Showing 51001 words to 54000 words out of 226732 words

Chapter 18 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12430

da ya rataya a wuyanka ko ban faɗa ba. Ka ji tsoron Allah a lamuranka, kar ka manta zai tambayeka duk wani abu da ka aikata a rayuwa."*

Bai mantawa a lokacin murmushi ya yi kawai.

*'Ba dai haka ka so ba Abbanmu. Sai dai ba za ka hana abinda Allah Ya yi ba.'*

Nan take ya ce a cikin ransa.

"Don ubanka ina magana kake dariya? Wane raini kenan?"

Kalaman Justice suka katse tunaninsa, ya ankara da murmushin da yake zabgawa har haƙoransa na bayyana.

"Ayi hakuri." Ya kara fadi.

Kowanne ya tofa albarkacin bakinsa kan ya riƙe amanar yarinya, daga nan ya yi musu godiya ya mike da uzurin Abulle na nemansa. Mahaifinsa ya bishi da kallo gami da addu'ar shiriya. Yaran ka haifa ba ka isa ka saita halayyarsu ba.

Kiciɓus suka yi, ba haka ta so ba. So ta yi da sauri ta bar dakin Abulle kafin ya cimmata. Shigarta dakin Abulle don kai mata goron da ta dauko a dakin Daddynta. Jin Abulle na mitar Aliyun ya zaunar da ita zaman jiransa ya sa ta katse hirartasu ta yi mata sallama ta fito tana sauri ta bar bangarennata. Sai dai kuma ba yanda ta iya tunda gashinan gabanta. Ta daure ta haɗiye komai dake tasomata.

"Ina wuni Yaya Aliyu."

Bai san yana da kunya ba sai a yanzun, ya kauda kai daga kallonta.

"Lafiya. Ya kike?"

Ba tare da ta amsa ba ta wuce da sauri ta yi hanyar kofar sashinsu. Bayanta ya bi da kallo, Muhibbat kenan. Ya sa kai dakin Abulle.

Salati ta shiga yi kafin ta hau yi mishi fadan sigari da ya sha. Taɓe baki ya yi, ya mance da hakan shaf bai jefa alawa bakinsa ba, bai kuma fesa turare ya tsaye a waje na mintoci ba kafin ya hau mota ya tuƙo. Ya mance rabon da ya shigo gidan yana warin taba.

"Wai ni don Allah ki bar kunnena ya huta. Shikenan don kin ji warin abu a jikina sai ya kasance sha na yi? Ko a addini an hana irin wannan yanke hukuncin. Idan ina sha tsawon lokacin nan ba za ki sani ba sai yanzu? Mtsw, Abokina ne ya sha, shi na ziyarta shi ne ƙamshin ya biyoni."

Hakan da ya faɗa sai kuma ta gyara zama ta hau jijjiga kai.

"Kuma fa hakane. To ka kara kiyayewa dai. Raɓar abokai ɓata gari ba naka bane. Na soke abotar. Yanzu dai ya batun lefe? Mahaifinka cewa ya yi na farko an maka, na biyu kai za ka yi. Duk da haka Alƙali da sauran kawunnanka sun ɗan ba ka wani abin ka haɗa ka yi."

Murmushi ya yi.

"Lefen Baby ina son ya fi na kowa. Ina son a bude a kirashi da lefe. Masu yi mata habaici da zagi a kan aurena su daina. Don haka da kaina naji zan hada abina koda ace hakan na nufin karyewar jarina."

Baki sakaka Abulle ta saki tana kallonsa kafin ta magantu.

"Um um dai Zakina, ba za'a yi haka ba. Ƴar dangi ma ba ka ce hakan ba sai akan bare? Ina rabaka fa."

Ya yi dariya.

"Abulle tawa ni kadai,  Baby ai ta isa na yi mata komai. Koda kuwa komai nawan zai ƙare a kanta."

Ta taɓe baki.

"Fadi dai sunanta na zahiri, shi zan fi fahimta. Ramlatu ko? To naji, ungo nan."

Ta daga filo ta fiddo damin kudi ta mikamasa. Ya karba ya zura a aljihu.

"Wai nikam me zai hana ka mayar da yarinyarnan ɗakinta ne? Naga dai tsiraicinka yafi rigar aro ta mutane."

Miƙewa ya yi tsam!

"Sai da safe Kakus. Kwanta ki yi bacci abinki. Nima na tafi nawa lissafin."

"Ai fa, ba dama a dauko magana sai ka kauce. Toh har gobe ban ga wata ɗiya da za ka kawo na ji ina sonta a raina ba irin Muhibba."

Daga kafada ya yi alamar ke ta shafa ba kuma tare da ya komai ba ya fice daga dakin. Ko a ransa bai ƙara tada zancen Muhibbat din ba.

***
  "Kai Allah Ya rayamana mai sunan Abba."

Fadin Zulaihat kenan cikin waya tana murmushi ranta fari ƙal. Ramlat na daga kicin tana dahuwar indomie ta ji wannan kalamin. Anan ta fahimci sunan Abba ɗan Rafee'ah ya ci. Kwalla suka tarar mata, a yanzu ba ta rabo da hakan. Tunda aka daura aurenta da Aliyu, komai ya daina yi mata dadi. Ba kuma don ba ta sonsa ba, har gobe tana jinsa a ranta. Wuyarta ya kira wayarta ko kuma ta kirashi, za ka ganta cikin farin ciki da annashuwa. Kalamansa masu taushi da dadi, wanda ke nuni da nutsuwa da kuma cikar hankali, sun fi komai yi mata dadi a ranta. Sai dai ba ta nufin ta rabu da yan uwanta a dalilinsa, duk suna amsamata idan ta yi magana, sai dai irin amsawar da gwamma kar su yi. Babu fara'a babu sakin fuska. Sama-sama suke amsawa kamar ba sa so. 

An kwaso kayanta kaf a gidan Hilal, a daren jiya ya zo har gidan ya riski Abba a falonsa. Sun jima suna magana sannan ya tafi. A hirar Zulaihat din da Hajiya ta ke jin cewa hakuri ya ba shi. Hakuri bisa sakin ƴarsa da ya yi.

"Ke wane rashin hankali ne za ki kunna gas har abu ya ƙone haka? Gobara kike son jazamana? Ko mu dinma kashemu za ki yi?"

Ta waiga ta dubi Zulaihat s'ilin da ta sanya hannu ta kashe gas din.

"Hajiya ta ce ki yiwa Mijinki magana za'a je a yi jere don Abba ya ce a satinnan za ki tare. Ya kawo muƙulli."

Tana kaiwa karshe ta fice a kicin din, kawai sai Ramlat ta fashe da kuka. Haka to za su ci gaba da yi mata?

Indo ta risketa tana kuka, ganin ta dage wurin rarrashinta duk kuwa da haushinta itama ta ke, ya sa ta daukar wayarta ta bar kicin din. Abincin da ba ta ci ba kenan.

***
  Akwati takwas cif Aliyu ya shaƙe da kaya na gani na faɗa. Yakasai gidan su Hajja aka kai lefen kamar yanda Abba ya bada umarnin a yi.

  "Anya Rabi'atu wannan yaron ba ya cin haram a aikinsa? Wannan wane irin kaya ne ya shaƙowa yarinyarnan?"

Hajja da mamaki ya kasheta a zaune  ke wannan furucin cikin waya ga Hajiya. Hajiya ta yi murmushi mai ciwo.

"Ko ya ya dai Hajja ai ita yarinyar ta fi kowa sanin yanda aka haihu a ragaya. Tunda ya kawo lefe an karɓarmata shikenan. Ta je ta yi ta sakamishi."

"Kai Rabi, na rabaku da irin wannan fushin fa. Meyasa Khalid ya biyewa yarinyarnan bai yi bincike ba? Har da gwal a sarkokin."

"Hajja ina zuwa zan kiraki."

Hajiya na fadin hakan ta katse kiran. Ba wai don abin bai tayarmata da hankali ba, sosai hankalinta ya tashi. Yaron da aka ce a kasuwar ma ba wani mayar da hankalin a zo a gani yake ba. Ba ta son tunkarar mijinta da wannan batun, don ta lura yana cikin damuwar auren Ramlatun har lokacin. Wannan ta sa ta kira Munir. Kafin ma ta yi nisa ya katse zancen.

"Hajiya ke mahaifiyata ce. Don girman Allah kiyi hakuri ki bar min zancen Ramlat. Hajiya ki zubamata ido tunda kun mata abinda take so. Ku yi hakuri ku bi ta da addu'a idan da bukatar hakan. Ba ita kadai ku ka haifa ba, muna raye zamu share kukanku. Ki yi hakuri, ki sanya a ranki hakan ya zama alheri ba sharri ba."

Da wannan ya samu ya zame kansa daga abinda Hajiyar ta kawomishi, na bincike akan harkar Aliyu.

'Wane bincike bayan mai afkuwa ta afku? Komai ta fanjama fanjam!'

Ya fadi a kasan ransa.

***
  "Ai yanzu kin girma, kin mallaki hankalin kanki, ba kya bukatar nasiha daga gareni. Duk abinda kika aikata ga rayuwarki daidai ne."

Kalaman Hajiya suka shigeta sosai, ta cikin laffayar da Zulaihat ta naɗeta a ciki, kuka take. Ba ta san sadda ta bude lulluɓin ba ta karasa ta dafa cinyar Hajiyarta.

"Don  son Annabin Rahma s.a.w Hajiya ki yafemin. Ki yafemin ko zan ga haske a rayuwata. Na yi miki laifi, ki yafemin don Allah."

Zuciyar uwa mai rauni, ta cika da tausayinta. Tausayi na abinda take hangomata wanda ita ba ta hanga ba. Shaye-shayen da Abba ya ce Aliyu na yi ya tsayamata a ƙahon zuciya. Ta daure ta mike bayan ta zame jikinta.

"Ku wuce Uwani, dare  yana yi. Allah Ya bada zaman lafiya."

Ba tare da ta ƙara magana ba ta shige banɗaki, Zulaihat wacce ko a jikinta ta amsa da Amin kafin ta ɗago Ramlat.

"Mrs Aliyu mu karasa ga Abba ko?"

Ta riga ta ɗan kusan da biyu Zulaihat ke kiranta da hakan, suka shiga Abban na zaune saman darduma yana karanta Alkur'ani mai girma. Ya ɗago ya dubesu, tunda ya dora idanu akan Ramlat bai kifta ba.

"Ramlatu an fito?"

Yanda ya furta cikin taushi ya sanya zuciyarta kara narkewa. Ya yi ƴar dariya.

"To mene abin kuka? Yanzu kin zama matar aure. Komai ki ka yi, ko za ki yi ki sani cewa Allah Yana kallonki. Ki ji tsoronSa wajen gudanar da lamuranki. Ramlatu duniya da kike gani tana da faɗi, sai dai zuƙatanmu sun fi ta faɗin. Idan mun yarda da hakan, mun  cikata da alhairai masu yawa, mun yi irin aikin da Allah Zai farin ciki da mu. Mu zama cikin ceto AnnabinSa s.a.w. Duk isa da taƙamar mace, ba komai ba ce a wurin mijinta. Ki rike wannan, ki bi mijinki sau da kafa. Kar ki sake ki zama mai tona asirinsa."

Abba ya ci gaba da koro jawabai, ba Ramlat kadai ke kukan ba, hatta da Zulaihat kukan take. Kukan tausayin wannan uba mai matukar don ɗiyarsa da alheri, mai mafarkin ya ga ta yi aure a inda ba za ta taɓa wulakanta ba. Sai dai kash, burinsa bai cika ba.

"Nagode Abba, Abba kaima ka yafemin. Hajiya ta ƙi yafemin. Abba ka tayani roƙonta."

Nan take ya umarci Zulaihat ta kira Hajiya. Ta bi umarninsa sai gasunan tare.

"Na yafemata idan don haka ka kirani."

Ta tari hanzarinsa don tasan kafiya irin ta Ramlat da naci.

Murmushi ya yi.

"Mun gode Hajiyarmu. Ban riƙe ki ba a rai kinji Ramlatu? Tashi ki tafi dakin mijinki. Allah Ya yi muku albarka. Ya dauwamar da ku a dakunan da'iman."

Daga nan suka mike zasu fita, dakatar da su ya yi. Da kansa ya taso ya lalubo hannun Ramlat wacce lallenta na tun bikinta da Hilal shi ne a hannun, har baƙin ya soma gogewa. Alkur'ani mai girma ya sanyamata a ciki.

"Babu wani hasken da ya wuce haskenSa. Babu magani da kuma waraka face ta hanyar karantashi da kuma addu'a. Kar ki yi wasa da tilawarsa."

Wani kukan ta kara kecewa da shi, maimakon Abban ya koma mazauninsa, sai ya kama kafaɗarta ya yi mata rakiya har cikin motar da Aliyu ya turo. Iyayen Aliyu su na kallo, sannan ya koma cikin gidan zuciyarsa a karye.

***
_*MRS ALIYU*_
 
Ya kara jawota jikinsa ya rungume, kuka take sosai. Duk kuwa da cewar ta tsarkake jikinta ba ta bar jin radadi-radadi ba.

"Haba Baby, damuwa kike son na shiga ne? Sai kuka kike, ya zan yi miki ki daina?"

Ta soma ƙoƙarin tureshi daga  jikinta.

"Ni ka rabu da ni."

Ya yi murmushi gami da kara kankameta.

"Ni ba zan iya rabuwa da ke ba Baby. Ki yimin duk abinda kika san zai sa ki huce. Kinji?"

Ta turo baki, ya sa hannu ya shiga sharemata hawaye.

"Fadamin me kike son na yi miki a rayuwa kwatankwacin wannan farin cikin da kika ban, kinsan an ce yaba kyauta tukuici."

Ta tsinci zuciyarta da jin dadin kalamansa. Ba ta san sadda ta yi murmushi ba. Damarta kenan, ya kuma kamata ta yi amfani da shi kar ya wuce.

"Karatu nake son ka bar ni na ci gaba."

Ya rungumeta yana ƴar dariya.

"Wannan mai sauki ne Baby. Ki ajiye a ranki kin yi karatu kin gama, wannan ya zamemin kamar farilla, fadi wata bukatar."

Ta yi shiru, jin saukar dumin hawaye saman fatar kirjinsa ya sanya shi ɗago haɓarta yana dubanta.

"Baby, meyasa?" Ya yi maganar kamar mai raɗa. Ta sauke kwayar idanunta daga kallonsa.

"Sanadinka na shiga tarin matsaloli. Na jure dukkan wuya, na karya dukkan alƙawura, don Allah ka rikeni amana, ka bani kulawar da iyayena da dangina zasu aminta da zaɓina. Ina  son mu ba marar ɗa kunya."

Ya yi murmushi.

"Kina shakku a kaina ne? Ko kina kokwanto akan son da nake miki? To ki daina, har mai ɗa sai mun ba kunya a zamantakewarmu. Ki kwantar da hankalinki."

Ta yi murmushi, so da kaunarsa na ninkuwa cikin ranta. Nan kuma labarin ya sauya.

***
  Soyayya ce tsantsa ke gudana a gidan masoyan, Aliyu dakyar yake iya fita kasuwa ya ga yanda yaransa ke tafiyar da lamura. Iya soyayya da shagwaɓar Ramlat har mamaki yake ba shi. Hakan ke kara susutar da shi. A wannan lokacin yana takatsantsan da shan dukkan wani abun maye a gaban Ramlat. 

   Sai da suka cika sati biyu da aure sannan suka shirya zuwa gaida iyayensa. Ta haɗe cikin leshinta maroon ta yafa farin mayafi sai takalmi da jakarta suma farare. Ta yi ado daidai gwargwado, ta ciko kadan, ramarta ta ragu sosai. Hakan ya ƙaramata kyau.

  "Babyna kin yi kyau kamar mu fasa fitar."

Ya fadi yana rungumo ƙugunta. Ta watsamishi kallon soyayya ya kama saitin kirjin gami da lumshe idanu yana murmushi.

"Ahh, kasheni za ki yi ko?"

Dariya sosai ta shiga yi ta kwace jikinta.

"Muje don Allah."

Ya kamma hannunta suka nufi motarsa. Tafiya suke suna jinsu kamar a gajimare. Wakar Nazifi Asnanic mai taken Jamila da Jamilu shi ke tashi a motar, hannunsa na dama cikin tafin hannunta. Ji take kamar ba ta da wata matsala da ta yi saura a duniya, kamar wata sarauniya haka take ji musamman yanda Aliyun ke rera wakar yana dubanta jefi-jefi. Har suka iso wakokin soyayya daga Asnanic da Nagudu kawai suke ji.

"Mun iso Madam."

Ta ɗan harareshi da wasa sannan ta yunkura da zummar maida takalminta da ta cire a zaman motar. Kafafunta suka taka wani dunkulallen abu kamar takarda. Ta sa hannu ta dauka sa'ilin da ta zura takalmin. Daidai sadda Aliyu ya bude mata murfi ta fito. Kirjinta ne ya buga, ko ba ta shan sigari, ta san wannan dai karan sigari ne.

"Mene wannan?" Ta tsinci kanta da watsa tambayar duk don ta samu tabbaci. Yatsuntsa ta ji ya sa ya karba gami da yin cilli da shi yana tsaki.

"Wannan banzan ne, G Baba ya sha min a mota."

Ta ji hankalinta ya kwanta, ta sauke ajiyar zuciya.

"Muje Baby, yau Kakus za ta ganki."

Ya karasa zancen da riko hannunta su soma tafiya cikin son basarwa. Har ga Allah ta yarda da zancensa.

***
  "Masha Allah, ashe kishiyartawa itama ba baya ba kamar wata balarabiyar Sudan."

Dariya Aliyu ya yi, itama Ramlat murmushi ta yi gami da ƙara sunne kai. Abulle kuwa har ranta ta ji tana son Ramlatun, ta dage akan sai ta ci abinci, a dole ta tsakuri tuwo miyar agushin da ta diremata. Daga nan suka fice sashin mutan gidan. Jikin Ramlat ya yi sanyi matuka da irin tarbar da ta samu a gurinsu, ta dauka zasu kaunaceta kamar yanda Abulle ta nuna, sai dai abin ba haka ba.

Bangaren karshe da suka shiga, bangaren Justice. Aliyu ya nufi falon Justice yayinda ya ce ta shiga ciki. Shi kam banda ma dole da Abulle ta yi mishi da ba zai shiga ba. Hajiya Maryam ta kalleta ta watsar, tun kan su shigo labari ya zo mata daga bakin Autar Kawu AbdulRashid, Hannatu. 

Sanye cikin hijabi ta fito daga dakinsu don amsa kiran Mamarta. Ta ci karo da Ramlat zaune ƙasan kujera ga Mamar ta kurawa talabijin idanu abinta.

"Muhibbat, ga matar Aliyu ta zo a gaisa."

Kusan lokaci guda suka kalli juna, kowannensu kallon ƙurillah yake yiwa ɗan uwansa. Kowacce so ta ke ta gano abinda ta fi ƴar uwarta.
Bangaren Ramlat, kammanin Aliyu  take gani a fuskar Muhibbat. Shakka babu ba ta hango abinda za ta gwada mata ba.

Hakanan Muhibbat, sai dai ta ce da Ramlat din baƙar fata a kanta, banda wannan ba za ta ce ga abinda za ta gwada mata ba itama.

  Murmushi suka saki a tare, murmushin da ya fi zama na yaƙe. Kowanne na kokarin danne abinda ya ke ji game da ɗan uwannasa.

Suka gaisa a mutunce sannan Muhibbat ta koma ɗakinta. Rufe kofa ta yi ta sauke ajiyar zuciya. Ya dace ta shafe komi a yanzu itama ta ci gaba da gudanar da rayuwarta.

A bangaren Ramlat, sai ta hango wani sanyi da taushin zuciya a wurin Muhibbat din, ba ta taɓa zaton ma za ta jure ganinta koda da sakan daya bane. Sai ta kasance mutan gidan ga dukkan alamu su ke tayata kishin.  Tana nan zaune har Aliyu ya turo a kirata, ya dubi kwayar idanunta yanda ya sauya. Cikin sauri ya tallafi fuskarta.

"Baby meke faruwa? An fadamaki wata maganar ne?"

Ganin hanyar baranda ce ta shiga falon Justice, sannan hanya ce ta jama'a yasa ta kauda fuskarta tana murmushi.

"Ba komai. Mu tafi."

Sauke ajiyar zuciya ya yi.

"Na dauka wani abin suka fadamaki yanzun na shiga na nunamusu ainahina."

Mamakin kalaman ya sanya ta dubansa, sai dai tuni ya soma tafiya yana bata umarnin ta biyoshi.

'Kin manta sunansa Aliyu? Gadanga ƙusar yaƙi. Ba dai zuciya ba.'

Faɗin wani bangare na zuciyarta. Ta samu tarba mai kyau kamar yanda ta zata, don dukkan dattawan sun karɓeta hannu bibbiyu da salama. Banda mata da sauran yan uwan Aliyu, wasu ƴan mata ma tana jin sadda suka saki wata shewa da guɗa, ta kuma san da ita ake.

A mota shi ke ta zuba hira banda ita, ta karanci abubuwa da dama a gidansu Aliyu.

Amman kuma suna isa gida ta bar zancen a gefe guda a ƙasan ranta saboda soyayyar da Aliyu ya shiga nunamata mai kashe duka lakan jiki.

***
  Tsakaninta da iyayenta sai waya, za ta kira su dauka a gaisa. Yaya Munir kuwa ta tabbatar blocking dinta ya I daga kiransa don a farko sai ta jira ya yi ta ringing ba zai ɗaga ba, yanzun kuwa gaba daya ma ta bar samunsa. Amrah kuwa ƙarara ta fito ta yi mata kaca-kaca akan ba ta son kiranta. Itama karshe ta nunamata tana da zuciya, ta tattara ta watsata a kwandon shara.

Sakamakon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login