Showing 165001 words to 168000 words out of 226732 words
ba shi da niyyar fitowa.
"Ka fara shiga, ina nan zuwa. Akwai wayar da zan amsa ne."
Bai takura mishi ba ya yi gaba zuwa ciki, Hussein ya kwantar da kai saman kujera gami da lumshe idanu. Hoton fuskar Chairman Aliyu Dikko ya kasa fice mishi. Ya kasa mance ganin da ya yi mishi a wajen Ramlat.
Kwankwasa gilashin motar da aka yi ne ya maido shi hayyacinsa, ya ɗago kai ya sauke gilashin. Ganin Hisham ya ja guntun tsaki. Hisham ya dora hannu saman windon.
"Yanzu na ga Twin brother dinmu, ya cemin kana mota shi ne nace bari na zo na ji abinda ha dakatar da kai daga shiga."
Hussein bai ce uffan ba, hannu kawai ya sa ya ƙaro volume na waƙar da ya ke ji.
Hisham ya zagayo ya bude mazaunin gaba ya shiga gami da kashe waƙar gaba daya.
"Kana da tabbacin abinda ka ke yi zai haifarmaka da ɗa mai ido? Kana da tabbacin wacce ka ke so za ta so ka a wannan halin? Meyasa ka ke kokarin hana zuciyarka abincinta a koyaushe? Meyasa ka ke hana idanuwanka ganin irin sadaukarwar da Ramlat ta yi maka da gangan?"
Hussein bai ce uffan ba, bai kuma katse shi ba don haka ya ci gaba.
"Anya Hussein ka san wace ce Ramlatu?"
"Mutum."
Ya amsa kai tsaye yana murmushi gami da kallonsa. Hisham ya harareshi.
"Eh mutum ce, amma ta bambanta da irin mutanen da ka ke mu'amala da su."
"Rabinta aljana ce?"
Ya ƙara watsamasa tambayar da ta ƙara kai Hisham bango.
"Kana ƙin gaskiya da gangan, amma magana ta gaskiya, Ramlat ba irin macen da namiji zai kyale ba ce."
"Ya aka yi ta rabu da uban ƴaƴanta?"
"Wai ban taɓa faɗamaka baban yaranta rasuwa ya yi ba?"
Hisham ya tambaya da mamaki. Hussein ya girgiza kai.
"Bana jin mun taɓa hirar, idan ma mun taɓa to na manta kam. Allah Ya yi mishi rahma."
"Amin."Hisham sai ya karkace ya hau ba shi labarin rayuwar Ramlat tun daga farko har zuwa rasuwar mijinta a tsakiyar filin sallar juma'a kuma cikin watan azumi.
Hussein ya yi shiru bai katse shi ba har ya kammala.
"To meyasa yanzu ba za ta auri Yallaɓai ba? Ko ba komai zai jiyar da ita farin cikin da za ta mance dukkan ƙuncin rayuwa."
Hisham ya ji kamar ya shaƙe shi.
"Ba wannan nake nufi ba, kai nake so ka auri Ramlat ko don irin son da ka ke mata. Wallahi ba ta dace da kowane namiji ba sai kai."
"Na taɓa ce maka ina sonta?" Hussein ya fadi kansa tsaye yana murmushi, wani irin murmushi tun daga ƙasan zuciya. Hisham ya kara jin haushi da takaicinsa.
"Dan iska kawai, sai ka zauna kar ka aure ta din!"
Yana kai wa nan ya bude motar ya fice. Hussein ya tashi motarsa ya yi ribas har ya kusa yin sama-sama da Hisham banda Allah Ya sa ya matsa gefe. Murmushi ya ke yi ganin yanda Hisham din ya fusata ya na surfa bala'i. Ya juya kan motar ya fice daga asibiti zuciyarsa kamar an narkar da ƙanƙara.
Awanni biyu zuwa uku, sai ga shi nan ya dawo niƙi-niƙi da kayan dubiya ya bar su a cikin motar, sai da ya shiga masallaci ya gabatar da sallar isha'i sannan ya karasa ciki.
Aka yi sa'a masu gadin Ramlat sun yi gaba bisa umarnin da Chairman din ya bayar. Sai kuma goben za su ƙara dawowa.
Kwankwasawa ya yi ya shiga da sallama, gaba daya mutanen da ke dakin suka amsa. Ya karasa shiga bai ko kalleta ba ya durkusa suka gaisa da Hajiya. Ta amsa da fara'arta tana kara taya shi murnar haduwa da ɗan uwansa. AlHassan na zaune yana cin abinci kai ka rantse dama can wani irin mugun sabo aka yi da juna. A'isha ce abokiyar hirar, ana ta dariya. Hisham wanda ya kauda fuska bai ko kalleshi ba. Hussein ya mike ya nufi gefen Ramlatu, tun shigowarsa kirjinta ke harbawa da sauri-sauri.
"Sannu, ya jikin?"
Ya fadi ƙasa-ƙasa, hirar da su AlHassan ke yi ya hana Hisham mai kasa kunne jin gulma.
A hankali ta dube shi., fuskarta ta yi fayau.
"Alhamdulillah da sauki."
"Allah Ya ƙara lafiya."
Ta amsa da amin ta kuma yi mishi godiya. Har zai juya ta yi magana.
"Na tayaka murna, Allah Ya kara kiyayewa."
Ya juyo kansa ya dube ta. Ta kasa gane ma'anar kallon don haka ta kauda kai.
"Na gode sosai."
Daga haka ya koma wurin su Hajiya. Nan Hajiya ta ba Aisha umarnin ga zuba mishi abincin. Bai yi musu ba don dama yana jin yunwar kadan kuma ba ya son ko loma daya na abina Zeenatu ta girka ya shiga cikinsu shi da ɗan uwansa. Kusa da Hisham ya zauna saman kujera maimakon gefen AlHassan wanda ke zaune saman darduma.
"Ka gama fushin?"
Ya fadi daidai saitin kunnen Hisham yana murmushi.
Murmushin shima Hisham ya yi. Ko ba komai zuciyarsa ta yi tas ganin bai ba shi kunya ba ya shigo. Aka zuba mishi abinci ya soma ci.
Ramlat gaba daya fa an kasa sakewa, ita ce ta ja mayafi ta gyara sai kuma ta ja zani. Har dai garin juye-juyenta ta fama ciwon aikuwa ta saki ƙaramin salati.
Ya ɗago idanu ya dube ta, ita din ma shi ta kalla. Sai ta janye da sauri tana amsa tambayar Hajiya.
"Lafiya lau Hajiya, fami nayi kaɗan."
"Sannu, ki dinga bi a hankali."
Cewar AlHassan. Ita kuwa Aisha ta mike ta nufi wurinta tana gyaramata zaman mayafin da ta ke ta fama da shi.
"Sis, wannan irin rashin sukuni? Ko duk a dalilin Hussein ne?"
Ta fadi murya ƙasa-ƙasa yanda Aisha din ce kadai za ta ji. Harara ta bi ta da shi ita kuwa Aisha ta yi ƴar dariya.
[3/16, 1:55 PM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA HAMSIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1009630651?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=ynI1KGJjd7sQQHwi7y8Hy%2FURSw8ZoDbiFN7aldIK5sou8xXacVQ1hbP5MNPCrtXe3NJxi6hvqSx39DOvHzE2aH8gSWFQR%2FiXs3hPnnEYhollJSFusGkC3Jmu6jUkimqk
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
51)
Shi kuwa gogan abincinsa kawai yake ciki fuskarsa cike da wani irin nishaɗi. Ya kammala ya dire farantin.
"Hajiya muna godiya."
Murmushi Hajiya ta yi don tagwayen ba karamin burge ta suke ba.
"Yaushe ne tafiyar taku Adamawa?"
AlHassan ya amsamata.
"Gobe da zarar an shiga kotu an fito za mu wuce."
"Allah Sarki, toh Allah Ya nunamana. Sai dai zan so na ji taƙaimaiman tarihin abinda ya faru gareku a baya."
AlHassan ya murmusa.
"Kar ki samu damuwa Hajiyarmu, in sha Allah komai za ku ji gaba dayansa."
Ta jinjina kai.
"Allah Ya nunamana lokacin."
Aka amsa da amin. Ramlat ta yi shiru, itama abinda ta ke son ji kenan, tana son sanin yanda har Hajiya Zeenatu ta yi nasara akan su.
Kwankwasa kofar da aka yi gami da sallama yasa duk suka mayar da hankali. Nos Farida ce. Suka gaisa sannan ta miƙawa Ramlat takarda. Cikin raɗa-raɗa ta ce.
"Gashinan, Khadija ta nemi da na ba ki."
Ta karɓa da mamaki ta kuma yi godiya. Daga nan Farida ta juya ta fice. Ta ɗago ta dubi mutan dakin wadanda ita suke kallo. Ta maida hankali ga takardar ta warware ta shiga karantawa.
_*Assalamu alaikum,*_
_*Ramlat ina miki fatan alheri da kuma samun lafiya. Akwai wani lamari da nake son sanarmaki. Wata mata ta yi barazanar hallaka ni matukar ban aiwatar da aikin da ta sanya ni ba, wato na kashe ki. Laifi ne da har abada bana fatan na aikata koda a kan maƙiyina ne. Ina mai ba ki shawara akan ki nar asibitin nan da gaggawa domin idan ma ni na kasa aiwatarwa za ta iya siye wani da kudi ya cikamata burinta. Taku mai kaunarku, Khadija Ashir.*_
Bakin Ramlat ya shiga rawa yayinda idanunta suka cicciko da kwalla. Tsam! Ya miƙe ya ƙaraso wurinta ba zato ta ji an zare takardar daga hannunta. Ta dubeshi, shima ita ya ke kallo cike da zargi kafin ya maida hankali ga takardar.
"Meyafaru ne?"
Hajiya ta nemi sani. Ya miƙawa Hisham, Hisham ya karanta a fili. Hussein ya sa kai ya fice daga ɗakin.
Su Hajiya suka sanya salati.
"Wai wace ce wannan matar mai neman ganin bayan Ramlatu? Oh duniya ina za ki da mu? Nikam ko maganin asibitin nan ban yarda a ƙara kawowa ki sha ba Ramlatu."
Maganar karshe na Hajiyar sai ya ba AlHassan dariya.
"Kar ki damu Hajiyarmu, ba abinda zai sami Ramlatu da yardar Allah. Sai dai ya kamata a bi shawarar Khadija, a ɗauke ta daga asibitin."
"Dama ai Likitan ya fadi, yanda take samun sauki zai iya ba mu sallama gobe ko jibi. To ai kuwa gwara a yi komai."
Can wayar Hisham ta yi ringing, Hussein ne. Hisham ya saurari bayaninsa sai ya yi murmushi ya katse kiran.
"Ga wanda ya fi mu can ma ya tafi nema maku sallama a darennan."
Da mamaki Aisha da AlHassan har su na haɗa baki wurin tambayar waye?
"Hussein." Aisha ta saci kallon Ramlat tana murmushi, itama Hajiya murmushin ta yi kawai ba ta ce komai ba.
Kamar dai da wasa, haka Hussein a daren ya yiduk cuku-cukun da zai yi har aka ba su Ramlat sallama a daren. Suka haɗa komatsansu, Hajiya da Ramlat a motar Hussein, shi kuwa Hisham da madam dinsa suna tare. Amrah wacce har ta kamo hanya, sai waya suka yi mata suka sanarmata da batun sallama. Ita kanta ta yi mamaki.
A hankali ta ɗago kai don tun shigar ta motar kan yana a ƙasa. Caraf suka haɗa idanu ta cikin gilashin kasancewar AlHassan ke tuƙin wannan karon. Ta sauke kanta, shi kuwa ya samu damar ƙarewa fuskar kallo yanda duk ta faɗa kamar wacce ta yi cutar wata guda.
A hankali ya kauda kai, suka yi ido hudu da AlHassan da ke satar kallonsa, murmushi AlHassan ya yi mishi shi kuwa ya gyara zama gami da ɗan ɗaure fuska kadan yana shan ƙamshi.
Har gida suka kai su, Ummi da su Ansar duk suka fito a guje suna mata oyoyo, za su fada jikinta Hussein ya yi saurin riƙo Affan wanda ya fi kowa kusantarta, ita kuwa ta dafe hannu tana kiran wash!
"Ba kwa ganin ciwonta?"
Ya faɗi a hankali, suka fasa rungumeta su na dariya. Ya kama hannunsu zuwa wurin mota.
"Ku zo muje"
Ramlat ta bisu da idanu kafin ta juya ta bi sahun su Hajiya zuwa ciki. Shi kuwa Hussein ledojin dubiyar da ya loda a boot, shi ya ciromusu ya damƙa musu.
"Oya, maza ku je a kaiwa Mami sai ta ba ku."
Affan ya hau washe baki ganin Hussein ya fiddo alewa daga aljihu ha bude ya sanya mishi a baki. Murmushi sosai shima ya yi mishi ya bishi da kallo har ya ɓacewa ganinsa.
Bayan Hussein sun koma gida, Hajiya Zeenat ta tarbe su da fara'a tana mai danne takaicin da suka ɗuramata. Hussein ya dan sakarmata.
"Ki yi hakuri, gidan Hisham muka ci abinci ba haka na so ba."
Ganin yanda ya fadi cike da kulawa yasa nan da nan ta ji zuciyarta ta sake. Ko ba komai hanyar lafiya a bita da shekara. Yanzun dai kaffa-kaffa ta ke yi kar kwaɓarta ta yi ruwa. Da haka ya nunawa AlHassan dakinsa kafin shima ya shige nashi dakin. Hajiya Zeenatu ta yi mamakin da ya bari ta kwana tare da shi duk da bai yi mata kama ko hannunta ba, asalima baya ya juya da nufin bacci yake ji.Ta so su yi batun tafiyarsu London ammata share, har lokacin jikinta a sanyaye yake, burinta yanzu gari ya waye ta shiga asibitin da Ramlatun take ta ga ko ta aiwatar da aikinta.
"Gobe in sha Allah zan yi ƴar tafiya."
Hajiya Zeenatu ta tsinci maganar Hussein wanda ta yi zaton bacci ya ke kamar daga sama, ta mike zaune gami da kunna fitila. Har sannan ya bata baya. Ya yi crossinh hannaye a kirji.
"Ina za ka je kuma?"
"Adamawa." Ya furta kai tsaye gami da juyowa ya kalli tsaka idanunta. Duk sai ta ji ta rikice, hanjin cikinta sun kaɗa. Ta haɗiyi miyau, Hussein zai je Adamawa?
Hannunta ya ɗan riƙe ba don ya so ba.
"Ya naga duk kin sauya? Ba kya son na je na ga ƴan uwana?"
Ta yi murmushin yaƙe.
"Ko kusa aa, amma na ji haushi da ba ka shirya tafiya da ni ba, da ace ka yi niyyar muje tare za ka sanar da ni akan lokaci."
Ya yi ɗan murmushi.
'Makira.' Ya furta can ƙasan ransa. A fili kuwa ya shafi gefen fuskarta.
"Ki yi hakuri, bansan yanda za su kalli lamarin aurenmu ba. Gwara naje na yi musu bayanin komai a tsanake cewa auren soyayya muka yi. Kinga hakan zai fi armashi."
Ta ji wani sanyi kamar kankara, tana so ta yi shakku akan zancensa sai dai kuma ta kasa. Ta shiga gasƙata dukkan kalamansa. Hussein ya ci gaba da yi mata daɗin baki har sai da ta gasƙata da kanta cewar dagasken Hussein sonta ya ke yi ba wasa a ciki. Da wannan ta ji salama amma duk da haka tana tsoron a hana shi dawowa.
"Za ka dawo garinnan kuwa?"
Ya yi murmushi ya lumshe idanu.
"Wa zan bar wa ke?"
Ya fadi ba da manufa biyu, ta ji wani sanyi har sai da ta dara cike da shauƙi. Da wannan suka kwanta bacci.
***
ƘARSHEN ALEWA..!
A ranar Talata sha biyu ga watan Maris, kotu ta yankewa Halima da Gwaska hukuncin shekaru goma zuwa sha biyar a gidan yari a dalilin yunkurin kisan kai.
Halima ta yi kukan nadama sosai, karshe ta nemi alfarma wurin ƙaninta akan ya je ya nemar mata gafarar Ramlatu. Yusufa na hawaye haka suka rabu da Yayarsa aka tsitsa ƙeyarta suka bar kotun.
A can gida, Ramlat ta ji labarin komai a waya daga Hisham, kuka sosai ta yi na tausayin Halima. Haka ta dinga samun kira daga tsofaffin abokan aikinta na ma'aikatar Revenue, da yawansu sai yanzu suka san dalilin kamen da aka yiwa Halima. Sun jajantawa Ramlat gami da yin Allah wadai da son abin duniya irin na Halima wanda ya kai ta ya baro.
"Ai godiya za ki yiwa Allah don yau kam duka ranarki ce. Ga shi dai an yankewa wadanda suka zalunceki hukunci, ga Kawunki Jamuli ya karɓi kuɗi, ya kuma tabbatarmin da kansa yau ba gobe ba, zai damƙawa Chairman kayansa. A yi ta ta ƙare. Ke kuma ya ce idan kima kara warwarewa ki je yana son ganinki.
Maimakon farin ciki sai ya ci gaba da hawaye jin kalaman Hajiya, dama tun safe ta karbi Atm card din kuma ta fice tare da Munir. Uwa daban ta ke, ita ta tsaya tsayin daka tare da Hajja wurin karɓar mata ƴanci.
Sallamarsu ce ta katse dukkan tunaninta. Suka dube su. Shaddar ba iri guda ba ce, sai dai kowannensu fari ƙal ya sanya. AlHassan da hula a kansa, yayinda gogan ya fidda nashi a mota, sai sumarsa kwance. Hajiya tun shigowarsu take murmushi da yi musu adduar neman tsari da kariya a ƙasan ranta.
Ita kuwa tun da ta kalle su ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki. Suka karaso suka durkusa suka gaida Hajiya ta amsa fuska a sake. Suka yi mata murnar shari'ar da ta gudana, ta ta yi ta musu addu'a sosai. Ana haka sai ga Zulaihat da Rafee'ah suma, sun ji labarin sallama.
Suka karaso daidai sadda AlHassan ya dubi Ramlat.
"Kanwata ya jiki?"
Ta yi murmushi. Ta gaishesu. Ya amsa shi kuwa Hussein ya yi kamar bai ji ba yana kallon twins din Zulaihat.
Bayan zamansu aka kara gaisawa su na muu godiya.
"Zamu wuce Adamawa Hajiyarmu."
"To ƴaƴana, sai kuma yaushe?"
Hussein ya amsa wannan karon.
"Nan ba da jimawa ba za mu dawo in sha Allah."
Ta jinjina kai ta yi musu fatan isa lafiya. Hakanan suka kama hanya. Rafee'ah ta yiwa Ramlat ido, ba musu ta mike ta takamusu, ba laifi yanzu hannun da sauki sosai. A daidai barandar shiga dakin ta ci burki.
"Allah Ya tsare, Ya kaiku lafiya. Na gode sosai."
"Ke za mu yiwa godiya sosai. Allah Ya bar zumunci."
Ta yi murmushi.
"A gaidamin Fatina."
Ya yi murmushi.
"Za ta ji in sha Allahu."
Daga haka ya yi gaba, Hussein ya dube ta.
"Yarinyar da kika aikomin hotonta?"
Ta gyada kai tana murmushi. Sai a sannan ta ga ya yi mata murmushin shima.
"Ina kara godiya gareki. Allah Ya ba ki miji nagari. Oh, ashe kin samu. Allah Ya nunamana aurenku."
Ya karashe yana taɓe baki. Ta rasa ma me za ta ce, ya bita da wani irin kallon da ta kasa fassarawa.
"Ki kula da shan magungunanki, kada ki tsorata, likita da kansa ya rubuta da kaina na karɓomaki. Ba za ki mutu ba."
Ta dan yi murmushin yaƙe, ya juya ya tafi. Jiki a saluɓe itama ta koma ciki.
***
HUSSEIN AMINU MAMMAN MODIBBO...
Alhaji Aminu Mamman Gidado, haifaffan garin Adamawa ne gaba da baya. Su goma sha biyar cif mahaifinsu ya haifa. Mamman Gidado yana da mata uku, uwargidansa wacce suke kira da Inna, ta haifamasa yara tara cif a duniya, sai mai bi mata Yakumbo wacce ta haifi yara biyu. Hassan da Hussaina wanda a karshe suka koma hannun Inna da zama. Hajara (Hajjo) kuwa tana da yaranta huɗu cif a duniya.
Wani irin rayuwa ake gudanarwa a gidan Mamman Gidado, rayuwar da hatta da maigidan shakkar Inna yake yi balle a kai ga mata da yara. Inna wata irin mace ce murɗaɗɗa mai baƙar zuciya, a duniya ba ta kaunar ace wani ne sama da ita koda a matsayi ko wani abin. Auren gida na zumunci aka yi musu da Mamman Gidado.
Sai kuma cikin ikon Allah ya zamana Yakumbo ta fito daga gida na sarauta a garin Mubi. Mahaifinta shi ne wazirin Sarki. Wannan girma da nasaba ta Yakumbo sai ya jazamata baƙin jini fiye da na kowa a wurin Inna.
Ita ta soma yiwa Yakumbo gorin zama bare a gidan don Hajjo ma ƴar aminin kakansa ce aka aura. Yakumbo tana shakkar Inna sosai, tana kuma bin ta sau da ƙafa.
Mijinsu ba karamin so yake yiwa Yakumbo ba, tana matsayi babba a zuciyarsa da bai jin ko Inna ta samu. Wannan ta sanya mutuwarta ba jimawa shima ya soma jinyar ajali. A gaban idanunsa Inna ta sha hana Amina da Aminu abinci, wataran Hajjo a sace take basu. Dangi kuwa ba'a taɓa ganin laifin Inna don a waje nunawa take nan duniya tana sonsu kuma tana riƙe da su da amana. Wannan tasa hatta ga yaranta maza da mata sun tsani su buɗe idanu su ga Amina da Aminu musamman ganin irin kyauta da gatan da ake nunamusu duk sadda suka kai ziyara Mubi suka dawo. Kayan da