Showing 162001 words to 165000 words out of 226732 words

Chapter 55 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12467

a fili, ta karɓi kudin ba don ta so ba ta zura a aljihun wandonta.

"Ina tsumayenki. Ga lambar wayata." Hajiya Zeenatu ta fadi karo na biyu tana miƙamata karamin complimentary card mai dauke da numbobin wayoyinta a jiki. Nan ma Khadija gyada kai ta yi.

"Je ki." Ta ba ta umarni, ta juya da sauri ta shige ciki har tana cin karo da wata mai tsohon ciki.

"Yi hakuri don Allah." Matar ta bita da kallo kawai gami da jan tsaki irin na masifaffun masu ciki. Haka ta wuce ta a mita.

Koda ta karasa dakin Nurses, ba ta tarar da kowa ba don haka da sauri ta ciro kudaden hannu na rawa ta cusa a jaka ta zuge zif. Bandaki ta shige ta soma watsawa fuskarta ruwa tana salati a ƙasan ranta. Yau da wane rashin sa'a ta fito daga gida? Kawai sai ta shiga hawaye, nutsastsiyar fuskar Ramlatu da kuma na Hajiya mai cike da dattako da kamala take tunawa. Ta ya ya? Ta wace hanyar za ta iya kashe wannan baiwar Allahn? Duk da dai idan ta so abu ne mafi sauki a aikinta, za ta iya kasheta irin kisar da zai yi wuya kafin a gane ita ce silarsa. Amma ina! Ba'a ba ta wannan tarbiyyar ba kuma ita ba haɗamammiya ba ce akan abin duniya. Kaɗan ma da ta ke samu ya wadatar da ita.

Sai da aka kwankwasa ƙofar sannan ta fito. Karo suka yi da Nos Jamila. Ta bita da kallo.

"Dije, lafiya?"

Murmushin yaƙe ta yi ta hau murza idanu.

"Ba komai, abu ne ya faɗa idanuna."

"Aa Dije, faɗamin gaskiya."

Girgiza kai ta yi, ba za ta iya ba, tana tsoron abinda zai sanadin rayuwarta.

"Ko haihuwar ki ka karɓa, don nasan halinki na tausayi."

Dariya ta ba ta.

"Oh na tuna, ashe fa ba duty naki bane yau." Cewar Nos Jamila karo na biyu.

Ita dai Khadija ta sulale ta fice daga ɗakin. Maganin ma kasa komawa ta ba Ramlat ta yi sai wata ta aika.

***
Hussein da AlHassan zaune a falon gidan Hisham suna cin lafiyayyen girkin Aisha. Gogan ci yake kamar an mishi dole.

"Wai Hussein lafiya? Ko kaima jinyar kake taya Ramlat?"

AlHassan ya fadi yana murmushi don tuni ya ɗago shi.

"Mene haɗina da ita? Kawai dai na damu da harbin ne, na kuma rasa waye zai yi ƙarya da ni ya harbe ta. Shiyasa na kasa fahimtar mai laifin, me ya sani tsakanina da ita da ya zaɓi hanyar kasheta ta amfani da ni."

"Da mamaki kam, amma ko ma mene in sha Allah nan ba da jimawa ba zai bayyana. Har wanda ake ɓoyemana."

Hisham ya furta yana kashe mishi io ɗaya, AlHassan ya yi kamar bai gansu ba ya ci gaba da kai loma yana murmushi. A yau jinsa yake kamar a duniyar gajimare tsabar murnar ganinsa zaune tare da ɗan uwansa.

Hussein din ma banda harara bai cewa Hisham uffan ba, saboda gudun zargin sai ya saki jiki ya ci abinci. Bayan sun kammala ya mike.

"Ina zuwa?"

Fadin AlHassan don ba ya son ya ji Hussein din ya matsa daga gareshi. Murmushi Hussein ya yi.

"Gidan Hajiya Zeenatu."

"Aa, bai kamata ka je kai kaɗai ba. Muje tare."

Jinjina kai Hussein ya yi cikin amincewa da zancen dan uwannasa. Suka ɗunguma suka fita, Hisham ya takamusu har ƙofa kafin ya dawo ciki. Kusan shima yau dai jinsa yake sak. Babu sauran damuwa.

***
RAMIN ƘARYA....
[3/16, 1:55 PM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA HAMSIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/S2N0l9OdWcb



🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

50)

Tun daga farfajiyar gidan ma'aikata suka dinga al'ajabin ganin ƴan biyunnan. Har dai Malam Bala mai guga ya ka sa hakuri.

"Yallaɓai ashe ku ƴan biyu ne."

Hussein suka dubi juna da AlHassan, kauna ta jini na ƴan uwantaka na ƙara ratsa zuƙatansu, banda kaddara me zai raba su? Su da suka rayu tare a mahaifa guda.

"Eh Malam Bala, we are twins."

Fadin Hussein wanda ya ƙarashe da kallon su John. Nan suka shiga washe hakora suna gaida AlHassan da fadin abinda ya bambantasu, hakan ya ba ƴan biyun matasan dariya. Hussein ya yi ciki yana murmushi, ya bar su da AlHassan. Yasan matar gidan ba ta nan kamar yanda ya ji daga masu gadin, don haka ya shiga bin ko'ina na falon da kallo. Tafkeken hotonsu shi da ita ya ƙurawa idanu kamar wani fulanin daji da bai san hoto ba.

"Ita ce. Makira."

AlHassan ya fadi a hankali, sai sannan Hussein ya juyo da rinannun idanunsa ya dubeshi.

"Idan na ce maka ban san ta ya ya na aureta na za ka yarda? Idan na ce maka ba da son raina..."

"Ba fa sai ka faɗi komai ba ɗan uwa, na maka farin sani na kuma san kalar macen da ka ke so. Ko ka mance cewa ka ban labarin haɗuwarku da tayin kaunar da ta yi maka? Ban san dalilin da yasa na kasa tunawa da hakan ba, ban kuma san dalilin da yasa na amince ka bar mu ne saboda ka auri wacce ka ke so. Amma ban taɓa kawo wa ita ce ba nasan dai babbar mace ce kamar yanda ka faɗi."

Sauke ajiyar zuciya Hussein ya yi gami da jinjina kai. Falon suka koma suka zauna. Nan kuma AlHassan ya shiga ba shi labarin abubuwan da suka faru a bayansa. Rasuwar Baba Naziru mijin Dada da kuma rasuwar ƴar uwar kakarsu da ta riƙe su kamar jikokinta da yaran cikinta suka haifamata ba su Dada ba.

"Allah Yay musu rahma. Yasa aljanna makoma. Baba Naziru ya rasu da bakin cikina."

Girgiza kai AlHassan ya yi.

"Kar ka ce haka. Wallahi har ya rasu kewar ka ya ke, ya kuma faɗa ya ƙara, ba halinka ba ne."

Hussein ya jinjina kai.

"Yaushe za ku tafi?"

AlHassan ya tambaya.

"A satinnan. Ina neman alfarma a wurinka, koda kun haɗu da ita kar ka nuna mata komai kamar yanda nima ba zan nuna ba."

Hussein ya faɗi idanunsa cikin na ɗan uwan. Da mamaki AlHassannya tambaya.

"Dalili?"

Hussein ya yi mishi bayanin duk abinda ya ke buƙatar yi, a farko AlHassan ya ji abin kamar babu amfani, a karshe kuma sai ya hau murmushi sosai.

"Good, hakan shi ne daidai."

Abinda ya ce kenan bayan gama sauraro. Hussein ya ɗan ciji leɓɓansa gami da shafa sumar kai.

Daga farfajiyar gidan kuwa, Hajiya  Zeenatu ce ta shigo ta yi parking ta fito. Ta sauke ajiyar zuciya ganin motar Hussein. Ta shirya tunkurarsa, ta shirya fuskantar kowane irin ƙalubale. Ita din mace ce, kissa ba komai bane. Murmushi ta dan yi tana mai jin ƙwarin gwuiwa da haka ta shiga gidan.

***
Yusufa ya zaro ido yana duban Halima da ke faman zuba zance.

"Yaya Halima anya kina da imani? Yanzu saboda kudi ki ka yarda ki aikata duka wannan? Yaya Halima ba ki yi tunanin rana irin wannan za ta zo ba? Ke fa talaka ce, ba ki da makaman yaƙi, su kuwa masu kuɗi ne, kinsan ba za su kamu ba. Meyasa kullum shi talaka kwadayi ke kai shi ya baro? Anya kuwa kin yiwa kanki adalci? Kin mana adalci? Ɗan abinda kike samu na albashi bai wadace ki ba?"

Yanda Yusufa ke hawaye haka itama ta ke sheshshekar kuka.

"Na cuci kaina, ban san cewa ni din mahaukaciya ce ba dai yanzu Yusuf. Nidai don Allah ka taimaka ka je ka sami Hajiya ka yi mata bayanin komai, nasan ba za ta rasa hanyar da za ta fitar da ni ba musamman idan ta ji ina  barazanar tonamusu asiri."

Ya share fuskarsa, shiru ya yi don babu alamar zai je din. Halima ta dinga yi mishi magiya da roƙo har tana durƙusawa. Ɗan uwa daban ya ke, nan da nan ya ji zuciyarsa ta karye, ya daukar mata alƙawarin a yau zai je ya sami Hajiya Zeenatu tunda washegari ne shiga kotu. Ta ba shi kwatancen gidanta har ma da na A&Z, daga bisani suka rabu akan duk yanda ake ciki zai dawo ya sanarmata.

***
Ramlat ta yi shiru tana tunani bayan tafiyar abokan aikinta wadanda takanas suka zo dubiya. Can dai ta kasa hakuri ya dubu Hajiya dake zaune saman darduma tana shan kankana.

"Nikam Hajiya ya ake ciki batun mayar da kudi? Su Kawu sun ƙara magana?"

Hajiya ta yi murmushi.

"Ina fa Ramlatu, Hajja ta ce na bar komai a hannunta. Yanzu dama abinda ake ciki, ina so ke ki bada katin ATM dinki na damƙawa Yayanki ya je ya ciro ya kawomin. Da kaina zan je na same su na damƙamusu kuɗaɗen idan ya so ko a yaransu ne su nemi ɗaya su aurawa Dikkon. Ke dai ki kwantar da hankalinki kawai. Kuma kada jin hakan yasa ki dauka na goyi bayan ki yi ta zama a gabana ne babu aure, sam, ba zai yiwu ba. Shima wannan din halayyarsa ce ba ta yimin ba kema kin sani. Don haka ki yi kokarin fitar da mijin aure. Ko Baba Dakta ai kin ji me ya ce."

Murmushi ta yi mai kama da yaƙe gami da gyaɗa kai. Hajiya ba ta san me ke damunta ba, ba kuma auren ne ba ta so ba. Kawai dai ba wanda ta ke jin kaunarsa a ranta irin Hussein. Bayan Aliyunta, shi ne namijin da ta yi amannar za ta iya rayuwa da shi a kowane yanayi. Sosai yanzun tana jin saukin hannun don ita kam da ace za'a ba ta sallama a ranar za ta so hakan. Sallamar da aka yi yasa duk suka dubi ƙofar gami da amsawa. Nos Khadija ce, ta ƙaraso ciki.

"Ke kuwa ɗiyata daga cewa bari ki ke ki dawo na ji shiru sai wata na gani a madadinki."

Murmushin yaƙe Khadija ta yi. Ta rasa ma me za ta ce, tuno zantukan Hajiya Zeenatu kaɗai yakan kaɗa hanjin cikinta balle idan ta ci karo da salihan bayin Allahn nan da ba su yi kama da mugaye ba. Ita kuwa in za ta iya aikata wannan ɗanyen aikin? Ai koda babu ƴan sanda tsaye a bakin ƙofar ba za ta iya ba.

"Ayi hakuri Hajiyarmu, ɗazun sallah na tsaya yi bayan na idar kuma wani aikin ya ɗaukemin hankali. Sannu Ramlat, ya jikin?"

Da murmushi itama Ramlat ta amsa.

"Alhamdulillah. Jiki ya yi sauki."

Ta jinjina kai.

"Dama zuwa na yi na muku sallama sai kuma Allah Ya kaimu. Zan wuce gida."

Suka yi mata godiya sosai sannan ta juya ta fice idanunta cike taf da kwalla. Ba ta tunanin har a ba su sallama za su ƙara ganinta.

***
  Sallamarta ta sanya su maida hankula gareta musamman AlHassan wanda ke zuci-zucin ya haɗa ido da matar da ta yi sanadiyyar rushewar dukkan farin cikinsu na tsawon shekarunnan.

Tun daga  bakin ƙofar shigowa ta saki jaka gami da ƙarasowa tana kallonsu kamar wasu sabbin halittu.

"Hussein! Kar ka cemin wannan ɗan uwanka ne. Ku ƴan biyu ne dama?"

Ta shiga nuni da Alhassan da yatsa da wani rawar baki ta karasa zancen. Kawai a karshe ma sai ta karasa da sauri.

"Innalillahi, wallahi kuna kama. Wa ye wannan din? Huss.."

Bai bari ya ci gaba da sauraron rainin hankalinta ba ya yi saurin katse ta.

"Yes yes, shi ne. AlHassan Aminu Modibbo, ɗan uwana ne. Daga Adamawa."

Ya fadi yana kallonta da burin ya ga yanayin da za ta shiga, sai ta maze ta hau sharar hawayen munafurci.

"Alhamdulillah. Allah Ma ji roƙon bayinSa. Allah yanda Ka nunamin dan uwan mijina ina roƙonka da Ka sadar da ni da nawa dangin." Kawai sai ta fashe da kuka sosai. Hussein ya ɗora kafa ɗaya saman kujera gami da rike baki da hannu ɗaya yana wani murmushi, AlHassan shi kansa abin nata dariya ya ba shi. Ido Hussein din ya mishi don haka ya shiga acting.

"Haba Hajjaju, ki kwantar da hankalinki. Komai ai na Allah ne. Ai ko shekaru miliyan za'a yi ana shuka rashin alkhairi, akwai ranar ƙin dillacin. Kinsan hausawa sun ce ramin ƙarya ƙurarre ne. Ina nufin da sannu kema Allah zai sada ki da naki ƴan uwan. Mun jima muna nemansa, a zatonmu ma ya mutu, sai dai kwatsam labari ya iso mana can Adamawa cewa an ga mai kama da ni a Kano, kamar da wasa ina zuwa na haɗu da shi. Ai ba abinda za mu ce ga Ubangiji sai godiya. Ya ban labarin irin kulawa da soyayyar da ki ke nuna mishi, muna godiya sosai sosai fa."

Mamaki, tsoro ko farin ciki? Oho, Hajiya Zeenatu ba ta san wanne ta ke ji ba. Dagaske ne Hussein bai zarginta da komai haka ma dan uwansa ko kuwa dai su na mata shigo-shigo ba zurfi ne?

_*"Kin manta waye Hussein? Mutumin da bai iya ɓoye ɓacin rai ba? Ga dukkan alamu son da ya ke yi miki ya hana ya zarge ki. Wannan ne zai sa ɗan uwansa ma ba zai zargeki ba. Ko ba komai daular kadai da suka tarar da dan uwansu a ciki, zai hana su zargi komai a kanki."*_

Wani sashi na zuciyar Hajiya Zeenatu ke mata wannan tunin, nan da nan ta gaskata hakan, wani farin ciki ya dabaibaye ta. Ta shiga rawar ƙafa gami da yin nan nan da AlHassan.

"Me ka fi so dan uwanmu, me za a girka maka?"

Ya yi murmushin da bai kai zuci ba.

"Ko me kika sa aka girka zan ci Hajjaju."

Ta yi dariya tana duban Hussein wanda ya dauke kai ya maida hankali ga wayarsa.

"Shikenan an gama! Kai fa Mijin? Me ka ke da muradin ci?"

Ba tare da ya dube ta ba ya amsa.

"Duk abinda ki ka sanya a girka."

"Shikenan. Ai yau da kaina zan shiga kicin, da hannuna zan muku girki don yau ranar farin ciki ce gare mu. Rana ce da ba za mu mance ba."

Anan ne Hussein ya ɗan kalleta ya yamutsa fuska. Ta wuce sama da sauri da niyyar sauya kaya. Bayan tafiyarta ya yi jifa da wayar ya riƙe kai zuciyarsa na zafi. Dakyar ya iya kai zuciya nesa bai shaƙe wuyanta ba.

"Akwai wuya fa, dakyar na iya jure kallon fuskar matarnan taka."

AlHassan ke maganar yana dubansa, ya dago ya ja guntun tsaki.

"Ka daina haɗa ni da ita please."

Murmushi kawai AlHassan ya yi ya dubi agogo.

"Ya kamata mu yi haramar tafiya masallaci, daga nan ina son wucewa asibiti na ga jikin Ƙanwata."

Shiru ya samu maimakon amsa daga bakin Hussein kawai dai ya mike ya nufi bandakin dake falon, can ya fito. Ganin alwalar ya yi  shima ɗan uwan ya mike ya shiga toilet.

Daidai sadda Hajiya Zeenatu ta sauko cikin wata doguwar riga ƴar kanti da ta matse ta, albarkatun tumbinta duk sun fito sun yi layi-layi. Ya kauda kai yana ji kamar ya yi amai da ya tuna tsawon lokacin da ya ɗauka yana haɗa jiki da ita.

"A'a, ya na ga kun miƙe? Ina shi AlHassan din?"

Hussein ya ci gaba da ɗora agogonsa bai ce komai ba. Don kanta ta ba kanta amsa.

"Oh, yana toilet kenan. Lallai kam don Magriba ta kusa. Bari na leka kicin sai na koma na yi alwalar nima."

Murmushin gefen kumatu ya yi jin wani sabon salo, kiran sallah da wutsir. Hajiya Zeenatu da batun ɗora alwala? Jinjina kai kawai ya yi ta sauke ajiyar zuciya ta yi hanyar kicin tana kwala wa John kira.

AlHassan na fitowa suka kama hanya. Daga masallaci, suka dawo suka shiga motar Hussein din, a waya ya ke sanarwa Hajiya Zeenatu fitarsu.

"Haba haba don Allah, girki fa zan muku yanzu."

Sai da ya daki sitayari gami da jan tsaki don wani irin ɓacin rai da shagwaɓar Hajiya Zeenatu ta jawomasa. Yana gani AlHassan na mishi hannu alamar ya nutsu. Ya daure ya amsa.

"Kiyi hakuri Madam, yanzu za mu dawo, ba wani jimawa za mu yi ba. Kayansa zan kai shi ya kwaso daga Hotel."

Bai bari ta karashe amsawar ba ya kashe wayar.

***
Yusufa wanda a kan idonsa mota ta fice daga gidan da Halima ta mishi kwatance, ya bi motar da kallo, ganin ba'a ganin na ciki ne yasa shi maido hankali ga Maigadin. Da sauri ya karasa tun kafin ya karasa rufe ƙyauren.

"Sannu Baba."

Maigadin ya dube shi.

"Yauwa ɗan samari, lafiya dai?"

"Lafiya kalau. Don Allah nan ne gidan Hajiya Zeenatu?"

Gyada kai Baba Maigadin ya yi.

"Eh kwarai, nan ne."

Sauke ajiyar zuciya Yusufa ya yi.

"Alhamdulillah, don Allah wurinta na zo. Idan ba damuwa ka yimin iso Baba. Ka ce mata Halima ce ta turo ni.  Sunana Yusufa."

"Toh banda abinka ɗan samari, Halima kawai babu wata inkiya ko wani abun? Idan ta ce ba ta gane ba fa?"

Yusufa ya yi shiru, ya san ko sunan ubansu zai faɗa a banza don ba lallai Hajiyar ta san ta da wannan sunan ba. Don haka dabara ta faɗomasa.

"Yauwa, ka ce ƙanin Halima ne ma'aikaciyar Revenue. Aikoni ta yi."

Kasancewar Baba Maigadi ba baya ba, daidai gwargwado yana da ilimin boko yasa fadin sunan bai ba shi wuya ba. Ya ce ya shigo ya tsaya daga bakin ƙyauren, Yusufa ya yi godiya ya shigo. Ya dinga bin tamfatsetsan gidan da kallo cike da jinjina irin dukiyar da ala narkar. Sai ya gan shi wani ƙaramin alhaki kuma wani almajiri a gaban gidan.

Koda Baba Maigadi ya isar da saƙon ga Hajiya Zeenatu, nan da nan ta daure fuska.

"Na ba ka damar barin ko wane kare da biri  shigowa gidana?!"

Baba Maigadi ya dan russuna a ladabce.

"Ki yi hakuri ranki ya daɗe, na dauka kinsan Halimar ne. Amma.."

"Kai dalla yimim shiru hakanan! Ka koma ka ce mishi babu wata Halima da na sani don haka ya gaggauta bar min gida tun kafin ya yi maka sanadin aikinka."

Jin haka ai da sauri Baba Maigadi ya kara bada hakuri tukunna ya kama hanya da sauri-sauri. Idan aka yi mishi sanadin aiki kuma ina ya kama?

Yusufa na hango shi ya ƙuramishi idanu. Maimakon ya ji ta ba shi damar ganawa da ita, sai ya ji akasin hakan. A ƙarshe ma Baba Maigadi bude mishi kyaure ya yi yana mai ba shi hakuri da roƙon ya tafi tun bai jazamishi ba. Haka Yusufa ya fita jiki a matukar sanyaye. Ta tabbata dai karshen Halima ne ya zo. Komai yanzun zai iya faruwa gareta tunda har ta bari zuciyarta ta rinjaye ta wurin aikata abin dana sani da kuma nadama.

***
A farfajiyar asibitin ya faka motar.

"Muje ko?" Cewar AlHassan ganin Hussein din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login