Showing 216001 words to 219000 words out of 226732 words

Chapter 73 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12443

dama ita kiranye aka bata, kuma har gshinan kwalliya ta biya kudin sabulu, ta kuma ci burin dole ta sanya ya saki Fa'iza ya auri wacce take so.  Ta kira wayar Hajiya Zeenatu ya fi a ƙirga don ta ba ta labari amma ba ta samunta, karshe ma ta ji wayara kashe.

Tana shirin sake gwada kiran, sai ga Mai aikinta ta shigo tana sanarmata da batun zuwan Emma daga gidan Hajiya Zeenatu. Nan ta bada umarnin ya karaso, Emma bayan sun gaisa ya fadamata halin da Hajiya Zeenatu ke ciki. Hankalinta ya tashi ba kadan ba, ta kaɗu sosai. Ba shiri ta ce ya je za ta leka asibitin. A yammacin ta je, ta yi mamakin yanayin da ta riski aminiyarta a ciki.

"Zeenatu! Ke ce haka?"

Hajiya Zeenatu sai ido da kuma hawaye. Da harshenta wanda maganar ba ta fita sosai ta ce.

"Ni..ce. Batool ki kai ni wurin Hussein."

Hajiya Batool ta girgiza kai ta riko hannunta.

"Ki bari ki warke, ki nutsu kiyi zamanki a asibiti a dinga yi maki magani tukunna. Zan turo Dije ta dinga tayaki zama, za ki warke. Da kafarki za ki je wurin Hussein."

Hajiya Zeenatu dai sai hawaye, a ranta kawai bakin cikin abinda  ya faru ta ke ji, da ace ta san hakan za ta faru da tun farko ba ta amsa wayar Manaja ba balle ta je kasuwar. Ji take inama ta kama hanyar Adamawa. Ta kara kallon Hajiya Batool dake ba ta labarin dawowar da ɗanta zai yi, haka kawai maimakon ta tayata farin ciki sai ta ji hassada da kishi sun kama ta, wato aikin Hajiya Batool har ya yiwu ita kuwa babu ɗaya da ta aikata, don aikin tulun ba zai yi tasiri ba sai ta je ta barbaɗawa Hussein hodar da Buzu ya ba ta. Haka tana ji tana gani Hajiya Batool ta fice daga asibitin gami da jadddamata za ta turomata Dije. Ita dai Hajiya Zeenatu gyada kai kawai ta yi, a yau ta ji takaicin rashin ajiye ƴar aiki mace da ta yi.

***
  ADAMAWA

Baƙin Kano sun sauka lafiya a family house, suka yada zango a ɓangarensu, wannan karon ma an musu tarba sai dai ba kamar yanda aka saba ba. Kawu dai jikinsa duk ya yi sanyi, a ranar da yammaci ya tara manyan dattawan gidan maza da mata yana kuka yana roƙar gafararsu.

"Sharrin shaiɗan ne, ku yafemin domin Allah. Itama Aminar da yaran yanzu zan je na nemi afuwarsu."

Kowa kam ya yi farin ciki da jin hakan,  ko ba komai har da rashin nadamarsa ne ya ba mutane haushi. Nan dai bisa jagorancin wani ɗan uwan Babansu, Surajo, tsoho mai ran ƙarfe, suka ɗunguma har iyalin Kawun, a yammacin zuwa gidan Dada.

***
Kwance yake saman doguwar kujera, yayinda ta ke kwance saman kirjinsa. Sai cuku-cukun miƙewa ta ke yi sakamakon raɗan da ya ke mata a kunne amma hakan ya gagara. Ta ko'ina ya matse ta gam! Ai kuwa bai yi aune ba, yana kai bakinsa saitin nata, ta yi azamar kama leɓensa na ƙasa ta ciza. Bai san sadda ya sake ta ba gami da kama baki.

"Aush!"

Ramlat na dariya ta mike, daga ita sai riga sky-blue marar nauyi, da kaɗan ta wuce gwuiwarta. Gashinta wanda tuni ta warware kitson yana tufke a baya.

"Sorry." Ta fadi tana ɗaga yatsunta bayan ta ja baya sosai tana dariyar mugunta. Hussein ya lashi leɓensa ya manna mata harara.

"Zan kama ki, yau ba mai kwatar ki."

Ta narkar da fuska.

"Haba don Allah Haskena, kai ɗin ne ka ƙi hakuri ka bari na kammala girki. Nikam kana sane ka ce sai wani satin za ka fara zuwa aiki. Don.."

Ganin ya yi wani irin miƙewa ya na kokarin cafkota ya sa da wani irin gudu ta shige kicin ta rufe tana dariya. Ya jingina jikin kofar.

"Za ki fito ki same ni, na san maganinki."

Murmushi kawai Ramlat ta yi mai bayyana haƙora ta ƙarasa wurin tukunyar miyarta, ba don na wutar kaɗan-kaɗan ta ke ci ba, ta tabbatar sai ya ƙone.

Shi kuwa gogan yana shirin komawa ya zauna, aka kwankwasa ƙofar falon da sallama. Ya amsa da ba da umarnin shigowa.

Hafsat ce, gaba daya jikinta a sanyaye. Ya dube ta fuska a tamke don har lokacin bai gama saukowa daga fushinta ba. Ta gaida shi ya amsa ciki-ciki.

"Dada ce ke kira."

Ya gyaɗa kai kawai ita kuwa ta miƙe ta fice kirjinta na dukan tara-tara. Tana tsoron abinda zai biyo baya idan ya ga waɗanda suka zo gidan. Sanin halin zuciya irin nasa ne yasa Dada kiran AlHassan a waya akan ya zo gidan bayan ta mishi bayanin komai. Wannan yasa ba ɓata lokaci, AlHassan ya kamo hanya don ba tazara sosai tsakaninsu.

"Heart, bari na je Dada na kirana. Kinji ko?"

"Toh."

Ta amsa ba tare da ta buɗe ƙofar ba. Ya gyara zaman brown tshirt dinsa ya zura silifas dinsa baƙaƙe na maza na yawo a gida ya fice. Tun a farfajiyar gidan ya ci karo da motoci, wannan ya ba shi mamaki ya tabbatarwa kansa baƙi suka yi, amma daga ina? Shi ne tambayar da babu amsarta a yanzun. A ƙofar falon ya ci karo da takalman maza da mata. Haka kawai ya ji gabansa ya fadi da sauri kuwa ya karasa ciki da sallama. Idanunsa bai sauka kan kowa ba sai a kan mutumin da ya fi tsana nan duniya zaune kusa da Dadarsa su na kuka. Ya fahimci komai, ya gane kuma Dada ta sauko ta yarda da dukkan ƙarairayin da ya shiryamata don haka shi ba shi da bukata. Tsigar jikinsa gaba daya ta tashi tsabar ɓacin rai, yayinda idanunsa suka kaɗa, ya ƙaraso ciki da zummar ƙarasawa kai tsaye ga Kawun ya shaƙe wuyansa babu ko tunanin yaransa da ke zaune a falon. Da sauri Baffa Surajo ya mike ya shiga tsakani. Ganin girma da cikar haibar dattijon mai tsananin kwarjini ya sa shi kasa ƙarasawa sai hawaye da suka shiga zubowa kawai daga kwarmin idanunsa.

"Me ya kawo shi nan?"

Baffa Surajo ya dafa kafaɗar Hussein kafin ya ja hannunsa ya bishi suka zauna saman kujera dakyar. Hussein banda girgiza ƙafa ba abinda ya ke yi yana hararar inda Kawun ya ke, ganin haka Baffa ya riƙe ƙafar.

"Ya isa ɗana. Ya isa."

Kawu ya taso zai ƙaraso inda Hussein ya ke, da wata irin tsawa ya dakatar da shi.

"Kar ka sake ka ƙaraso nan! Kar ka yi wannan gangancin!"

Daidai da shigowar AlHassan da sallama, ya kalli mutanen falon ya kuma dubi Hussein mai magana ya sauke ajiyar zuciya. Ya san dama hakan za ta iya faruwa, bai ma yi tsammanin zuwan wannan ranar nan kusa ba, sai dai Allah ne Mai shiryarwa.

Ya karasa ya gaisa da Baffa Surajo da matan Kawu har ma Kawun. Ya koma gefe ya zauna gefen Hussein.

"Ka yi hakuri mu ji ta bakinsa, ya riga ya zo kuma da iyalinsa baki daya, ka tuna, idan shi ne ya yi mana laifi, iyalinsa ba su da laifi tunda shi ne shugabansu."

Da kalamai irin haka Baffa da AlHassan suka taushi zuciyar Hussein. Ya yi shiru bai kara magana ba, wannan ya ba Kawu damar soma magana cike da jin wani tsananin kunya, wato wannan a duniya kenan ma, ina ga na lahira? Allah Ya tsaremu.

"Ku yi hakuri, ku yafemin. A ƙiyayyar da na nunamaku har da sharrin zuciya da shaidan. Na sani, Innarmu a baya ita ce kan gaba wurin ƙara rura wutar ƙiyayyarku a zuƙatanmu,  sai ya kasance ni abin ya zame min ciwo domin kuwa ya juye zuwa hassada da tsana. Ban ƙara jin tsanar Amina da Aminu ba, sai bayan auren Amina da mutumin da nake ganin ban kama ƙafar arzikinsa ba. Wato dai Marigayi Naziru, ban kuma gama farfadowa daga wannan bakin cikin na ci gaban da Amina ta samu ba a rayuwa, sai ga Aminun da muke tunanin ma ya mutu, ya dawo. Tun kan ya zo Kano wurina, labari ya riskeni, na yi bakin ciki sosai, Karime kanwarmu ta fadamin da murnarta ni kuwa ban ga abin murna ba a dawowarsa musamman da naji labarin ai rayuwa ta mishi kyau ya dawo har da matarsa da kuma yaransa ƴan biyu. A wannan halin sai ya kawomin ziyara duk kuwa da tarin kiyayyar da nake mishi, sai dai na gasamishi baƙaƙen maganganu wanda har ya mutu a lokacin ban yi dana saninsu ba sai ma dadi da naji a lokacin ganin ya bar min filin duniyar na ci karena babu babbaka."

Kawu ya numfasa saboda kukan da ya shaƙe shi, iyalinsa da su Dada kuka suke yi cike da mamakin irin wannan salon ƙiyayyar da bawan Allahn ke yiwa ɗan uwansa na jini. Shi kuwa Hussein ba zai ce ga yanayin da yake ciki ba, sai dai ko kallon Kawun ba ya son yi.

Kawu ya ci gaba da magana bayan ya sharce majina.

"Bayan shekaru da dama, a wani ziyara da Amina kika sa Husseini ya kawomin, lokacin ya samu hutun karatun da yake yi a Dubai. A wannan zuwan ne yaron ya ban tsoro har nake ganin nan gaba zai iya cin mutuncina a gaban ko su waye. Saboda tunda nake da ke da Aminu, babu wanda wuyansa ya taɓa yin tsaikon da zan faɗa ya faɗa, sai Husseini, ko Hassan bai taɓa yimin cin fuskar da nake ganin  Husseini ya yimin a lokacin ba. Wannan ne dalilina na farko da na ci alwashin sai na tarwatsa rayuwar Husseini. Sai ya rasa dukkan farin cikinsa. Sai dai me? Kafin na kai ga aikata duk wani abu da na yi niyya, na samu labarin ɓacewar Husseini, ya gudu ya bar gida ba'a san inda ya shiga ba. A lokacin idan ka tona zuciyata banda tsananin farin ciki babu abinda na ke ji, har addu'a nayi Allah Ya dauki ransa ma. Bayan watanni uku da ɓacewar Husseini, wataranar lahadi ba ni mancewa, ni da kaina ke tuƙi a mota daga kasuwa zan koma gida, a hanya na hangi wata tsohuwar kwastama ɗita, a baya takan zo ta sararwa Hajiyarta atamfofi a shagona ko kuma yadika na maza ta tafi, a sannan tana budurwa ko kuma nace mace mai zaman kanta amma a karkashin ikon wata Hajiya mai safarar yara zuwa Makkah da sauran ƙasashen waje don aikatau ko akasin haka. Zeenatu kenan, tun a baya Hajiyar ta sha  aiko ta shagona tun ban kai ma ga auren ita Maimuna ba, (Anti Amarya), tun a wancan lokacin muka saba, nakan ba ta shawara akan ta yi aure gudun kar ta ɓata rayuwarta don ni nasan wace ce Hajiya Balki uwar ɗakinta, saboda na sha zuwa gidan muyi cinikin kaya ta siyawa ƴan matan yaran da ke gabanta ko kuma ta siyar, na kuma san irin kalar sana'arta. Daga baya kuma sai na bar ganin Zeenatu, sai wata Raliya ake turowa. Koda na tambayi Raliya, ta bani tabbacin ai Zeenatu ta tafi Makkah, a sannan na ji ba dadi kwarai don ban so ta cuci kanta ba sai dai dama daga yanayin Zeenatu na fahimci maganata ba wani shigarta ya ke ba."

Kawu ya numfasa, nan kuma dai dakin tsit ya yi babu mai kuka sai jin wannan labarin mai ban mamaki daga bakin Kawu. Ya ɗora zancensa.

"Ganin da na yiwa Zeenatu a haɗaɗɗiyar mota, bai sa na kasa ganeta ba, asalima fuskarta ko kaɗan ba ta sauya ba duk kuwa da ɗumbin shekarun da aka ɗiba. Parking ta yi a gaban wani katafaren shagon siye da siyarwa na maƙulashe, na juya kan mota da sauri na faka a gefenta. Sai dai ban kai ga fitowa ba, idanuna su ka sauka akan Husseini, ba karamin razana nayi ba, sai nake ganin abin kamar a mafarki, fuskokinsu kadai ya nuna suna cikin tsantsar farin ciki. Ban karasa ba, har suka shiga suka fito, mantuwa suka yi ko mene? Ban sani ba, na ga Husseini ya fita ya koma ciki, har zan je wurinta sai naji tsoron kada ya fito ya gan ni, sai kawai na koma cikin mota na jira har ta tashi motarta ta kama hanya ta bar wurin, na bi su a baya har suka isa gidansu. Koda na ga gidan kawai sai na juya da zummar zan dawo na same ta don ba na kaunar Husseini ya gan ni. Bayan kwanaki biyu, a wani yammaci na isa kofar gidan, cikin saa na isketa tana kokarin shiga cikin kyauren, ganin ita kadai ce na yi hon ta juyo, ni kuwa na ja na tsaya na fito. Ta shiga bi na da kallo kamar na neman ƙarin bayani da kuma son tuna inda ta san fuskar, nan take ta tambaye ni. "Kamar na sanka." Na ba ta amsa da eh, kafin na ce kin manta Modibbo na Kwari? Nan da nan ta saki fuska muka kara gaisawa. Na ce "Yaushe kika dawo?" Nan ta ke sanarmin ai ta kai shekara guda da dawowa, daga nan kuma na nemi mu keɓe don mu tattauna wata muhimmiyar magana. Sai dai na tambayeta ko akwai wani saurayinta a ciki? Idan akwai na juya.  Ni kuma na dadi haka don na gane irin zaman da suke yi da Husseini, burina ta cemin ba zaman aure ba ne.
Abin ya ba ta dariya. "Aa ai kuma yanzu an girma da wannan kalar rayuwar, aure nayi."  Na jinjina kai ina murmushin da bai kai zuci ba don ba haka na so ba. Sai dai ina bukatar mu zauna na ji bayani sosai. Koda muma shiga ciki, ta sanya aka kawomin lemo da ruwa, abinci kuma na ce aa. Bayan mun nutsu na kara kai duba ga hoton Husseini da ita wanda tun shigowata ya dauken hankali, shakka babu aure ne suka yi. Anan na sanar da ita gaskiyar alaƙarmu da Husseini, a farko ta razana sosai har ma ya ɗaure fuska tamau. Nayi dariya sosai na ce ta kwantar da hankalinta ina bayanta domin ba na shiri da iyayensa, don haka ni ko nan da bangon duniya ma tana iya kai Husseini muddin ba za'a gan shi ba. Faɗin hakan keda wuya ta kwantar da hankalinta saboda na biyomata ta sigar da dole ta samu nutsuwa. A karshe ta ban labarin duk yanda aka yi na dinga dariyar mugunta. Ni kuma na yi mata alƙawarin ko na ji ana raɗe-raɗin an gan shi zan sanarmata, zan kuma yi asirin da zan rufe bakin duk wanda naji yana raɗe-raɗin ya ga ko mai kamarsa ne a kwaryar Kano. Na kuma kara mata da cewa dole tana bukatar asirin da zai kara jin nan duniya ya tsani a tayar da zancen danginsa ko a tambayeshi, amma ta bar komai a hannuna. Wannan ne abinda na san na aikata, ya kasance ana neman Husseini, ni kuma nasan inda ya ke, amma na yi gum. Shiyasa koda Ramlatu ta zo da zancen Husseini, na kore ta na ce ba ruwana. Ban yi ƙasa a gwuiwa ba na sanar da Zeenatu, nan muka ce kawai a kashe ta yanda babu wata hanya da za'a san labarin komai. Sai dai kuma abinda Allah Ya riga ya tsara, ba wanda ya isa dakatar da shi."

Kawu Modibbo na kaiwa nan ya dakata ya ci gaba da kuka sosai. Falon banda salatin da Baffa Surajo ke maimaitawa cikin zubar hawaye, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan yaran Kawu Modibbo.

"Ku yafemin, ku yafemin don Allah. Na tsaneku akan ba ku aikatamin komai ba, na cutar da rayuwarku. Na hana yarana zumunci da ku duk don bana kaunarku. Ku yafemin. Husseini ka yafemin, Aminatu, Hassa.."

Ya kasa ci gaba saboda kuka, Hussein kawai miƙewa ya yi ya bar falon, Baffa ya yi nasiha mai ratsa jiki gami da nuna ladan da ke tattare da wanda ya yi hakuri. Dada nan take ta yafemasa, ta ce komai ya wuce, hakanan shima AlHassan. Wannan abu ya yiwa Kawu da iyalinsa dadi, itama Hajja Fatuma ta nemi gafarar Dada na yanda ta dinga wulakanta ta ita mai miji dadi, Dada na murmushin da ya fi kuka ciwo ta ce babu komai ya wuce. Haka dai aka yi ta neman yafiyar juna.  Taheer sai satan kallon Hafsat ya ke, ita kuwa gaba daya kunyarsa ta ke ji, a gefe guda tausayi da kaunar dan uwanta Hussein ya kara mamayeta, wato dai shi ya san dalilinsa na tsanar Kawu. Ashe mugun abu ya ƙulla masa har haka.

***
Ramlat da ba ta san hawa ba ba ta san sauka ba, ta ga mutum ya fado falon, kallo daya ta yi mishi ta gane ba lafiya. Ya zube saman kujera ya runtse idanu, fuskarsa abinka da farar fata ta koma jawur da ita. Ta shiga ambaton Allah a ƙasan ranta, miƙewa ta yi ta zauna gefensa, ba ta ce komai ba amma ta kamo tafin hannunsa ɗaya tana murzawa a hankali, a ranta addu'oi kawai ta ke karantomasa. A hankali kuma ya shiga sauke ajiyar zuciya, ya bude jajayen idanunsa ya dubeta. Sai da ta ji gabanta ya fadi, gaba daya sai ta tsinci kanta cikin damuwa mai tsanani.

"Lafiya Haskena?"

Gyara zama ya yi, bai ɓoyemata duk abinda ke faruwa ba, kawai sai ta shiga hawaye tana mamaki da tsoron lamarin mutum. Idan naka ya yi maka haka, ina hujjar da za ka ji haushin wani don ya yi maka? Sai kuma ta fahimci kuskurenta, hawayen ba zai ƙarar da Hussein da komai ba face ya kara ganin girman laifin da Kawun ya mishi har ya kasa yafemasa. Don haka ta yi azamar sharesu, ba ta kai ga magana ba sai ga AlHassan ya yi sallama ya shigo, Dada tafe a bayansa. Ta mike da sauri tana musu sannu da zuwa, Allah Ya taimaka ma tun fitarsa ta suturta jikinta sakamakon shanyar da ta kwaso a bayan gidan wurin shukoki. Ta gaida su Dada, Dada ta amsa fuska a ɗan sake. Sai dai itama fuskarta kamar na Husseini, ta yi ja, kuka kam ko ba'a faɗa ba sun yi shi, balle AlHassan.

Za ta shige ɗaki, Dada ta hanata, ta bata umarnin zama. Shiru ya ɗan biyo baya. A hankali kuma Dada ta shiga yiwa Hussein nasiha, sosai ta ke yi mai ratsa jiki tana kawomishi misalai na irin hakurin da Annabi s.a.w ya yi da yan uwansa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login