Showing 132001 words to 135000 words out of 226732 words

Chapter 45 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12450

na ranar Talata, Rasheed ne zaune yana faman haɗa gumi ga idanunsa da suka kaɗa suka yi ja tsabar tashin hankali. Labarin ɓatan amininnasa ya matuƙar girgiza shi.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"

Ya furta a fili, Dada dai hawaye ta ke yi hakanan Hafsat da ke raƙuɓe a gefe ta dora hannu saman cinyar Dada. Rasheed ya dubi AlHassan cikin harshen turanci.

"Ban ji dadin wannan labarin ba sam! Sai dai ina ji a jikina duk inda Hussein ya ke yana raye, bai mutu ba. Sannan meyasa ba ku yi cigiyarsa ta gidajen rediyo  da talabijin ba? Na dauka wannan ce hanya mai sauki da za ku yi saurin ganoshi."

AlHassan ya jinjina kai.

"A farko duka mun yi wannan amma a karshe sai muka watsar mu ka fawwalawa Ubangiji. Ni kaina ban yarda cewa Hussein ya mutu ba. Amma ya zamu yi? Babu inda ba mu nemeshi ba, sai dai ba wani labari."

Rasheed ya runtse idanu cike da ɓacin rai, ransa na suya.

"Kuma babu wani abokin gaba da ya ke da shi? Wanda ku ke zargi?"

"Babu."

Rasheed ya yi shiru, so ya ke ya tuna ko akwai abinda ya manta game da Hussein. Duk iyakar kokarinsa ya kasa, a ƙarshe dai AlHassan ya shiga roƙonsa akan ko labari ya ji na abinda ya danganci Hussein don Allah ya sanarmusu.  Bai bar gidan ba sai da ya ci abinci, nan ma kawai cusawa yake, ba zai ce cimarsu ta bambanta ba don shi kam ruwa biyu ne, mahaifiyarsa ƴar jahar Katsina ce. Jimami da alhinin ɓatan Amininnasa ne ke sukarsa. Da wannan ya musu sallama ya bar gidan.

Ranar dai ya tayarmusu da alhinin Hussein, wunin ranar sun yi shi sukuku ba daɗi idan ka cire Taheer da bai san me ake ba.

Burinsa kawai ya shaƙu da Hafsat kuma ta kaunaceshi, sai dai abin ya faskara.

***
  KANO

Wata wawuyar dariya Hajiya Zeenat ke yi tana ƙara rungume wayarta a kunne, ƙafafunta kamar za su rabu da cinyarta tsabar girgizasu da take. Kallo ɗaya za ka yiwa yanayinta ka fahimci ko ma wane kalar labari ake ba ta ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba.

"Kai Dikko! A ganka nan a bar ka inda kake! Da ace za ka san daɗin da wannan labari ya min za ka sha mamaki. Kai ma kwallon shege ne!"

Can kuma ta ƙara nutsuwa ta ce.

"Kana ji na? Kar ka sake ka yi wasa! Kar ka ɗaga ƙafa, wani ganin ba ta sonka ko ta tsaneka wannan duk a banza ce muddin ta faɗo hannunka. Ka dai ƙara ƙaimi wajen sakarwa makwaɗaitan iyayennata aljihu, na tabbatar maka ƙarfin dukiya ya fi komai tasiri a duniyarnan. Don ubanta dole ma ta sarara ta aureka. Ni kuma na maka alƙawarin wata kyauta mai tsoka muddin ka mallaketa matsayin matarka."

Jin haka daga can ɗaya ɓangaren, Chairman ya shiga zuba godiya da kirari, wannan ya ƙara fasa kan Hajiya Zeenatu, har wani lumshe ido take tana murmushi, koda ta ji motsin saukowar mutum daga bene ta yi sallama ta ajiye kan wayar. Duban mijinta ta shiga yi tana murmushi sosai, ranta na wani irin sanyi kamar ƙanƙara. Shi kuwa bai san ma tana yi ba, kacokan hankalinsa yana kan wayar da yake amsawa na Hisham game da kasuwanci na haɗin gwuiwa da suke son yi.

Har ya sauko ya ƙaraso bai kammala ba, ganin irin kallon da ga ke jifansa da shi yasa shi fadin.

"I will call you back." Daga nan ya katse wayar.

"Lafiya?"

Abinda ya ce kenan. Ta yi farr da ido, ya kauda kai.

"Ba komai, kawai dai kyau ka yimin Yallaɓaina."

Ɗan murmushi ya yi bai ce uffan ba.

"Amm, dama ina son zuwa asibiti."

Ya dubeta.

"Meke faruwa?"

Cike da ƴar damuwa ta ce.

"Kwanakinnan komai na ci sai na ji kamar zan yi amai, ga yawan kasala."

Kirjinsa ya bada dam! Haka kawai zaton da ya yi sai bai mishi wani dadi sosai ba. Ya daure ya gyada kai da murmushin da ya fi kama da yaƙe.

"Ya kamata ki je, ba'a wasa da lafiya."

Ta ƙara rausaya ƙwayar idanunta.

"An gama Baby, da safe za shirya na je. Fatana Allah Yasa mu ji alheri."

Ta ƙarashe tana shafa cikinta, ya yi murmushi kawai ya maida hankali kan wayarsa. Hotom Fatima ya buɗe yana kallo, gani yake idan har Hajiya Zeenatu za ta haifamasa irinta, toh yana marhaba. Kaunar yarinyar ya ke ji sosai. Abu daya ya tuno da ya ji ba dadi, wato dai rabon da ya ga Ramlat ma a online tun ranar da ta turo mishi hoto.

"Wannan kuma wacece?"

Tambayar Hajiya Zeenatu da ya yi saurin maidoshi tunaninsa. Ya sauka daga whatsapp din ya rufe wayarsa, cikin faɗuwar gaba ya ƙirkiro ƙarya ya shirgamata.

"Ƴar sister din Hisham ce. Ta miki kyau ko?"

Nan da nan annashuwar saman fuskar Hajiya Zeenatu ya dawo, ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi.

"Sosai yarinyar ta yi kyau. Zamu haifi fiye da hakan ma."

Ya gyaɗa kai kawai.

***
"Wai wa ya faɗamaki ina sonsa? Ni wallahi ban taɓa sauraronsa ba."

Ramlat ke faɗi a gundure, gaba ɗaya zancen Chairman ya isheta. Ta kuma lura mitar Rafee'ah ba mai ƙarewa ba ce.

"Ai shikenan, idan dai kina son a tabbatar da hakan sai ki daure ki fiddo miji. Ko kuma shawara, ki samu Baba Dakta kawai ki faɗamasa."

Cewar Rafee'ah.

Ramlat ta yi shiru, da sun san damuwar da take ciki na son maso wani da basu takuramata da zancen Chairman ba.

"An faɗamaki Baba Daktan shima zai saurareta ne idan ba wani ta kawo ta ce shi za ta aura ba? Malama ki yiwa kanki faɗa tun wuri wallahi idan ba haka ba za'a ji kunya. Baban Twins yana da labarin Chairman Dikko, ba abinda ban sani ba na tarihinsa."

Wannan karon ma shiru ta yi, Ramlat ta yi dana sanin dawowarta gidan da wuri, da ace ta san da zuwansu ba abinda zai kawo ta. Ta dawo ta iske Hisham ya gaji da zolayar ya aikomata motarta. Yinin ranar da tunanin Hussein ta cinyeshi, don dakyar ta dinga fuskantar aikin da ke gabanta, yanzun kuma ta zo ta iske yayyunnata, sun sanyata tsakiya kowanne da kalar nashi zancen.

Tsam! Ta mike tsaye ta kwashi tarkacenta na ofis da zummar wucewa.

"Au, mu za ki yiwa rashin ta ido? Don ana faɗamaki gaskiya?"

Ta kasa ba Anti Zulaihat amsa, cike da damuwa ta dubeta kawai.

"Wuce abinki, ke kika sani. Rayuwarki ce."

Ta furta a zafafe, Ramlat ta ciji lebbanta tsabar takaici, karshe ta yi gaba zuwa daki tana ji Hajiya na fadin su bita a sannu.

Ruwan ma kasa watsawa ta yi don haka ta bi lafiyar gado ta kwanta, a hankali ta shiga fitar sa hawayen baƙin ciki. Kewarsa ta ke ji kamar ta yi me, ga wani irin sonsa da ke nuƙurƙusarta, kwana biyu ba su yi magana ba, bai ganta online ba kuma bai nemeta ta waya ba. Wannan yasa ta ƙara tabbatarwa ita kaɗai ke haukan sonsa. Ta kai minti goma sha biyar a haka ba ta iya ko motsawa ba, tausayin kanta take ji, da ace su Ummi na gidan, ko ya ya zasu ɗebemata kewa, kiran sallar Magriba ce ta tasheta. Ta faɗa banɗaki ta kama ruwa ta yi alwala.

Sai da ta idar da sallah kafin ta ninke Hijab ta fice zuwa falon. Wannan karon ta yi ƙoƙarin saita zuciyarta ta ƙaƙalo walwala, suka ci gaba da hira da ƴan uwanta kamar wani abu bai faru ba. Tattaunawa ce game da bikin da ya taso a Daura, wanda zasu tafi dukkansu don karshen sati ne. Su ma basu ƙara tayar da batun Chairman ba.

Sai bayan sun bar gidan, Hajiya ta shige daki don watsa ruwa, itama ta faɗa nata ɗakin da niyyar hakan.

Ganin hasken shigowar saƙo bai sa ta yi wani rawar ƙafa ba, hakan ya faru ba adadi a yini biyunnan, sai dai daga ta duba, saƙon Muhibbat ne ta ke gani, wani lokacin Hilal, wani lokaci kuwa saƙon kamfanin layukanta. Tunanin hakan yasa ta ƙin daukar wayar har sai da ta fito daga wanka ta gama shafe-shafenta ta shirya cikin riga da wando na bacci. Ta dora rigarta na sallah ta shimfida darduma. Sai da ya idar da sallar Isha'i ta yi duk abinda ya dace sannan ta ƙara samun nutsuwa.

Kai tsaye ta nufi wurin wayar, sunan da ta gani a saƙon ya sa ta jin nauyi a ƙafafunta, kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, haka ta buɗe bayan ta zaune gefen gado.

*Na lura kina da kishi, wato don ban nemi ki turomin hotonki ba ne yasa ki ke shan ƙamshi ko? Oya, a turomin yanzu. Happy?*

Lumshe idanu ta yi tana murmushi.






  
[3/16, 1:55 PM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA ARBA'IN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ysuMTT3Orcb





🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

42)

Dukkan godiya tabbata ga Sarki Allah. Tsira da aminci su kara tabbata ga Ubangijin Talikai.

Ina kara amfani da wannan damar wurin godiya gareku gaba daya. Alhamdulillah na kammala exams lafiya sai fatan sa'a in sha Allah. Ina godiya da hakuri da uzurinku gareni. Allah Yabar zumunci. Ameeen. Sai dai kar ku manta dama ba kullum nake posting ba, ina tsallake kwana daya. Allah Yasa mu ga karshen Ƙarfen Ƙafa lafiya. Ameen.



******

*Ya ya zan yi in misalta soyayya..? Ya ya zan yi in fasalta soyayyaa..? Ita ce ba'a siye da kudi duk dukiyaa..Ita ce mai gida na mulki shi ne zuciyaaa..Ta sanya mai ƙarfi ya sunkuyaa..ya zubda hawayen idaniyaaa..!* Umar M Shareef

Hoton ɗan aljan mai murmushi kawai ta tura mishi. Aka yi sa'a ya hau online. Ganin ya buɗe ta yi saurin kife wayar ta runtse idanu kamar yana gabanta, kirjinta na wani dukan tara-tara. Jin ƙarar shigowar saƙo yasa ta karkata wayar a hankali kamar marar gaskiya ta duba.

*"Please."*

Don ƙara tabbatarwa ta ƙara murza idanu ta duba, roƙonta fa ya yi? Anya? Kuma akan hotonta? Ina Hajiyarsa?

Duk wannan tambaya ce da babu mai amsamata sai shi, har abada kuma ba za ta tambaya ba. Ta jingina kanta jikin gado tare da miƙar da ƙafafunta.

*"Angel ɗina ya hana ni aikawa kowa hotona."*

Ta ba shi amsa duk kuwa da cewa ba ta ji dadin amsar ba, sai dai ta lura idan ta biyewa kanta, za ta iya tona asirin zuciyarta har ya gane inda ta dosa.

Ya buɗe, kusan mintuna biyar shiru, goma, sha biyar, duk shirun ne, shi bai sauka online ba kuma bai ce uffan ba. Ramlat dai har bacci ya soma fisgarta babu amsa daga Hussein. Don haka ta ajiye wayar ta mike ta kakkaɓe shimfidarta ta kwanta. Ta soma addu'oin kwanciya bacci kenan wayarta ta yi ringing. Da sauri ta kai idanunta, lambar da ta gani ya hargitsa kwanyarta, miƙewa zaune ta yi b shiri. Sai da ta kusan yankewa kafin ta samu nutsuwar ɗagawa. Leɓɓan ke rawa, zuciyar na ƙara ƙaimi wurin bugu sai dai lanƙwasa harshen har ta iya haɗa kalma kwakkwara ta gagara.

'Haka so yake?' Ta jefawa zuciyar tambaya. Ta san ba wannan ne farkon soyayyarta ba, wanda ta shimfiɗa a baya ya girmi wannan. Sai dai wannan shigarsa da tasirinsa mai sauri ne kuma mai sanyaya zuciya da ruhin ma'abocinsa.

"Kin yi shiru."

Ta dawo daga duniyar tunanin abinda ya yi mata nisa, TAZARAR DA KE TSAKANINSU kamar tazara ƙasa da sararin samaniya ne. Ɗumi ta ji a kumatunta, wani ɗanɗano na gishiri ya sauka a  leɓɓanta ta cije leɓɓan. Kitt! Ta katse kiran, ba ta tsaya anan ba sai kawai ta kashe wayar gaba daya ta jefa gefen gado. Kwanciya ta yi ta runtse idanu, me ya rinjayeta har haka? Hussein fa? Kamanninsa suka yi dirar mikiya cikin idanunta, tunaninta ya ɗauketa ya cillar tun daga ranar da ta soma ganinsa har zuwa yanzu da suke tare.

"Ka fi ƙarfina Hussein, Allah Yayemin wannan jarrabawar."

Ta furta a fili, ta yi addu'a ta kunna Mp3 Suratul Baƙara na tashi a hankali tana bi. Tun tana tunani har bacci ya yi awon gaba da ita.

***
  "Baƙo?"

Ta furta a mamakince tana mai tsurawa Baba Maigadi idanu, tana kyautata  zaton kunnuwanta ne basu ji daidai ba. Daga ita sai hijab saman rigar baccinta wanda ta dora zani a samansa.

"Nima kaina nayi mamaki Ranki ya daɗe, sai dai kuma kallo ɗaya na yi mishi uzuri."

Daga haka ya juya bai ƙara dogon jawabi ko ƙarin bayani ba. Ta bi bayansa baki galala sannan ta ɗago idanunta ta dubi agogo dakyau. Bakwai da rabi da safe.

'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!'
Ta furta a zuciya, Hajiya ba ta kai ga tashi ba. Itama baccin ta kasa, ta rasa ya za ta yi da ranta, babu jimawa da fitowarta falo ta ji kwankwasar Baba Maigadi, ya kuma isar da saƙo ya bar ta tsaye da mamaki da fargaba. Ta dai daure ta yi shahada ta zura silifas ta fito. Fuskarta fayau sai dai albarkacin ruwan alwala da ta yi yasa ya yi kyan gani.

Ido da ido suka dubi juna, daga shi sai riga da wando na sport. Ya zura hannu cikin aljihun wando, idanun sun yi luhu-luhu hakanan sun kanƙance, gashinnan a birkice kamar yanda fuskarsa ta nuna. Ta kasa kauda idanunta kamar yanda shima ya kasa kauda nasa, kirjinta lugude yake kamar ana surfa gero. Ya tako har gabanta ya tsaya.

"Me na miki? Ki fadamin laifina, kiyi hakuri."

Ta lumshe ido ta bude don mamaki, sai a sannan ta samu damar magana.

"Me ka yimin Hussein? Ba abinda ka yimin ni."

Ya girgiza kai, ta kalleshi sau daya ta kauda idanunta da sauri.

"Kin kashe waya ba ki yimin magana ba, don nace ki turon hoto? Wasa nake maki. Ki yi hakuri, na shiga rayuwarki da yawa."

Ta girgiza kai, kamar yanda idanunsa ya kaɗa, haka nata ya cicciko da kwalla.

"Ni wallahi ba abinda ka yimin, kuma maganar da nayi wasa ce kawai nayi ba wai da wata niyya ba. Shi ne dama ka doko sammako? Ka yi hakuri."

Ya yi shiru bai daina kallonta ba. Ganin shirun ya yi yawa ta kara kallonsa.

Hussein tambayar kansa yake abinda ya ruɗashi, ya hargitsa tunaninsa. Mene abin ɗaga hankali don Ramlat ta kashemasa waya? Me ya birkita kwanyarsa har bacci ya kauracewa idanunsa kamar yanda ya kasa bambance daidai ko akasinsa? Hajiya Zeenat baccinta take sharɓa ya fito, meyasa tunanin ta farka ta nemi ba'asi bai faɗomasa a rai ba sai yanzun da ganin Ramlat ya haifarmasa da sukuni da kwanciyar hankali? Sai dai kuma akwai wani duhu da ya kasa nemo haske a cikinsa, watakila sai nan gaba! Ya ayyana a ransa.

"Shikenan, zan tafi. Ki gaida su Mama."

Daga nan ya juya ya shige motarsa, iska da sanyin safiyar na busata, ba ta fasa kallonsa ba har ya shiga motar. Gilashin ya sauke yana kallonta, sakanni biyu zuwa uku kafin ta farga, ta juya da sauri ta faɗa gida. Ya ja motar kamar wanda kwai ya fashewa a ciki.

Allah Ya taimaka Hajiya ba ta falo, da sauri ta shige dakinta ta rufe, a bakin ƙofar ta zame ta cure wuri guda, kuka ko dariya za ta yi? Ba ta sani ba, ba ta da tabbacin abinda kwakwalwarta ke kokarin hasasowa sai dai ta jera Hussein a sahun mutanen da suka san ƙima da darajar *ƊAN ADAM*. Ta sauke ajiyar numfashi tare da neman tsari daga Ubangijinta akan sharrin zuciya da saƙe-saƙenta.

***
  "Daga ina kake?" Ta yi tambayar ba tare da ta bari ya ƙarasa fitowa daga cikin motar ba, ya kalleta kallon tsaf. Gabansa na faɗuwa sai dai akwai wani ƙwarin gwuiwa da yake ji na iya kallon cikin idanun Hajiyar da ɗan ƙaramin kuzari.

"Bai kamata ki fito haka ba."

Ya fadi a sanyaye ganin daga ita sai doguwar rigar bacci, damtsen hannun duk a waje ga tumbi da ya ɗaga rigar. Hajiya Zeenat idanunta a kaɗe, ji take kamar ta shaƙe wuyan Hussein saboda wani irin kishi da ya mamayeta. Tasan ƙarya ne a kowane yanayi mace ta ga Hussein ba ta ƙyasa ba, ta kuma sani ba zai taɓa zuwa wajen kowace mace ba musamman da safiyar fari. Amma tana son tabbatar da inda ya je don ta samarwa zuciyarta hujjar da za ta nutsu sosai.

Gaba ya yi zuwa cikin gidan, ta mara mishi baya. Yana niyyar taka matattakala ta riƙe hannunsa. Ya runtse ido da sauke ajiyar zuciya alamar gajiya, bai bari ta ƙara tambaya ba ya tari numfashinta.

"Wasu takardu na kaiwa Hisham. Shikenan?"

Ta bishi da kallo tana mai sakin hannun, ya haye sama. Ƙarya abu ne mafi muni cikin munanan ɗabi'u, ya shiga istigfari a ƙasan zuciyarsa. A ɓangaren Hajiya Zeenat, tasan waye Hussein, ƙarya ba ta daga cikin shirginsa, don haka sai ta gasƙata amma ta soma jin tsanar Hisham a ƙoƙon ranta. Yana neman shigemata hanci da ƙudundune. Ta yi ƙwafa kawai ta bishi saman.

Kwanciya ya yi ya rufe har kansa da bargo saboda bai shirya amsa wasu tambayoyin daga Hajiya Zeenat ba bayan wancan. Murmushi ya tsinci kansa da yi, murmushi sosai, Ramlat da firgicin dake kwance samam fuskarta shi ya ƙayatar da shi a yanzun.

***
"Jimin ja'irar yarinya! To ba kya sonsa wa kika kawomana za ki aura? Ko an faɗamaki akwai wani cikin iyayennaki da za ki je wa da wannan magana su ɗauka?"

Dada ke wadannan kalaman sadda Ramlat ta kai mata ziyara da kuma roƙonta akan a janye batun Chairman. Jin abinda ta ce Ramlat ta ɓata fuska.

"Da ace kinsan waye shi da ke za ki zama farkon wacce za ta ce aa."

Ta zayyanemata kaf labarin Chairman, tun Dada na faɗin toh meye a ciki? Har ta yi shiru tana gyaɗa kai. Ramlat na kaiwa aya ta dubeta.

"Toh yanzu ya dace ace kun bayar da jininku ga wannan mutumin? A ma ɗauke duk wannan, bana sonsa. Ba shi da kyawawan ɗabi'un da zan kaunaceshi dominsa. Bana son na maimaita gidan jiya, abin nufi, ina gudun na saɓa umarninku a karo na biyu naga ba daidai ba."

Murmushi Dada ta yi ba tare da ta furzar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login