
Murmushi Hussein ya yi don shi mamaki ma maganar ya ba shi.
"Wai zan sha wuya hannun Ramlat? Anya? Don Allah na yi kama da mazan da za su sha wuya hannun mace?"
Murmushin shima AlHassan ya yi gami da gyara zaman gilashinsa.
"Da sauranka ɗan uwa. Bari na kyaleka, gani ya kori ji. Nidai idan ta fara gasa maka aya a hannu, kar na ganka a ƙofar gidana."
Suka yi yar dariya a tare. Shi Hussein dariya yake don ganin hakan yake kamar wani almara ko tatsuniya. Bai ce Ramlatun ba ta da kyau ko tsarin da namiji zai rikito a kanta ba, tunda shi shaida ne, ganinsa da ita tun farko ya ji kawai ta burgeshi kafin ya tantance abinda ya ke ji taƙamaiman a kanta, sai dai ya na da ja akan cewa akwai macen da za ta iya juyashi ba tare da asiri ba kamar dai Hajiya Zeenatu a baya. Amma zai jira ya ga irin juyawar ta Ramlatu. Kulawar ba zai nuna ba kamar yanda dan uwansa ya buƙata har sai bayan aurensu.
***
Tana tuƙi a hanyarta na zuwa Ofis bayan ta sauke yara a makaranta, tana tunanin zantukan Hajiyarta.
_*"Magidannaki fa ya bukaci ki bar aiki hakanan tunda can Adamawa za ki zauna. Ko ba don haka ba dama na fadamaki duk radda kika tashi aure idan mijin da za ki aura bai amince ba, to za ki bar aiki."*_
Sauke ajiyar zuciya ta yi. Kenan dai rabuwarta da yaranta ya zo, wani kewarsu ta ji ya kamata. Dama tasan aiki ko ba dade ko ba jima za ta bar shi kamar yanda suka yi da Hajiya a farko. Hon da aka cikamata kunne da shi yasa ta kara nutsuwa a tuƙinta, ganin ma ba wani tare hanya ta yi ba sai abin ya yi mata zafi, ta cikin gilashi ta ke duban motar, sam ba ta ganeta ba. Don haka ta yi gefe ta ba mai motar hanya. Ido suka hada ya yi mata murmushi ita kuwa dubansa ta shiga yi baki a sake sai kuma ta dara.
"Hilal?" Ta furta a bayyane, a hankali ta ga ya ja gefe ya yi parking, itama dolenta ta tsaya don su gaisa. Ba ta kai ga fitowa ba ya rigata isa wajenta.
"Ranki ya daɗe."
"Yaya Hilal? Saukar yaushe a garin?"
Ya yi ƴar dariya.
"Ko kwanaki uku ban yi ba da zuwa, shima daurin auren abokina ne ya kawoni, amma nan da jibi zan koma in sha Allah."
Ta yi murmushi.
"Allah Ya nunamana. Ya Fa'iza da Ɗiyarmu?"
"Suna nan kalau. Ai nake gidan Sis Bilki jiya, na ji kuma abin alheri. Allah Ya sanya albarka. Yasa zamu gani."
Ba ta yi mamakin yanda aka yi Bilkisun ta sani ba, tana da tabbacin daga bakin Mijinta ne. Amma faɗawa Hilal sai ta gani kamar da biyu ne. Cike da jin nauyinsa ta amsa.
"Amin. Ina godiya. Wato dai da ace ba mu haɗu ba anan sai dai mu ji labarin ka tafi ko?"
Dariya ya yi.
"Ni na isa na shigo garin nan ban je na ga Hajiyarmu ba? Aa sam. Wallahi yau nake cewa zan shiga zuwa yamma haka."
Ta jinjina kai.
"Allah Ya nunamana."
"Amin amin. Bari na bar ki kada na sa ki makara. Sai na shigo din."
Ta amsa da toh gami da yi mishi fatan alheri, ya rufemata murfin motar sannan ya wuce zuwa tashi motar. Ta ja numfashi ta furzar, Hilal kenan, mutumin da ya kaunaceta don Allah. Gaba daya ya sauya ya ajiye kumatu. Ga duk wanda ya gan shi zai fahimci yana cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Wayarta ce ta yi ringing daidai sadda ta ke kokarin hawa titi. Ba tare da ta duba ba ta daga gami da karawa a kunnen da sallama.
"Ke da waye tsaye a titi?"
Tambayar da aka watsomata ba tare da an amsa sallama ba yasa ta gane ko waye. A hankali ta ɗaga kai ta dubi mirror, motarsa na nesa kaɗan da nata. Ta fi kyautata zaton daga wurin motsa jiki ya ke. Murmushi ta yi daidai sadda ta hau titi ta harba motarta.
"Ba ka da hurumin sanin da wanda nake magana. Kar ka manta ban kai ga zama matarka ba."
"Hakane, ba ki kai ga zama ba. Amma kin manta cewa haramun ne nema cikin nema? Ke musulma ce."
Dariya ya ba ta jin yanda ya zaƙalƙale. Yanda ta ke tafiya a sannu, haka yake biye da ita da motarsa a sannun. Ta kauda kai kamar ba ta san da shi din ba.
"Babu wanda ba ya kuskure."
"Haka kika ce? To naga kin ƙara tsayuwa da wani ɗan iskan! Duk abinda na yi mishi, ke kika ja. Sannan lokacin da za ki ajiye yawon gantalin aikinnan ya yi! Ba zan lamunta ba."
"Wannan kuma ba ka da hurumi a ciki, ajiye aiki sai lokacin da naga dama. Ka bar tada jijiyoyin wuya tunda har yanzu aure bai tabbata ba tsakaninmu. Akwai sauran lokaci."
Tana kaiwa nan ta katse wayar ta taka motarta, sai dai ba ta je ko'ina ba ya zo ya gifta ta har yana kokarin buge wani ɗan sahu. Bai ko tsaya ba ya yi gaba. Ta bi shi da kallo tana dariyar farin ciki, ko ba komai ta san ta ba shi aiki. Wannan nishadin yasa ta ware waƙar Breaker na Jarumar Mata tana saurara har ta karasa wurin aiki.
Hussein bai kara kiranta ba kwata-kwata a wannan ranar.
***
Bisa umarnin Yayanta Munir, ta rubuta takardar barin aiki. A wannan satin Rafee'ah ke zuwa ta kai ta gidan mai gyaran jiki. Ya kasance Ramlat ba ta da lokacin kanta balle na yara, ɗawainiyarsu ta koma hannun Hajiya da direba mai safa da marwar kai su makaranta da daukowa. Waya ba ta kara shiga tsakaninta da Hussein ba sai dai kokari kawai ta ke yi itama don tana kewarsa. Ya aiko da wani leshi mai tsadar gaske da kuma atamfofi har kala uku suma masu tsada sai mayafai da jaka da takalma, sai kuwa tsarka kala biyu da abin hannu duk na fitar biki. Ba ɓata lokaci aka kai wurin dinki tare da wanda Munir ya siyamata.
"Wai ke angonnaki yana zuwa hira kuwa? "
Ta dakatar da shafa man da take yi a jiki ta dubi Amrah wacce ke zaune saman gado tana shayarwa. Taɓe baki ta yi.
"Mutumin da ko waya ba ya kirana."
Da mamaki Amrah ta ce.
"Bana son sharri Ramlat."
Harararta ta yi.
"Kawai sai na zauna na kantara maki karya saboda ina tsoronki ko?"
Murmushi Amrah ta yi. Nan ta kwashe duk yanda ake ciki ta faɗamata har maganarsu ta karshe.
"Kai amma kin fadi mai zafi da yawa Ramlat, to ko za ki rama ai kya bari ya zo hannu tukunna. Shima dai da alama yana da zafin kishi tunda ya kasa nemanki har yau. Amma kar ki kara tunanin wai ba ya sonki, wallahi Hussein na miki son da ba ki san adadinsa ba. Da kansa fa ya je ya fadawa Baba Dakta yana sonki da aure tun ma a lokacin Chairman. Abinda kawai na kula, kamar yanda ya faɗamaki, shi mutum ne da bai yarda da wata soyayya kafin aure ba. Ya fi imanin cewa soyayya ta gaske tana zuwa ne bayan an yi aure. Kuma kar ki yi mamaki, irin su Hussein sun iya tattali da nuna kauna ga mace. Ina goyon bayanki, idan ku ka yi aure ki nunamasa kefa mace ce, amma ba wai ina nufin kar ki masa biyayya ba, aa, ki dai ja ajinki yanda zai gane shayi ruwa ne. Ke ba yarinya ba ce, na tabbatar kin gane me nake nufi."
Suka yi dariya gami da cafkewa don tuni Ramlat ta taso ta dawo gefenta.
"Ai ko yanzu ya ganki ya san kin sauya. Kin kara kyau gyaran jikin ya karɓeki. Duk inda kika gifta kamshi kawai kike kamar mai wanka da turare. Nidai akwai tsarabar da zan maki na kananun kaya, saura ki ƙi sanyawa."
Murmushi Ramlat ta yi, sai kuma ta ji zuciyarta na neman karyewa.
"Allah Ya jaddada rahma ga Aliyu."
Ta furta a fili, Amrah ta amsa da amin. Nan kuma suka shiga tuna baya, sai da Amrah ta ga dagasken Ramlat kukan take son yi don idanun sun cicciko da kwalla, sai ta share gami da sanyo wata hirar.
"Zan so naga yanda waccan bakar munafukar za ta yi idan ta ji labarin aurennan."
"Ni kuma kinga tsoron ranar da za ta sani nake yi. Sai kuma mamakin dalilin Hussein na ƙin ɗaukar mataki a kanta. Idan na yi tunanin ko yana sonta dagaske, ba ki san ya nake ji ba."
"Gaskiya da mamaki ace yana sonta, nidai jikina sai ya bani kamar so yake sai ya nunamata ita din ba komai ba ce kafin ya dauki mataki. Ai ko don yanda ta dinga kai maki hari, ya cancanta dama Hussein ya aureki mu ga ta tsiya."
Ramlat dai dariya kawai ta yi.
"Kin sanar da Muhibbat?"
"Eh na fadamata, ta ce za ta shigo ranar daurin auren tunda dai wunin ma duk rana daya ce."
"Allah Ya nunamana."
Ramlat ta amsa da amin gami da lumshe ido.
A daren bayan ta yo wa Amrah rakiya kofar gida don Dahiru ya zo daukarta, sai ganin Hussein ta yi. Suka dubi juna da Amrah da mamaki. Amrah ta murmusa.
"Kinga ɗan halak, ashe dai yana tafe."
Ita dai Ramlat mamaki ma ya hanata cewa uffan. Suka karasa daidai sadda ya fito daga mota suna gaisawa da Dahiru, daga nan ya amsa gaisuwar Amrah har da karɓar Baby ya yi mata wasa sannan ya yi musu sallama ya shige ciki ko inda Mutuniyartasa ta ke bai kalla ba. Ita ma ta dauke kai ba ta damu ta gaidashi ba.
"Wai ke ba Angonnamu kenan ba? Shi ne ko gaisuwa."
Dahiru ya fadi cike da zolaya. Ta harareshi don dama sun saba.
"Ban ga damar gaidashi din ba."
Ya daga kafada.
"Ai shikenan. Mu dai maza ba'a ja mana aji."
"Ko?" Cewar Amrah cikin son a tuna baya. Ya yi dariya kawai ya bude motarsa ya shiga.
"Allah Ya bamu alheri Amarsu. Sai da safe kafin wannan Madam din ta ɓallomin ruwa."
Dariyar suka yi kawai, ta bude gidan baya ta ajiyewa Amrah ledarta. Ba ta juya ba har sai da ta ga sun ja mota, ta koma ciki tana son ganin yanda za su kwashe da Gogannata.
A hankali ta ke takawa tamkar mai tafiya akan ƙaya, murmushi kawai ta ke zabgawa tana duban sararin samaniya wanda taurari da kuma watan na Rajab da bai fi kwanaki shida da bayyana ba. Hakan na nunk da kusantowar da wata azumin Ramadan ke ƙara yi. A hankali kuma ta maida kanta ƙasa ta ci gaba da tafiya har ta kusa barandar da za ta sada ta da falonnasu. Yanda ta ganshi a tsaye hakan ya dauremata kai, ta yi zaton yana ciki su na gaisawa da Hajiya, ko kuwa dai ya shiga ne ya fito? Oho. Ba ta da tabbaci, ganin kallonta kawai ya ke yi sai ta sunkui wa kai, koda ta karasa har za ta gifta sai kuma ta ga rashin kyautuwar hakan, don haka sai ta tsaya ta gaishe shi.
Maimakon ya amsa kawai sai ya kuramata idanu, idan ya ce ba ta sauyamasa ba, to ya yi karya. Ta wani cicciko ta yi haske, kamshi ke tashi kawai a jikinta. Ramlat ta ji shirun ya yi yawa don haka ta ɗan ɗago kai. Nan da nan ya daure fuska ya hadiye murmushin da ya yi niyyar suɓucemasa. Ya wayance da ɗan jan karan hancinsa da jan hancin kamar mai mura.
"Am...Meyasa ki ke giftawa cikin maza da uban ƙamshinnan? Koda ace babu maganar auren wani a kanki, kina sane da cewa haramun ne ko?"
Kanta a kasa ta yi murmushi a kasan ranta ta ce.
'Ka ji da masifaffen kishinka.'
"Ni ko fita ba na yi yanzu."
"Ko? Meyasa na ganki a waje? Idan mijin Amrah ne, mijinki ne?"
Ta ɗago ta dubeshi sai ma ya ba ta ƴar dariya. Maimakon ta ba shi haushi sai ta burgeshi, kawai sai ya jingina kai jikin gini yana kallonta. Ganin haka ta hadiye dariyar.
"Allah Ya huci zuciyarka."
Lumshe ido kawai ya yi ya bude.
"Matso, magana za mu yi."
Ba musu ta dawo ta tsaya daga gefensa. Kamar ta ce masa su nemi wurin zama amma kawai sai ta share.
"Kamar yanda na san cewa kin sani, yana da kyau na kara faɗamaki da bakina. Bayan aurenmu Adamawa zan kaiki. Kano sai dai mu zo ziyara. Abu na biyu babu batun aiki, ko a Kanon ko a Adamawa. Ba zan jure ganin ina fita nema, matata na fita ba. Kar ki ce za ki haɗa kanki da Zeenatu, wannan daban take hakanan tsarin rayuwarta daban da taki. Ina fatan kin fahimta?"
Ramlat da ta kasa haɗiye kishin Hajiya Zeenatu, ta gyada kai, ciki-ciki ta amsa.
"Na ji."
Jin yanayin