Showing 45001 words to 48000 words out of 226732 words

Chapter 16 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12433

ciki, haka ta shiga taka barandar asibitin. Idan yaro zai yi mata kallo ɗaya, nan take zai ayyana a ransa cewa mahaukaciya ce. Ga duk mai hankali kuwa zai ga tsantsar tashin hankali da damuwa cike fal shimfide a saman fuskarta.

"Mutuwa akai mata da alama."
Ta tsinci muryar wasu mata a gefe, ba ta kallesu ba balle ta tofa. Ba kowa ta ke ganewa ba,ba kuma kowa take gani ba. Abbanta kawai take son sanyawa a idanu. Da shi ta kwana kuma ta tashi.

Hijabin jikinta duk ya cukurkuɗe ya yi jirwaye na ruwan hawayen da ta dinga gogewa da shi. Silifas ne a kafarta na baƙin gidansu, ba ta san inda nata yake ba. Ta dai tuna da shi Hajja ta yi amfani wurin dukanta. Fuskarta yatsun Amrah ne kwance a samansu wadanda har yanzu basu baje ba.  Tana fashin sallah, wannan yasa ba ta kalli gabas ba balle fuskar ta ci darajar wanki. Ta dai tsarkake inda ya zamemata dole saboda kyankyami irin nata, ko ba komai kula da lafiyar jikinta ne. Ta shanye komai a awannin da suka biyo baya. Zagi, tsinuwa da ma duka, duk ta dauka daga dukkan wadanda acewarta sun kai su yi mata su. Ta ji ta dau komai idan har za'a bar ta ta ji da abinda ke cin ranta.

Har ta iso dakin da Abba ke kwance tana tunani mai zurfi, ta gane dakin a dalilin hango Mijin Rafee'ah, Isma'il da ta yi zaune a saman kujera, gefensa Yaya Munir ne su na magana.

Yaya Munir na kallonta tana kallonsa.

_"Ban yarda ɗayanku ya taɓa lafiyarta ba, kar wanda ya tuhumeta akan abinda ta yi, ni da kaina zan auramata wanda take so. Na dauki laifina na yi mata auren dole kamar yanda ta ce."_

Ya tuna kalaman Abbannasu a jiya ga Hajiya, Zulaihat da kuma shi Yaya Munir din. Sai dai ya yiwa kansa alkawarin babu shi babu Ramlat. Don haka ya kauda kai kamar bai ganta ba. Isma'il ne ya tsayar da ita suka gaisa yana mata fadan ba ta kyauta ba, tsam Yaya Munir ya mike.

"Muje ga Rafee'ah ko?" Ya katse Isma'il. Hakan yasa shima ya mike suka tafi. Ta bisu da kallo idanun taf da kwalla sannan ta murda kofa ta shiga dakin Abban da sallama.

Babu kowa a ciki sai Abban dake kwance ya yi shiru idanunsa biyu. Ya juyo ya dubeta, ga mamakinta murmushi ya yi mata. Ta sunkuyar da kai ta ji saukar hawayen da take riƙewa a saman kuncinta. Hannu ya miko.

"Zo nan Ramlatu."

Tana tafiya kamar a iska tsabar ramar da ta yi ta zauna saman kujerar gefensa ta rike hannun sai kuka.

"Abba don Allah ka yafemin. Abba na tsani kaina, na kasa rankwafar da zuciyata na yi maku biyayya. Abba ka yafemin na tuba. Na shirya zama da Hilal kamar yanda ku ke so. Ku ce ya maidani. Wallahi zan zauna."

Murmushi Abba ya yi, ya shiga girgiza kai.

"Kin ji nace ba zan ba ki Aliyu ba? Ko wani ne ya ce hakan? Ki yi shiru ki daina kuka, ni na yi laifi da na dage wurin yi miki aure da wanda bakya so. Ki yi hakuri ki yafemin kinji? Zan aura maki Aliyu cikin satinnan in sha Allahu. Yau zan koma gida ba zan ƙara kwana a asibitin nan ba. Idan har Khalid na raye, sai kin auri zaɓinki. Ki daina kukan. Na yafemaki duniya da lahira. Allah Ya yi maki albarka."

Ya ƙarashe da rarrashi, ta kasa gane zantukan Abban suka dosa. Ta kasa gane dagaske yake maganar ko kuwa mai harshen damo ne? Don haka ta bi umarninsa ta share hawayen. Ya dinga jan ta da hira har ta yi dariya. Hankalinta ya ɗan kwanta. Amman maganar Abban ta shiga yawo a kwanyarta cike da rashin gamsuwa. Maimakon ma ta yi murna, sai ta shiga firgici da kuma faduwar gaba.

Daga nan ta karasa dakin Rafee'ah, ba ta shiga ba, ta hango baby mai kyau dai, ta yi murmushi sannan ta koma ga Abban.

***
Kwana biyu da sallamar Abba, ya sallami dukkan baƙi ƴan Daura, ya basu hakuri akan abinda Ramlatu ta yi. Daga nan ya tara iyalinsa ya tsawatar akan bai yarda ko maganar banza wani ya yiwa Ramlat ba.

Abba da mahaifin Amrah, da ma wasu a ƴan uwa, suka dunguma har gidan su Hilal. Suka ba iyalinsa hakuri cike da nadamar abinda Ramlatun ta aikata don tuni sun ji abinda ta yi har ya saketa. Bai ɓoye wannan ba. Wannan ya ɗan sassauta ran iyayen Hilal, ko ba komai iyayen Ramlat sun nuna ba hannunsu. Basu nemi sulhun kome ba, koda sun nema iyayen Hilal sun yanke wannan alaƙar. Hatta Alhaji Aminu mahaifin Hilal wannan karon ya yi Allah wadai da irin Ramlatu. Toh Abban ma bai da ra'ayin komawarta.

Washegari kuwa kamar yanda suka nemi iyayen Aliyu, sai gasunan sun zo. Ba ɓata lokaci Abba ya karbi sadakin ƴarsa. Nan aka daura auren Aliyu da Ramlat don duk wani bincike an yi ta hanyar Yaya Munir an kuma tabbatar daga Hilal har ita Ramlatun babu idda a kanta.

"Ga sadakin aurenki Ramlatu, na auramaki Aliyu. Ina fatan wannan zai faranta ranki. Zai sa ki dawo da walwalarki. Ki kuma maido soyayyarmu a zuciyarki?"

Ta ɗago ta dubi Abba tana hawaye. Abban murmushi yake har hakoransa tana hangowa. Ita ya kamata ta yi irin wannan kalar fara'ar, sai ya kasance ita ce mai kuka, Abban da mutan gidan na dariya.

Hajiya ma sosai ta sakarmata fuska.

"Ramlatu matar Aliyu. Allah Ya baku zaman lafiya."

Wannan ne kalaman Hajiyar kafin ta fita zuwa asibiti wurin Rafee'ah duba lafiyarta.

Ramlat ta shiga daki ta zauna, ta yiwa kudin da Abba ya damƙamata kuri da idanu, abin mamaki su dinma jiƙasu ta soma da hawayenta. Ranar da ya kyautu ta yi rawa da juyi, ranar da ya kyautu ta fi kowa farin ciki. Abin mamaki kuma ya sanyata, kukan ta shiga yi kuwa iyakar ƙarfinta, koda za'a shaƙeta ba za ta ce ga dalili ba.


Ba ta da masaniyar cewa Mafarin kenan!!!

***






🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

_Littafin Ƙarfen ƙafa dungurugum sadaukarwa ce gareki yar uwa kuma mai bani kyawawan shawarwari a dukkan tafiyata. Barr Firdausi Kabir. 🤩🤩🤩👏🏿Allah Ya bar zumunci. Baki ba zai iya misalta godiyata gareki ba. Allah Ya bar kauna fisabilillah. Ameeen. 💞💞Madallah da yar uwa kuma ƙawa ta gari._🤲🏿💃🏿💃🏿


16)


Juyi kawai take amman baccin ya ƙi zuwa. Tunanin Aliyu na shan sigari ya fi komai dagula lissafinta. Kishin yabon Muhibbat da ya yi a gabanta ya fi komai ci mata tuwo a kwarya. Ga kewarsa da take ji, tun zuwanta gidan basu taɓa raba makwanci ba. Wannan na daga dalilan da ta kasa bacci ba tare da shi a kusa ba.

Kamar yanda ba ta yi bacci ba, haka shima. Karfe kusan ukun dare ta fito falon da zummar daukar ruwa. Ji ta yi an rungumeta ta baya, za ta yi ihu ya rufe bakin.

"Baby ni ne fa." Sauke ajiyar zuciya ta yi, sai kuma ta shiga kokarin tureshi.

"Ka rabu da ni."

Ba ta yi aune ba ta ji ya ɗauketa cak zuwa dakinsa, duk yanda ta so ta kwace abin ya ci tura, sai da ya ajiyeta saman gado kafin ya yi saurin ƙarasawa ya datse kofar yana nishi.

"Baby kin soma nauyi wallahi. Wai! Kin ji hannuna?"

Ta kara murtuƙe fuska sai hawaye.

"Ni ka budemin na fita, ƙishin ruwa nake ji."

Ruwan ya miƙomata na roba, ta karɓa ta sha. Zama ya yi gefenta gami da narkar da murya. Gaba daya ya koma kalar tausayi.

"Baby na tuba. Ba zan ƙara ba. Zan yi kokari na daina idan hakan zai sa ki farin ciki."

Ta ɗan soma jin sanyi, ya sa hannu ya shiga sharemata ruwan hawayen. Yana kara kashe jikinta da kalamai masu dadi, duk inda ta ɓullo sai ya toshe. Har dai ya ci nasarar shawo kanta.

***
  "Kai Zakina, kana da hankali kuwa? Duka-duka yaushe Alƙali ya ba ka gudunmuwar biki? Yanzu don rashin ta ido ka ke so ya karamaka jari? Kar fa ka manta ba haifarka ya yi ba."

Kalaman Abulle sun matukar ɓatamasa rai.

"Eh ki gorantamin! Dama kema nasan ba sona kike ba, kowa ma a gidannan ya tsaneni ya tsani ci gabana. Toh ai shikenan, duk abinda zai faru ya faru. Idan aka soma bi da ni ofishin ƴan sanda kwa fidda kudi wurin belina."

Yana kaiwa nan ya sa kai zai fita, Abulle tuni ta yunkura ta rike gefen rigarsa.

"Haba Zakina, Gadanga ƙusar yaƙi. Me ya yi zafi shi ba wuta ba da za ka dinga batun ƴan sanda, da yardar Allah ba za ka taɓa tozarta haka ba har abada. Jari ko? Ka kwantar da hankalinka ai ni na haifi Alƙali ba shi ya haifeni ba, don haka dolensa ya yi yanda nake so. Sha kuruminka anyi an gama. Haba ɗan marayana? Yi dariyar mana."

Yanda ta yi din sai ya sanya shi murmusawa.

"Yauwa ko kefa Kakus, ke fa kika haifesu, ba wanda ya isa ya ketare umarninki. Idan ma sun gwada ki yi musu kuka da barazanar tsinuwa ki ga idan za su ƙi."

Ya ƙarashe murya ƙasa-ƙasa, bai damu da duk ma abinda za ta ce ko ta aikata ba, shi dai ya tsira a wajen Alhaji Yusha'u, ya biyashi kudadensa ya kuma farfaɗo da kayan shagonsa.

"A'a, bai kai ga nan ba. Ai idan an tafi ga hakan ban ma isa ba, shi a wa? Kai dai ka kwantar da hankalinka kawai. Da kaina zan kiraka na damƙa maka."

Sai sannan ya saki dariyar farin ciki, wannan ya kwantar da hankalin Abulle. Kauna da tausayin Aliyu na kara ratsa ta. Kusan dagaske babu mai sonsa a gidan, ta kuma sani halinsa aka tsana, toh hannunka kuma ai ba zai ruɓe ka yanke ka yarr ba.

"Yanzu ka sa ranka a inuwa dai. Wannan bushewar taka ne ban san ta menene ba Zakina. Kodai kishiyartawa ce ba ta kiwatamin Kai yanda ya dace?"

Ya sanya harshe ya lashi busassun leɓ ɓansa yana murmushi.

"Babyna tana kiwata fiye da zatonki. Har ta fi diyarku kula da ni."

Taɓe baki Abulle ta yi.

"Mu gani a ƙasa, wai an ce da kare ana biki a gidansu. To Allah na tuba ko sadda kake auren Muhibbat ka fi haka kyau da sheki."

Miƙewa ya yi gami da jan tsaki.

"Kinga Kakus na tafi, ba zai yiwu na tsaya sauraronki kina zagarmin mata ba. Sai anjima."

Bai bari ta kara tankawa ba  ya yi wuf ya fice a ɗakin ya bar ta ta dogon salati.

  Shi kansa ya sani yanzun sigari da kayan maye na kara hudashi yana shiga cikin jikinsa. Ƴan dabarun da yake yi ma a baya don kar gano komai zuwa lokacin ya gani ya daina. Shikenan kuma ba zai huta da rayuwarsa ba? Zai ɓata lokaci da tsoron mutan duniya. A'a. Ya gaji. Ba ruwan Ramlat a ciki, shaye-shayensa ne.
  Ya ayyana hakan a ransa.


***
"Saboda bishiyar kudi ce da ni?" Ya furta ransa na wani zafi, zafin ba na komai bane sai irin yadda Mahaifiyartasu ke biyewa son ran Aliyun kamar shi kadai ne jikanta.

"Kai AbdulRazaƙi, ni kake faɗawa haka? Na shiga uku ni Abulle, dama akwai ranar da zan yi magana ka nunamin iyakata? Oh duniya ina za ki da mu? Allah Ya jiƙan Malam, Allah Ya kawo nawa ajalin na mutu ku huta."

Justice ransa ƙara ɓaci, ya yi maimakon ya lallaɓata kamar yanda suke yi idan ta soma irin wadannan zantukan, sai ya hau faɗa, ta inda yake shiga ba ta nan ya ke fita ba.

"Nan kika ɗaurewa yaronnan gindi ya je ya haɗa lefen burga, ba yanda ba muyi don a tsawatar ba kika hau yi mana barazana da tsinuwa muka kama bakunanmu. Shi yaron bai an muna da details na dukkan abinda yake shukawa ba a gari? Ko an fadamasa don mun ba shi jari ba ma sanya idanu? Sai ki yi ta zama kina biyewa yaro yana ƙara lalacewa? Sisina ba zai ƙara shiga hannun Aliyu ba da sunan wai jari."

Yanda ya dage yana surfa ruwan faɗa sai Abulle ta yi lakwas ta kuma kasa kataɓus. Ko irin rikon da Aliyu ya yi ga ƴarsa bai sa ya ɗauki zafi irin na yau ba. Duk cikin yarannata ta fi su sanya da  kuma yanke hukunci cikin sanyin zuciya ba da hargagi ba, ta san Alƙali magana daya yake, idan kuwa ya yi to fa shikenan ta zauna. Yana da wahala ya yi ja in ka da ita, yau kam ko daga yanayin fuskarsa za ka fuskanci ransa dagaske a ɓacen yake don har wani ja-ja yake yi.

"To ai shikenan, zan aika kauye wurin Shehu,(mijin mai tayata aiki Ladidi da ta damƙa mishi amanar kiwo) ko bijimina ne sai a siyar na ba shi. Amma ka yi hakuri ka tambayeshi wanda ke binsa bashi ka biyamishi. Ka yimin wannan alfarmar domin Allah da Annabi s.a.w. Yaronnan maraya ne, babansa bai da karfi. Ni ce komai nashi, hannunka ai ba zai ruɓe ka yanke ka yar ba."

Ta yi maganar cikin karaya har da sharar kwalla, yasan har yanzu dai ana jika. Abulle ba za ta taɓa bari Aliyu ya san zafin nema ba da kansa, kowane gata burinta ta yi mishi. Ganin hawayenta ya sa shi saurin magana.

"Shikenan, bashi ko? Zan biyamishi, zan tura da kaina wurin Alhaji Yusha'un da ya ce yana binsa. Na san mutumin a yanzu shi ne shugaban ƴan kasuwar kwarin, da kaina zan biya. Wannan ya miki?"

Sai ta hau dariya da sanya albarka. Haka ya fita yana kara jinjina kaunar jika da kaka dake tsakanin bayin Allahn.

***
*Bayan Watanni Biyu*

Allah Madaukakin Sarki Mai sauya dukkan lamura, Shi ke da ikon mayar da talaka Sarki, ya kuma maida Sarki talaka. Kamar haka, Ya kawo sauyuka masu dama a rayuwar auren masoyan.



***
Handout ne a hannunta tana haskawa da fitilar waya. Ta bararraje a kan gado daga ita sai karamin vest da gajeran wando. Mace ce mai gashin jiki, ga zufa. Duk da kasancewar ta bude winduna ta daga labulayen dakin, hakan bai hanata jin zafi ba, karatun ma ba shiga yake ba. Aliyu kuwa tunda ya sa ƙafa ya fita da maraice, har yanzun karfe takwas na dare ba shi da niyyar dawowa.

Ta miƙe tana jan tsaki ta hau rage kaya ta faɗa wanka. Wankanta na biyu kenan daga Magriba zuwa lokacin. Ta goge jiki, wannan karon bata bi ta kan undies ba, ta zura karamar rigar bacci mai jikin cotton, duka-duka tsawonsa iyaka guiwarta ne. Ta tufke gashinta wanda rabonsa da relaxer tun na aure. Hakan yasa ya kakkarye, kitso kawai take buƙata yanzun.

"Haka za'a rayu babu wuta? Nepa ma ba samu ake ba? Tab."

Ta furta a fili, za ta iya cewa tun tasowarta ba ta san matsalar wuta sosai ba a gidansu. Koda zasu rasa wuta, na ƴan kwanaki ne. Yanzun kuwa a gidan Aliyu ta haura wata bata ga kyallin wuta ba. Ƴan Nepa sun musu zagaye ya fi kirga akan su biya kudi sai dai Aliyu ya ce bai da halin biya, suka gaji suka yanke jonin direct din da suka yi.

Banda wannan ma lamura da dama sun sauya, idan ta ga Aliyu ya yi cefanen kaza toh fa wata ribar mai tsoka ya ci a kasuwa. Naman miya na neman kakare musu. Duk wata cima ta jin dadi ya ja baya. Ta miƙe a hankali ta fito zuwa falo ta na kallon farfajiyar gidan. Motar Aliyu na nan kamar yanda ta zata don a yanzu sai ya shafe kwanaki biyu na bai fita da mota ba sai mashin da ya siya, duk a dalilin jarinsa ya karye.

Jingina ta yi jikin window ta kurawa hasken farin wata idanu tana tunani. Tunanin gidansu take, tunanin yanda aka yi watsi da lamuranta. Abba ya hanata taka gidansa, duk sadda ta ce za ta je sai ya ce mata duka-duka yaushe ma aka yi auren. Karshe ya rantse idan ya ga kafarta a gidan yanzu zai saɓamata.

*"Kewarku nake Abba, kewa sosai, babu wanda ke zuwa gidana, daga dangin Aliyu har ku, ya kuke so nayi da rayuwata? Har yanzu ba ku bar fushi da ni ba?"*

*Tana jin sadda ya yi murmushi mai sauti.*

*"Kiyi hakuri Ramlatu, muna sonki ne, da ba ma sonki ba zamu tayaki son abinda kike so ba kinji ko? Ki shekara tukunna, ki shekara. In sha Allah a sannan ko ba ki fadamin ba, ki taki da iznin mijinki ki zo mu gaisa. Hakan ya miki?"*

*Ba haka ta so ba, sai dai kuma babu yanda ta iya, ta amsa da toh yayinda kwalla suka cikamata idanu. Ba za ta iya fadawa Abba cewa Aliyu na shan taba ba har a gidan kuma a gabanta, tasan dariya zai yi mata. Don haka suka yi sallama bayan ta bada saƙon ya gaida Hajiya domin ba ta daukar wayarta.*

Ramlat ta sauke ajiyar zuciya, ɗumin da ta ji a saman fuskarta ya tabbatarmata da zubar hawayenta, ta sa hannu ta share. A yau ta tsinci zuciyarta da kewar ƙawa kuma aminiyarta Amrah. Gashinan dai makarantarsu ɗaya, abinda suke karanta ma ɗaya, sai dai koda wasa Amrah ba ta taɓa bata fuskar da za su gaisa ba balle magana ta haɗasu. Ranar da ta taɓa kuskuren yi mata magana, nan take Amrah ta yi mata Allah Ya isa idan ta kara nunawa ta santa. Wannan ne ya bata haushi har ta kasa ɓoyewa ta sanar da Aliyu, sai da ta yi danasanin fadamasa da ta yi don zagin Amrah ya yi, irin ashar din da idan wani zai ce mata Aliyun ya iya, za ta musanta.

*"Babu ke babu ita! Babu ke ba ita! Kika kara ma kulata nima ban yafe ba!"*

Kalamansa sun mata tsauri, ta yi danasanin furtawar da ta yi, kusan ma ba ya ganin mutuncin kowa nata yanzu, daga ta soma batun kewar gida zai ce ai basu damu da ita ba.

Tunaninta ya katse

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login