Showing 171001 words to 174000 words out of 226732 words
fusata. Jikinsa har rawa ya ke yana kumfar baki.
"Ni ka ke faɗawa baƙar magana?! Ni? Na maka kama da sa'an Uwarka?!"
Hussein caraf ya mike a fusace, bai san sadda ya soma ɗaga murya a magana ba.
"Kawu! Tsanar ta isa haka! Haba! Wadannan mutanen da ka ke zagi babu ranar da ba sa yi mana nasiha akan mu bi ku mu yi biyayya! Mene laifinsu ma zuwa a bare?! Waye bare? Ina ku ka samo wannan al'adar marar tushe?! Wallahi wallahi! Ina girmamaka ne domin Dada, darajar su ka ke ci nake ragamaka a dukkan wulakanci da cin kashin da ka ke yi! Amma... (Ya nuna shi da yatsa) Daga yau na zubar da girman a idona na take shi! (Ya yi amfani da ƙafarsa wurin murje ƙafet ɗin ɗakin) Daga kai har zuri'arka duk wanda ya ƙara gangancin cin zarafin iyayenmu sai na nunamaku cikakken ɗan halak ne Hussein! Mu zuba da ku!"
Yana kaiwa nan ya juya yayinda kalaman Kawu ke shiga kunnuwansa.
"Ni ka ke gayawa magana haka? Lallai zan nunamaka ƙarshenka!!"
Wannan kalaman tsaf sun shiga kunnensa sai dai ko kaɗan bai ji ko ɗar ba, bai tsaya sallama da kowa ba ya kama hanyar fita. A zaure suka hadu da daya cikin samarin gidan ɗa ga Hajja Fatuma, Bashir. Fiito ya soma yi yana waƙe wanda hakan ya ƙular da Hussein ya kuwa haɗa kansa da bango ya bishi da lafiyayyen mari.
"Ubanka ma ya yi kaɗan balle kai!"
Daga haka ya fice ya bar shi da ihu da kururuwa.
Ranar dai gidan abokin Baba Naziru ya kwana washegari da sassafe ya juya gida Adamawa. Kwanansu uku, ya yi mamakin yanda Kawu bai kira Dada ya sanarmata ba, shima ya haɗiye bai faɗa ba. Har hutunsa ya ƙare bai ji wani bayani ba don haka da dariyar mugunta ya bar ƙasar. Ya dai gane a baya ma Kawunnasu wuri ya samu!
***
Daga AlHassan har Hussein, kowanne ya na iyakar kokari wajen yin karatu yanda ya dace. Basu da wani buri face su fito first class ko don su farantawa uwa da uban da suka rikesu tamkar su suka haifesu rai.
Hussein saurayi ne mai daure fuska da tsauri a wasu lokutan, zai yi wuya ka ga dariyar Hussein. Ya killace kansa ya kasa yin abokai sai abokinsa daya haifaffen garin Saudiyya kuma mazaunin can, Rasheed. Sun shaƙu sosai da Rasheed wanda ya kasance ruwa biyu. Mahaifiyarsa irin Takarunnan ne dake zuwa daga ƙasashe daban-daban, sai dai ita din ƴar Katsina ce a Nijeriya. Mahaifinsa kuwa haifaffen garin Makkah ne a Saudiyya. Zama ne ya haɗasu har aka kai ga yin aure, Allah Yasa Rasheed ta hanyar aure suka haifeshi.
Wasu ƴanmata basu a gaban Hussein, akwai da yawa da suka yi suka gaji bai ko kallesu ba. Don ya wulakanta duk macen da ta tunkareshi ba kunya ta nuna tana sonsa, ba komai ne a wurinsa ba lokacin. Hakan yasa wasu da yawa suke komawa tsanarsa shi kuwa ya dau hakan wai harara a duhu don bai ɗaukesu da wata ƙima ba.
Ɓangaren karatu, kusan yana daga cikin ƙwarin ajinsu wadanda za'a iya kira da gifted. Allah Ya ba shi fasaha da saurin daukar karatu hakanan Rasheed.
Da taimakon Allah lokacin yayesu daga makaranta ya yi. Murna a wurinsu ba'a magana idan ka cire Rasheed da Hussein wadanda basu kaunar rabuwarsu. Sun tabbata sai ziyara ce za ta ƙara haɗa fuskokinsu, kafin ma a ziyarci junan zai iya daukar lokaci.
***
Hajiya Zeenatu Bashir wacce ta kasance marainiya, ta tashi a hannun kakarta mai son abin duniya. Sanadin hakan ne ta hadata da wata Agent mai safarar yara zuwa Saudiyya aikatau da Bara. Ta yi wannan aikin na shekaru goma kafin a karshe kanta ya waye ta samu ta tara kudi sosai ta dawo gida Nijeriya. Haifaffiyar garin Katsina ce, sai dai kasuwancinta da kuma rasuwar Kakarta a shekarun baya, ya maidota Kano da zama. Ta zama mace mai zaman kanta, sun haɗu da Ƙawarta Hajiya Batool wacce itama ta ke kasuwanci, a jirgi sadda za ta dawo daga Saudiyya. Nan suka ƙulla aminta sosai, don haka koda ta dawo Kano sai suka hada jari suka ci gaba da harkallar kasuwanci. Tana da zaurawa da dama waɗanda ta k rage dare da su,wannan a wajenta bakomai ba ne, a irin wannan harkar ne ta san da zaman Aliyu Dikko wanda a baya sun zuba lokacinsu tare duk kuwa da tazarar shekaru biyu da ta ba shi.
Haduwarta da wani ƙusa a gwamnati yasa jarinta daɗa faɗaɗuwa, ta soma fita sarin kaya Dubai tana kawowa katon shagon da ta buɗe a nan Sabon gari, kuma takan taɓa siyasa musamman wurin kamfen.
A wani zuwan karshe da ta yi ne a wani shagon kayan kwalam ta haɗu da wata ƙawarta da suka hadu a aikin Hajji, Hajiya Basira ƴar asalin garin Katsina da aure ya kai ta Saudiyya.
Da mamaki ta kira sunanta, Hajiya Basira na ganinta suka cafke suna dariya. Kowannensu bakinsa cike da hira, karshe dai tare suka fito zuwa masaukin Hajiya Basirar. Anan ne ta ke jin cewa ɗanta Rasheed ne ya kammala karatu ta zo bikin yayeshi.
"Ke dai Hajiya Zeenatu kin ƙi yin aure kin zauna kina cin karenki ba babbaka, nima fa nayi irin rayuwarnan a baya kafin Allah Ya tseratar da ni, kin fi kowa sanin yanda rayuwa irin haka ke ƙarewa."
Wani fari da murmushi Hajiya Zeenatu ta yi.
"Me kike ci na baka zuba ne? Tunda na tara abinda na tara dagaske yanzun nima aure zan yi. Kwantar da hankalinki."
Suka yi dariya gami da cafkewa.
"Yauwa, yanzu naji batu."
Da wannan suka shiga hirarsu kafin a karshe Hajiya Zeenatu ta yi mata sallama da alƙawarin goben za ta zo su je taron yaye ɗanta a makaranta.
***
Washegari kuwa ta cika alƙawari, a gidan Rasheed da Hussein suka kwana sai dai da sassafe suka koma cikin makaranta.
Hajiya Zeenatu suka ɗunguma zuwa makarantar. Wuri ya cika ya batse, dalibai sun sha kyau sun gaji. Baba Naziru ne kaɗai ya zo wa Hussein, hakan ma ya mishi dadi sosai.
"Yauwa ga ɗannaki." Muryar Hajiya Basira ya katse Hajiya Zeenatu daga kan wayarta, tunda ta ɗora idanu akan wani matashi da bai fi shekaru ashirin da biyar ba, mai cikar kamala da zati ta ji kamar an shanyemata jinin jikinta. So da kauna da sha'awa wanda ya fi komai rinjaye, ya tafi kacokan kan HUSSEIN. Tafe suke tare da Rasheed yana murmushinnan mai kashe zuƙatan ƴan mata.
Har suka ƙaraso suka ɗan russuna suka gaishesu, Hajiya Zeenatu ba ta iya amsawa ba. Kallo ɗaya Hussein ya yi mata bai ƙara ba tuni kuma ya ɗan daure fuska, kallo ne irin wanda ya san ƴanmata da ke bibiyarsa na yi gareshi, wannan ma kusan ya fi nasu muni a wajensa don kallo ne har da na haram.
"Ana gaisheki." Sai a nan ne Zeenatu ta dawo hayyacinta ta amsa gami da taya musu murna. Hussein dai rarraba idanu ya ke, can ya hango Babansa, da sassarfa ya karasa ya rungumeshi. Shima Baba Naziru shi yake nema, suna murmushi suka saki juna ya mishi fatan alheri.
Har suka bar wurin Hajiya Zeenatu tunanin Hussein ta ke yi, so da kaunarsa take ji na ratsata. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta nemi lambarsa wurin Rasheed. Ta kuma nuna ta na son ganinsa. Rasheed bai kawo komai ba ya gayyaci Hussein gidansu, haka ya bar Baba Naziru a Hotel ya zo.
Suka kebe da Hajiya Zeenatu
"Lafiya Mama?" Abinda ya soma cewa kenan da ya soki Hajiya Zeenatu a ƙahon zuci. Murmushi ta yi da yin fari cikin jan sa.
"Lafiya dai dan samari, oh, Hussein na Hassan."
Ya ɗan daure fuska.
"Sauri nake yi."
Ta gyara zama.
"Ka yi hakuri na sa an kiraka na kashemaka dukkan uzuri ko? Ba komai bane Hussein, wallahi sonka nake tun ganin da .."
Dariya da ya shiga yi ne ya dakatar da ita kafin ya gimtse. Kallon raini ya watsamata ya mike tsaye
"Dube ki don Allah! A haihuwar kauye wallahi kin haifen amma hakan bai sa kin ji kunyar ki kalleni ki ce wai kina sona ba! Ƴanmata ma basu isheni kallo ba ballantana kuma ke ƙatuwar da an girma ba'a san an girma ba. Don Allah ki kama girmanki , zai fi miki akan wannan budurwar zuciyar."
Daga nan kama hanya zai fita. Muryarta ya tsaida shi.
"Za ka yi dana sanin wadannan kalaman da ka furta gareni Hussein."
Ya juyo yana murmushi ya dubeta don dagaske abin dariya ya bashi musamman na ganin hasashensa ya zama gaskiya, girgiza kai ya yi.
"Naji daga bakin ƴanmata bila adadin. Ki yi duk abinda kika yi niyya, ni din dai har abada na fi karfinki."
Daga haka ya banko labule ya fice ya bar Hajiya Zeenatu na cika da batsewa.
"Alwashi na ci! Wallahi wallahi Hussein sai na aureka, sai na juyaka kamar waina a tanda."
Ta furta a fili.
Bata rabu da Rasheed ba sai da ta yi mishi dabarar da ta karbi har address din Hussein na Adamawa kamar yanda ya fadamasa.
Da wannan ta koma Kano cike da shaukin Hussein da bege.
***
Ƴan biyun Dada suka dawo Adamawa da sakamako mai kyau, kowa a dangi murna yake. A sannan aka yi bikin ƴan matan Dada su uku, aka bar ta daga ita sai Auta Hafsat wacce a sannan take ajin farko a Sakandire.
Da shekara daya suka kammala bautar ƙasa aka shiga neman aiki, a sannan ne alaƙa ta soyayya ta ƙullu tsakani Alhassan da Kausar. Shi kuwa Hussein ya rantse ba zai auri kowa a dangi ba don auren dangi ba ya burgeshi musamman kasancewar a sanadinsa aka tsani iyayensa.
"Duk da haka ka fito da matar aure. Ba zamu zubamaka idanu ba." Abinda kakansu kuma mahaifin Baba Naziru ya ce kenan. Taɓe baki Hussein ya yi.
"Ga matarka nan Hajiya Zahida mai naira, nikam ta isheni." Aka sa dariya. Hajiya Zahida ta gyada kai.
"Eh na isheka, amma ina bukatar abokiyar zama."
Miƙewa ya yi.
"Bari naje, ina da aiki dagaske." Ya fadi da harshen fulatanci.
***
MAFARIN KOMAI...
Yammacin Laraba ce a garin Adamawa, fitowarsa kenan daga katafaren shagon Ikhlas, hannunsa rike da leda ya siyo Ice-cream.
Tana tsaye jikin motarta, tun fitowarsa daga gida ta ke biye da shi, koda shigarsa shagon, ta ja kwallin da Gora ya bata, da tabbacin duk inda ta yi ido hudu da Hussein, komai zai kasance yanda ta so.
Da wannan ta yanke tunaninta ta ƙarasa inda yake.
"Hussein." Fuska a daure ya ɗago ya dubi mai maganar, ido cikin ido suka kalli juna. Wannan ɓacin ran da ya tasomasa da wannan daure fuskar, sai ya nemesu ya rasa, wata soyayya ce ke shigarsa da kauna. Kansa ya yi wani nauyi, ga mamakinsa, murmushi ya shiga yi mata.
"Nasan ba ka gane ni ba, Hajiya Zeenatu ce da ku ka haɗu a Dubai."
Maimakon baƙar magana sai ya yi ƴar dariya da lumshe ido.
"Na ganeki mana, Zeenatu ai kyanki kadai ma ba zai sa na manceki ba."
Wani dadi da farin ciki ya kusan zautar da Hajiya Zeenatu. Gora da Hajiya Batool ta shiga sanyawa albarka. Sanadin Hajiya Batool ta san Gora, yau gashinan ya ba ta abinda bata taba tsammanin zuwansa da sauƙi ba.
***
Tun daga wannan ranar magana da tunanin Hussein ya koma kan Hajiya Zeenatu, kamar yanda ta kwaɓeshi da faɗar alaƙarsu a gida, haka ya bi. Idan bai ji muryarta ba har hawaye yake fitarwa ya bazama hotel din da ta sauka.
Hussein ya sauya a gidan, Dada ta zaunar da shi ta mishi tambayar duniya ya nunamata ba komai. Hakanan Hassan ya kasa gane kan ɗan uwansa.
Haduwar Hajiya Zeenatu da Hussein na karshe ta fashe da kuka ta nunamasa idan har yana sonta ya amince ya biyota su wuce Kano a dauramusu aure don kuwa ta tabbatar ba wanda zai amince da aurensu a danginsa tunda ta girmeshi. Hussein ya ji maganar babbarakwai, hankalinsa ya tashi. Yana so ya ce mata a'a amma abin ya faskara, ganin bai ce komai ba ta ƙulla gaba da shi ta ce ya rabu da ita har abada ba ta sonsa. Kowa ya kama gabansa.
Ta fadi hakan ne don ta san ba mai yiwuwa bane, tuni ta juyamasa ƙwaƙwalwa ta hanyar zubamishi siddbaru a abinci da abin sha. Wani irin soyayyarta ke addabarsa da wani irin tsoro.
Sai dai batun ya bar ƴan uwansa dominta ne ya ji kamar ya mishi nauyi. Da wannan suka rabu ta koma Kano kamar yanda Hajiya Batool ta bata shawara, sun riga sun san zai biyo bayanta don aikin da aka yi mishi mai karfi ne. Layu ne aka sanya a gaban gawar mace. Hakanan an kwaƙule idanun jariri sabon haihuwa an haɗa da maganin.
***
Kwanaki uku ya biyo baya Hussein ya rame ba walwala. Wannan ya tashi hankalin kowa. Aka haɗa meeting aka zaunar da shi don jin bayani.
"Aure nake so a yimin. Na samu matar aure amma ta girmeni don za ta yi shekaru arba'in. Wallahi ita nake so, don Allah kar ku hanani aurenta."
Ran kowa ya ɓaci, nan Baba Naziru ya rantse ya kara ba zai aureta ba. Kowa kuma ya goyawa hakan baya ba tare da sanin abinda hakan zai haifar ba. Ga mamakin kowa Hussein ya mike a fusace.
"Eh dama ai kun fi son Hassan! Shi da ya kawo wacce ya ke so wane ne ya hanashi? Sai don zan auri bare? To ai nima uwata bare ce a cikinku don haka ba wanda ya isa hanani auren wacce nake so!"
Daga nan ya fice daga dakin ya bar kowa baki a sake. Dada kuka ta sanya saboda kunyar da Hussein ya bata.
A karshe Baba Naziru ya fusata ya ce da kansa zai zaɓamasa matar aure.
***
Washegari cikin dare Hussein ya shirya kayansa da takardunsa masu muhimmanci, ya kalli Hassan dake bacci na ƴan dakiku. Kirjinsa na faduwa hakan bai sa ya sauya ƙudurinsa ba. Hannu ya kai ga wani hotonsu da suka yi a tsaye da ƙananun kaya, asalin hoton a waya suka yi amma saboda kyansa suka wankeshi suka sanya a frame. Ya dauka ya cusa a jakarsa. Ji yake kamar muryar Hajiya Zeenatu na amsa kuwwa a kunnensa. Gani yake idan har ya kara kwana bai je inda take ba haukacewa zai yi. Daga wannan tunanin ya sa ƙafa ya bar gidan. Maigadi na can yana sharar bacci ya fice gaba daya.
Wannan tafiyar da Hussein ya yi, shi ne tafiyar da bai ƙara takowa gidansu ba har wannan lokacin.
***
Koda ya isa Kano ya nemi Hajiya Zeenatu, ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Da kanta ta daukoshi daga tasha zuwa gidanta.
"Nasan dama ba za ka iya rayuwa babu ni ba."
Da jajayen idanunsa ya dubeta ya bi ta da murmushin yaƙe.
Ta mike zuwa dakinta ta faɗa bandaki, zirr ta yi ta wanke jikinta da ruwan magani kafin ta dawo ta shirya ta rambaɗa kwalli. Wani gari ta ɗebo a hannunta ta dawo falon.
Yana kallonta har ta zauna, a hankali ta bude tafin hannun ta huramasa a fuska. Tun yana ganinta daidai har ya yi luuum ya soma lumshe ido.
Wani magana ta shiga yi mishi a dodon kunne yana nanatawa.
"Ni kadai ce a wajenka, ni kadai ce a zuciyarka, ba ka da dangin da ya wuce ni. Ba ka da kowa a duniya sai ni."
Ya nanata, tun yana yi har a hankali ya kwanta kamar mai bacci. Wani mahaukacin dariya ta sanya.
***
Malami har gida ta kirawo ya daura aurenta da Hussein. Rabon goro da aka yi a makwafta ne ya sa suka san ta yi aure. Daga wannan lokacin Hussein ya zama mallakin Hajiya Zeenatu ita kadai, jallin jal!
Ya samu aiki a wani babban kamfani ta hanyarta, tun yana matsayin ma'aikacin har a karshe saboda jajircewa da amanarsa da kuma sanin makamar aiki, ya zama Manajan kamfanin.
Hajiya Zeenatu likkafa ta ci gaba, ta gina shaguna da dama, auren Hussein sai ya zama kamar wani buɗi a kasuwancinta. Ta dinga samun albarka a ciki kamar me. Har ya kasance ta bude shagon siyar da gwala-gwalai a sabon gari, tana kuma da na abayoyi, takalma da jaka a sabon gari. Suka hadu ita da mijinta suka bude katafaren shagon kayan maƙulashe mai suna A&Z Snacks and more.
***
CI GABAN LABARI...
[3/17, 9:18 AM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA HAMSIN DA UKU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1012068713?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=j0FhiwXlITINd2s%2FHQAEEJr6H0gN34Yx%2FYGs482Ps7p3eJzBM%2FSmZhkqmfmpfxwFqACqKgF4HYZBiBOLOGtFCjGLt%2FaBpqaFBTls4fQJ%2Fq25n%2BYh6%2FU6TYbmPJBSRTTM
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
53)
ADAMAWA
Hafsat ce tsaye a farfajiyar gidan suna hira da Tahir, murmushi sosai ne saman fuskarta, ko ba'a faɗa ba duniyar ta mata daɗi. Tahir kuwa jin komai yake yi kamar a mafarki, dama an ce mai hakuri kan dafa dutse har ya sha romonsa, yanzun gashinan ya gani. A hankali soyayyarsa ta kama zuciyar Hafsat.
"Dariya na ba ki?" Ya fadi yana murmushin shima. Hafsat ba ta kai ga ba shi amsa ba, suka ji hon. Nan da nan ta rude, ta san AlHassan ne don ya kira Dada ya sanarmata cewar yana hanya, ba wanda zai zo gidan da darennan idan ba shi b, hakan yasa ta dubeshi.
"Mu yi magana ta waya. Bari na shiga ciki."
Ba ta bari ya kai ga amsawa ba ta yi gaba da sauri. Tahir ya shafi ƙeya yana murmushi. Daidai sadda motar AlHassan ta faka, ya nufi wurin. Sai dai ya tsaya cak yana kallon wanda ya soma fitowa daga mazaunin gefe. Kamar AlHassan kamar ba shi ba, kafin ya kai ga tantancewa sai ga AlHassan ya buɗe murfin ƙofar ya fito
Wani tsalle da Tahir ya yi ya rungume Hussein yana ihun murna sai da ya ba AlHassan mamaki, sai kuma ya yi dariya. Duk wanda ya zauna da Dada ko na minti talatin ne, sai ya san yanda take kewar Hussein. Balle kuma Tahir wanda dama shi a baya ya san Hussein din, duk da ba su wani saba ba. Sanadin zamansa a garin kuma a gidan yasa shi damuwa da damuwar Dadan har yakan taya ta addu'a.
Suka dunguma ciki zuwa falon, Hussein jikinsa har rawa yake, burinsa kawai ya sanya Dadarsu a ido.
Tana falon zaune, a gefenta Fatima ce