Showing 108001 words to 111000 words out of 226732 words

Chapter 37 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12448

ta kuma daina yi mishi kallon banza. Idan har hakan ta faru shi zai san yanda zai yi ya shawo kanta.

Da wannan ƙudurin ya ji wani sauki daga abinda ke cinsa duk akan Ramlat.

***
  Ruwa ake tamkar da bakin ƙwarya, tana tsaye gefen titin da babu yawaitar ababen hawa sai tsilli-tsilli, kamar ta yi kuka haka take ji don tsabar baƙin ciki. Ace motarka ba ta tashi ɓaci ba sai a wannan lokacin? Ta dauki duk abinda yake da muhimmanci ta fito bayan tsagaitawar ruwan hannunta rike da lema. Sai da ta buɗeshi kafin ta rufa jikinta. Ta dauki jakarta ta rufe dukkan gilasai da kuma motar. Nan kuma ɗan sahu ya yi mata wuyar samu. Tsaki ta ja ya fi a ƙirga, ranar Asabar din ƙarshe wata ne, daga gidan Rafee'ah ta ke nan kan titin Rijiyar Zaki. Ba don ta riga ta yi mata sallama ba ta fito, kuma daga titi zuwa lungun gida Rafee'ah akwai tazara sosai, da babu abinda zai hanata juyawa ta koma.

  Daidai sadda wata baƙar Ford ta wuce ta a guje, a hankali kuma mai motar ya yo baya har zuwa gabanta. Ta kalli motar ta kauda kai, za ta yi gaba ne ya sauke gilas.

"Assalamu alaiki."

Juyowa ta yi ta dubeshi, sanye cikin baƙar rigar sanyi marar nauyi, hular rigar mai igiya biyu kwance a baya wuyansa, duka duka tsawon hannun rigar iyakar damtsensa ne wannan ne ya bada damar bayyanar murɗaɗɗun hannuwansa masu zubin ƙarfin, tsintsiyar hannunsa daure da agogon fata baƙi sai zobunan azurfarsa da ba ya rabo da su.

Ta tsinci kanta da maida mishi martanin murmushin tana mai amsa sallamar. Ba ta taɓa tsammanin ganinsa a wannan lokacin ba.

"Motar ce ta samu matsala?"

Maimakon ta yi magana sai ta ji kamar an ɗaure bakinta, hakan ya sa ta gyaɗa kai. Ya ɗan dubi sararin samaniya har ruwa na ɗigarmasa a saman karan hanci.

"Gashinan kuma ina tsoron ruwa balle na fara gwada aikin kanikanci a kan motarki. Shigo na kai ki."

Turus ta yi, kamar ta ce a'a, maganganun da suka yi da Amrah ya faɗomata a rai, ta zagaya ta shiga sannan ta zuge lemarta, za ta ajiye a ƙasa wurin kafarta ya karɓa ya cilla baya. Ta rufe ƙofar ta dubeshi.

"Nagode."

Ya ja motar yana murmushi.

"Rike godiyarki ki fatan Allah Ya kaimu lafiya tukunna."

Murmushin itama ta yi.

'Matsoraci mijin hajiya.'

Duk a zatonta a zuciya ta fadi, sai ji ta yi ya yi wata dariya kafin ya ce.

"Hajiyar da na yi wuff da ita ko?"

Da sauri ta dubeshi duk sai ta ji kunya ya kamata ta hau kame-kame.

"Lah ni wallahi ban ce ba. Me ma nace?  Me wai ka ji na fada? Don Allah I'm sorry."

Ya kannemata ido ɗaya yana murmushi kafin ya maida idanunsa saman titi.

"Alright, naji ba ki ce komai ba. Ni dama ban ce kin fadi ba duk kika wani tsargu kanki. Kin dai kirani da Your Heart ko?"

Wannan karon ji ta yi inama yana da halin buɗe motar ta yi ficewarta.







 

 I just published "BABI NA TALATIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ULR1OMRi4ab



🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

35)

"Shiru?"

Ta maida kai ga kallon gilas duk ta rude.

"Ramlat."

Ya Rabb, tamkar wani balarabe haka ta ji sunan ya fito raɗau a bakinsa. Ba ta san sadda ta juyo ta kalleshi ba. Hankalinsa na kan tuƙi, hanyar da ya ɗauka bai mata kama da inda ta nufa ba, asalima miƙa wa cikin rijiyar zaki kawai ya ke.

"Ina zamu je?"

Ta fadi murya na rawa. Murmushi ya ɗan yi.

"Siyar da ke zan yi, ko ba komai hankalin Madam zai kwanta."

Abin sai ya bata dariya, ta yi murmushi mai sauti gami da lumshe ido ta budesu.

"Nikam ba zan siyu ba."

"Really?" Ya furta  gami da ɗan ɗaga gira yana jifanta da wani irin kallo. Cikin dakiya ta amsa.

"Kwarai ma kuwa, idan ka siyar da ni ba wanda zai kyaleka."

Ya yi ƴar dariya.

"Kuma sai ya kasance ba wanda ya ga shigowarki motata."

"Amma ba ka daga cikin marasa imani, ba ka yi kama da ɗaya ba. Ina kyautata maka zato."

Bai ce komai ba banda murmushi irin wanda har fararen haƙoransa suka bayyana. Hannu ya kai ya kunna music, waƙa ce ta yabon Annabi s.a.w da harshen larabci  na Maher Zain mai taken Ya Nabi Salam Alayka. Shiru ta yi duk da ba jin larabcin ta ke ba amma yabon yana ratsata sosai, muryar Hussein mai bin waƙar ya fiye mata muryar mawaƙin daɗi. Ta  kara yin laƙwas gami da bada dukkan nutsuwarta. Daidai wurin wani tukuba wacce a gefenta kujeru ne wuri-wuri cikin wata ƴar rumfa, ya nemi wuri ya tsaya.

Ta kalli wajen tana mamakin yanda ruwa bai sa babu cunkoso a wajen ba, kamar ta ce mishi sai ya bi uban layinnan zasu tafi sai kawai ta fasa ta yi shiru.

"Ban mintuna kaɗan." Bai jira amsawarta ba ya ɓalle seat belt ya fita. Sai a sannan ne ta lura da cewa three-quarter ce jikinsa, kunya ta sa ta kauda kai daga kallonsa.

Fitarsa ba jimawa wayarsa ta shiga ringing.

"Zeenat." Sunan da ta gani kenan saman kafcecan screen din da babu tsaga ko ɗis, gabanta ya faɗi. Har ta kammala ringing ba ta yi karambanin ɗagawa ba, kafin dai ya dawo ta yi ƙara fiye da sau uku. Anan ta ƙara gane naci da rashin hakuri irin na Hajiya Zeenat. Ta tsinci zuciyarta da daukar zafi, har hura hanci take don takaicinta, ita kanta ba ta da dalilin jin hakan.

Yana zuwa ya ajiye ledojin a baya hadi da kallonta.

"Sorry, na bar ki kina jira."

Duk sonta da ta saki fuska ta kasa.

"Bakomai."

Hannu ya kai ya dauki wayar, nan da nan ya ɗan sauya.

"Ɗan yi shiru please." Kallonsa kawai ta yi ganin yanda ya nutsu, waya yake latsawa kafin ya ɗaga. Anan ta ji yana ban hakuri kafin daga bisani ya ce yana hanyar dawowa. Taɓe baki  ta yi ta kauda kai gefe, tasan da za'a ce tsoro yake zai ce ba haka ba. Can kuma ya ajiye wayar ya tashi motar suka tafi.

  Jin wannan karon bakinsa ya mutu ne yasa ta kalleshi. Fuskarsa kamar a sake kamar kuma ransa a ɓace, ta kauda kai cike da jin babu dadi don haka ta ja shi da hira.

"Yaranka nawa?"

Murmushi ya yi ya ɗan dubeta.

"Kina son yara ne?"

Ta maida dubanta ga titi tana murmushin itama.

"Yara ai abin so ne. Wa zai ƙi su?"

"Naki ba su isheki ba?"

Ta ɗan yi shiru tana tunanin wa ya fadamasa tana da yara ne? Ko dai Hisham ne? Muryarsa ta katse tunaninta.

"I saw your WhatsApp profile."

Fadin hakan da ya yi shi ya tunasar da ita hoton yaranta ne akan dp dinta sannan a settings dinta kowa yana iya ganin dp idan har yayi saving lambarta.

"Hakan na nufin.."  Ta fadi da sauri tana kallonsa. Wani kallo ya jefamata da ta kauda ƙwayar idanunta.

"Wajen Hisham na karɓi lambar, ba don komai ba kuma, kar ki fassara please ki yi zaton sabon kamu kika yi."

Ta murmusa.

"Dama kai kam ai sai Hajiya."

Ya yi shiru kaɗan yana murmushi, har ta fidda rai zai yi magana can ta tsinkayeshi.

"Amma dai kin san ni mijin mace huɗu ne ko?"

Ta dara kadan.

"Um um, ban ga alamun hakan ba. Kai da aka kafamaka ƙahon zuƙa ana bi duk inda ka yi?"

Ya shiga jinjina kai gami da kaɗan yatsa jikin sitiyari.

"Ke ba'a kada ki a magana ko?"

Ya ba ta dariya.

"I'm sorry."

Ta furta kanta tsaye. Ya kai hannu ya dauki gilashinsa baƙi ya manna a idon, ta saci kallonsa, murmushi kawai ya ke dokawa da ya ƙara masa kyau. Wani ajiyar zuciya ta sauke. Ba ta ga baƙin Hajiya na kishin wannan haɗaɗɗen ba.

Har suka isa bai ƙara magana ba banda muryar Maher Zain da ya ƙaro  a waƙarsa ta Thank You Allah. Nutsuwa sosai ta yi har da kwantar da kai jikin kujera tana sauraron waƙar. Koda suka iso Sharada, shiru ta yi ta zuba ido tana so ta gani ko zai gane gidansu. Ta sha mamaki ganin ya shiga kan layin. Kamar wancan karon ta juyo ta dubeshi.

"Zan sauka anan."

"Don me? Kar saurayinki ya ganni?"

Ya furta yana tafiya a hankali a dalilin ruwan da ya cika wurin. A raunane ta ce.

"Ni wallahi ba wani saurayi, kawai dai.."

"Kar ace ni saurayinki ne?"

Ya fadi wannan karon idonsa a kanta, daga cikin gilashin yake ƙare mata kallo. Ganin kamar kallon na ƙurillah ne ya sanya shi kauda kai ya maida bisa hanya. Ita ta ma rasa ta cewa. Ganin ya tsaya daidai ƙofar gidansu ne ta fahimci rannan dai ya gane gidan da ta shiga. Dubansa ta yi, ya fidda gilashin ya dubeta.

"Shikenan?"

Tsuke baki ta yi kafin ta bude motar za ta fita ta ce.

"Nagode Allah Ya saka da alheri."

Murmushi ya yi ganin tana shirin rufo ƙofar.

"Ji mana."

Dakatawa ta yi gami da duban ƙyauren gidan a tsorace sannan ta sunkuyo kanta ta dubeshi kamar ta yi kuka.

"Mene ne?"

"Ban mukullin motarki. Zan sa a kawomaki."

Ta ciro ba musu ta miƙa masa har da godiya. Dama burinta su saba yanda za ta tunkareshi da batun ƴan uwansa. Tasan kuma tana bukatar jin ta bakin Hisham ko akwai abinda ya sani shima.

Hannu ya kai ya ɗauko lemarta da ƙullin leda ɗaya na nama ya miƙamata yana faɗin.

"Idan ba so kike mu dawo gidannan da Madam ba, riƙe ki tafi da su."

A tare suka yiwa juna dariya, ta karɓa ta mishi wani irin kallo kwatankwacin wanda ta yi don baƙanta ran Hajiya.

"Itama ta san ni din ba kanwar lasa ba ce yanzu."

Ya ɗaga gira.

"Really? Idan kin yarda za ki maimaitan kallonnan a gabanta, shigo mu tafi."

Wani irin kunya ya mamayeta, ta yi saurin ficewa ta rufemishi ƙofar, ya lumshe idanu ya bude yana kallonta, dab da za ta shige gidan ta juyo ta ɗaya mishi hannu tana murmushi, ga mamakinsa shima ɗagamata ya yi, ta juya ta shige ciki shi kuma ya ja ya tafi duk jikinsa a sanyaye.

Kamar yanda mamaki bai bar shi ba hakanan itama ta ke ta mamakin kanta. Abin mamaki har ta shiga falon Hajiya murmushin ta ke yi.

Ta tarbi yaranta har da ɗaga Affan ta juya da fadin

"Oyoyo Babyn Mami."

Suna ta dariya ta karasa ta zauna gami da fadin wash.

"Sannu, amma kin jima. Mun yi waya da Rafee'ah ta cemin kin bar gidanta da wuri. Ina kika tsaya?"

Ta ajiye mayafinta a gefe bayan ta ajiye ledar a saman tebur, lema kuwa Ummi ce ta karɓe ta nufi ɗaki da shi.

"Mota ce ta macemin a hanya wallahi."

"Ya Salam, to yanzu ya kika yi?"

Murmushi Ramlat ta yi, fuskar Hussein ke yawo a kwayar idanunta.

"Abokin Hisham ne ya ganni, shi ya kawoni har ƙofar gidannan."

"Mijin Hajiyarnan?" Yanda Hajiya ta fadi ido waje sai ya ba ta dariya.

"Shi."

"Ai shikenan ke kika sani, ki yi ta jajiɓo yaronnan idan ta zo har gidannan ta jibgeki ba abinda zan ce."

Dariya ta yi.

"Ta jibgeni fa Hajiya? A gabanku?"

"Atoh, ai naga alamar kamar alaƙar taku ƙara yin gaba ta ke."

Jiki a sanyaye ta girgiza kai.

"A'a fa Hajiya, ba komai tsakaninmu wallahi banda mutunci."

Hajiya ta murmusa.

"Allah Yasa toh."

Ramlat ta basar da zancen.

"Ga nama nan ma ya siyamin."

Daga nan ta mike ta nufi ciki don sauya kaya sai dai maganar Hajiya ta ɗan shigeta. Dagaske sabo ke neman shiga tsakaninta da Hussein. Kamar kuma irin sabonnan da ba shi ta nema ba, irin wanda ba shi suka shirya da Amrah ba.

Ta kai hannu ta fiddo wayarta daga jaka, kai tsaye ta shiga whatsapp kan dp dinta. Hoton yaranta ne, Affan da Ansar sanye da shadda iri daya, hular Affan har  goshi, Ansar kuwa ta zauna ɗas a kansa. Ummi daga bayansu ta dafa kafadunsu suna dariya kamar yanda mai hoton ya basu umarni. Murmushi ta yi ta shafi hoton tana tuna kalaman Hussein. Wato dai ya san tana da yara kuma ba ta da aure? Da alama a wurin Hisham ya nemi ƙarin bayani.

  'Har zuciyarki ta soma saƙa wani abu akan wani ɗa namijin?'

Wani bangare na zuciyarta ya ankarar da ita, ta yi saurin kashe wayar ta ajiye gefe, rage kayan jikinta ta yi ta faɗa wanka. A ganinta wannan kuskure ne babba. Don haka dole ta yi takatsatsan, kyakkyawan jihadin da ta yi niyya kawai za ta aiwatar akan wadannan ƴan biyun. Daga nan babu komai!

***
  Washegari safiyar Lahadi da misalin ƙarfe takwas na yamma, Malam Bala ya yi sallama a kofar falon. Ita kadai ce a falon tana taimakawa Ladidi da tsintar shinkafa, yara na ɗaki wurin Hajiya,ta amsa ta leka suka gaisa. Muƙulli ya miƙomata.

"Gashinan wani ne ya kawo ya ce a ba ki inji Yallaɓai, ga motarnan an shigo da ita ma."

  Ta karbi mukullin.

"Ya tafi?"

Malam Bala ya amsa da eh. Ta mishi godiya sannan ta dawo ciki ta ajiye mukullin. Wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta dauka ta duba.

"Mota duk ta yi datti ba wanki, gashinan, za ki biya kudin wankinta."

Abinda aka rubuta kenan, wannan ya ba ta tabbacin har wankemata ya sa aka yi. Dariya ta yi kafin ta maida mishi martani bayan ta ƙare wa lambar kallo.

"Nagode Yallaɓai, Allah Ya bar zumunci."

Ta aikamasa kenan ta ga akwai saƙon da ya shigo ba ta ko lura ba. Hilal ne. Kirjinta ya fadi, idan ba ta mance ba yau an zarta sati da maganarsu, damuwa ta sauka saman fuskarta a yayinda ta karanta saƙonsa.

  "Ban sani ba ko hidima ce ta miki yawa kamar yanda ta sha kaina har ban samu zuwa akan lokacin da muka tsayar ba. Ina fatan komai lafiya? A sanyamin ranar da zan zo idan ba damuwa."

Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta rasa ma amsar da za ta ba shi. Ita ta sani, babu soyayyar bawan Allahn nan (Hilal) a ranta face tausayi da kuma ganin daraja da ƙimarsa. Ta yi addu'ar istihara sosai amma ba ta jinsa ko kaɗan. Ta rasa amsar bayarwa don haka ta ajiye wayar kawai ta ci gaba da aikinta.

   Ita da kanta ta yi musu girki, shinkafa da miya. Tana kammalawa ta fito falon inda suke zaune ya yi daidai da shigowar Munir gidan dauke da yaransa. Daga ganin yanayin fuskarsa da irin daurewar da ya yi ka san cewa akwai matsala. Ya zauna yana gaida Hajiya a daure, ta amsa gami da jefamasa tambayar dake zuciyar Ramlat.

"Lafiya kuwa? Meyafaru na ganka da su Yasmeen?"

Ya shafi kai yana amsa gaisuwar Ramlat kamar ba ya so. Ya ba Yasmeen umarnin su shige ciki da su Ummi. Yasmeen ta ja  ƙannenta uku suka ɗunguma gaba daya zuwa ciki. Da yake yarinya ce mai wayo, gaba daya itama fuskarta ta koma kalar tausayi.

"Wata ƴar hatsaniya aka yi da Bilkisu da Hunainah akan kawai yarannan su na shiga bangaren Hunainah. Ita yarinyar tana sonsu tana kuma jansu a jiki, toh ashe ita Bilkisu ranta na baci. Dama ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba ta ke nuna ba ta kaunar zuwan yaranta wurin Hunainah. Yau da na gaji don Yasmeen ta kwana sashin Hunainah shi ne ta kama yarinyar ta buga, ni kuma na yanke hukuncin zamansu a wurin Hunainah tunda abin haka ne, toh wai shi ne Bilkisu ta dauko wuka har da kai wa Hunainah yanka a kafaɗa ta yankamata hannun riga, wai ita ta rantse idan har na rabata da su za ta kashe Hunainah. Wannan ne dalilin da yasa ni kuma na korata gidansu na kwashi yaran na ce bari na kawosu nan idan ya so zuwa anjima sai na tafi da su. Haba! Wannan masifar ta ishe ni, Hajiya kusan kullum sai Bilkisu ta ɓullo da sabon rikici. Daga wancan sai wannan! Nikam gaskiya ta soma isata don zan iya sauwaƙe..."

"Kar ka fara! Nace kar ka fara! Idan ka yi ba da yawuna ba wallahi. Wane shashashan namiji ne zai saki matarsa ta farko kuma Uwar ƴaƴa? A'a kar na kara jin batun rabuwarnan a bakinka. Yanzu kai dama anan ba sai da na gujemaka irin hakan ba? Ban maka magana game da haɗa matannan gida ɗaya ba? Ka nunamin kai namiji ne da mace ba ta isa tankwarawa ba. Ai zaman lafiyar ake nemamaka. Toh ga irinta nan, tun ba'a je ko'ina ba ta soma yunkurin kashe baiwar Allah."

"Hajiya ɗan rigima fa ɗan rigima ne, koda ba gida ɗaya suke ba, sanin da na yiwa Bilkisu za ta iya takawa har gidanta. Toh Hajiya a hakan ma fa zargina take da rashin adalci ina kuma ace gidansu ba daya ba?"

  Ramlat dai ta yi shiru tana kallonsa yanda duk ya fice a hayyacinsa.
 
   Yanda aka banko labulen falon aka shigo yasa duk suka kalli kofar. Bilkisu ce buguzuzum da ita. Kalar mayafin daban da atamfar da ke jikinta. Da ganinta ka san ba'a nutse ta ke ba.

Kai tsaye wurin Munir ta tunkaro hannunta a ƙugu.

  "Ka bani yarana tunda ba kai ka haifamin ba!"

Idanunta jage-jage da ruwan  hawaye. A fusace ya mike Hajiya ta yi saurin riƙe hannunsa.

"Kai bana son hauka. Yi shiru abinki Bilki, zauna don Allah ki nutsu. Yaranki suna nan, kuma zan ba ki kayanki ki tafi da su."

Wani kwafa ta yi ta zauna tana kuka har da share majina. Ramlat ta mike ta yi ɗaki don ita takaicinsu ma ta ke ji. Mace ta riga da ta raina mijinta ko kadan ma ba ta ganin girmansa.

"Allah Ya kyauta." Ta faɗi a fili.

Kayan islamiyya ta fiddowa yaranta ta ba kowanne nashi kafin ta shiga shirya Affan. Har ta kammala ta fito ta zubamusu ruwa a robobi ta basu Hajiya na ta shari'a tsakanin miji da matar. Idanunta ya kai ga Bilkisu, wata uwar harara ta watsamata, ita abin ma sai ya ba ta dariya ganin ai ba ita ta kai zoman ba, ratayar ma ba'a ba ta ba. Hijab ta sanya don ta fi kaunar ta bar musu gidan wannan yasa ta dauki wayarta ta yiwa Hajiya sallama da zummar za ta kai su Ummi makaranta daga haka ta fice don hankalin Hajiyar ma ba ya gareta kawai ta amsa da jeki.

***

  Koda ta miƙa yaran ta wuce gidan Umman Amrah. Ta saki baki ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login