Showing 54001 words to 57000 words out of 226732 words

Chapter 19 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12436

jarrabawarsu ta fito, Aliyu da kansa ya shiga fafutukar nemarmata Admission a B.U.K.

  _"Kai Baaba, kar ka yarda matarka ta fi ka Degree idan kuwa ba haka ba kana cikin kwale-kwale."_

Sa'ad ke ba shi wannan shawarar sadda ya shiga jami'ar Bayero wurinsu. Shi kam bai jin wannan a dalilin da zai tauye farin cikin Ramlat. Ko ba komai shi ma DAN ADAM ne, yana da zuciya, ya kuma yarda da cewar ta mishi halacci.
 
_"Bar ɗan iska! Wato kai za ka yi jidalin kudin karatun ma?"_

G Baba ya furta hakan. Aliyu ya toshe kunnensa ya kuma zagesu tas. Karshe suka zuba ido su ga gudun ruwansa.

***
*WASA FARIN GIRKI*

Tsalle ta shiga yi har da juyi kafin ta kara wani tsallen ta faɗa jikin Aliyu, ya kuwa yi mata kyakkyawar runguma suna dariya. Murnar ba ta komai ba ce illa ta samun Admission a jami'ar Bayero.

"Wash! Baby karyamin wuya za ki yi wai?"

Ta sakeshi suka yi dariya.

"Ban isa ba Sweet Aliy. Nagode sosai sosai. I love You so much."

Ya ja hannunta ta faɗa jikinsa.

"Muje ki nunamin a zahiri."

Daga nan ya shiga yi mata raɗa a kunne. Ta kauce suna dariya.

Sai da komai ya kammala sannan ta yi mishi rakiya har wurin motarsa, kamar kar su rabu haka ya ja ya fice Kasuwa.

Wayarta ta dauka da zummar kiran Hajiyarta su gaisa, sai dai abin takaici ba kudi a ciki. Nan take ta tuna katin da Aliyun ya siyamata a darenjiya da suka fita shan ice cream, yana tsokanarta akan ba zai bata ba sai ta ce tana sonsa sau cikin carbi, ita kuwa dariya kawai ta yi. Daga nan ya zura a aljihu ta mance ba ta karɓa ba.

"Alhamdulillah." Ta furta a bayyane cike da nishadi, ta nufi dakinsa. Kai tsaye wandon da ya cire jiya ta fiddo a kwandon zuba kayan wanki. Zura hannunta keda wuya, ta ji kwali da wani abu. Ba ɓata lokaci ta ciro duka. Kirjinta ya bata dam!

"Kwalin taba da lighter?"

Ta faɗi a mamakince, zama ta yi gefen gado jiki ba ƙwari, ta kasa yarda Aliyu mashayin taba ne. Ganin komai ta ke kamar a mafarki.

'Ba ki ganin yanda leɓɓansa keda duhu?'

Faɗin wani sashi na zuciyarta. To ta ya za ta yanke hukunci da hakan bayan cewa akwai masu irin halittar? (Baƙin leɓe)

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Allah Yasa tunanina ba gaskiya bane."

Ta fadi a fili. Kamar ta maida inda ta ganshi, sai ta barshi a saman gadon don kawai ta ji me zai ce. Jiki ba kwari ta shiga laluba daya bangaren, anan ta ci karo da katin wayar ta ciro, ta maida wandon kayan wanki ta fita.

Murnar da take duk ta dusashe don haka koda ta gama shigar da katin a waya, sai ta ɓige da rubutawa Abba text tana mai sanarmishi da cewa ta samu Admission a B.u.k.

***
Abba na zaune sun karyawa a falo, da iyalinsa. Wayarsa ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ya kai duba sa'ilin da yake kokarin kurɓar shayin citta da kanumfarin Hajiya. Ganin sunan Ramlatu na yawo a saman wayar yasa shi ajiye kofin a gaggauce ya bude sakon. Murmushi ya ɗan yi.

"Madallah."

Ya furta cike da dakiya. Hajiya ta dubeshi tana murmushin itama. Suka hada ido.

"Ƴarki ta samu gurbin karatu a jami'ar Bayero. Sai ki bita da addu'a."

Idan ya ce ƴarki, ta gane wacce yake nufi, don haka ta kauda kai ciki-ciki ta ce.

"Allah Ya bada saa."

Abba ya amsa da Amin gami da godiya. Ita mamakin Abban ma take yanda yake nuna halin ko'inkula da abinda Ramlat ta yi musu. Mutum mai tsauri idan aka taɓosbi, shi ne ya sauko har haka. Tana mamaki kam. A wajenta abu ne da bai da saukin wucewa, ba kuma ta jin kafafunta za ta taka gidan Ramlat har abada.

***
Ɗaure fuska ya yi.

"Binciken kuma na menene kike yimin?"

Ta bude baki gami da tattara fatar gira tana kallonsa.

"Bincike? Ni ba bincike na je ba, katin da ka siyamin na je ɗauka. Sweet Aliy don Allah ka fadamin gaskiya. Hankalina ya kasa kwanciya wallahi, sigari ka ke sha?"

"Idan ina sha sai me? Please Baby Ina roƙonki ki kyaleni. Haba, na shigo gida ba ki kai ga ban abinci ba za ki ƙara min yunwa? Tunda nake da MUHIBBAT ba ta taɓa yimin irin haka ba. Bana so please ki bari idan kina so a zauna lafiya."

Yana kaiwa nan ya shige bandaki gami da rufo ƙofar. Da ace tasan asarorin da suka hau kansa a Kasuwa, da ba za ta tareshi da batun wani banzan sigari ba. A dalilin ya burgeta, ya yi amfani da maƙudan kudadensa na saro kaya ya haɗa lefe, bai tsaya anan ba sai da ya haɗa da cin bashi. Yanzun kwanciyar hankalinsa daya, ya samu Abulle ta shigemasa gaba wurin Justice ko zai ga haske.


Ta kasa kwakkwarar motsi, kamar dai kunnuwanta ne basu ji daidai ba. Ta fi tunanin mafarki ne, za kuma ta farka.

*Wannan zahiri ne, mai dogon zango!*
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

_Assalamu alsikum ƴan uwana. Na gode sosai da addu'oinku. Allah Ya bar zumunci. Ameeen ameeen._


17)


Tun fitowarsu take bin bayanta, har suka bar wurin jama'a sosai. Tsayawa ta yi cak gami da juyowa a fusace.

"Wai Malama bibiyar ta menene? Me kike nufi? Kin san ni ne?"

Maganar ko kadan ba ta fusata Ramlat ba. Asalima hawaye ta soma ƙoƙarin zubarwa. Amrah da sauri ta kauda kai gefe, ba ta son ko kusa ta karya zuciyarta, ita kanta ta yi kewar aminiyarta sai dai kuma tunda har hakan ta zaɓamusu zai fi.

"Kiyi hakuri, don Allah ki yi hakuri ki yafemin Amrah. Kowa yan guduna, idan kema kin gujeni wa nake da shi? Da ke kadai na saba shawara, ki yi hakuri ki yafemin kuskuren da na maki."

A ɗan sace Amrah ta kalleta.

'Ta rame.' Ta ayyana a ranta. A fili kuwa ƙara tamke fuska ta yi gudun kada ta nuna rauninta a fili.

"Ai ba ki yimin laifin da na riƙe ki da komai ba. Mutum duk abinda ya zaɓarwa kansa, sai a zuba ido a bar shi da zaɓinsa. Ba ma miki mummunan fata ko kadan."

Ta juyo don ta san idan ta ci gaba da tsayuwar tsaf Ramlat za ta kalamance ta. Yanzun sai ta sauya dukkan ra'ayinta.

"I am pregnant."

Ta furta a hankali bayan ta kara matsawa gaba kadan. Cak kuwa Amrah ta tsaya, ta juyo tana dubanta. Gyada kai ta shiga yi tana share fuska.

"Eh Amrah."

Har ga Allah jin cewa tana da ciki ya sanyayawa Amrah jiki.

'To ko wannan shi ake kira rabo? Wannan auren kaddarar Ramlat ce.'

Ta yi maganar a zuciya, ganin jama'a na kallonsu ya sanya Amrah magana.

"Allah Ya raba lafiya. Na miki murna sosai. Kinga ana kallonmu, ki wuce gida kawai, gobe ma hadu a makaranta. Na yafemaki."

Ta ƙarashe da dan murmushi. Ramlat ta ɗan rungume kafaɗarta tana ƴar dariya. Ko ba komai za ta maido amintarsu.

Tare suka jera suka fita waje, abin hawa ne ya rabasu. Hatta Amrah sai sannan zuciyarta ta yi sanyi.

***
  Kofar falon a bude, wannan ya kara tabbatar mata da zargin maigidan na nan, tun a bakin ƙyauren ta ga motar da a yanzun ta shaida na abokinsa G Baba ne. A gajiye take lis amman murnar shirinta da Amrah ya mantar da ita hakan.

  Tun kafin ta saka ƙafa a falon, ƙaurin sigari da kuma hayaƙinsa ya baƙunci hanci da idanunta. Hira suke suna haɗawa da ashariya. Ji ta yi zuciyarta na tashi. Ta daure ta karasa shigowa falon da sallama. Suka dubeta. Aliyu ya saki murmushi.

"Baby, kin dawo?"

Gyada kai ta yi, don takaici ko kallon G Baba ba ta tsaya yi ba balle su gaisa ta yi ɗakinta. Zama ta yi bakin gado ranta na wani irin zafi. Kallon agogon bangon ta yi, shida na dab da yi. Kwafa ta yi ta rage kayan jikinta fa faɗa wanka.

  A falon kuwa, G Baba ya zuƙi sigari ya fesar.

"Madam dinka fa ba ta yi murnar ganina ba. Hala ba ta son wannan hayaƙe-hayaƙen?"

Wani tsaki Aliyu ya ja, ɓacin rai sosai Ramlat ta jazamishi.

  "Don uwarta an fadamata ni ban isa da gidana bane? Ko an fadamata shashashan miji ne? Zan je na sameta ai! Sa'arta ɗaya tana dauke da Baby."

Wani mugun kwarewa G Baba ya yi, Aliyu ya tsaya cak yana kallonsa.

"Lafiya? Ka zuƙa over Malam."

Sai da G Baba ya kora ruwa sannan ya samu nutsuwa. Ya ɗan dubi kofar dakin sannan ya juyo ya kalleshi.

"Ciki? Kai murna kake Madam dinka ta haihu yanzu? Kasan irin nauyin da zai ƙara hawa kanka kuwa? Wani fita eh yane, wani hawa gajimare duk raino zai sa ka daina. Kai Zaki! Yawane wallahi! Nawa kake ma yanzu? Gaskiya ku san abin yi game da cikin."

Aliyu ya daure fuska kamar bai taɓa dariya ba.

"Malam kar ka kara yimin zancen banza! Shege ne da za ka ce kar na bari ya fito duniya? Kai ka fi kowa sanin duk iskancina bai wuce zuƙe-zuƙe da ƴar romance ba, amma bana babbar harka balle a samu akasi. Toh don me za'a haifarmin ɗan sunnah ka nemi ka kashen gwuiwa. Ba dan iskan da zai sa na zubar da cikin Baby."

Ya ƙarashe gami da watsawa G Baba harara. Shi kuwa G Baba ya kara yarda da irin son da Aliyu ke yiwa Ramlat. Ya tabbata shi ya shafi abinda ke cikinta. Aliyu kaifi daya ne idan ya ga dama, idan har ya yi irin tsaurinnan to ba mai juyamishi ra'ayi wannan ta sanya ya ja bakinsa ya wayance da yi mishi kirari hadi da fadin.

"Ko ba komai ai ma zo mu ƙarawa sama ado."

Suka cafke gami da wata irin dariya.

***
  Ramlat zamanta ta yi a dakin bayan ta idar da sallar La'asar da ba ta yi kam lokaci ba. Tana jin yunwa, sai dai ba ta kaunar ganinsu. Kwantar da kai ta yi a saman hannunta jikin gado tana daga zaune saman darduma, tunani mai zurfi ta faɗa gami da riƙe cikinta. Har sannan tana kara jinjina lamarin, wai ciki ne da ita. 

'Cikin mashayi.' Wani bangare na zuciyarta ya ayyana mata, ta jima anan zaune har wahalallen baccin da ba ta samu yinsa da safe ba ya soma fisgarta sai dai cikinta na ta ƙara saboda yunwa.

A hankali ta ji hannu saman fatar cikinta. Firgigit ta bude idanu, Aliyu ne durkushe ya daga rigar yana shafa cikin. Suka hada ido, murmushi ya sakarmata. Ita kuwa warin sigari ke tayarmata da zuciya don haka ta mike da sauri ya riko hannunta gami da miƙewar shima.

"Baby lafiya?"

Ta rufe baki da hancinta da hannu ta shiga tureshi tana girgiza kai.

"Don Allah ka fita, warin taba, zan yi amai wal..."

Yunkurin aman ya katseta, da sauri ta faɗa banɗaki shi kuwa ya fita daga dakin. Ba wani abin kirki ta amayar ba, ta wanke baki ta fito, ganin baya dakin yasa ta daukar turare mai sanyin kamshi a bakin madubi ta ɗan fesa a jikin wani dan handkerchief ta toshe hancin sannan ta bude winduna  dakin.

Kiraye kirayen sallar Magriba ne ya sa ta mike ta zura hijabinta. Sai da ta yi sallah sannan ta mike ta nufi falon don Aliyun ya shigo har sau biyu kafin ta idar. Maimakon ƙamshin sigari, sai ta ji ƙamshin turaren wuta. Ba kowa a falon hakan ya bata tabbacin Aliyun ne ya kunna. Ta saba duk sadda ya gama busa hayaƙinsa za ta yi azamar daukar kaskonta ta kunna gawayi ta saka turare. Sai ta ji hakan da ya yi ya burgeta, kaso hamsin na damuwarta ya yaye. Sai a sannan ta ci dora abinci mai saukin dahuwa ta ci, ta shiga karatu.

***
Washegari da ɗokinta ta fita daga gidan. Aliyu ne ya kai ta saman mashin dinsa.
   Koda ta shiga Malami ya shigo basu sami damar gaisawa da Amrah ba sai dai wannan karon sun samu zama wuri guda. Ana tashi, kowa ya fice daga ajin suka yi zamansu.

"Mai ciki ba za ki ci komai ba? Rana fa ta yi." Fadin Amrah cikin murmushi. Harararta ta yi sannan ta ja guntun tsaki.
  "Ni har tsoron haihuwar ma nake."

"A gidan Aliyun ko kuwa me?"

Tasan Amrah da biyu ta yi tambayar, ba kuma ta so ta bada kofa yanzu Amrah ta san sirrin gidanta. Ta fi kaunar Amrah ta dawo da tausayi da kaunarta a zuciya kamar dai a baya.

"A'a, kada na mutu wurin haihuwa."

Dariya Amrah ta yi.

"Sai kuma aka fadamaki haihuwar ƙarar kwana ce? Addu'a za ki yi, In sha Allah za ki haihu lafiya. Af, ga saƙon Umma ma. Ta cemin ki dinga shan kayan marmari da abinci lafiyayye. Kar kuma ki yawaita daukar abu mai nauyi. Kuma wai ko nan gaba za ta aikomaki mene? Oho na manta. Ta ce dai na miki albishir tana nan zuwa."

Dadi, farin ciki da annashuwa suka cika zuciya da fuskar Ramlat. Daga washe haƙora tana dariya sai ga hawaye na fita. Hawayen tana da wata uwa da ba ita ta haifeta ba, amman ta tuna da ita. Tana kokarin ba ta kulawa irin ta uwa.

"Meye abin kukan?"

Fadin Amrah da ke jin zuciyarta itama na neman karyewa. Ta daure ta tattaro dauriyar wuri guda, ta shiga zolayarta.

"Oh, wa ya ga Ramsy da ɗa? Naga yanda za ki yi raino. Wai har ki shayar."

Ta ƙarashe gami da sanya dariya, itama ba ta san sadda ta dara ba ta hau share fuskarta.
 
"Kema ai kamar yau ne."

Taɓe baki Ramlat ta yi.

"Ni da aure sai na kammala karatu in Sha Allah."

Murmushi Ramlat ta yi kafin su taɓa hira, so take Amrah ta jefomata tambayar da ta shafi gidanta ko dangin mijinta, sai dai ta lura kokarin kaucewa hakan ma Amrah ke yi. Don haka itama sai ta kara rufe cikinta ba ta kaunar su sami wata matsalar.

***
   Bayan sati biyu hankalin Ramlat a kwance, za ta yi waya da Abbanta da kuma Hajiya wacce a sannan ta ɗan sassauta kadan. Umman Amrah kuwa kiranta take sosai su yi hira ta yi ta kwantar mata da hankali. Ta dauketa kamar ƴar da ta haifa a cikinta. Bangaren Aliyu, ya rage zuwa ya yi mata shaye-shaye a gida kamar yanda ya daina shigomata a buge. Hakan ya kara kwantar da hankalinta ba kaɗan ba. Abinda ke yawan bata mamaki ya daure mata kai, banda Abulle babu wani ko wata a dangin Aliyu dake zuwa gidanta, zargin ba sa kaunarta ya kara tabbata a kansu. Don haka ta ja jikinta ta kama kanta. Hakan bai hana ta kira mahaifin Aliyun ta gaidashi, shi kam lafiya sumul yake amsamata.
 
   A yammacin juma'a ta fito falon bayan ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando Pakistan. Tashinta daga bacci kenan bayan ta dawo daga makaranta. Kicin ta shiga ta hau kiciniyar yin tuwon semo da miyar kuka kasancewar hakanan ta ji tana sha'awarsa. Sai dai me? Babu gas.

"Ya Salam." Ta furta a fili. Jiki a sanyaye ta fito falon tana jan tsaki, waya ta dauka ta lalubo lambar Aliyu ta kira.

  "Kamar ya babu gas? Har gas din gidan ya ƙare?"

Shi ne tambayar da ya jefomata bayan ya saurari bayaninta. Ta ciji leɓɓanta ta kasa cewa komai. Sai kuma ta ji ya ja tsaki kafin ya ce.

"Nidai wallahi banda kudi, kema kin sani kuma. Yanzu haka ganinan wani banza dan gin..."

Kiit, ta katse kiran, a duniya ta tsani ta ji yana ashariya. Abin na ƙona ranta.

"Allah Ka shirya." Ta firta a fili, ita kam yunwa ta ke ji don haka ta mike. Ta tuna da lemun da ta gani Aliyu ya ajiye a fridge da safiyarnan, sadda aka kawo wuta. Ta soma shiga kicin ta dauko ragowar bireda ta fiddo lemun. Tun kafin ta ƙaraso ta bude ta shiga kwankwada. Sosai ya yi mata dadi. Tana zama ta hau tauna biredin, idanunta na kan wayarta dake ƙara kuma sanin Aliyun ne ta ƙi ɗagawa. A hankali kuma ganinta ya soma zama dishi-dishi. A kokarinta na  ajiye robar lemun saman Centretable sai ya zube a ƙasa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Mene haka?"

Ta fadi cike da karfin hali. Ita ta san me take ji. Jirin na kwasarta, yana kokarin fitar da ita daga hayyacinta. A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ta danna. Cikin muryar ƴan maye ta soma magana.

"Aaaaaliiii."

Ba ta ji me yake cewa ba ta wurgar da wayar, ta mike ta na tafe tana rangaji da zagaye falon, ba ta yi aune ba ta ci uban tuntuɓe da takalminta ta bugi gefen mararta da tv stand ta zube anan. Duk da ba'a hayyacinta take ba sai da ta saki ƙara.

***
A hargitse ya banko kofar falon ya shigo. Kallo ɗaya ya yiwa robar lemun ya san abinda ke faruwa. Jijjigata ya soma.

"Baby! Baby! Ramlat!"

Ya rasa na kira, cak ya ɗagata ya fita. Ba kuma zai yiwu ya sanyata a mashin ba, dole ya dawo da ita ya fita ya taro ɗan sahu suka bar gidan zuwa asibiti.

***
"Ka yi hakuri, cikinta ya riga da ya zube."

Bayanin Dr Lamin kenan bayan ya gama faɗawa Aliyu cewa a jininta da aka auna an samu tabbacin ta sha kwaya mai ƙarfi, ya kuma yi faɗan meyasa ya bar ta yin shaye-shaye duk kuwa da sanin da ya yi tana da ciki. Ga mamakin shi kansa Aliyu ya kasa cewa komai, har Likitan ya yi faɗa ya kammala. Batun zubewar cikin ya fi komai ɗagamishi hankali. Idanunsa suka kaɗa.

'Ko mene laifinka ne ai! Da ba ka ajiye a gidan ba, ta ina za ta gani ta dauka tunda ba halinta ba ne!'

Faɗin wani sashi na zuciyarsa.

***
Awanni kaɗan bayan farfaɗowarta ya shiga. Ta ɗago idanu ta dubeshi sai ta soma hawaye.
  "Kaga abinda halinka ya jazamana ko?"
Ya zaune gami da riko hannunta.

"Laifinki ne, meyasa ba ki ɗaga wayata ba ina ta kira? Tunawa nayi na ajiye a fridge shiyasa na so na gargaɗeki."

Ta kauda kanta kawai, cike da bakin ciki. Abin kunya sanadin shaye-shayen mijinta, cikinta ya zube.
 
 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login