Showing 75001 words to 78000 words out of 226732 words

Chapter 26 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12452

gaba daya ya ji wani nadama ta mamayeshi. Idan ance akwai ranar da zai ji kunyar mace zai rantse ƙarya ne.

"Wannan ba damuwata ba ce. Damuwata haihuwar da nake yi da kai. Aliyu ba don ina tsoron halakar da zan faɗa ba wallahi ina maka rantsuwa da Allah sai na zubda abinda ke cikina. Sai dai na sani laifi ne zan kara akan kuskuren da nayi tun farko na auren mutum irinka wanda bai san darajar kowa ba sai kansa! Kai har kaima ba ka san darajarka ba! Ba ka san darajar da Allah Ya yi maka ba. Ba ka taɓa godemaSa ba ta hanyar aikata nagari wanda kowa zai gani ya sakamaka albarka. Mun haihu da kai kuma ga wani rabon Aliyu, idan a baya ba ka da wani da ka ke jin kunyarsa ai a yanzu ko don darajar yaranka wani abin za ka kiyaye. Wane ɗa ne zai farin cikin kasancewarsa ɗanka? Ummi idan ta isa aure kana tunanin manemanta ba zasu gano tarihin ubanta ba su fasa? Shikenan kai babu wani abu naka nagari, shikenan duk inda za'a je a tambayi tarihinka kai mutumin banza ne? Aliyu meyasa ka rufemin kai waye, meyasa ka ɓoyemin munanan halinka ka nunan kai nagari ne? Kaicon abinda ka sani na aikata, kaicona da na zaɓi na saɓawa iyayena akan mutum irinka. Ba duniya ba, daidai da ni kaina tsanar kaina nake idan na tuna irin tijara da fito na fiton da nayi da ƴan uwana akanka. Yanzu gashinan ina girbar abinda na shuka. Wallahi ban kyautawa kaina ba."

Ta cure wuri guda gami da saka kanta cikin cinyoyinta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, idanunsa suka kaɗa suka yi ja, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi, a gefe guda kalaman Ramlatun suna mishi zagaye cikin ƙwaƙwalwa da zuciyarsa. Ummi kuka take yi ganin yanda uwarta ke kuka, Ramlat ta kasa ɗago kai balle ta karɓe ta. Cak ya mike ya fita kafin ya dawo ya yi zaman dirshan a gabanta, har sannan kansa ciwo yake kamar ya kife a wurin.

"Kiyi hakuri Baby, kiyi hakuri."

Ɗago kai ta yi tana kallonsa da ɗan murmushi. Majina ta ja.

"Um um Aliyu, ai kamata ya yi muyi yanda muka saba, ka kamani ka jibga, ka kamani ka zagi iyayen da suka kawoni duniya. Iyayen da na bijirewa umarninsu a kanka, na guji zaɓinsu duk domin na faranta maka. Idan yau ka zagesu waye ya bada ƙofar? Gani kake ni na baka ƙofar ka yi musu duk abinda ka so, ka fadi dukkan wasu bakaken kalamai a kansu. Toh Aliyu naji ni ce, amma na dauka idan so da kauna na gaskiya ne, karen gidanmu ma sai ka girmamashi balle kuma wadanda suka yi silar zuwana duniya? Na gaji, Aliyu na gaji. Aliyu idan kana sona dagaske, kana kaunar Allah da ManzonKa s..a.w, kana kuma kaunar iyayenka ka sauwakemin na je na yiwa iyayena biyayya. Ka sakeni na je nayi auren da martaba da darajata za ta..."

"Ramlatu!" Gaba daya suka kai duba ga bakin ƙofar, Baba Dakta ne a bayansa Amrah da Umma. Ya ƙaraso ciki da sallama suka amsa. Aliyu ya mike ya gaidashi, Amrah sakin baki ta yi tana duban hawayen da Aliyu ke fitarwa. Baba Dakta ya amsa gami da yi mishi sannu da jiki. Daga nan ya gaida Umman Amrah cikin girmamawa. Itama ta amsa ta mishi sannu.

Bayan sun zauna ya dubi Ramlat.

"Kina cikin hayyacinki kuwa? Mijinki kike cewa ya sakeki? Kinsan zunubin da kika kwasa sanadin wannan furucin? Kar na ƙara ji, duk tsanani yana tare da sauki musamman idan bawa ya miƙa lamarinsa ga Allah. Kar fa ki manta kina dauke da juna biyu, wannan damuwar sai kin daina sakawa ranki. Kinji ko?"

Ta gyada kai tana share hawaye wasu na zubowa. Amrah mai saurin kuka har ta soma tayata. Baba Dakta ya mike suka fita tare da Aliyu. A waje ya yi mishi dukkan nasiha ya kuma kara da cewar ya riƙe amanar ƴarsu da suka damƙamishi. Aliyu ya yi godiya don ko ba komai ya taimaka masa daga daurin dabaibayin da Ramlatu ta yi mishi, yasan ba don shi ba haka zasu yi ta ja in ja akan ita sai ya saketa.

***
  Ranar da aka sallami Aliyu ya dawo gidan, tuni dama Ramlat ta rigashi dawowa. Sosai kuma likita ya gargadeshi akan shaye-shaye da illolinta.

  Kwanakin da suka biyo baya suna faruwa ne sama-sama ga mutanen gidan.  Duk kokarinsa na shawo ka Ramlat abin ya ci tura, ya kasance ba ya fita yawon dare, idan ya shigo gida da yamma shikenan sai dai ko masallaci da yanzun ya soma zuwa sallah. A baya zuwan bai dameshi ba, ya gwammace ya yi sallarsa a daki. Ta yi faɗan har ta gaji ta bari.

Wataranar Asabar ta tashi tana son ziyartar yayyunta, gidan Munir ne ba ta jin za ta iya takawa  tunda ya nuna ba zai iya yafemata ba. Ta tabbatar idan ta je duk abinda ya yi mata ita ta kai kanta.

Tun safe ta lura ba shi da niyyar fita, wuraren karfe goma ta cimmasa a daki. Kwance yake yana juyi, kwanakinnan tana lura da shi a fisge. Yana cikin damuwa, girki ma idan ta yi bai fiye ci ba. Ga yawan shan Panadol da ya shiga yi kusan kullum ciwon kai.

Kallonta yake tun shigowarta dakin sai kuma ya ja guntun tsaki ya kauda kai.

"Ina kwana." Bai amsa ba, bai kuma kalleta ba. Ta haɗiye ta kara gaidashi.

"Ba zan amsa ba! Ki rabu da ni idan ma mutuwar ce na mutu Baby! Ya ku ke so mutum ya yi? Me kuke so ya zama?! Ance Aliyu dan iska ne kuma mashayi! Yanzun kuma da Allah Ya taimaka ya soma kokarin gyara rayuwarsa, nan ma bai burge ba! Kin juyamin baya ba kya shigowa inda nake sai dai ki yi girki ki dankwafarmin ki shige daki saboda mayunwaci ne ni! Ke haka Allah Ya ce ki yimin? Haka Ya ce ki yiwa Mijinki?!"

Ya na kaiwa nan ya mike zaune gami da jan tsaki kafin ya riƙe kansa da bai bar sarawa ba.

  Ta yi mishi ƙurr da idanu tana kallonsa kafin ta nisa.

"Ka saka a ranka ba don mu kawai za ka gyara ba, saboda karan kanka da kuma Ubangijinka. Ba mu da wuta ba mu da aljanna. Nayi kuskure, ka yi hakuri."

Ganin ta sauko yasa shima ya sauko ya lallaɓa don dama neman shirin yake, ya gaji da zaman gabar. Sai da ya biya bukatarsa kafin ya bata umarnin ta shirya da kansa ma zai sauketa gidan Zulaihat din. Wannan ya kara tabbatarmata dagaske Aliyun ya soma kimtsuwa.

Ta shirya cikin wata atamfarta da ta ware cikin sabbin da za ta dinga fita unguwa, ta shirya Ummi cikin riga da wando ƴan kanti ɗaya daga cikin kayan da Abba ya siyamata. Ta yiwa gashinta ado da ribbons kala-kala ya yi mata kyau.

Duk wanda ya gansu yasan suna cikin farin ciki. Har kofar gidan Zulaihat ya kai ta, suka yi da shi za ta je gidan Rafee'ah a can zai isketa ya ɗauketa. Hakan ya sa ya bata ɗari uku ya riƙe dari biyunsa, a cewarsa ita kenan a aljihun, dari biyar.

***
Kallonta Zulaihat take har Ramlat ta gaji ta yi magana.

"Wai Maman Khalifa lafiya?"

"Kin rame ne, kuma kamar dai kina da ciki."

Ta kauda kai a kunyace ta dai daure ta amsa da eh.

"Ciki dai Ramlat? Yanzu ba ki ji shawararmu kin yi family planning ba?"

Zulaihat ta furta don takaici bai sa ta iya ja bakin ta yi shiru ba. Ramlat ta kasa magana ta yi shiru kawai sai hawaye.

"Tab, Allah Ya kyauta to. Ya raba lafiya."

Nan ma kasa maganar ta yi.

Ganin kamar Ramlat din batun cikin na tada hankalinta yasa Zulaihat ta barshi suka shiga hirar bikin da ya taso na su Naja'atu da su Maryam jikokin Hajja. Su biyar cif za'a aurar nan da wata biyu.

"Ki dai samu ya yi maki koda anko ne koda bai bada ma gudunmuwa ba, ke sai ki duba idan kina da hali ki yi. Sannan don Allah ki dinga cin abinci sosai ko za ki ɗan maido jikinki kar a yi ta yawo da ke a cikin taro."

Ta gyada kai.

Sai wuraren karfe hudu ta nufi gidan Rafee'ah. Ita kanta ta yi mamakin ganin Ramlat da ciki sai dai banda Allah Ya raba lafiya ba abinda ta ce don ba ta son shiga sabgarta da Aliyu.

Aliyu bai zo daukarta ba sai wuraren takwas na dare. Sun gaisa da Rafee'ah da mijinta sannan suka bar gidan.

***
BAYAN WATA DAYA..

Tsumma ne a ƙasan ƙafarta tana goge inda mai ruwa ya ɓatamata a falon tana tsaki. Sati biyu kenan da dawowarsu sabuwar unguwa kuma sabon gidan da ko ruwan famfo babu sai dai a siya.

Aliyu ya fadamata ƙudurinsa na siyar da gidan don ya samu na jari, ba tare da ta san inda zasu koma ba ta amince. A cewar ta da ta zo ta ga yanda ginin yake da ba ta amince ba sannan ga dukkan alamu idan damina ta zo dakunan zasu yi warin ruma da kuma alamun danshi a jikin bangon. Ciki da falo ne a gidan sai fyallen daki guda daya, sai kicin hade da store. Ba daki daya a tsakar gida.

Babban damuwarta bai wuce ganewar da ta yi yanzun Aliyu tuban muzuru ya yi, ta kamashi ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba yana shan sigari a ɓoye. Ta yi kukan ta yi faɗan amma a banza, wannan ta sa ta zubamasa ido ta maida hankali ga kaiwa Allah kukanta.

Shigowarsa falon ne ya bata damar dauke tsummar ta amsa sallamarsa a ciki.

"Baby wani wari kamar na gardi nake ji."

A kufule ta amsa.

"Mai ruwan da ka turo ne."

Ya ja tsaki.

"Kai rashin ruwan nan ya soma damuna. Ga cacar kashe kudi. Mtsw."


A ranta ta ce kai ka sani, ta shige kicin abinta.

***
"Biki ko na dangina fa bana anko ke kin sani. Yanzu ma da muke ta kai, wa ke ta kaya?"

Wannan na daga cikin dalilin da ba ta son tambayarsa wata bukata. Kusan ma yana daga abinda Abbansu ya gargadesu, tambayar miji wata buƙata kar ya kawo maka raini. Wani abin ne ba za ka iya shiru ba.

"Aliyu ban taɓa neman ka yimin wata sutura ba sai yanzun, abu ne na fita kunya. Cikin dangi da yan uwana zan shiga. Don Allah ka taimaka dai ka yimin."

Ya ɗan yi shiru yana wani cin magani, can kuma ya ce.

"Shikenan kiyi addu'a a samu kudi. Sannan batun sutura har yau ai kina morar suturorin da na miki, ko ba komai na kashe sama da miliyan daya a lefenki."

"Ba sai ka gorantamin ba."

Ta fadi ranta a ɓace. Bai ce uffan ba don yanzun bai fiye bari su yi dogon sa'insa ba, a cewarsa juna biyu ne da ita. Hakanan yana kokarin ganin ya kiyaye kai hannu jikinta da sunan bugu.

Ta shige daki a fusace ta kyaleshi anan tare da ƴarsa.

***
Allah Ya taimaketa dai ta samu ya kawomata atamfar ankon amma ba kudin ɗinki. Hakanan ta yi godiya ta ƙuƙuta ta bada ɗinkin, zuwa yanzu takan leƙa makwafta saboda halin rayuwa da son kiyaye shari'ah.
Ta ciko ba laifi sai dai ga duk wanda ya ganta da ciki sai ya tanka. Har ta gaji ta fice daga cikin masu auren ta koma bangaren Amaren cikin ƴan mata ta zauna.

Kallon kowaccensu take cike da burgewa. Amrah ta saje a cikinsu ta ci ado har ta gaji sai hira da shewa ake. Ta tuno da nata ƴanmatancin, kauda kai ta yi gami da mirza idanunta gudun saukar ruwan hawayen da ya tahomata. Ita da ƴan uwanta amma a karan kanta kunyar kanta take ji na abubuwan da suka afku wanda har abada tarihinta ba zai goge a zuƙatansu ba. Ko ba komai ta bar baya da ƙura.

Amrah na hankalce da ita hakan yasa ta miƙewa ta karɓi Ummi a hannunta ta zauna ta shiga jan ta da hira har ta saki jiki.

***
Aka kammala biki lafiya aka kai yan matan dakunansu, ba ta samu zuwa kai su ba don ta gaji da habaice-habaicen da wasu a dangi ke mata game da aurenta. Zamanta ta yi a gida abinta.

Kamar koyaushe bayan kammala girkin dare ta yiwa ɗiyarta wanka ta shafe jikinta da hoda yanda za ta ji sauƙin zafin da ake a gari, ga ba wuta a unguwa don sai a fi sati biyu ma ko wata babu kyallinta kamar yanda ta soma shaidawa kuma ta ji daga bakin makwafciyarta. Shigowar Aliyu gidan ya bata mamaki, koda dai yanzun bai kaiwa dare sosai a waje, amma ta yi mamakin ganinsa wuraren bakwai da mintuna. Zama ya yi gefen gadonta yana dan yamutse-yamutsen fuska.

"Lafiya?" Ta nemi ba'asi.

Dan guntun tsaki ya ja yana mai ɗan sosa kirjinsa.

"Kamar dai banda lafiyar Baby, zuciyata sai ta dinga tashi ga gudawa da nake tun safe haka nake zaryar banɗaki a kasuwa."

"Allah Ya sauwake, Ya baka lafiya. Ya kamata ko chemist ka leka."

Ya jinjina kai yana mai sa hannu ya dauki Ummi dake faman mikomasa hannu tana ɓangala dariya.

***
ABU KAMAR WASA....I just published "BABI NA ASHIRIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/f5qPHpmrzab




🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

26)

Cikin kuka ta dubi Hajiyar.

"Wallahi Hajiya ba ƙanjamau ce da shi ba. Jita-jita ce kawai. Ciwon zuciya ce ke barazanar kama shi sakamakon shaye-shaye, sai Infection da ya jawomasa gudawa shine har ya kwanta asibiti na kwana ɗaya. Abba ka tashi don Allah, Abbana kar ka mutu saboda damuwata. Abba ka yafemin. Kaicona "

Kukanta ya ƙi tsayawa, Abba ya kara damƙe hannunta.

"Rabi ki yi shiru. Ki yi shiru. Haka Allah Ya tsara wa Ramlatu. Dakta."

Ya maida dubansa ga Baba Dakta.

"Ka taimakamin a yiwa Ramlatu gwajin jini, idan har tana dauke da cutarnan don Allah a gaggauta dora ta kan magani."

"Abba, wallahi lafiya kalau. Abba dagaske nake maka, ina rantsuwa da ..."

"Kina da tabbas? Mene hujjarki?!"

Munir ya katse a zafafe. Ta dubeshi sai kuma ta kasa magana. Baba Dakta ya bada umarnin duk a fita a bar Abban. Suka fita dukkansu, likitan Abban ya shigo ya kara dubashi sannan ya fito.

"Muje Ramlatu." Fadin Baba Dakta. Ramlat ta dubeshi kamar wata wawiya, yau ita za'a yiwa test akan cutar da ko a mafarki ba ta taɓa ganinta da shi ba? Me ya jawomata wannan tozarci da wulakancin?

'Auren Aliyu.' Cewar wani ɓangare na zuciyarta. Sai a sannan kuma ta tuno tare ta zo da Aliyu, ta waiga baya wurin hakan yasa ta maida dubanta ga Baba Dakta.

"Baba Dakta wallahi wallahi..."

"Yi hakuri, yi hakuri Ramlatu. Kwantar da hankalinki, ki bari ayi din ko don samun nutsuwa da kwanciyar hankalin Abbanki. Kina so ya samu lafiya ko?"

Ta gyada kai gami da jan majina.

"Yauwa ko kefa, muje."

Ta bi bayansa bayan ta bi yan uwanta da kallo. Munir harara ya watsamata, ta kauda kai tana kuka.

Test aka yi mata na jini sannan ta dawo wurinsu ta zauna.

"Ya ake ciki? Me sakamakon ya bayar?" Fadin Hajiya tana dubanta.

Ta bude baki za ta amsa sai ta kasa, kuka ya ci ƙarfinta ga wani bakin ciki da ya tsayamata a ƙahon zuci. Auren Aliyu ya jawomata wulaƙanci, yau ita ake yiwa kallon mai cutar ƙanjamau?

'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!'

Ta fadi a karo na barkatai.

"Hajiya nifa banda komai, bana dauke da kowace cuta. Hajiya don Allah ki yarda da ni. Wallahi ba ƙanjamau ne da Baban Ummi ba."

"Allah Ya tsinewa kalar so irin naki Ramlatu! Son da har za ki ɓoye cutar mijinki ki rufamasa asiri ki cuci kanki! Wallahi Hajiya ya ci ace kun fidda hannunku a lamarin yarinyarnan, wanda fa ya yi nisa ba ya jin kira! Sanadinta Abba ya fada cikin wannan halin, ai ba ita kadai ku k haifa ba! Tunda ita ba ta bi ku ba, kuma bai kamata ku damu da lamuranta ba. Ta je idan ma mutuwa za ta yi ta mutun mana idan har Abba zai rayu! Mtsww!"

"Kai kuma mene sunanka?! Me za mu kiraka da shi? Ka tsaya kana fada alhalin Abba ba lafiya? Wannan shi ne girman?!"

Zulaihat ke maganar a fusace, tun ɗazun ya kai ta wuya dannewa kawai ta yi.

"Ke! Ni kike faɗawa magana?"

"An fadamaka din! Don kawai kana babba..."

"Ya isa! Haba mana!"

Hajiya ta katsesu a tsawance, faɗan Muniru da Zulaihat sakamakonsa bai fiye kyau ba.

Muniru ya juya a zuciye ya bar wurin, Hajiya ta dubi Zulaihat.

"So ku ke ku nunan halinnaku a asibiti? Shikenan ai."

Ta ƙarashe a fusace. Rafee'ah dai banda hawaye ba abinda take yi, magana ma ta kasa saboda tunanin Abban yayinda A'isha ta kwantar da kai a cinyar Rafee'ah ta yi shiru tana kallon kowa. Ramlatu kuwa kukanta ma har ya yi yawa.

Suna nan zaune Baba Dakta ya nufosu fuskarsa dauke da murmushi. Suka zubamishi idanu.

"Alhamdulillah, koda Aliyu na dauke da wannan kwayar cutar, bai kai ga shafamaki ba Ramlatu. Komai naki lafiya kalau yake. Ki kwantar da hankalinki."

Gaba daya suka sauke ajiyar zuciya. Murnar da suke bai wuce yanzun Abban zai farfaɗo ba idan ya ji sakamakon gwajin da aka yiwa Ramlatun.

Baba Dakta ya shiga dakin ya karasa har gadon Abban yana murmushi, sai dai me? Cak murmushin ya dauke da sauri cikin rawar jiki kuma ya kai hannu bisa tsintsiyar hannun Abban. Ya kara kaiwa saman kirjinsa don bai gasƙata abinda ke faruwa ba.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"

Baba Dakta ya furta kafin ya dubi fuskar Abban, kamar za ka kira sunansa ya amsa ga wani dan murmushi. Hannu ya sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login