Showing 105001 words to 108000 words out of 226732 words
In sha Allah. Sai na ƙaraso."
Daga haka suka yi sallama, shiru ta yi na ɗan lokaci, so take ta gani ko za ta iya fahimtar manufar yin hakan, sai dai duk iyakar tunaninta ba ta gane komai ba. Tasan dai ko mene ba alheri ba ne tunda mutumin Hajiya ne.
Miƙewa ta yi ta shiga wanka, a gaggauce ta shirya cikin doguwar rigarta na Atamfa, mai kawai ta shafa kafin ta zura hijabinta dogo ta dauki duk abinda take ɓukata ta fito. Sai a sannan ta tarar da missedcalls har uku duk daga mutanen Department dinsu ne. Ba wanda ta bi, ta karasa ta gaida Hajiya dake zaune suna hira da Ladidi.
"Yau dai babu niyya. Daga jin sanyin gari kin shantake."
Dariya ta ɗan yi.
"Wane sanyi? Ai da saura ruwan Hajiyarmu. Bai kankama ba tukunna!"
"Allah Ya bamu damina mai albarka dai." Fadin Hajiya, suka amsa. Ta gaidata karo na biyu kafin ta dubi Ladidi su gaisa sannan ta karya a gaggauce ta fita. Ba ta iya ta sanarwa Hajiya sauyin da aka yi mata ba, bar wa cikinta ta yi har sai ta je ta ji asalin abinda ke wakana.
***
AKWAI WATA A ƘASA!.I just published "BABI NA TALATIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/WcD6L9EP0ab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
34)
AKWAI WATA A ƘASA...
Gaban Notice Board ta soma tsayawa, shakka babu dagaske Salisu yake, ajiyar zuciya ta sauke bayan kammala karanta bayanin sauyin da ta samu. Sati mai zuwa za ta fara sabon duty dinta.
"Allah Yasa hakan ya fi alheri." Ta fadi a fili sannan ta karasa cikin ofis dinsu wanda kiris ya rage ta bar shi. Bayan sun gaisa ta zauna.
"Za dai mu yi kewarki anan Ramlat, ko ba komai kin fi wasu a nan."
Fadin Oga Ɗalhatu, aka ɗan dara idan ka cire Halima da hassada da bakin ciki ya cikamata zuciya, yanda ta ke jin tsanar Ramlat a yanzun har ya fi na baya. Ta jima tana burin kasancewar mai aiki a ƙarƙashin Chairman duk kuwa da cewa hakan bai rage ko ƙara albashinta ba, amma dai tasan alhairan da ita za ta kwantar da kai ta samu wurin Chairman, ba lallai ne ita Ramlat ta yi ba.
"Ki dai bi sannu don kinsan ko waye shi."
Cewar Halima tana yamutse fuska.
"Kedai ba ruwanki, zato zunubi. Kuma kin fi kowa sanin Ramlat da halayyarta." Fadin Zuhra kenan.
Ramlat kallonta kawai ta yi ba tare da ta tanka ba, tsaf ta gama gane wacece Halima da kuma irin takun saƙar da take yi da ita wanda ita kam ba ta ga dalilinsa ba.
Da wannan damuwar ta dawo gida ta sanar da Hajiya halin da ake ciki.
"Toh ke meye naki na damuwa? Sauyi ne fa kawai, idan batun kamun kai ne ai na yarda da ke bana jinki a wannan ɓangaren. Allah Yasa hakan ya zamemaki alheri."
Ta amsa da amin.
Bayan Magriba suna zaune tana koyawa yaranta Homework, Maigadi ya yi sallama a bakin ƙofar suka amsa. Jin saƙon wai ana sallama da Ramlat ya ba ta mamaki, ta dubi Hajiya, itama kallonta take tana murmushi.
"Ka ce tana zuwa."
Bayan tafiyarsa ta dubi Hajiya.
"Haba Hajiya, mutum da bansan ko waye ba, yanzun ai ba'a irin haka, da ace ya san ni toh ba zai rasa lambar wayata ba. Ta nan zai neme ni."
Harararta Hajiya ta yi.
"Kuma ya zama dole ki fita ba, naga alamar kin fi kaunar zama a haka babu aure, toh ya isa. Nima kamar Babanki Dakta, ba zan ƙara biyemaki ki kori masu zuwa wajenki ba. Idan ma a baya an yi bai wuce na tausayawa marayunnan ba. Tashi maza ki je."
Kamar ta yi kuka ta ce.
"To wa zai ƙarasa koyamusu?"
"Jeki, nasan duk daɗewa ba za ki wuce awa ɗaya ba. In Sha Allahu ma ba su kai ga yin bacci ba. Tunda kin sallami Affan ai da sauƙi."
Miƙewa ta yi ranta duk ba dadi, hijabi kawai ta zura ta kama hanya su Ummi na kiran a dawo lafiya, a tahomusu da alawa. Harara kawai ta watsamusu ta yi gaba ta bar Hajiya da dariya.
Sai dai me? Wanda ta gani ya matuƙar shayar da ita mamaki, sakin baki ta yi kafin kuma su yi dariya a tare.
"Kai Yaya Hilal, yaushe ka zama baƙo a gidannan? Kuma fa ko Malam Bala bai fadamana wanda ke sallamar ba."
Dariya ya yi. Sanye yake cikin shaddarsa ruwan toka, ya karya hularnan ta zannah Bukar ta zauna caras a kansa. Yana daga cikin mota zaune a inda ya fiddo ƙafarsa ɗaya waje.
"Ke din ce sai da hakan, farko na so kiran wayarki sai kuma na fasa tunda nasan dai zai wahala ace a wannan lokacin ba kya gida. Malam Bala kuma ni na roƙeshi akan kar ya ce ni ne saboda yau zuwan naki ne ke ɗaya."
Ta ɗan sadda kai ta yi shiru, ta san tatsuniyar gizo ba ta wuce na ƙoƙi. Abu ne da ba ta jin har abada za ta iya aminta da shi.
"Ɗan zagayo mana ki zauna."
Ba tare da musu ba ta zagaya ta bude motar ta shiga, kamar yanda ya bar ƙofa a buɗe, itama hakan ta yi. Gaidashi ta soma tare da tambayar iyali da wajen iyayensa. Ya amsa mata cike da annashuwa.
"Kin ɓuya da yawa, ta ko'ina gujemin kike kamar rai da ajali. Na rasa hanyar ɓullomaki. Sai na kiraki ki share ki ƙi ɗauka, daga baya na samu text dinki wai ba kya kusa ne nayi hakuri. Anya kuwa?"
Kunya ta kamata, ashe dai ya gane. Ita kuwa dalilinta na yin hakan a ganinta mai ƙarfi ne. Kokarin nesanta kanta da shi ta ke yi ta kowace hanya don ba ta son jawowa kanta magana.
"Ka yi hakuri."
"Na yi, amma ba duka ba. Ramlat, Maman Ummi, Ansar da Affan. A karo na biyu ga Hilal nan, bai kuma zo da niyyar yaudara ba. Aure ne ya kawoshi idan har kin amince."
Ajiyar zuciya ta saki don dama ta san maganar kenan, jikinta ya yi sanyi da irin wannan soyayyar ta Hilal gareta. Ta dubeshi, shi dinma ita yake kallo babu ƙaƙƙautawa. Ɗan kauda idanunta ta yi.
"Ko da can ma ba ka zo min da niyyar yaudara ba balle kuma yanzu. Asalima ni ce na yaudareka. Ka yi hakuri Yaya Hilal. Don Allah ka yi hakuri."
Ta ƙarashe a raunane, ita sam ba ta san ta
"Ka yi hakuri."
"Ba hakuri za ki bani ba, dalilinki na guduna za ki faɗamin. Idan da wajen da na kuskuro na gyara."
Girgiza kai ta shiga yi, kwalla ta soma ciccikomata idanu. Hilal wane irin mutum ne mai matukar sanyi da hakuri? Wace irin soyayya yake mata da ya kasa ganin laifinta?
"Akwai abubuwa da dama da ya kyautu na gujeka dominsu. Ba ka taɓa yimin laifi ba, ba zan iya kallon danginka a karo na biyu ba a matsayin matarka. Bayan abinda ya faru wa kake tunanin zai ƙara kallon Ramlat matsayin matar kirki? Wallahi da kaina na faɗa, bani da kirki, ban yi halin hakuri da dattako na iyayenmu ba. Ka yi hakuri Hilal, mu ƙaddara ba'a rubuto aure tsaka.."
Ta kasa ƙarasawa saboda kunya da kuma irin hararar da ya watsamata. Can kuma ya numfasa ya runtse ido. Da ace ta san yanda yake jinta a rai da ba ta ce haka ba, a gefe guda kuma bai mance irin kalaman da iyayensa suka yi gareshi ba muddin ya ce zai aureta ko bayan ransu ne. Kansa ya yi zafi da yawa.
"Ka yi hakuri."
Ta kara nanatawa, a wannan lokacin tuni hawayen sun zubo. Ya bude idanunsa da suka kaɗa ya dubeta.
"Bana jin har abada zan manta da ke Ramlat, you are my first love. Ki daina bani hakuri, da ace zan iya da tuni na rarrashi zuciyata. Aurenki da Aliyu na dauki hakan matsayin rubutaccen al'amari wanda ba makawa sai ya faru. Albarkar auren gashinan mun gani (yana nufin yaranta), don haka ni wallahi tuni na yafe abinda kika yi gareni. Idan da naki a sannan, nima ai akwai nawa tunda ni na naace akan sai na aurekin ko ba so. Kar ki saurin yanke hukunci a kanmu, na baki nan zuwa sati kiyi tunani mai kyau, koda ba ki kirani ba, da zarar lokaci ya cika zan kawo kaina."
'Allah Sarki.' Ta furta a ƙasan ranta. Da wannan suka rabu ya bata kayan maƙulashe na alawa da biskit da ya siyowa yara. Ta karɓa gami da godiya suka yi sallama ta shige ciki.
Hajiya zaune a falo ta a gyangyaɗi kaɗan-kaɗan, yaran sun ƙurawa talabijin idanu su na kallon Angrybird.
"Waye ne ya zo?"
"Yaya Hilal ne."
Hajiya ta mike zaune.
"Yaronnan dai dagaske ya ke yi."
Ramlat ta zauna jikinta a sanyaye.
"Na rasa ya zan yi Hajiya, ya dage aurena ya ke son yi. Na rasa hanyar ɓullomasa ya fahimci illolin da hakan zasu haifarmin a danginsa da wurin matarsa."
"Nima bana goyon bayan aurenki da shi, sai dai bamu san abinda Allah Ya ɓoye ba tunda har ya kasa hakuri ya dawo karo na biyu. Shawara ki dage da addu'ar neman zaɓin Allah, duk abinda Ya yi mai kyau ne."
Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa.
***
A kwana a tashi ba wuya a wurin Mai Rahma, bikin Munir ya taho. Ana gobe za'a yi ɗaurin aure ƙalilan daga mutanen Daura suka iso don Hajiya ba ta yi gayyata ba duba da cewar ba'a jima da bikin A'isha ba.
An daura aure lafiya, a daren aka yi shirin tafiya dinnerparty. Ramlat da yayyunta mata har A'isha da Amrah wacce basu daukarta bare cikinsu, ankonsu iri daya na wani leshi peach colour. Kowannensu riga da skirt ya zauna ɗas a jikinsa.
Motarta daga ita sai Amrah don Yaya Munir ya ce babu yara. Suna tafe suna hira, anan take ba ta labarin sauyin da aka yi mata wurin aiki, ta kara da fadin.
"Tsorona daya, rashin sanin taƙamaiman manufar wannan Chairman ɗin. Ina tsoron ya kasance wani mugun abin ne."
Amrah tana taunar cingam din da ya zamemata ciki tun tana laulayi har a yanzun da cikinta ya shiga watansa uku.
"Kar wannan ya dameki, ai kinsan kanki. Daidai gwargwado kin san mutuncin kanki kina kuma karewa. Addu'a za ki yi ta yi akan Allah Ya kareki daga sharrinsa. Ba abinda zai faru amma shakka babu dai akwai wata a ƙasa!"
Jinjina kai Ramlat ta yi.
"Wallahi ko ba ki faɗa ba Amrah, ni ban taɓa ganin mace mai irin kishin na wannan matar ba."
Amrah ta ɗan muskuta.
"Af, kin ce za ki nunamin hotonsa."
Ta yi murmushi.
"Mu ƙarasa tukunna."
Daga nan suka faɗa wata hirar ta daban har ta ke sanarmata da kiran da Baba Dakta ya yi mata. Amrah banda dariya da hamdala ba abinda ta ke yi.
Wurin ya cika sosai, mafi yawa dangin Amarya Hunainah ne.
"Ke me ya kawo waccan wurin nan?"
Cewar Amrah tana kallon Salma kanwar Bilkisu.
Idanun Ramlat ya kai gare ta. Taɓe baki ta yi.
"Au ke duk hirar da su Maman Twins suke yi ba ki ji ba? Cewa fa aka yi itama Bilkin za ta zo. Ita gwanar kissa."
Suka yi dariya suka karasa ciki basu kara kallonta ba. Salma ta bisu da harara ta ja dogon tsaki gami da fadin
"Munafukan banza!"
Koda sun ji basu tanka ba.
Sai da suka samu wuri suka zauna kafin Ramlat ta fiddo wayarta ta lalubo hoton ƴan biyun da ta dauka ta miƙa wa Amrah. Sakin baki da hanci ta yi tana kallonsu.
"Wow! Ke wai Twins ne? Toh ai banda gilashin da ke idanun daya, ba za ka ganesu ba. Lallai wallahi ban ga laifinta ba, dole ta yi kishi. Amma kika ce babba ce?"
Amrah ta ƙarashe fuskarta ɗauke da tsantsar mamaki. Dariya ta ba Ramlat.
"Dattijuwa ma kuwa don idan ma ba ta yi sa'ar Hajiyarmu ba, kadan ya yi mata saura ta yi. Ke kin gani kinsan wuff ta yi da shi."
Suka yi dariya can kuma Amrah cike da tausayawa ta ce.
"Wallahi nidai sai naga kamar ba banza ta bar shi ba. Wannan kyakkyawa ya tsaya a auren sa'ar uwarsa? Gaskiya jikina na bani akwai wata a ƙasa Ramlat."
Ramlat ta gyara zama don ta sosamata inda ke mata ƙaiƙaiyi.
"Ke kenan da ba ki ma ga matar ba. Ni banda duka wannan kinsan cikin biyunnan na hoto ba wanda ban hadu da shi ba?"
"Me kike nufi?" Amrah ta tambaya da rashin fahimta.
Ramlat ta bata labarin kaf haɗuwarta da Mutumin Mall (AlHassan) da kuma Hussein da ma yanda aka yi ta ga hotonnan.
"Tun ganin bayanin da ya rubuta kasan hoton na kara tabbatar da zargina. A farko da na ganshi a shago na gane ƴan biyu ne, tunanina sai ya ba ni ko su na tare ne da ya zo Kanon jin daga baya ya ce shi Adamawa su ke. Wannan ne ya kara sanyawa na dasa alamar tambaya ga lamarinnan. Mai yiwuwa su na nemansa ne basu san ma inda ya ke ba, mai yiwuwa kuwa mallakeshi Hajiyarnan ta yi sun san inda ya ke amma ya ƙi sauraronsu."
.
"A'a haba dai, me kika ce ya rubuta? Allah Ya bayyanamusu shi, kinga kuwa basu da masaniyar a inda yake rayuwa ma kenan. Gaskiya Ramlat babban jihadi za ki yi idan har kika zama silar saduwarsa da ƴan uwansa."
Jinjina kai Ramlat ta yi zuciyarta cike da tsantsar tausayin Hussein da AlHassan.
"Ina fatan na yi hakan Amrah, sai dai abu ɗaya, ina tsoron na ɗauki matakin da zai sa ya bar gari a rasa inda ya shiga. Ma'ana, idan kai tsaye na cewa shi Abban Fatima cewa nasan inda ɗan uwansa ya ke, idan ya zo ya ganshi shi kuma ya ƙara sauya garin da za'a rasa ina ya ke, kinga anan an yi ba'a yi ba, wannan ne dalilin da yasa zan fi kaunar na soma sanin meke faruwa ko ya ya ne daga shi na Kanon kafin a san abin yi. Wallahi tun sadda na ga wannan hoton, Hussein ya shiga cikin jerin mutanen da nake tayawa da addu'a. Tausayi ya ke ban, na kuma rasa dalilin da yasa nake yawan tunanin lamarinsa."
Wani murmushi Amrah ta yi gami da dafa hannunta.
"Tunda kika ga haka, babban alheri ne haɗuwarki da wadannan bayin Allahn. Ɗari bisa ɗari na goyi bayanki, ko yaya ki samu ki soma tunkarar Hussein, sai dai ki sani, idan har bai saba da ke ba, ba lallai ne ya ba ki damar da za ki san wani abu dangane da shi ba. Ki nemi yardarsa kafin ki nemi ko menene. Abu na biyu ki yi takatsantsan da duk abinda zai sa matarsa ta ƙara ganinki tare da mijinta. Na uku kuma wanda shi ne ma ya kasance na farkon fari, ki haɗa da addu'a sosai, nima zan tayaki. Allah Yasa ta dalilinki wannan bawa ya sadu da ɗan uwansa."
Murmushi sosai Ramlat ke yi har dimple dinta na fitowa raɗau.
"Amin amin."
Ta amsa cike da jin dadi da kuma farin cikin samun Aminiya kuma ƴar uwa ta gari.
Washegari aka kai Hunainah ɗakinta, Ramlat ba ta je ba don ta san za ta hadu da dangin Hilal sosai a bangaren Bilkisu. Ta dai ji irin salon Bilkisu wacce ba ta nuna komai ba asalima nunawa ta yi ta karɓi Hunainah da hannu bibbiyu za kuma su zauna da juna bisa amana. Da wannan dangin Hunainah suka miƙata ɗakinta wasu na yabon hakurin da Bilkisu ta yi yayinda wasu ke fadin ai ta ciki na ciki.
***
Ranar Litinin ta soma aiki a matsayin sakatariyar Chairman. Tana zaune a inda aka tanadar mata ya shigo bayansa daya daga cikin ma'aikatansa ne rike da jakarsa. Kallonta ya yi sannan ya shige ciki bayan a ladabce ta mishi barka da zuwa.
Jimawa kaɗan ya kira wayar dake saman teburinta, ta mike ta shiga ciki tana kara gyara zaman ƙaton hijabinta don ta yiwa kanta alkawarin ba za ta ƙara sanya mayafi ta zo aiki ba ko don tseratar da kanta daga sharrin Chairman. Idan ma wancan karon wani abin ya hango, wannan karon sai dai ya gama baza idanun ya haƙure. Abinda ba ta sani ba shi ne, tafiyarta kaɗai ma abin ɗaukar hankali ne.
Yana zaune ya na waya, ta shiga da sallama bayan ta kwankwasa ya mata iznin shigowa. Tana tsaye har ya kammala wayar wannan mayun idanunnasa yana kan fuskarta kamar ya cinyeta. Ta yi tsaki ya fi a ƙirga a ƙasan ranta.
"Malama Ramlatu, have a seat."
Abin ya mata banbarakwai namiji da suna Hajara, ta zauna a ɗarare. Bayani ya shiga koromata akan abinda ya shafi aikinta, ita dai kai take gyaɗawa a ladabce tana amsa da kuma fadin za ta kiyaye. Abu ne da Staff Officer ya gama shaidamata, ba ta ga dalilin da a karo na biyu zai maimaita ba, a ganinta don hira ne kawai.
Bayan ya kammala ya ce.
"Ba ki yi mamakin dalilin da yasa kika dawo ƙarƙashina ba?"
Sai lokacin ta dubeshi, ta yi saurin kauda kanta don ba ta kaunar wannan shegen kallon ƙurillar da yake jifanta da shi. Kallo na ƴan duniya.
"Aiki ba inda ba ya kai mutum."
Abinda ta ce kenan kawai. Ya yi baya ya kwantar da kai jikin kujera yana ƴar dariya.
"Hakane kuma. Har kin kara burgeni, da alama kina da kyautata zato. Nayi tsammanin za ki firgita ganin kusancina da Hajiya Zeenatu."
Fadin hakan yasa gabanta ya fadi, ta dubeshi cikin dakiya.
"Ko kusa, ai mutum bai isa yi maka abinda Allah bai yi ba."
Maimakon ta ba shi haushi matsayinsa na shugabanta, sai ta burgeshi ainun, ya kara jin kamar wani magnet na fisgarsa zuwa gareta. Ba ya so ya yaɗa manufarsa da wuri, don haka cikin dakiya ya sallameta bayan ya ba ta umarnin duk wanda ya zo idan har staff ne ba ya buƙatar ganinsa. Da wannan ta amsa sannan ta fice daga ofis din don dama abinda ta ke jira kenan.
Bayan fitarta Chairman Aliyu Dikko ya runtse idanu ya ɗan bugi tebur yana murmushi.
"Wannan ita ce daidai da ni, ita ce kalata."
Ya fadi a fili cike da jin wani nishadi. Abu na farko da zai soma siye zuciyarta da shi, shi ne kyauta. Zai yi komai da zai sa ta saki jikinta da shi