Showing 57001 words to 60000 words out of 226732 words

Chapter 20 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12479

"Kaicona." Ta furta a fili, sai kuka. Kewa, kewar iyayenta take. Don haka ta juyo ya dubeshi.

"Bani wayarka."

"Ki yi me?"

"Abbana zan kira."

Ya daure fuska.

"Ki ce mishi kin sha abin maye cikinki ya zube? Asirinmu za ki tona? Dama ya lafiyar giwa ballantana an jefeshi da kashi? Toh ki je ki gwada tona asirin namu. Naki ne zai fi wari, ni dama ba ganina suke da gashi ba."

Daga haka ya mike ya sa kai ya fice a zuciye. Ta bishi da kallo, wani malolon abu ta ji ya tsayamata a maƙogwaro. Tana jin haushin irin kalaman da Aliyu ke yi akan iyayenta. Ko ba komai iyayenta kuma su suka haifeta. Dole ta takawa abin burki.

'Kin manta ke kika bada ƙofa.' Cewar wani bangare na zuciyarta, hakan sai ya karyarmata da gwuiwa. Ta yi shiru ta soma hawaye. Tana jin haushi da tsanar kanta akan duk abinda ya faru tsakaninta da yan uwanta, a gefe guda kuma don Aliyu ya zama kamar bugun numfashinta wanda ba ta jin za ta iya rayuwa babu shi. Sai dai kuma hakan ba zai hana ta janyo ƴan uwanta jiki ba, ta dinga ziyartarsu koda ba su zo mata ba. Ta kudurta sauya takunta tun kan abu ya yi nisa.

***
  Sai da ta yi kwanaki uku aka sallameta daga asibiti. Shi ne lokaci na farko da ta ga matan mahaifin Aliyu a gidanta da sunan dubiya. Ba su kadai ba, har su Abulle da Mamar Muhibbat sun zo. Kana ganin fuskokin za ka san dole akai musu.

"Ikon Allah, kema dai ina ce ba shi ya jawomaki ɓarewar cikin ba?"

Cewar matar Malam (mahaifin Aliyu) ta farko, Atine.

"Wane zancen banza ne haka ke Atine? Wa kike nufi da ɓarar da ciki? Au dama sharrin da za ku yiwa Zakina kenan?"

Fadin Abulle cikin masifa. Wannan yasa Atine fadin

"Allah Ya ba ki hakuri Baba."

Abulle ta yi kwafa. Ramlat dai tana zaune ta dukar da kai a saman kujera don Abulle ta hanata zama ƙasa.

   Sun jima a gidan don har sai da Abulle ta saka yanmatan jikokinta su yiwa Ramlat girki a risho. Haka suka shiga suna kunkuni. Har gobe ba sa kallonta da gashi, Muhibbat ce tasu. A karshe kowa ya watse aka bar ta ita daya ta yi ta godiya kuwa.

Komawa ciki ta yi ta ga yanda suka yi kaca-kaca da kicin din, ta kuma sani da biyu suka yi hakan. Haka ta daure ta kimtsa ko'ina. Tana jin sadda Abulle ke cewa Zalihat diyar Atine ta zauna ta kwana biyu yarinyar ta yi kememe uwarta na turata ta fice ta shige mota. Murmushi ta yi mai ciwo. Ta dauki waya cike da so da kewar iyayenta ta dannawa Hajiya kira. Ringing uku ta ɗaga da sallama.

"Hajiya." Ta fadi a raunane zuciyarta a karye.

Daga dayan bangaren Hajiya ta ji gabanta ya fadi, ta daure. Kwanakinnan da tunanin Ramlat take kwana da tashi. Tun sadda aka ce ta yi ɓari ta kira Zulaihat da Rafee'ah akan su shirya su je. Yanzu kam sun amince zasu je bisa umarninta.

"Ramlatu, ya gida? Ya jikinnaki?"

Wani sanyin dadi ya saukarmata a zuciya. Yau ne karon farko da Hajiyar ta kira sunanta ta kuma bata kulawar da ta dace.

"Jikina da sauki Hajiya. Hajiya yaushe za ki zo? Ki yafemin don Allah Hajiyata."

Kukan da take riƙewa ta shiga yi.

"Hajiya kin yi shiru. Hajiya ki yafemin."

"Na yafemaki Ramlatu, na yafemaki duniya da lahira. Ki kwantar da hankalinki. Ki bi mijinki, Allah Ya yi maki albarka. Gobe yayyanki zasu zo."

Rasa kalar farin cikin da za ta yi ma ta yi. Sai ga ta nan tana dariya. Suka yi sallama da Hajiyar ranta fari sol. Ta ɗago kai kenan ta hada ido da Aliyu. Yana jingina kansa cikin bangon falon yana zuƙar taba da fesarwa. Ganin ta kammala wayar ya tako ya zauna gefenta.

"Su waye zasu zo?"

Ta mance da batun wani sigari ko warinsa, rungumeshi ta yi sosai cike da farin ciki ta amsa.

"Tayani murna, Hajiya ta yafemin, ga Anti Zulaihat da Anti Rafee'ah zasu kawomin ziyara gobe."

Ga mamakinta sai ta ji ya ja tsaki. Ta ɗago tana kallonsa.

"Da yake ba ki da zuciya ko? Duk irin rashin kaunar da suka nunamana akan wani banzan Hilal bai ishemu ba? Wane irin kalamai ne ita Zulai din ba ta ce a kaina ba? Ita kuwa Rafee'ah wato tsabar tsana har.."

"Ya isheka! Ya isheka!!" Ta tsinci muryarta da fada, bakinta da kakkarwa, jikinta da rawa. Ta miƙe tsaye kyam da ƙafafunta. Idanunta a rufe cike da masifa! 

Kallonta kawai yake yana zuƙa da fesarwa, maimakon ɓacin rai, murmushi yake, murmushi sosai har da dora ƙafa daga saman Centre Table.

"Ƙarya nayi?"

Shi ne abinda ya furta.

🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

19)

Dakin ya yi shiru, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan Ramlat. Abba jikinsa ya yi sanyi jin abinda Aliyun ya aikata ga ɗiyarsa. Ga duka ga kuma kwatar dukiyar da ta ke mallakinta a yanzu.

  "Wannan yaron anya zai zo?"

Fadin Dakta wanda ransa ya soma ɓaci da shirgasu da Aliyu ya yi. Abba shima nashi ran a ɓace yake.

"Ka rabu da shi Dakta, idan ma bai zo ba, za ta koma. Kawai dama so nake ya zo din don na gargadeshi akan duka, ba jaka ba ce."

Hajiya dai banda uhm ba abinda ta ce. Ita kuwa uwar gayyar yanzun ma kukan ya kasa fita, ta yi shiru kawai tana kallon kafet da kumburarrun idanunta.

Har aka kwashe awa daya, Dakta ya mike ya yi musu sallama zuwa wurin aikinsa. Shima Abba ya mike ya shirya ya fita.

"Duk abinda ke faruwa ke kika jazawa kanki Ramlatu! Gashinan tun ba'a je ko'ina ba kin fara girbar abinda kika shuka. Kin bude baki kin nunawa namiji ƴan uwanki ba sa sonsa, kin jawowa kanki da kuma iyayenki raini. Kin kafe akan ke lallai sai yaronnan, yanzu ai gashinan auren da ba'a shekara ba an soma jibgar Amarya. Ban kuma san me zan ce ba."

Hajiya ke maganar a zafafe, sai kuma ta miƙa ta bar falon ranta na ƙuna. Ramlat ta yi shiru tana tauna maganar Hajiyar. Tabbas ko me ya faru ita ce silarsa. Wani duka, zagi, cin mutunci da akai mata kafin aure, ba wanda ba ta faɗa wa Aliyu ba. Asalima shawararsa ta ke bi ta aikata duk abinda ta aikata.

'Shi yana zagin nasa ƴan uwan a gabanki banda iyayen Muhibbat da suka ɓata ransa?'

Faɗin wani bangare na zuciyarta, tabbas ta sani, ko batun ƴan uwansa za ta yi, zai ce ba ya so. Ta sharesu tunda shi za ta aura. Ba su damu da shi ba, amman shi kam bai yarda an wulakantasu ba. Sai ita ce wawuya ta saki baki har ya rainamata ƴan uwa?

Sai a sannan ta ji hawayenta sun zubo.

"Na yiwa kaina illa da kaina."

Ta furta a fili, dakyar ta mike ta shige tsohon dakinsu wanda yake mallakin A'isha a yanzu. Kwanciya ta yi tana tunane-tunanenta kafin wahalallen baccin ya kwasheta.

***
  "Tana gidansu!" Ya fadi cike da tsawa ganin Abulle na neman takura mishi da tambaya. Ita kuwa gani ta yi daren jiya da kuma safiyar ranar duk a gurinta ya ci abinci.

"Idan ma abincin naki ne ba kya son na dinga zuwa ina ci ai shikenan, sai na zauna na mutu kowa ma ya huta. Komai Aliyu! Komai Aliyu! Ƴan uwannawa ma ba sona suke ba, da Ni mai arziki ne bibiyar da za'a dinga yimin ba kaɗan ba."

Abulle dai ta kama bakinta ta yi shiru jiki a sanyaye. Ta gane yau ran Zakinnata a ɓace yake. Sai da don kansa ya ci gaba da shan shayin da biredi da kwai sannan ta soma magana a nutse cike da rarrashi.

"Allah Ya huci zuciyar Gadanga ƙusar yaƙi. Haba Zakina, mene abin fushi don nayi tambaya? Abin bai kai nan ba ka ji, ba wanda ba ya sonka, halinka suke cewa sun tsana wannan ma nasan don ba su baka damar kun zauna tare ba ne. Ita kuwa Ramlatu me ya yi mata zafin da har ta tafi gidansu?"

Ransa ya ɗan sosu, idan yace bai yi kewar matarsa ba toh wannan karya ne. Yana son Ramlat, irin son da bai yiwa wata mace ba. Haushin da ta ba shi akan me ba za ta taimaka mishi lokacin babu ba. Yana sane ya ƙi zuwa gurin iyayenta, tsoro yake kar ace ya saketa, shi kuma ko sama da ƙasa za ta haɗe  bai ga wani dan adam din da zai sa ya saki matarsa ba.

"Hutu na ba ta, za ta dawo."

Abinda ya cewa Abulle kenan, ganin za ta matsa ya mike ya mata sallama ya wuce.

A kofar gidan suka yi kiciɓus da Malam mahaifinsa.

"Kai zo nan."

Ya karasa ya ɗan russuna yana cin magani.

"Meke faruwa ne kai da iyalinka? Mahaifinta ya kirani akan yana son ganinka."

Ya kara tamke fuska.

"Ba abinda ya faru, anjima zan je."

Malam ya yi shiru yana dubansa, yana son yaron, halinsa ya tsana. Girgiza kai ya yi. Da alama shima da nashi kuskuren, ko kusa ya watsar da lamarin Aliyun ba ya ta tashi sam. Ya fi bada kulawarsa ga ƙannensa.

"Aliyu ka ji tsoron Allah a lamuranka. Wannan yarinya amana ce ta Allah a hannunka. Duk abinda ka yi mata ka sani Allah sai Ya tambayeka. Har sai yaushe za ka gyara halayyarnan taka ka zamo abin so da kauna ga kowa a dangi? Aliyu ba fa kai muka tsana ba, halayyarka ce ba ma so."

"Toh Malam don ba kwa so ai hannunka dai ba zai ruɓe ka yar ba. Addu'a za ku ci gaba da yi mini."

Takaicinsa ya kama Malam, haka yake. Ba dai a yi magana bai maida martani ba.

"Shikenan addu'a ko? Za mu ci gaba da yi, za kuma mu ɗora akan wanda muke yi. Yanzu dai don Allah ina rokonka, don yanzu ka fi karfin na umarceka, ka je ka taho da matarka. Ka dawo da ita ɗakinta. Duka-duka yaushe aka yi auren? Shikenan za'a soma ƙirgamaka aure?"

Ya shafi ƙeya, ko ba komai yau Malam din ya fadi kalamai masu nuni da sassauci da kuma kwantar da hankali a gareshi. Ba kamar yanda ya saba haduwa da ƴan uwansa su yi mishi caa ba. Sai ya tsinci zuciyarsa da yin sanyi kadan.

"Zan je anjima idan na tashi daga kasuwa."

Murmushi Malam ya yi.

"Ko kaifa, Allah Ya shiryeka. Ya yi maka albarka."

Ya amsa da amin, ya mike ya tafi. Ya manta rabon da maganar arziki ya shiga tsakaninsa da Malam din.

***
Tana daki ta yi jugum tana tunanin yanda ta yi fashin makaranta. A gefe guda Aliyu ne a ran, tunaninsa da kuma so da kauna su ke addabar zuciyarta. Ta yi kewarsa ba kaɗan ba. Don Aliyu wata jarrabawa ce daga Allah wanda ba za ta iya tsallakewa ba. Mutan gidan ba laifi sun sakarmata musamman Abba.

A ranar misalin biyar na yamma ta ji Abba na fadin Aliyu ya zo. Gabanta ya fadi. Ta koma cikin daki ta zauna bakin gado, can kuma sai ga A'isha ta shigo tana kallonta a fisge.

"Ki zo inji Abba."

Ta mike ta zura hijabinta ta fita. A falon saukar baƙi suka ta iskesu. Kallon juna suka yi da Aliyu, kowannensu da abinda yake saƙawa a zuciya. Ta kauda idanunta ganin Abba na hankalce da su.

  Abba ya bata dama ta fadi duk abinda ya faru, Aliyu nan take ya amsa duka laifinsa. Ya kuma ba da hakuri da daukar alkawarin ba zai kara dukanta ba. Ya kuma ce muddin ya samu kasuwa ta koma daidai zai mayarmata da zinarenta. Abba ya tambayeta ko  ta yarda da hakan, nan take ga mamakinsa ta yi na'am. Ya jinjina lamarin, sai kuma ya yi dan murmushi.

"Ai shikenan, Allah Ya kara kauda fitina, Ya kiyaye gaba. Ki je ki shiryo ku wuce."

Ta mike ta koma ciki. Ba jimawa ta fito ta dubi Hajiya dake zaune a falo.

"Hajiya Abba ya ce na bi shi."

Murmushi Hajiya ta yi. A ranta dama tasan Ramlat fushinta na ƙalilan ne.

"Toh, Allah Ya kiyaye gaba."

Ta amsa. Har ta yi gaba Hajiya ta yi magana.

"Ko kina son jar miya sai na bayar a yi miki, gobe a kawo kinga zai taimaka maki saboda karatunki."

Ta rasa kalar farin cikin da za ta yi, ta hau washe hakora.

"Ina so Hajiya. Nagode sosai."

Hajiyar ta murmusa kawai. Ta bi ƴarta ta da kallo a raunane.

'Allah Ka zama gatanta. Ka shaida, na yafewa Ramlatu.' Ta furta a ƙasan ranta.

Falon Abba ta shiga yana zaune shima.

"Abba zan wuce."

Ɗago kai ya yi ya dubeta. Shiru na ƴan mintuna kafin ya nisa.

"Shikenan Ramlatu, Allah Ya tsare gaba. Don Allah ki dinga kiyaye harshenki, miji ya fi gaban wasa. Ya wuce dukkan wani matsayin da kika sani. Aljannarki na gareshi. Ki yi mishi biyayya, ki kuma kasance mai hakuri a rayuwarki. Ramlatu addu'a, karatun Alkur'ani, su ne babban makaman kowane bawa da kike gani. Ki rike su ba da wasa ba. Wannan rayuwar ta sauya, ku dinga nemawa kanku tsari daga sharrin masu sharri ta ko'ina. Musamman matan aure yanzu, wata Alkur'anin ma ba daukarsa take ba balle har ta karanta. Sai ki ga abin kunya mace na cewa ita rabonta da tilawa ma ta mance. Karatun sai na Sallah, wata ma sai a sallar ta kakare idan ta idar ta bude ta duba inda ya kufcemata shikenan ta mayar ta ajiye. Me ya yi zafi? Me muke nema a duniyar? Ramlatu kar ki wasa da Alkur'ani, kar kuma ki yi wasa da ibadarki. Idan na ce ibada har bin mijinki. Kinji?"

Ta gyada kai gami da furta Toh. Da gaskiyar Abba, ita kam tunda ya bata Alkur'ani sai dai ta dauka ta goge ƙurar ta mayar ta ajiye amma ba za ta ce ta bude ta karanta ba. Addu'a ma tana yi amma ba ta dagewa yanda ya kamata.

"Nagode Abba, zan kula In sha Allah. Abba ba zan gaji da neman gafararku ba..."

"Sau nawa zan ce na yafemaki Ramlatu? Toh idan ba ki gaskata ba yau ki gaskata. Wallahi ni Khalid na yafemaki duniya da lahira. Allah Ya miki albarka, Ya baki ikon cinye wannan jarrabawar. Sai hakuri Ramlatu, ko yaya bawa ya yi ba daidai ba, ko ya ya zai ga sakamakon hakan. Ki yi hakuri, ki ƙara hakuri a kowace tafiya. Maza idan suka shiga halin babu ba abinda ba zasu yi ba, zuciyarsu kan tunzura ne nan da nan. Komai mace ta yi sai zuciyar ta ayyanamusu cewa saboda yanzun basu da shi ne. Shima ki dinga tayashi da addu'a, addu'ar mace ga mijinta babu hijabi."

Kuka take, kukan da ta kasa riƙewa. Abba kuwa ban baki yake ba ta gami da nasiha har sai da ya sanyata dariya. A ranta kaunar Abbannasu na kara shiga zuciyarta. Abba mutum ne mai riko da fushi, sai dai tana mamakin sauyawarsa. Dama mutum kan sauya har haka?

Shi kuwa Abba ji yake kamar ya tambayeta Aliyun ya daina shaye-shaye amma sai ya bar wa cikinsa. Addu'ar da ya ce ta shafe komai.

***
  A hanya suna tafe cikin ɗan sahu, don Aliyu bai je da mashin ba. Kowannensu ya yi shiru babu mai kula dan uwansa, asalima kowanne wuri daban ya zauna. Shi yana karshen kofa, itama haka. Tsakiyar suka bari fili ba kowa. Har suka isa gidan ta shige shi kuma ya tsaya sallamar ɗan sahu.
Kallon ko'ina ta hau yi, ya yi kaca-kaca, dama tasan hakan ce za ta faru. Yana daga cikin mazan da basu iya koda tattara kaya ba, balle akai kan shara. Kai tsaye ɗakinta ta faɗa ta shiga banɗaki ta dauro alwalar Magriba jin an soma kiraye-kirayen.

Sai da ta idar kafin ta faɗa wanka, garin ba laifi sanyi ya soma shigowa kadan-kadan. Doguwar rigar bacci ta sanya ta ɗora zani a saman. Yanda ta bar dakin haka ta iskeshi, ta rufe kit ta mayar mazauninsa, ta tattara ko'ina.
Tana kokarin fita falon suka ci karo a bakin ƙofa. Dauke kai ta yi daga cikin nashi shanyayyun idanun masu kashe dukkan wata gaɓa ta jikinta.

"Zan wuce." Ta fadi ganin duk inda ta bi sai ya bi ya kare. Ba zato ya rungumeta tsam a jikinsa. Ba ta da kuzarin kwace jikinta. Ita kanta hakan ta fi buƙata. Wasu hawayen ta shiga fitarwa, ya dinga shafa gadon bayanta yana bata hakuri.

"Ki yi hakuri, nayi laifi ba zan kara ba,  ke ce kin kasa fahimtar cewa babu ce ta ke cina. Idan ba ki rufamin asiri ba wa zai rufamin? Duk fa kudin da nake samu akanki yake ƙarewa. Bashi na ci wanda ake barazanar kai ni ƙara kotu, Baby idan ba ta hanyar dukiyarki ba, wurin wa zan je? Wa zai rufamin asiri?"

Hakan da ya fadi sai ya kashe jikinta. Ta ɗago kai tana kallonsa.

"Shi ne za ka kwata da ƙarfi, meyasa ba ka yimin bayani yanda zan fahimta ba? Dukana fa ka yi Sweet Aliy, duka fa? Ina soyayyar da..."

Bai ba ta damar ƙarasawa ba  ya haɗe bakunansu wuri guda. Karshe ma suka koma cikin dakin zance ya sauya.

***
  Tun daga wannan ranar sai komai ya wuce, zamansu ya dawo lafiya kalau. Hajiya ta mata aiken jar miya kaya guda. Taimako daya da Allah Ya mata, Aliyu yasa an gyaramusu wutar nepa kuma ko yaya zai wuya rana ta fito ta faɗi ba'a kawo ba, wanna ya bata damar saka miyar a fridge. Idan ta dawo makaranta sai dai ta dumama. Wataran kuwa ba ta amfani da shi, sai dai ta yi tuwo da miya ko kuma jellof.

Rayuwar sai sam barka, samun Aliyu yana ƙara ja baya. Har ta rage damuwar shaye-shayensa. Yanzun ta fi maida hankali ga tilawar Alkur'ani da kuma addu'a kamar yanda Abba ya tunasar da ita, sai take jin ta wata daban.

  Satinta uku bayan sun kammala gwajin aji ta soma amai da ciwon kai. Tashin farko da likita ya aunata ya tabbatar tana dauke da juna biyu. Wannan karon Aliyu bai yi wani ɗoki ba, a hanya ma jimamin yanda rayuwar za ta yi mishi tsada yake.

"Ga kudin makarantarki, ga cefanen gida kuma yanzu ga ciki."

"Allah zai rufa asiri."
Abinda ta iya cewa kenan, tana jin sadda ya ja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login