Showing 111001 words to 114000 words out of 226732 words
Zaituna.
"Wai Umma har yanzu ba su ɗauketa ba?"
Umma ta dara.
"Sun dauka mana, maidomin abata suka yi. Kusan tun bikin Muniru."
Ramlat ta murmusa.
"A'a wannan dai ta zama kishiyar ta gaske. A bar maki ita kawai."
Kama baki Umma ta yi.
"Wannan Babannata ne zai bar ta?Bari kiga nan kusa za ki ganshi ya zo daukarta. Yaran yanzu da shegen son ƴaƴa, wa ya sani ma ko ita ke turoshi."
Dariya sosai abin ya ba Ramlat.
"Kema dai ɗiyata ina nan ina addu'a Allah Ya zaɓamaki miji nagari mu sha biki. Ba na jin dadin ganinki a gida da kuruciyarki. Ai ina jin ba ki yi talatin ba ko?"
Da murmushi ta girgiza kai.
"Ban kai ba Umma. Kin manta watanni kawai na ba Amrah."
Umma ta yi dariya.
"Ke da Amrah ai rigimarku sai ku, ki ce kin girmeta itama ta ce ta girmeki."
"Allah na girmi Amrah."
Ita dai Umma ta amsa da toh sannan ta mike zuwa daki tana dariya, can ta fito rike da wani littafin adduo'i ta mikawa Ramlat.
"Ki dinga karantawa, akwai adduo'i sahihai da kuma nafiloli. Kar ki yi wasa don Allah."
Ta amsa da toh, mutanennan suna da burin ta yi aure, ba za ta ce ba ta so ba. Sai dai tana duba yaranta, ba ta kaunar yin nisa da su. Aure kuma ance ba inda ba ya kai mutum.
Kwanciya sosai ta yi saman kujera sadda Umma ta mike ta wuce bangaren mijinta da ta ji tsayuwar motarsa. Wannan ya ba Ramlat damar danna waya, lambar Hussein ta bude ta ga dacewar ta yi saving. Cak ta tsaya tana tunanin sunan da za ta ɗora akan lambar, can kuma ta yi murmushi ta rubuta Mr Wuf. Ita kanta abin dariya ya bata.
Daga haka ta faɗa whatsapp ta shiga duba contact har ta faɗa saman lambarsa. Dp dinsa na wani ƙaton ocean ne sai rana da ta ɗauko faɗuwa daga sama. Murmushi ta yi ta je kan Status na profile. Busy kawai aka rubuta da alama kuma ya jima sosai a hakan.
Tana komawa kan whatsapp ta ci karo da sallamar Alhassan. Ganin yana online ta amsa da sauri. Suka gaisa ta tambayi Dada da iyalinsa. Ya amsa har da turo emoji na nuna jin dadinsa da hakan. Ya tambayi mutan gidansu shima.
_*"Ina nan shigowa Kano karshen satin da zamu shiga in sha Allah. Zan kawomaki Fatina ku gaisa idan ba damuwa. Address?"*_
Ganin abinda ya rubuta ne yasa ta saurin miƙewa zaune. Alhassan zai shiga Kano? Kodai yana da ƴan uwa a Kano?
Wannan tambaya ce da ba ta da amsarta. Ga haɗiyi wani yawu kafin ta amsa mishi.
_*"Kano na marhabin da ku, Allah Ya kawoku lafiya. Ashe muna da ƴan uwa a Kano kenan._*
Ta tambaya cike da ƙaguwa . Dariya ya aikomata kafin ta ga yana recording. Ta bude ta saurara.
"Eh toh, muna da yan uwa. Akwai yayan Babanmu a Kano. Yanzun ma biki za'a yi na samarin yaransa har biyu, shi ne zan kawo su Dada da Maman Fatima. Ina fatan za ku hadu ku gaisa?"
Abinda ya ce kenan, ta yi shiru, gaba daya ya dulmiyar da ita cikin tunani. Kenan Alhassan suna da dangi a Kano? Toh ta yaya zai yiwu ace ba su taɓa cin karo da Hussein ba? Anya zai yiwu? Ace kuna gari daya ba ku taɓa sanin juna ba. Kodai Hussein din ne bai da zumunci?
Abinda ta yi ta rayawa kenan,can ta tuno ba ta ba shi amsa ba, gudun kar ya yi tunanin wani abin ne yasa ta ba da amsa.
_*Wow, Allah Ya kaimu toh. Zan so na ga Fatima.*_
Suka ɗan taɓa hira kafin su yiwa juna sallama. Ita dai ta ajiye wayar kawai amma hankalinta gaba daya ya tafi ga tunanin wannan lamarin mai ban mamaki da ɗaure kai.
Ba ita ta bar gidan ba sai da lokacin tashin yaranta ya yi, ta so ta ƙi shiga wurin Baba Dakta saboda kar ya yi mata batun aure, a karshe dai ta daure ta shiga kuma har suka gaisa ta fito suka taɓa barkwanci, bai mata zancen ba.
Tana shiga da yaran falon Hajiya, ta ga babu su Munir balle yaransu sai Hajiya da Ladidi da ke tattaunawa. Hajiya na ganinta ta yi dariya.
"Ja'ira, wata kika gudu kika bar ni da su ko?"
Tana dariya ta zauna.
"Me zan ce? Na saka baki Yaya Munir ya ce na mishi rashin kunya? Ya suka ƙare?"
Taɓe baki Hajiya ta yi.
"Na yi musu dai nasiha daidai gwargwadona. A karshe sun ba juna hakuri suka kwashi yaransu suka yi gaba."
"Allah Ya daidaita lamarin."
Suka amsa addu'ar Ramlat da Amin.
***
LAMIƊO CRESCENT.
Kallon abincin ta ke kamar ta fasa ihun kuka tsabar takaici da bakin ciki. Ta dage ta yi girki da ruwan maganin tarkinta amma Hussein ya tahomusu da wasu manyan kifaye har uku gasassu da aka sanya chips a gefe da kayan tumatir albasa sai ɗan yaji a wata ƙaramar roba. Ci ya ke yana jin dadinsa ya dubeta.
"Madam tunanin me kike ne? Wannan fa don ke na siyo. Please come and join me."
Ita a dole shagwaɓa irin ta masoya, ta yamutse fuska.
"Ni a'a gaskiya, na dage na maka girki da kaina da hannuna yanzun kuma ka cemin ka ƙoshi?"
Ya yi murmushi.
"Shikenan, ki sanyamin a fridge I promise you, da shi zan yi breakfast. Hankalinki ya kwanta?"
Ta ji sanyi a ranta, murmushi ta kasheshi da shi, ya maida kai ga abinda ya ke ci. John ta kwalawa kira ya shigo sanye da rigar kuku, umarnin ya juye ya sanya a fridge ta ba shi sannan ta matso ta soma tayashi cin kifin. Sanin da ta yi Hussein ba ya magana biyu, zai wuya ya ƙi yin abinda ya furta yasa hankalinta kwance ba ta ko damu ba.
Sai dai kuma ga mamakinta da safe tashi ta yi sai filin gado ita kadai babu shi ba dalilinsa. Takardar da ta gani ta dauka ta karanta, sanarmata ya yi ya samu kiran gaggawa zai wuce Abuja meeting, abu ne da suka sanya rai har sun fidda za'a samu sai gashinan ya yiwu, ta yi hakuri idan ya yi rashin kyautawa. Hawaye ne kawai Hajiya Zeenatu ba ta yi ba. Ta kirashi a waya sai dai a kashe, ta ja tsaki ya fi a ƙirga.
***
Kuɗin take ƙarewa kallo ba tare da ta iya kataɓus ba. Ta kasa bin umarnin Chairman ɗin nata ta dauka balle har ya je jakarta. Kuɗin da ya ninka albashinta sau biyu. Da mamaki ta dubeshi, kallonta yake ƙasa-ƙasa.
"Me zan yi da su?"
Dariya ya yi, duk a zatonsa ta ruɗe ne saboda yawan kuɗin, bandir na dubu har guda uku ai ba wasa ba. Ya kara turo kuɗin.
"Dauka dai ki riƙe tukunna Madam Ramlat."
Girgiza kai ta yi.
"Ka yi hakuri Yallaɓai ka faɗamin kudin na menene tukunna."
"Kyauta ce daga gareni, wannan ba komai bane daga irin kyautar da nayi maki tanadinsu. Don Allah kar ki ce ba za ki karɓa ba. Ke musulma ce,k kuma kin san ba kyau maida hannun kyauta baya."
Har wani gumi ta ji ya tsastsafo saman goshinta duk da sanyin nu'arar Ac dake kaɗawa.
"A'a, a'a, ka yi hakuri. Nagode wallahi amma ba zan iya karɓa ba."
Daga haka ta kama hanya har tana tuntuɓe ta shiga kokarin ficewa daga ofishin, kiranta ya yi ta tsaya cak jin muryarsa ta koma irin ta ubangida da bawansa.
Sai da ta juyo ya ɗan saki fuska ya koma magana a tausashe.
"Ga duk wanda ya sanki a wannan ma'aikatar, yabon kyawawan dabi'unki ke fitowa daga bakinsa, ban ci karo da wanda har yau ya kusheki ba. Don Allah kar ki sa na ga baƙinki, ki karɓi kyautarnan domin girman Allah da Annabi s.a.w"
Kallonsa ta ke kawai, ya koma kamar ba Chairman ba, ya maida kansa mutum mai rauni. Banda ma rainin wayo, su waye suka santa a wannan ma'aikatar har haka da yake cewa wai an shaideta. Bandir daya kawai ta dauka shima sai da ta ji wani faduwar gaba, ta kudurta a ranta ba za ta kashe ko sisi daga kudin Chairman ba. Za ta adana ko don gaba. Zai kara magana ta ce.
"A'a, ka yi hakuri don Allah, wannan ma ya isa. Kar ka yimin dole. Nagode Allah Ya kara girma."
Ya yi murmushi, ko ba komai ya ji dadi. Ta sanya kudin a jaka ta fice ta barshi da shafa sanƙo. Gani yake kamar yanzun ba son jikinta kadai ya ke yi ba, har da ma halayyarta da ɗabi'unta. A hankali ya shafi sanƙonsa yana jin kamar ya samu mata ta uku.
***
I just published "BABI NA TALATIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/GuBmViwNabb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
36)
A hanya tana tafe tana juyayin wannan lamarin, ta kasa gane inda Chairman ya dosa. Tana tsaka da wannan tunanin ne wayarta ta yi ƙara. Ganin sunan Hilal na yawo yasa ta kasa ɗagawa, can dai ta ga bai kamata ba don haka ta ɗaga. Maimakon muryar Hilal ya doki kunnuwanta, muryar matarsa Fa'iza ce. Sallamar da ta yi ma ba ta samu amsarta ba.
"Ai shaiɗanu irinku basu bukatar a amsa sallamarsu. Ke ba ki ji kunya da kike bibiyar mijin aure ba? Mijin da kika so cutarwa har kika yi ikirarin kashe shi? Koda dai, ba ke ya kamata na fadiwa hakan ba, shi marar zuciyar da kika lashewa kurwa shi ya dace na tunkara da batun! Ina miki gargadi tun wuri ki fita daga rayuwar mijina! Ki fita! Mijina ba sa'an aurenki ba ne! Ya fi karfinki! Ke ba ma shi ba, duk wani kamilin miji da yasan me yake ba zai tunkareki da sunan aure ba sai da karuwanci! Ko ba komai ba wanda bai san kina da ƙanjamau ba, kowa yasan tsohon mijinki!"
Tun soma maganarta, Ramlat ta gangara gefen titi ta faka motar. Shiru ta yi mata har ta kai aya. A zantukan ba wanda ya yi mata zafi kamar na sanya Aliyu da ta yi a zancen. Ta sa hannu ta share hawayen da ke sauka daga kwarmin idanu har suna kokarin shigewa bakinta. Ta bude baki da zummar magana ta ji muryar Hilal a ɗage yana yiwa matarsa masifa.
"Wane rashin hankali kenan?! Da iznin wa kika ɗauki wayata?...
Ba ta jira ta ƙarasa jin hayaniyarsu ba ta kashe wayar gaba daya don ba ta bukatar ji daga kowa. Kwantar da kai a saman sitayari ta yi zuciyarnan na tafarfasa. Ko mene ita ta aikata abinda dole a zageta don shi, sai dai babu dalilin da za'a sanyo Aliyu cikin sabgarnan. Aliyu ya yi kyakkyawar mutuwa irin wanda ko mutumin kirki ne ya samu ya dace. Da ace Fa'iza ta kwantar da hankalinta, babu Hilal a zuciyarta, ba ta yi mishi so irin na aure. So take mishi na ƴan uwantaka, tana mishi kallon yayanta da suke ciki ɗaya. Ajiyar zuciya ta saki kafin ta maida hankali ga kallon yanda hadari ya yiwa garin luf. Wani murmushi ta saki mai ciwo tana share hawaye, addu'a ta yiwa Aliyunta sannan ta kunna karatun Alkur'ani, ta ja motarta.
Ba ta faɗa wa Hajiya abinda ya faru ba sai dai har dare wayarta a kashe. Kamar daga sai ga Hilal, lokacin suna falo zaune saƙon zuwansa ya isketa daga bakin Malam Bala. Ta yi shiru, Hajiya ta dubeta don dama ta lura gaba daya ba ta da walwala. Sanin da ta yi koda ta tambaya babu amsa yasa ta yin shiru kawai ta zubamata idanu. Yanzun da saƙon zuwan Hilal ya risketa, ta lura da yanda ta ƙara ɗaure fuska.
"Meke faruwa ne da ke? Tun shigowarki kin wani cukune, yanzu an ce ana kiranki kuma kin ji wanda ke tafe amma ba ki da niyyar zuwa."
Ramlat ta dubeta kamar ta yi kuka.
"Hajiya ba komai, kawai..."
"Tashi ki je." Ganin umarni ne kai tsaye ta ba ta yasa ta miƙewa ta shige daki, can ta fito yafe da gyale akan doguwar rigar atamfarta ta fice.
Yana tsaye kamar koyaushe jikin motarsa, ta karasa ba tare da ta bari sun hada idanu ba. Sallama ta mishi kafin su gaisa sannan ta ja bakinta ta yi shiru.
"Ramlat na miki laifi, kiyi hakuri."
Murmushin yaƙe ta yi.
"Ba abinda ka yimin, asalima ko me Fa'iza ta fadi gaskiya ce ta faɗa. Sai dai don Allah ina roƙonka akan muyi hakuri hakanan. Kaunar da ka nunamin Allah Ya saka da alheri. Har abada nasan banda masoyi kamar ka."
Ta ƙarashe da wani irin rauni, kuka ke son kwacemata, tunaninta ya tafi a shekarun baya na irin cin kashin da ta yi mishi. Hawaye ta shiga fitarwa ba tare da ta sani ba.
Ta ɗago ta kalli farin hankicif da ya miƙomata kafin ta dubeshi, murmushi ya ke mata wanda ya fi kuka ciwo yayinda idanunsa suka kaɗa. Zuwa yanzun shima ya saduda kuma ya ji zai hakura ko don kar ya faɗa fushin iyayensa. Akan Ramlat, yau Fa'iza ta kai ƙararsa gurin iyayensa. Sosai aka buɗemishi wuta kuma sun kara rantsuwa akan tsinuwa gareshi idan ya dage akan aurenta.
Ta sa hannu ta karɓa ya soma magana.
"Ramlat kar ki damu, nima na ji a raina yanzun zan iya hakura da ke ba kuma don ina so ba. Ina miki kyakkyawan fata a koyaushe. Ina roƙon Allah Ya kawomaki sauyi a rayuwa, Ya zaɓamaki mijin da ya fi ni, mijin da zai kularmin da ke ya kuma nunamaki dukkan kauna da soyayya. Allah shaida ne, na so na aureki, sai dai a matakin da nake kai yanzu zan iya faɗawa fushin iyaye da na Mahaliccina. Ya zamemin dole na hakura kar biyewa son zuciyata ya jazamini."
Ya ci gaba da kalaman da ke nuni da irin alhininsa na rabuwarsu. Haka ta yi ta fidda hawaye a karshe suka rabu ran kowannensu babu dadi.
Allah Ya taimaketa Hajiya ba ta falon sai yara da suka sheme duk sun yi bacci, jiki a saluɓe ta kai kowannensu makwancinsa ta yi musu addu'a sannan ta koma falon da zummar kashe kayan kallo.
"Yaushe kika shigo?" Ɗagowa ta yi bayan ta kashe socket din talabijin ta dubi Hajiya.
"Ban jima da shigowa ba."
"Lafiya?"
Ta watsomata tambayar ganin yanda take fidda hawaye, ta kasa danne kukanta, kawai sai ta fashe da kuka. Umarni ta bata akan ta zauna su yi magana. Nan ta zayyanemata yanda suka yi da Hilal. Jinjina kai Hajiya ta yi.
"Allah Sarki, yaron kirki. Dole ki yi kuka Ramlatu, rashin mutum mai hakuri da nagarta kamar Hilal abu ne mai ciwo. Da ace ba mai hakuri bane, hanyar ma da kika bi ba zai kalla ba ballantana har ya bi ɗin. Allah Ya sasanta shi da mai ɗakinsa, ke kuma Allah Ya yi maku zaɓi."
Ta amsa sannan suka yi sallama kowannensu ya shige ɗaki. Wanka ta soma yi ta sauya kaya gami da kwanciya saman gado. Tausayin Hilal kawai ta ke ji yana nukurkusarta, a karshe ta yi addu'a ta kwanta.
***
Washegari tun safe ta shirya ta fita da yara makaranta. Caa suka yi mata kowanne da nashi kalar ƙorafin, daga ba'a ga fensir ba sai mai kawo ƙarar Antinsu ta bugeshi. Ita dai ban da murmushi ba abinda ta ke yi, idan da sabo ta saba, kowanne da nashi ƙorafin musamman Ummi da Ansar wadanda har sun soma koyawa Affan.
Ƙarar wayarta ne yasa ta dauka, ganin sunan Mr Wuff ya ba ta mamaki. Ta dakatar da hayaniyar su Ummi kafin ta ɗaga da sallama daidai sadda aka tsayar da su a junction.
"Yaranmu ne suka sanyaki murmushi ko tunanin bazawarinki?"
Abinda ya ce kenan bayan amsa sallamar, hakan ne yasa ta saurin kallon titi. Gaban wata Jeep ta hangeshi zaune a kujerar kusa da direba. Da alama wani abin ya tsayar da su, kallonta ya yi kafin a hankali ya rufe gilashin motar.
"Hey, kar ki cinyeni da kallo. Kamar ma kin manta cewar tuƙi kike ko?"
Harara ta bankamasa don ta san koda ita din ba ta kallonsa, shi idanunsa yana kanta.
"Meye abin kallo a fuskarka? Nikam ban ganshi ba. Na kalleka ne don na tabbatar kai dinne da sassafe haka ba wani ba."
Murmushi ya yi tamkar tana kallonsa.
"Allah Ya tsare hanya, drive carefully."
Daga haka bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta ajiye wayar ba ta kara kallon inda motarsu take ba amma ya sanyata dariya.
A bangarensa kuwa, ƙara jingina ya yi yana ƙaremata kallo daga ita har yarannata, ya lura babbar ta fi ɗiban kama da ita akan na tsakiyan da ƙaramin. Yanda suke ta hira suna karkatowa da zummar kallon fuskarta ba karamin burgeshi ya yi ba.
Direba dai ya yi bakam, ga labari na sukarsa amma ba wani da zai faɗawa. Burinsa kawai su kai gida ya samu Joseph mai gadinsu, inyamuri kuma mai jin yaren Hausa sosai su tsegunta. Da alama dai Yallaɓai aure zai yi, sun tabbata ba karamin bomb ne zai fashe ba.
Har aka ba su hannu yana satar kallon Ogannasu, hankalinsa duka yana ga Ramlat da yaranta. Kusan tunda ya daukoshi daga Airport bai yi mishi wani kwakkwaran magana ba sai yanzun da ya ga budurwarsa. Farin ciki sosai direban ke yi, ko ba komai Yallaɓai zai samu sa'ida daga wurin Hajiya Zeenatu. Su kansu suna mamakin yanda akai ya ƙare da auren mace kamarta.
***
Har ta sauke yaranta a makaranta ta kama hanyar ofis ba ta bar tunanin wayar da suka yi da Hussein ba. Sosai ta ke mamakinsa, idan da a farkon ganinta da shi wani zai ce mata yana da sauƙin kai har haka toh fa za ta musanta, za kuma ta ƙaryata nan take. Da alama wannan yana daga cikin nasarar jihadinta. Ta shaƙu da shi sannan a ƙarshe ta shiryashi da ƴan uwansa. Wannan kaɗai ne burinta.
Tana faka motarta ba ta kai ga barin parking space din ba, suka ci karo da Halima. Wani irin kallo Halima ke bin ta da shi tana murmushi. Bayan sun gaisa ta ce.
"Sakatariyar Chairman, wato ko nemanmu ma kin daina."
"Ko rannan na shiga ke kuma ba ki zo ba." Fadin Ramlat cikin dakiya don yanzun ba ta kaunar shiga duk wani lamari da ya shafeta. Ta riga ta gane ba masoyiyarta ba ce. Halima ta ɗan taɓe baki.
"Oh, haka fa. Ai mancewa na yi,