Showing 87001 words to 90000 words out of 226732 words
"Malama rufe bakin." Muryar Samira ta katse tunaninta, ta harareta.
"Bana son iskanci." Suka yi dariya, ita kuwa Ramlat bayan sun gaisa gaba ta yi ta kyalesu don samar musu abinci.
"Hali Dubu!"
Halima ta juya tana neman mai kiranta, ido hudu suka yi da Salma ƙanwar Bilkisu, kuma abokiyar karatunta. Nan da nan ta saki fuska ta mike ta nufi wurinta, itama Salma ta nufota suka rungume juna kafin a saki ana shewa da murnar ganin juna.
"Kai Salma, dama kina duniya?"
Salma ta yi dariya, kiɗan da aka kunna ne yasa ta jan hannun Halima suka ɗan fita daga hall din.
"Halima Halee Baby! Kin kama ƙasa kin yi bakam ba'a ji da ganinki kwana biyunnan har a whatsapp."
"Wane kama ƙasa aikin da bai taka kara ya karya ba Salma? Kedai muna fatan nan gaba mu kama ɗin, mu samu wani mai hannu da shunin."
Suka yi gami da kara cafkewa.
"Family din Ango kike ne?"
Salma ta tambaya tana dubanta. Taɓe baki ta yi.
"Ko ɗaya, yayar Amaryar ce ta gayyacemu. Abokiyar aiki na ce. Ofis din mu ɗaya."
"Ramlat?"
Fadin Salma cike da mamaki. Itama Halimar kallonta take gami da ba ta dukkan hankalinta.
"Kwarai ita fa."
Yamutse fuska Salma ta yi.
"Amma dai ba ƙawarki ba ce?"
"Meyasa ki ka yi wannan tambayar?"
Cewar Halima cikin zaƙuwa.
"Tab, kin tuna auren wani Cousin brother dina da na ba ku labari a WhatsApp? Wanda nace maku matarsa ta kusa kashe shi ranar da aka kai ta gidansa?"
Da sauri Halima ta shiga gyada kai kamar ƙadangaruwa.
"Yes yes, na tuna!"
"Toh ai ita ce. Sanadin da ya saketa kenan, ta dage da auren wani Aliyu. Na fadamaki sai ya yi shaye-shaye ya zo ya yi mata tsinanan duka ya kyaleta ba ci ba sha. Dakyar dai ta samu salama bayan mutuwa ta rabasu. Ni naji ma Anti Bilki na cewa wai Ƙanjamau ta kasheshi."
Halima ta saki baki da hanci kafin ta yi wata dariya.
"Ke Salma! Ki rantsemin da Allah."
Salma ta ja tsaki.
"Na taba yi maki irin wannan wasan? Lallai ma, ai yanzu ta ƙi auruwa kowa tsoronta yake ji. Ku dai bi a hankali da ita ko a ofis kar ta shafamaku mugun abu."
Halima wani dadi da farin ciki ya mamayeta, wannan labarin ya fi komai yi mata dadi. Ko ba komai anan za ta huce haushin tsanar da ta yiwa Ramlat da cin mutuncin da ta ja mata a ofis.
Suka yi sallama da Salma suka dawo wurin bikin, a hanyar ma sai ƙaramata gishiri da siga ta ke yi. Abinda aka yi da wanda ma ba'a yi ba duk ta haɗa ta faɗawa Halimar. Burinta itama ta ɓatawa Ramlat suna a ko'ina.
Koda Salma ta koma mazauninta, gaba daya ta kwashe yanda suka yi da Halima ta fadawa Bilkisu. Dadi kamar ya kasheta. Har kyauta ta ce za ta yi mata. Suka yi ta dariya ransu fari ƙal.
A ɓangaren Ramlat kuwa, haka ta yi ta hidima da ƴan ofis dinsu har suka tafi, ta yi mamakin yanda Halima ta sakarmata kamar ba ita ba. A karshe ta yi musu rakiya har wurin mota bayan ta kaisu sun gaisa da Hajiyarta sun mata fatan alheri.
"Amma zaku zo dinner goben ko?"
Ta fadi sadda ta kama murfin motar tana dubansu.
"Me zai hana? Za mu zo." Halima ta fadi cikin sauri. Duk suka dubeta. Ba wanda ya yi magana suka amsawa Ramlat da cewa zasu zo. Ta kuwa ji dadi ta yi godiya. Daga nan suka ja suka bar wurin ta koma ciki.
***
WASHEGARI...
LAMIƊO CRESCENT...I just published "BABI NA ASHIRIN DA TARA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/FLZKsoqJJab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
29)
LAMIƊO CRESCENT
A hankali ya ɗago kai daga kallon jaridar da ya ke ya maida saman fuskar wayarsa dake faman ruri a saman tebur. Murmushi ya yi, irin murmushin da idan har ka gani saman fuskarsa to bai ɗauki mutum nan kusa ba. Ko sallama bai kai ga yi ba ya soma yi mishi mita.
"Kai dai wallahi anyi ɗan iska, wato dagasken dai ba za ka zo ɗaurin aurena ba ko? Ni za ka yiwa wannan tsiyar!"
Dafa goshinsa ya yi gami da ɗan runtse ido.
"Oh no, dagasken gaske na mance fa. Yi hakuri."
"Hakuri kake bani? Ba zan hakura ba wallahi muddin ban ga ƙeyarka a dinnerparty ɗina ba! Ka kyauta sosai!"
Hisham bai jira cewarsa ya katse wayar, sakaka ya bi wayar da kallo kafin ya ajiye yana murmushi.
Tunda ta soma taka matattakalar benen idanunta gaba daya a kansa, yanda yake murmushi ya sanya ta jin wani abu mai kama da kishi ya soki ƙahon zuciyarta. Kaf duniya ba ta jin akwai wanda ya isa shiga rayuwar mijinnata har ya sanyashi ya murmusa idan ba ita ba. Tunaninta gaba daya ya tafi ga zargi kamar yanda ta saba, wato da mace yake waya. Wannan ya ƙaramata saurinta ta shiga haɗa step bibbiyu tana saukowa, ikon Allah ne ya kawo Hajiya Zeenatu cikin falon ta yi mishi kerere a ka.
Ya ɗago ya dubeta gami da lumshe idanu ya bude.
"Me akai?" Ya nemi sani cikin halin ko'inkula. Hannu ta kai ta ɗauki wayarsa ta shiga sarrafawa don tunda suke bai taɓa sanya password lock a wayarsa ba, koda zai sanya, Hajiya Zeenatu ta san mabuɗan, abin da ke ba shi mamaki, ba shi da hurumin da zai ɗauki wayarta ya sarrafa yanda ta ke sarrafa nasa.
Bai katseta ba har ta gama shiga da ficenta, asalima maida hankali ya yi ga jaridarsa, zuciyarsa na jin ciwon abinda ta ke aikatawar, bakinsa ya kasa motsawa balle ya tsawatarmata, bai ji yana da jarumtar da zai ce ba ya so ba.
Zama ta yi gefensa gami da riƙo hannunsa tana murmushi, ya dubeta ya maida martani wanda ya fi kama da yaƙe.
"Ashe fa Hisham an yi aure? Gaskiya bai kamata ace ba ka je daurin aurensa ba."
Ya jinjina kai yana dan yaƙe.
"Hakane, yanzun ma ya ce lallai fa sai naje mishi Dinner."
Ta yamutse fuska.
"Wane irin dinner kuma? Salon ka je wata ƴar iska ta ganka ta nuna tana sonka? Abinda ba zai yiwu kenan ba, ya yi hakuri daga baya idan sun tare sai muje har gida mu ga Amarya."
Ya dubeta ya ɗan ɗaure fuska, yana jin kamar ta ragemishi wani farin ciki a rayuwa, sai dai ita din ba ta laifi koda ace uwa da ubansa ta zaga.
"Shikenan, duk yanda kika ce, hakan daidai ne."
Hajiya Zeenatu ta yi murmushi mai kyau har ruwan ɗorawar hakoranta suka bayyana. Ya kauda kai, ta shafi gefen fuskarsa.
"Shiyasa nake ƙara sonka mijina ni kaɗai! Zan fita sai na dawo."
Gyada kai kawai ya yi sannan ta mike, doguwar rigar shadda ce a jikinta sai wani karamin mayafi da ta yafe kanta da shi, san shigar bai mishi tsarin da matar aure za ta fita da shi ba. Ya kauda kai gami da sauke ajiyar zuciya. Inda za ta je ma bai sani ba, ba jimawa dai ya ji tashin motarta. A hankali ya kwantar da kai jikin kujera gami da lumshe idanu. Yana bukatar tunani, sai dai tunanin ya jima da gushewa. Duk kokarinsa, duk irin yaƙin da yake da zuciya da kwakwalwarsa, sun kasa ba shi haɗin kai. Kamar yana aka saba ne ya afku, matsanancin ciwon kai wanda ya sanyashi hakurin dole ya miƙe ya haye sama.
***
Tun ƙarfe takwas na dare farfajiyar ƙawataccen Event Centre din na Marhaba, ya cika ya batse da yan mata da samari matasa sai tsirarun iyaye. Kwalliya iri-iri kawai ka ke gani. Wasu tuni suka shige dakin taron yayinda wasu suka tsaya ƙyam jiran saukar Amarya da Ango. Tana daga can gefe tsaye cikin wani arnen baƙin lace, ta ɗora silver head. Ummi kadai ce ta biyota wurin taron, zaman ɗankwalinta take gyaramata tana faɗan muddin ta ƙara cirewa sai dai ta nemi mai ɗauramata don ita ba baiwa ba ce.
"Ni kuma bawa ne, na yarda na amince idan har ƙarƙashinki zan yi aiki zan yi din koda ba biya."
Tun soma maganar ta juya tana kallonsa. Ya haɗe cikin wata gogaggiyar shaddarsa ruwan ƙasa, murmushi kawai ya ke yana dubanta babu ko kyaftawa.
"Uncle Hilal!" Faɗin Ummi kafin ta fisge jikinta daga na uwar ta yi gaba a guje ta rungumeshi. Ya durkusa yana mai ɗago fuskarta yana dariya, dariyar ba ta komai ba ce sai na ganin yanda Ramlat ta haɗe fuska don Ummi ta tafi ta bar ta da ɗankwali a hannu wanda ya warware gaba daya sai jerin ƙananun kalbar da aka yi mata ke yawo a iska.
"Kin ƙara yiwa Mami laifi. Kinga."
Ya yi mata nuni da Ramlat, ganin haka Ramlat ta kauda kai bayan ta watsawa Ummin harara, ta rufe motarta ta jefa muƙulli jaka ta nufosu. Ganin hakan yarinyar ta tsorata ta yi bayan Hilal da sauri gami da fadin.
"Mami please ki yi hakuri, sunan Hajiya fa ne da ni."
Kusan da hakan ta saba cin galabarta, Ummi akwai wayo da saurin ba da hakuri bisa laifi. Kusan dariya ta basu daga ita har Hilal din. Ya mike tsaye bayan ya yakice Ummi dakyar a jikinsa.
"Ba za'a yi mata afuwa ba?"
Ta ɗan harareshi tana murmushi, ya lumshe idanu ya budesu a kanta, sai kuma sannan ta farga da katoɓarar da ta yi, ko meye na yi mishi murmushin? Da saurinta ta kauda kai ta soma tafiya da nufin barin wurin. Riƙon da ya yiwa ɗankwalin Ummin ne yasa ta kallonsa, kasancewar ya tarkata dukkan nutsuwarsa a kanta yasa kai tsaye idanunsu suka sarƙe cikin juna, ta yi saurin janye nata idanun.
"Ana kallonmu fa."
Ta furta a ƙagauce, zuciyarta har zafi ta soma. Takaici da haushin kanta ne ke mamayeta. Wani sashi na zuciyarta ihu yake mata, yana mata tunin bai kyautu ace har ta mance baya ba. Bai kyautu ta saurari kowane namiji ba, ko ba komai ta yiwa kanta alƙawarin gudanar da rayuwarta babu aure, ta raini yaranta har su zamo abin alfaharinta duniya da lahira.
"Lah, Yaya Hilal?" Kusan a kidime ta kai duba ga mai maganar, Salma ce tare da Halima. Zuwan su Halimar kenan ta ha hannunta don ta yi mata hotuna.
"Ramlat?" Fadin ita Halimar. Lokaci guda Hilal da Ramlat suka dubi juna kafin ta kauda kai da sauri ta sakarmasa ɗankwalin Ummin ta yi gaba wurin Halima. Murya na rawa ta ce.
"Ha..lima., yaushe ku ka zo?"
Halima wacce a farko bakin cikin hadadden gayen da ta gani tare da Ramlat ke tafarfasa zuciyarta, ta ji wani sanyi jin da ta yi Salma ta ambaceshi da Hilal, wato shi ne dai wanda Ramlat ta gujewa aurensa.
'Marar rabo.' Ta fadi a ƙasan ranta, a fili kuwa murmushi ta yi tana wani ƙwarkwasa a sonta ta burge Hilal.
"Bamu jima da zuwa ba, ashe kina nan kina tsinkar fure. Ki ce shiyasa ki ka ƙi sauraron Oga. Kina da zazzafa a hannu."
Kalaman Halima wanda da biyu ta yi, ya kara baƙantawa Salma rai, ta karasa ga Hilal a zafafe. Ita kuwa Ramlat kallon ba ki kyautamin ba ta watsawa Halima ta yi gaba, Ummi ta rarumi dankwalin ta bi uwarta a guje tana kiran ta ɗauramata.
Salma kuwa ta dubi Hilal cike da bakin ciki.
"Yaya kar dai ka cemin ka dawo a karo na biyu zawarcin Ramlat? Duk abinda ta aikata gareka ka mance?"
Daure fuska ya yi yana kallon yarinyar da duka-duka ba ta dade da daina yoyon majina ba, a cewarsa.
"Ke, yaushe muka soma ƴar haka da ke? Sa'anki ne ni?"
Ta ƙara turɓune fuska, zarginta dai ya tabbata. Tasan idan ta kara magana to zai iya yi mata duk abinda ya so, wannan ne dalilinta na juyawa fuu ta ja hannun Halima su bar wurin a fusace. Ta kuma rantse babu mai dakatar da ita daga faɗawa su Anti Fa'iza da Murja, ko ba komai ta hanyarsu saƙon zai fi saurin isa kunnen iyayen Hilal waɗanda suka rantse ko bayan ransu basu yarda da aurensa da Ramlat ba koda hakan akwai yiwuwarsa. Wannan rantsuwa ce da umarni da suka faru tun Ramlat na gidan Aliyu, tun sadda ta fusata zuƙatan iyayensa.
A ɓangaren Ramlat dakyar ta samu ta maido walwalarta sai dai ko yaya ta waiga ta hangi Halima manne da Salma sai ta ji wata irin faɗuwar gaba, a bakin Naja'atu Azare take jin ashe sun san juna tun suna B.U.K. Jin hakan bai ƙare ta da komai ba sai ƙarin fargaba.
Ana kammala dinner, Ango Hisham ya wuce da Amaryarsa gida don dama sai da aka kai ta sannan aka taho Dinner. Daren ranar baccin Ramlat rabi da rabi ne, tunaninta me zai biyo baya don ta tabbatar dole Salma ta sanarwa Halima wani abin da ya danganci rayuwarta ta baya, tana ganin kiran Hilal da text dinsa akan yana so su yi magana koda ta mintuna ne amman ta ƙi ɗagawa, a ƙarshe ma ta kashe wayar gaba daya.
"I am sorry Hilal." Ta furta a fili yayinda wasu zafafan hawaye suka zubomata ta ɗaukesu da tafin hannu.
***
Ta shiga ofis dinsu da sallama tana mai duban abokan aikinta.
"Yau dai Hajiya Ramlat kin so makara."
Ta yi murmushi tana duban Salihu mai wannan furucin, ko kusa ba ta son jaye-jayen wasa hakan yasa ta wucewa bayan ta gaida kowa ta zauna a mazauninta. Matan ta duba da mazan da suka halarci daurin aure ta yi musu godiya da fatan Allah Ya kara dankon zumunci daga nan ta maida hankali ga wani aiki da Oga Ɗalhatu ya ba ta tun wancan satin.
Ta dukufa wurin aiki, Ofis ya cika irin cikar da ta tsana, wato ƴan wasu ofishin su shigo nasu domin hira, wannan yasa tunda ta sunkuyar da kanta ta wasu rubuce-rubucenta a computer ba ta ɗago ba, kamar yanda ta daure fuska kamar ba ta taɓa dariya ba musamman ganin har da Oga Ahmad wanda ke kokarin sanyata a hirar tana ƙi. Babban abinda ke ba ta mamaki wasu cikin matan ma da aurensu amma yanda suka zage kamar ba auren a kansu. Kamar da wasa ta ji Halima ta zage tana bada labarin da nan take ya sanyata gumi duk kuwa da irin sanyin Ac da ke kaɗawa a ɗakin.
"Toh ai yanzu zamanin ne ya sauya. Soyayyar da ƙarfi da yaji ma kwatarta ake yi Oga. Sai na tuno da labarin wata da aka bani, ranar da aka kai ta ta nemi kashe Angon saboda ba ta sonsa, aikuwa ya saketa ta auri zaɓinta amma fa ta ci gidansu. Duka, zagi ba wanda ba ta sha ba. A karshe dai yanzu sun rabu, ta na nan kuma ta dawo tana bin shi saurayinnata na farko kamar jela, kai ka ce karyar da ta hango ƙashi, nema take ƙarfi da yaji sai ya aureta."
Buɗar bakin Oga Ahmad ya ce.
"Ai wallahi ta yi kaɗan don ubanta! Wannan ma an yi ƴar iskar gaske. Au sai da ta ga rayuwa za ta dawomin?"
"Ni kuma da ni ne, zan aureta ko don na koyamata hankali. Sai na sa ta raina kanta fiye da yanda wancan na farkon ya rainata."
Fadin Salihu kenan har da cire hula hira ta yi dadi.
Abin sai ya koma kamar muhawara, wannan ya kawo nashi, waccan ta kawo. Halima ta saci kallon Ramlat yanda nan take ta fice hayyacinta, ta kauda kai tana wani irin murmushi, ji take kamar nan duniya ba ta taɓa samun farin ciki da walwala kamar ta ranar ba.
Zaman ofis din ya gagareta, ta tabbatar idan ta ci gaba da zaman to fa ruɗun da ta shiga zai bayyana kowa ya gane. Tsalam ta mike gami da daukar jakarta, hannunta har rawa yake ta zura takalminta da ta cire don kafafun su huta kai tsaye ta nufi hanyar fita.
"Ah, Ramlat ina za ki je kuma? Da sauran lokaci fa a tashi."
Fadin Halima kamar ta daka tsallen murna, Ramlat ta juya ta watsamata wani banzan kallo ita kuwa ta murmusa gami da kashemata ido ɗaya. Wannan ya kara ba Ramlat tabbacin da gayya ta yi. Tana sane ta yi mata abinda ta yi din.
"Ba ta ko saurari kiran da wasu cikin ofishin ke mata ba, ta bude kofa ta fice. A hanyar baranda suka ci karo da Ogansu Ɗalhatu. Ya dubi agogo, sauran bai fi mintuna talatin ba a tashi.
"Ramlat, tafiya? Lafiya kuwa?"
Ta dubeshi dakyar, ba don ya zamto shugaba ba a gareta, za ta iya giftashi kawai ta wuce don yanda ta ke jin kanta. Yaƙe ta yi.
"A yimin afuwa Oga don Allah, ban jin dadi dauriya nake."
Cike da tausayawa ya ce.
"Assha, sannu. Allah Ya ba ki lafiya. Ko dai na sanya a kaiki?"
Ta girgiza kai.
"A'a zan iya tafiya ba komai. Nagode."
Zai kara magana tuni ta giftashi ta wuce da sassarfa. Sai dai tun kafin ta karasa ga motarta, hawaye sun wankemata fuska, hannu na rawa dakyar ta iya bude ƙofar motar ta shiga. Kuka sosai ta ci fuskarta cikin mayafi, dakyar ta iya dauriyar share fuska ta yi ribas ta fita.
Rabin tuƙin yinsa take yi ba'a nutse ba. Abinda ta ke gudu ya faru, a hankali abinda ta shuka ya soma fitar da tsirrai, tana tsoron ya fidda ƴaƴan da zasu nuuna har nata ƴaƴan su samu rabonsu. Tun ba'a je ko'ina ba, komai ya soma bayyana. A yanzun da tsoro ya shigeta, tana ji a ranta za ta iya barin aikinta idan har hakan zai tseratar da mutuncinta da na yaranta a idon duniya. Za ta killace kanta a gida.
'Kin manta cewa watan watarana dama sai rana makamancin wannan ya zo? A gidan a tunaninki kin tsira?'
Ta hau gyada kai kamar ƙadangaruwa kamar mai ganin zuciyarta a fili.
"Zan tsira, yarana ba zai shafesu ba tunda ba su da laifi! Ni mai laifin a yimin kowane irin zagi zan jure!"
Tana maganar a fusace ita daya a mota, ba ta yi aune ba ta kai dab da dab da wata mota, duk kokarin ganin ta ci burki hakan ya faskara har sai da ta daki bayan motarsa. Masu