Showing 210001 words to 213000 words out of 226732 words
duk suka kwalalo idanuwansa da fatar duk ta tattare saboda girma ya ja, a ransa ya ce tsoffin banza kawai. A fili kuwa ya yi wata arniyar dariya wanda gaba daya hankalinsu ya kwanta.
"Ai wannan auren ba inda zai je, zan miki aikin da shi yaron da kansa zai tattaro ya dawo wajenki, ita kuma yarinyar zan mata aikin da za ta shiga bariki ya daina ganinta da daraja. Hakan ya yi?"
Wata dariya Hajiya Zeenat suka sanya har da tafawa ita da Hajiya Batool.
"Gora mai gayya mai aiki! Shiyasa duk inda naje sai na dawo gareka nake ganin daidai a lamuran rayuwata (Allah Ya ganar da masu hali irin naki). Hakan ya yimin daidai, dama nafi tunanin kamun kan yarinyar ne ya rinjayi Hussein ban da haka ban ga wani kyau a tattare da ita ba. Na ba ka wuƙa da nama."
Ya yi dariya.
"Hajjaju kenan, sai dai wani hanzari ba gudu ba, aiki ne mai tsauri domin sai na haɗa da tattaunawa da Sarkin bakaƙen aljanu, kinga kenan sai an yi zubar jini na dabba da jaririn mutum kafin a cimma yiwuwar aiki. Don haka aikin zai kama miliyan biyar."
Hajiya Batool ta kalleshi a hargitse kafin ta dubi Hajiya Zeenatu, ta ga alamar ko a jikinta. Asalima ba ta sani ba, yanda Hajiya Zeenatu ke ji a yanzu ko don ta dauki fansa, za ta iya kashe ko nawa ne domin hankalin Hussein ya karkato gareta karo na biyu kuma wanda ta ke fatan ya zama na mutu ka raba.
"Na shirya, na shirya ba da koda duk abinda na mallaka ne muddin Hussein zai dawo gareni."
Gora ya ji kamar ya daka tsalle, shakka babu ya samu kudaden nan zai gudu ne ya bar garin a nemeshi a rasa, dama har yau shi kansa bai san asalinsa ba, daga almajiranci ne ya zama gawurtaccen Bokan Mata. Zai sauya ƙasar gaba ɗaya ya je ya kama wata sana'ar mai kauri. A fili kuwa cikin dakiya ba tare da ya nunamata komai ba ya amsa.
"Shikenan, sai na jiki."
Daga nan ya karkata ga Hajiya Batool, itama dai Miliyan Biyu ya nema, nan da nan ta hau zufa sai dai shaiɗan wanda ya kaɗamata ganga da kuma taimakon zigar Hajiya Zeenatu ta yarda ta kuma amince za ya san abin yi. Da wannan suka rabu akan nan da kwanaki uku za su dawo su damƙa masa kudaden da ya bukata.
A ɓangaren Hajiya Zeenatu, ta yanke siyar da A&Z ga wani hamshaƙin matashin ɗan kasuwa wanda ya jima yana muradin wajen yana son ya ƙara ƙawatashi ya haɗa da filinsa da ke a gefen wajen ya gina Park na wasan manya da yara ma. Amma fir a lokacin ta ƙi yarda bisa shawarar Hussein da ya ce ba hannunsa idan ta yi hakan. Yanzu kuwa ta shiryawa hakan. Dama a yanzun shagonta na siyar da gwala-gwalai da manyan fashion ya ja baya don ta jima ba ta fita Dubai siyayya ba hakanan ba wani balance na kirki Manajan wurin ke kawomata ba. A ranta ta kudurta siyar da shagon ta bude babban boutique na kayan jarirai da na yara.
***
"Damuwa ce ta ke neman illata tunanin yaron, sai kuma yunwa da ke dawainiya da shi wanda ya haddasa masa jiri. Muna tsoron kamuwarsa da hawan jini, don haka don Allah Baba a yiwa yaronnan abinda ya ke so."
Wannan bayanin na Likita ya kara ɗaga hankalin Modibbo. Gumi ya shiga tsastsafowa daga goshinsa. Yan da labarin komai daga bakin Uwargidansa, yana da labarin cewa soyayyar Hafsatun Dada ke dawainiya da kwakwalwar Taheer. Bai san kuma ta inda zai soma magancewa ɗansa matsala ba don shi da kansa kunyar zuri'ar Dada ya ke ji. Ga yan uwansa sun juyamasa baya, kowa ya yi tirr da baƙar zuciya irinnasa da ba ta iya yafiya ba alhalin ma tun asali ba abinda Amina da Aminu suka aikata garesu, bisa tunzurawar Innarsu ce ta sa suka tsangwamesu. Haka ya amsawa Likita da cewar zai bincika damuwar Taheer sannan ya mike ya fita. Su Anti Amarya da ke tsaye suka zubamasa idanu har ya shiga ɗakin da aka kwantar da Taheer. Bacci ya ke sosai, ya zauna gefen gadon ya tsuramasa ido.
"Ta ina zan soma yi maka maganin matsalarka alhalin nima ina da tarin laifuka a wurin bayin Allahnnan? Ka yafemin, ka bar ni na soma zuwa na gyara nawa ɓarnar kafin a yi maganarka."
Ya furta cikin harshen fulatanci, shi kadai ya ke zancensa don Taheer bai ma san yana yi ba, a karshe ya mike babu kuzari ya fice daga asibitin gaba daya ba tare da ya cewa matansa da yaransa dake wurin komai ba.
***
ADAMAWA...
Wankan da ta yi na musamman ne a daren ranar talata, ba don komai ba sai don sanin da ta yi Hussein babu alamar sassauci a ƙwayar idanunsa. Ya lura da sallolin da ta yi a ranar, wannan ya sanya ya ke faman rawar ƙafa. Koda ya fita, zuma ta dauka ta sha sosai bayan ta wuni a ranar tana kama ruwa da ruwan ɗumi. Idan da sabo har ta saba don zai wuya ka ga Ramlatu na amfani da ruwan sanyi a wannan wuri.
Kayan baccin ma da ta sa na musamman ne, riga da dogon wanda marasa nauyi. Rigar mai hannun vest sai top dinta mai dogon hannu. Babu wani underwear da ta sanya a ciki. Ta tabbatar daga kallo ɗaya Hussein ɗinta ba zai iya dauke kansa ba. Duk da Top din rigar da ta ɗora hakan bai hana komai bayyana ba. Ta ƙara mulke jikinta da turare, sai da ta kammala ta tabbatar babu inda ba ya tashin ƙamshi a jikinta sannan ta fito falon inda ya ke zaune ya maida hankali ga danna Laptop, AlHassan yake aikawa credentials dinsa ta email kamar yanda ya buƙata. Koda rashin haske a falon, hakan bai sa hasken tv gaza haskakamasa ita ba. Ya nemi nutsuwarsa na ƴan sakanni amma ina! Sun yi hannun riga, kawai sai ya tsinci hannunsa da rawa, ba don Allah Yasa ya kammala aikawa ba to shakka babu zai haɗa da shirme. Har ta karaso ta zauna a nesa da shi kaɗan bai iya ɗauke kai ba, ba tare da ya tunanin saƙon ya je ko bai je ba, ya kashe Laptop din kawai ya rufe. Mikewa ya yi ya kashe tv, sannan ya karaso, lalubo inda ta ke kawai ya yi ya ja ta jikinsa. A haka ya karasa dakin da ita.
***
WASHEGARI..I just published "BABI NA SITTIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1028701620?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=0Ip%2BQlXDoaoxyM7eqonDyl6cCNMjLR7b13cfWz0PO6rluIvQeUuu1jHeHigNXBE4IV%2Fm159PS%2BDsIeqGDHiIXMY5fTO3p4OINuf3vYe6Dx12trWJCYsK2knobbhhwa9y
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
64)
_*Assalamu alaikum yan uwa Barkanmu da wannan lokaci. Ku yi hakuri kun sha jira, da yardar Allah kiris*_
Wani ƙaton enlargement ne na ɗaya cikin hotunanta da ya ke da su, ta karkace kai tana murmushi har fararen haƙoranta sun fito, sai wani ƙaton kwali da ba za ta iya cewa ga abinda ke ciki ba sai kuwa akwatuna jere reras har guda sha biyu. Ta kai dubansa gareshi, murmushi ya ke sakarmata sosai. A hankali ya matso ya kama hannunta suka karasa cikin falon. Wani ƙaramin kati mai adon heart da fulawoyi ne ya soma daukar hankalinta don haka ta sa hannu ta ɗauka ta bude.
_*From the moment I first laid eyes on you, I knew you were a perfect match for me. I love everything about you Heart.*_
Ta juyo ta dubeshi, yana tsaye kawai hannuwansa cikin aljihun wando yana zubamata murmushi. Da ido ya mata nuni akan ta ci gaba da buɗewa. Ba musu ta kai durkusa ta kai hannu ta bude wani karamin gida na zobe, ai kuwa zoben ne mai matukar sheƙi, ya fi mata kama da na azurfa. Ya yi masifar burgeta, idanunta ya ƙara kaiwa saman wani kwalin karami da aka ɗaure bakinsa da igiya mai ƙyalli, ta bude, ganin mukullin mota kawai sai ta ɗago ta dubeshi, idanunta nan da nan suka cicciko da kwalla. Ta ajiye kafin ya taimaka mata da bude akwatinan, kaya ne maƙil, kowanne da set dinsa. Yanda dai ku ka san lefe irin na budurwar yarinya don wannan ma ya fi na budurwar kyau da tsari. Ko iyaka haka aka tsaya a na budurwa sai sam barka. Laces, atamfofi, mayafai, shadda, yadika, abayoyi da dukkan sauran kayayyakin shafa da sarƙoƙi ba abinda ba'a haɗa ba. Wannan ya bata tabbacin ba yau ya soma haɗawar ba. Bayan sun mayar da komai ta dubeshi, tuni hawayen da ta ke dannewa sun zubo. Ya kai hannu da sauri ya ɗaukemata su. Ba ta bar kallonsa ba ta soma magana.
"Allah Ya saka da dumbin alheri, na.."
Ya kai yatsa saman lebbanta.
"Shii...Ba kalar godiyarnan nake so, buƙatar fin haka nake. Kar ki manta kuma haƙƙi ne na maki sutura da ma duk abinda bai fi ƙarfina ba wanda zai farantamaki. Kin cancanci fiye da haka."
Ya ƙarashe gami da ɗagamata gira. Kunyar ta nema ta rasa, kawai sai ta juyo gaba ɗaya ta rungumeshi har bayansa na jingina da kujerar. Ya kuwa ba ta kyakkyawan mazauni a kirjinsa, kafin kuma kiɗa ya sauya salo.
***
KANO..
Wutar da ta tashi a wani gida dake unguwar ya sa mutane duk suka fito, cikin dare ne da misalin karfe biyu da mintoci. Banda salati da kokarin kashewa ba abinda ake yi. Da yawa suna aikin kashe ta amma fadi suke don kawa kar wutar ta haɗa da nsu gidajen ne amma banda haka dama sun gaji da Maigidan, bokancin da ya ke yi musu a unguwa yana tare matasa abin ya ɓaci.
Gora kuwa yana daga ciki banda ihu da neman agaji ba abinda ya ke yi, ya rasa ta inda aka yi wuta ta soma cin gidansa, babban abinda ya ƙara haukata shi neman jakar kudadensa da ya yi ya rasa, ga yaronsa ba ya nan. Wannan ya ɗan ankarar da shi cewa cin amanarsa ya yi. Nan fa ya haukace, tun akwai hanyar ficewa har ya zamana ya rasa ta inda zai bi ya tserar da rayuwarsa daga halaka. Haka dai kafin mutane su yi nasarar tsayar da wutarnan, Gora rai ya yi hali.
A ɓangaren yaronsa kuwa har da shi cikin masu kokarin kashe wuta kamar gaske, har ya tafi sai ya yi tunanin gwara ya tsaya ya tabbatar da mutuwar Gora kafin ya gudu, idan kuwa har aka yi rashin sa'a ya tsira, to ya tabbatar duk inda ya shiga a duniya ba zai tsira daga ta'addancin Gora ba. Ganin an fito da Gora a mace ya sanya ya ji wani sanyi a ruhinsa, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya hau mashin dinsa ya wuce can filin makaranta inda abokinsa Jabir da suke kira da Jabson ke jiransa su wuce. Yana zuwa suka cafke su na dariya. Nan ya ba shi labarin komai, ya dubeshi da kyau.
"Jakar fa?"
Jabson ya yi wani malalacin murmushi gami da mishi nuni da aji. Ya bubbuga kafadarsa suka dara kafin ya shige gaba zuwa ajin, sai dai shigar ya yi daidai da sokamishi wuƙa a baya ta ɓullo ta ciki, Jabson ne. Sai da ya tabbatar ya kashe shi har lahira sannan ya ɗauki jakar ya tsallakeshi. Mashin dinsa ya haye ya bar wurin a miliyan. Shi da garin Kano kuma sai nan da wasu shekaru.
Misalin ƙarfe sha biyu na rana, labarin ƙonewar Gora da tsintar gawar yaronsa ɗan aikensa Salmanu, ya karaɗe unguwar. Ko'ina maganarsu ake yi, ga Jabir abokin Salmanun da aka nema sama ko ƙasa aka rasa. Dama almajirai ne, wannan yasa aka shiga tunanin ko sace Jabir din aka yi bayan kashe Salmanu. Daidai sadda ake wannan hargitsin, motar Hajiya Zeenatu ta tsaya. Tun kafin su fito cikinsu ya ɗuri ruwa ganin yanda gidan Gora ya zama kango lokaci guda.
"Ke Zeenatu, anya gidan ne?"
Hajiya Zeenatu ta kasa amsawa Hajiya Batool, kokari ta yi kawai ta yi parking suka fito, yaran almajirai na ciki su na ta ɗage-ɗage ko za su yi tsintuwa. Daga ƙasan bishiya wasu samari suka hangosu. Ɗayan ya ce.
"Waɗannan su ne na goma sha takwas kenan, wannan mutumin fa yana wankar mata, yanzu haka ma wani mugun aikin su ka zo ya musu."
Wani ya mike.
"Bari mu je mu ji, idan ma shi suka zo nema mu ba su labari ko Allah zai sa su tsorata da lamarin rayuwa su shiryu."
Ganin haka sauran ma suka mara mishi baya don ba za'a yi babu su ba.
"Hajiya wurin Gora ku ka zo?"
Hajiya Batool da Zeenatu wadanda sun rasa ta ina za su soma, su ka dubi saurayin kusa a tare suka amsa da eh.
"Ayya, ai a daren jiya gobara ta cinye gidansa tas babu abinda ya tsira. Shima ya mutu ɗazunnan aka dawo daga binne abinda aka tsinta na gangar jikinsa. Shima dai yaronsa Salmanu an tsinci gawarsa a filin makarantar Firamare an kashe shi."
Hajiya Zeenatu sai da numfashinta ya bar motsi na wani lokaci kadan, ta kasa magana sai kawai ta ɗora hannu a kai ta fashe da kuka. Jiki na rawa Hajiya Batool ta ce.
"Shikenan Gora ya mutu dai ku ke nufi?"
Suka bisu da kallo kamar taɓaɓɓu, kusan ma duk kalar ruɗewar da sauran matan da suka zo suka yi, bai kai na wadannan Hajiyoyin ba. Mai magana ɗazu ya matso.
"Eh ya mutu. Duk wani mugun aiki da ya ke shukawa ya kare. Ya koma gidan gaskiya inda zai girbi abinda ya shuka din. Kuma ya kamata ku ji tsoron Allah ku tuba daga tafarkin shaidan tun kan lokacinku ya ƙure. Idan har ba so ku ke yi kuma ku zama tarihi ba, ku tafi a wofi."
Hajiya Batool ba ta ce uffan ba balle Hajiya Zeenatu da ke faman kuka, ashariya kawai ta ke narkawa Gora kamar ta mance da cewar ya mutu. Har dai dakyar Hajiya Batool ta maidata mazaunin kusa da direba ita kuma ta tuƙa motar suka bar layin, yara duk an cika ana binsu da kallo.
Haka suk isa gidan Hajiya Batool hankali a matukar tashe. Ita kanta Batool din dakiya kawai ta fi Zeenatu, amma ba ta ga laifinta ba don kuwa ta fi ta zazzage bakin aljihu a wannan harkar. Nutsuwa ta gagaresu, Hajiya Zeenatu kawai zama ta yi kamar kayan wanki a saman kujera tana ci gaba da surfa ruwan bala'i ga Gora da ya jima a gushewa.
"Yanzu shikenan Hussein da Ramlatu haka zan zuba ido ku cigaba da cin amanata?! Shikenan wai hakan na nufin sun yi nasara?! Wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na ga bayan Ramlatu da Uwarsa! Sai Hussein ya dawo karkashin ikona. Ba zan dauki wannan dumbin asarar ba! Batool nemomana Maryama a waya! Zuwa Nijar ya kama mu, ya zama dole mu kara gwada aikin Bokansu. Buzaye ne!Za mu yi nasara, za mu yi nasara."
Ta na maganar kamar wacce ta samu taɓin kwakwalwa. Itama Batool ta gane zuwannasu Nijar din kawai shi zai zame musu mafita don haka ba musu ta zaro waya ta dannawa Maryama kira lokaci guda kuma tana sharce gumi. Magana sosai suka yi, ba ta ɓoyemata duka asarorin da ya hau kansu ba. Maryama ta jajanta musu sosai karshe ta ce musu za ta yi musu booking na layin ganin Boka Buzu, kawai dai da zarar sun saka ranar zuwa su fadamata.
"Gobe ma zamu taso jibi mu iso."
Hajiya Batool ta katse ta da gaggawa, ƴar dariya Maryama ta yi kafin ta amsa da toh hadi da musu fatan zuwa lafiya.
Washegari kuwa da sassafe suka kama hanyar Nijar, direba ne ya kaisu. Yardaddan direban Hajiya Batool, Audu. Wannan karon ma sun tattara maƙudan kudade don ita Hajiya Zeenatu ba ta bi ta kan Manajanta ba, ta nemi manyan gwala-gwalanta har biyar ta shiha kasuwa ta siyar. Itama dai Hajiya Batool sai da ta haɗa da siyar da kadara, kowaccensu ta taho cike da burin samun abinda aka je nema. Idanunsu ya rufe, gani suke yi tamkar ga su ga burinsu har ya cika tsabar imanin da suka yi da abinda zai kai su.
Wuraren karfe sha biyun rana da mintoci suka iso Damagaran, anan suka kwana washegari da sassafe suka kama hanyar Niamey. Sun sha tafiya sosai kafin su isa Niamey, kai tsaye suka kira Maryama a waya. Da kwatance da tambaya suka iso katafaren gidanta wanda ya sha kayan alatu. Ta musu kyakkyawar tarba, ba kamar wancan lokacin ba, wannan karon gidanta ne na kanta ba na Maigidanta ba. Tun bayan rasuwar Mijinta ta siya gida inda ta ke harkar safarar yara zuwa Ƙasar faransa da ma wasu ƙasashen yawon bariki. A yanzun da su ke zaune a falon suna cin abinci bayan sun yi wanka, ba tare da kowaccensu ta damu da kallon gabas ba, ƴan mata ne ke safa da marwa cikin shiga mai ƙayatar da masu iri halinsu na bin maza. Babu wacce ba ta fito ta gaida baƙin Madame dinsu ba, a karshe Hajiya Zeenatu ta kora ruwan sanyin da aka ajiyemusu ta dubi Maryama.
"Kin tabbatar dai goben babu fashi a zuwanmu wurinsa ko?"
Wani murmushi Maryama ta yi ta dauki tuffa ta gutsira.
"Haba Hajjaju, zan maki ƙarya ne?"
Ganin haka Hajiya Zeenatu ta saki fuska.
"Ba haka nake nufi ba, kin dai ji komai ai daga bakin Batool, banda haka nan da kike ganina duk sadda zan runtse idanu ba abinda nake haskowa sai Mijina tare da waccan karamar karuwar. Gani nake duk kwana daya tamkar shekara ce."
"Ki sa ranki a inuwa, za ki sha mamakin yanda komai zai lalace. Mijinki ya dawo kamar kwai a hannunki sai yanda ki ka yi da shi."
Dariya suka yi har da cafkewa, nan da nan zuciyoyinsu suka ɗan waske sai dai ko ya ya suka tuna asarar da ta hau kansu na miliyoyi sai sun tsinewa Gora. Basu ma batun nemar masa gafara.
Kamar yanda Hajja Maryama ta fadi, hakan ce ta kasance. Washegari bisa jagorancin yaronta sai dai ba wancan na farkon da ya taɓa yi musu rakiya ba, suka rankaya gidan Bokansu Buzu. Koda suka tsaya babu layi sosai, kamar wani layin asibiti haka aka basu kati karami mai dauke da numero (number). Wannan dai ba ɗayan bane, wani sabon Boka ne gagarumi da Maryama ta tabbatar musu cewa aikinsa wane