Showing 123001 words to 126000 words out of 226732 words

Chapter 42 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12478

ke bin ta da shi ba. Ta shiga motarta ta bar wurin cike da jin haushi kanta, me ya kai ta wannan gangancin?

***
MAFARIN KENAN.....








 

  I just published "BABI NA TALATIN DA TARA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/dCw5vESQqbb




🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

39)


Jikin Hajiya ya yi sanyi bayan gama sauraron Ramlat. Sam ba ta tsammaci hakan ce za ta faru ba. Ta dauka dai faɗa akan fiddo mijin kawai za'a yi mata. Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon yanda Ramlat ke kuka kamar ranta zai fita.

"Ke fa na yarinya ba ce, kin kuma sani dama can ba'a yi miki dole ballantana a kwata wannan karon. Da ace wani ne ba shi Maigidannaki ba, toh ba lallai ya dameni ba. Amma sam bana son wannan haɗi na Yaya Bello. Duk ke kika jaza wa kanki ai Ramlatu, tun yaushe ake biyamaki karatun fidda miji kin ƙi haddacewa balle ki yi aiki da shi? Yanzu gashinan an miki shigo-shigo ba zurfi."

Ramlat ta dubeta tana sharce hawaye.

"Nima Hajiya ba wai ba zan bi umarninsa ba ne, sai dai nasan waye Chairman tunda ni ke aiki karkashinsa. Ya sha nunamin zai zo gidanmu ina ƙin ba shi dama don na riga na san waye shi. Ban ɓoyemaki komai dangane da alaƙarmu ba. Yanzu kam an zo gaɓar da zan bar ma'aikatar Revenue, ba zan iya ci gaba da zamansa ba. Ya kamata ace dama tun a baya na yanke wannan hukuncin. Amma yanzun ma lokaci bai ƙuremin ba."

Kai Hajiya ta jinjina.

"Ina bayanki, ya dace yanzu kuma ki bar masa ma'aikatar duk da ba tasa bace ta gwamnati ce, kinga kenan ba shi da wata ƙafar da zai yi amfani da ita wajen cin zarafinki ko yi miki bita da kulli. Ni ai tunda ki ka ce ya san waccan matar hankalina bai kwanta ba."

Nan da nan Hussein ya fado ranta, ta dubi Hajiya. Ta ji tana son zayyanemata komai.

  "Hajiya kin tuna baƙinmu na Adamawa?"

"Ta ya zan mance su, mutane masu karamci haka Ramlatu? Meyafaru?"

Hajiya ta tambaya cike da ƙaguwa. A zatonta, abinda ƴan uwan Ramlat din ke zargi ne zai tabbata, wato soyayya tsakanin Alhassan da ita. Abinda ba za ta yarda ba kenan ko don mutunci da girmamawar da Kausar ke mata.

"Kinsan kuwa suna da alaƙa da Hussein da nake ba ki labari mijin Hajiya Zeenatu?"

Ido waje Hajiya ke dubanta.

"Alaƙa wace iri?"

Tiryan-tiryan ta ba ta labarin duk abinda ta sani. Sai ga Hajiya na salati har da hawayen tausayi.

  "Kai duniya! Mata me muka dauketa ne? Matattarar da za'a dauwama ko me? Zunuban kanmu kaɗai bai isa ba sai mun zalunci wasunmu? Kaico da wannan rayuwa. Allah Ya sakawa wannan yaro, Allah Ya karya ƙadarin wannan mata."

Hawayen Ramlat suka ci gaba da ambaliya, sam ba ta faɗa wa Hajiya abinda ya faru tsakaninsu a yau ba, hankalinta ya yi kansa sosai, tana son ta ji muryarsa ko don tabbatar da lafiyarsa.

"Amma wannan fa ba karamin aiki ba ne na wasa, addu'a ce sosai zamu dukufa ga yi masa. Zuwa anjima zan kira Kawunki Malam Yakubu. Na tabbatar shima zai taimaka. Ba a banza matarnan ta bar shi ba."

Zantukan Hajiya masu dadin sauraro suka katsemata tunani. Wani sanyin dadi ta ji, har ta mance kaso mai yawa na damuwarta, ta yi murmushi gami da godiya. Daga wannan ta mike ta bar mata dakin zuwanata.

Nan ta iske yaran sun yi baja-baja saman gadonta ana game a waya. Dubansu ta yi gami da murmushi, haka kawai ta ji har ta soma kewarsu. Maimakon ta korasu kamar yanda ta saba, kawai sai ta zauna ta biyemusu tare da alƙalanci.
   Sai da wani tunani ya faɗomata sannan ta karɓi wayarta ta basu umarnin zuwa falo. Agogo ta duba, ƙarfe shida da rabi na dare, so ta ke ta kirashi amma ba ta kaunar abinda zai je ya dawo don haka ta zaɓi aikamasa saƙo.

***
  LAMIƊO CRESCENT...

Yana zaune kamar kurma yana sauraron Hajiya Zeenatu da ke buɗewa John wuta akan ya yi girkin da mijinta ya kasa ci. Ɗora laifi kacokan ta yi akansa, shi dai ƙara russunar da kai ya yi yana ambaton "Sorry Ma." Hussein da abin ya ishe shi, miƙewa tsaye ya yi gami da daukar wayarsa.

"Please ya isa haka, na fadamaki yunwar ce kawai ba na ji, ba wai girkin ba ne."

Yana kaiwa nan ya nufi matattakala. Ta bishi da kallo kafin ta maido dubanta ga John, harara ta watsamasa gami da ba shi umarnin tafiya. Hankalinta ya koma ga tunanin abinda ta shirya yi. Wato shan maganin da Gora ya ba ta wanda ya tabbatar da zarar Hussein ya kusanceta za ta samu ciki. Samun cikinta ne zai mantar da Hussein tunanin kowa da komai face tattalin da zai koma ba ta.

  Wannan ta sa da sauri ta jawo kofin ruwa ta daga riga ta ciro ƙullin maganin ta zuba gami da gaurayawa ta kafa baki, ba ta ɗago ba sai da ta shanye tas tana wani murmushi.

  Shi kuwa Hussein, zube wayoyin saman gado ya yi ya shiga rage kayan jikinsa, wanda ya ke da niyyar shiga, ƙarar shigowar saƙo ya ɗauki hankalinsa. Duban wayar ya yi, kamar kada ya buɗe sai kuma ya tuna da saƙon da za'a aikomasa na abinda ya shafi aikinsa. Madadin hakan ya ci karo da sunan da hannunsa ya rubuta saman lambar da ya ɗauketa da wani irin muhimmancin da bai san dalili ba.

  _*Heart*_

Ya furta tamkar baya so kafin ya kai ga buɗewa.

*_"Dukkanmu ajizai ne, mukan yi kuskure da saninmu ko kuma akasinsa. Bana fatan na yi abinda zai jefaka cikin ɓacin rai da damuwa. Shakka babu, Ramlat mai laifi ce, na yarda na shiga personal life dinka, na zaƙe da yawa. Ka yi hakuri, ka yi hakuri. Hakan ba za ta ƙara faruwa ba. Ka ji?"*_

  Murmushi ya yi, ya kara karantawa ya fi sau uku, ya so ya gogeshi daga wayar amma ya ji ba zai iyaba. Wani nauyi hakan ya yi mishi don haka sai ya fasa, ya sanyawa wayar muƙulli ya jefa saman gado. Har ya shiga banɗaki bai bar murmushi ba.

Fitowarsa ba jimawa ya sanya kayan bacci, shigowar Hajiya Zeenatu ne ya sa shi dubanta. Saura kaɗan wata dariya ta kufcemasa. Rigar bacci ce a jikinta shara-shara kuma marar tsawo don duka tsawon iyakarsa gwuiwa. Ƙaton tumbinta da  ruguza-ruguzan mamanta wadanda suka zube sun kwanta luf sun bayyana cikin rigar. Damtsenta kuwa a cike sosai sai dai ba ka misalta shi da na karfafan maza ba. Akwai bambanci.

Duba sosai ya ke mata, riga dai gatanan mai ɗan karen kyau da daukar ido. Lumshe idanunsa ya yi yayinda wani tunani ya bijiromasa.

  'Za ta yi kyau sosai.' Ya furta ƙasa ransa, ankara da kuskuren kalaminsa ne yasa shi jan istigfari. Sai kuma lokacin ya tuna da bai yi sallar Isha'i ba ya ke shirin kwanciya. Abin yana damunsa, ya rasa me ke shagaltar da shi daga bautar UbangijinSa, ma'ana gabatar da sallah akan lokaci. Abin yana mishi ciwo, sai dai mafi yawan lokaci ji yake kamar wanda aka mantar. Sau tari ma wani bacci ke zuwa ya rufe idanunsa da zarar an soma kiraye-kirayen sallah.

Ganin ya mike yasa Hajiya Zeenatu tunkaroshi, hannayenta biyu ta sanya saman kugunsa.

Ya yi mata murmushi mai kama da yaƙe. Duk yanda ya so nunamata tsana ko wani abun, sai ya ji ya kasa.

"My Zeenat, kin yi kyau sosai."

Wani sanyin dadi ya mamayeta, ta sumbaci leɓɓansa.

"Nagode Sweetheart."

Ganin tana kokarin wuce gona da iri yasa shi janye jiki.

"Bari nayi sallah."

"Sallah, wace sallar?"

Yanda ta fadi a mamakince shima sai ta jefashi cikin mamakin kalamanta. Ya zubamata idanunsa mai adon fari ƙal da baƙin kwayar idanu siɗik.

"Me kike nufi? Wace Sallah muke yi matsayinmu na musulmai?"

Gaban Hajiya Zeenatu ya bada dam!

_*"Kiyi duk yanda za ki yi, ki dinga shagaltar da shi daga ibada, zamu turamasa arnen aljan wanda zai tayaki yaƙi. Ina kara gargadinki! Kar ki kusa ki bari ya dinga sallah akan lokutanta!!!"*_

Wannan yana daga cikin farkon abinda Gora ya fadi mata sadda suka soma zuwa wurinsa a karon farko game da lamuran Hussein.

Ganin ta tsaya tana kallonsa yasa shi giftawa ya fice zuwa banɗaki. Ta bi ƙofar da kallo.

'Ke me zai dameki? Ba yanzu za ki yi aikin da za ki samu ciki ba? Idan kika samu komai zai zo karshe!'

Wani ɓangare na zuciyarta ya tunatar da ita. Ta sauke ajiyar zuciya tana wani irin murmushi kafin ta zauna gefen gadon. Tana kallonsa ya yi sallah a tsanake, ya yi addu'a kafin ya naɗe dardumar ya mike.

Mintuna talatin da suka biyo baya, komai ya kammalu kamar yanda ta ke so, murmushi kawai take kamar koyaushe cike da gamsuwa idan ka ɗauke Hussein wanda ransa sam ba dadi. Kusan hakan ce ta saba faruwa da su, zai iya cewa wahalar da shi kawai ta ke yi a kowace tafiya don ba wani gamsuwa yake ba. Ganin ta soma jan munshari yasa shi miƙewa ya faɗa banɗaki. Can ya fito ya sauya kaya, yunwar ɗazun ce ta dawo mishi. Matsawa ya yi ya tasheta. Cikin magagin bacci ta dubeshi.

"Lafiya?"

"Muje ki ɗan ɗumaman abinci, nasan yanzu John ya sanya a fridge."

Yamutse fuska ta yi.

"Wallahi na gaji, ko nan da can ba zan iya motsawa ba. Ka je kawai ka tasheshi ya yi maka."

Daga haka ta juya ta cigaba da bacci, girgiza kai ya yi gami da gyaramata abun rufa. Wayoyinsa ya dauka ya fita daga dakin cike da damuwa. Kamar akwai abinda ya rasa, kamar yana da wata damuwa amma ya kasa gane kan zaren.

Maimakon ya kira John da ya wuce Boysquarters, sai ya ɓige da dafa ruwan shayi, ya zaɓi shan tea da bread kawai. Sai da ya kammala ya dawo falon, wayarsa ya fiddo ya kunna Data. Kwanaki biyu kenan rabonsa da hawa online, wannan tasa saƙonni suka shiga faɗowa, da na mutanen da ya sani da baƙin lamba kamar koyaushe. Ya kuma riga da yasan baƙin lambobin bai wuce na mata, idan da sabo ya ci ace ya saba.

  Saƙonta ya ɗauki hankalinsa, ya kuma yi mamakin ganinta online, ya kara duban lokaci. Ƙarfe goma daidai na dare. Murmushi ya yi ganin amsar da ta ba shi a wancan lokacin, maimakon mayar da martaninsa sai ya ɓige da wata tsokanar.

"Ba ki yi bacci ba? Da wa kike hira toh?"

Yana aika hakan sai ya maida kai ya ci gaba da shan shayinsa. Tausayinta ya ji ya mamaye zuciyarsa, shakka babu sam bai kyauta ba.

***
A ɓangaren Ramlat, tana kwance ne tana kallon Status, duk duniyarta ba dadi. Ga lamarin Chairman ga kuma Hussein da ya yi fushi da ita. Tana shirin sauka ganin uban hamman da ta ke dokawa, sai ta nemi baccin ta fasa ganin saƙon da ya shigo. Da wani irin ɗoki ta buɗe ta karanta. Murmushi sosai take yi haɗe da dariya ciki-ciki. Ko ba komai hankalinta ya kwanta.

"Kai nake jira, hakuri nake so na ƙara ba ka."

Abinda ta aikamasa kenan.

***
  Yana kammala shan shayin, ya dauki wayar, ganin abinda ta ce yasa shi jin wani daam, lumshe idanu ya yi kafin ya buɗesu. Sai kawai ya zaɓi kiranta. Kai tsaye ya dokamata kira, sai da ya kusan katsewa sannan ta ɗaga.

***
  "Kira war haka? Ina Madam dinka? Ka rufan asiri."

Abinda ta ce kenan bayan ɗaga wayar.

"Ni kenan na tonawa kaina asiri ko? So kike yi a gane damuwar da ke kwance saman fuskata na jefaki a damuwa?"

Maganarsa sai ta yi mata nauyi, ta rasa amsar bayarwa, can ta daure.

"A'a, ni ce mai laifi, ni na zaƙe da yawa. Ka.."

"Kika ƙara bani hakuri ina miki rantsuwa da Allah za ki ganni a gidanku yanzu."

Yanda ya yi maganar daga ji ka san ba wai faɗa ya yi ne kawai ba. Kirjinta ya soma bugu da ƙarfi, ta ji kanta na neman tarwatsewa. Ta kasa gane a maudu'in da za ta jefa kalamansa. Ta rasa abinda ya haɗa kalmar hakuri da batun ziyartarta a wannan lokaci don haka sai ta kasa cewa uffan.  Shiru ya biyo baya na ƴan sakanni sai numfashin junansu da kowanne ke jin fitarsa.

"Ɗazun na ce kinsan me? Ba ki bari na ƙarasa ba, yanzun ki bani damar na ƙarasa maganata."

Ta kasa ce mishi uffan. Har ya kara magana.

"Na baka." Ta furta a hankali.

"Ke ce mace ta farko bayan Zeenat, da lambarta ya shiga cikin wayata har nayi saving. Ke ce mace ta farko da ƙafata ya taka har gidansu, ke ce mace ta farko da na zauna muka yi hira da ita har na tsawon mintoci ba tare da naji hirar ta ishe ni ba. Kawai dai idan so ki sani, kina da babban matsayi a rayuwata da ba zan ce gashinan ba. I want you to keep staying in my life, ina jinki kamar wata ƴar uwata mai bani ƙwarin gwuiwa. Kamar dai kina ban ƙarfin ci gaba da rayuwa, na daina tunanin inama Allah Ya dauki raina, na bar tunanin bani da kowa a duniya. Please Ramlat, kar ki gujeni ko me zai faru, ko me zan miki. Kiyi hakuri, nayi maki laifi a ɗazun da ni kaina ba haka na so ba. I just can't do otherwise idan aka zo irin wannan lamarin. Ban kuma san dalili ba."

Wani sabon yanayi ke shigarta game da HUSSEIN, wani abu take ji na yawo tun daga tsakar kanta har yatsun ƙafafu. Zuciyarta gaba daya ta cika da tausayinsa. Ganin kamar tana neman wuce gona da iri yasa ta saurin magana.

"In sha Allah hakan ba za ta faru ba. Allah ne Ya haɗa mu, ban isa na kawo karshen zumuntarmu ba. Ina rokon Allah Ya yayemaka dukkan damuwarka. Sai dai don Allah ina roƙonka akan ka dage da kai kukanka gareSa. Kamar yanda ka bani shawara a ɗazun, kaima yanzu ina so ka yi amfani da hakan."

Murmushi ya yi mai sauti yana ƙara gyara mazaunin wayar, ƙafafunsa a saman kujera.

"Kina shiga haƙƙin Madam ɗita fa."

Harara ta bugamishi kamar yana kallonta, wani abu ta ji kamar ya soke ta a ƙahon zuci mai kama da KISHI.

"Ai ba ni na kiraka ba, sai da safe."

Tana ji yana dariya sadda ta datse kiran. Ita kuwa kwanciya ta yi ta shiga duniyar tunani. Murmushi sosai ta ke yi, wani sabon yanayi take ji game da Hussein wanda a yanzu ta kasa ƙaryatawa. Tunaninta ya tsaya cak! A gefe guda kuma tausayin kanta ya mamayeta. Wato dai ta gama fahimtar ta faɗa SON MASO WANI.

Miƙewa ta yi ta faɗa banɗaki ta dauro alwala, nafila ta shiga yi kafin ta yiwa Hussein addu'a ta musamman.

***
  Washegari ta tashi ranta fari ƙal, kaso mai yawa na damuwarta ya yaye. Ta yarda ta kuma aminta, ta rasa dabara ko wani makami da za ta kare kanta na cewar ta faɗa tarkon SO.
Tana kai yara makaranta ta wuce kai tsaye Head of service inda ta kai takardar neman transfer da ta rubuta. Kusan sun yi waya da Zulaihat da Rafee'ah, duk sun goyi bayanta don a cewarsu mutunci ya fi komai.
   Kai tsaye ofishinsa ta nufa ganin da ta yi ya iso. Kwankwasawa ta yi gami da sallama, jin muryarta da gaggawa ya bata umarnin shigowa. Ta shiga fuska a haɗe. Kallonta yake har da ɗan miƙewa duk ya rikice. Ya san da cewa ya mata laifi amma ba yanda ya iya, gani ya yi idan ya biyemata to fa za ta kai shi ta baro ne. Ba tare da ta damu ta gaidashi ba ta fiddo ƙaramar envelope waanda ta sanya dukkan kuɗaɗen da ya bata.

"Idan har wannan ce damar da ka samu na zuwa tambayar aurena a gidan iyayena, to ka sani daga yau na rusata. Kuma kar ka manta, ni ba yarinya ba ce ballantana ka yi tunanin za'a tursasani ko a yimin dole akan aurenka."

Ta zazzage kudin saman tebur.

"Ka ƙirga ka gani, idan da su kake taƙama har ka yimin wannan aika-aikar, ko sisi ban taɓa a cikinsu ba. Ina fatan daga yau komai zai wuce. Kar kuma ka kara tunanin cewa zuwa wurin Kawu Bello zai ba ka dukkan wata dama a kaina."

Daga haka ta juya da zummar tafiya ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Ta juyo tana dubansa fuska a daure. Gaba daya ya sauya fuska.

"Haba Ramlat, saboda na bi hanyar da addini ya tsara na neman iznin aurenki gurin magabata shi ne za ki watsan ƙasa a ido? Wannan wace irin kiyayya kike nunamin? Ina da kudi, ina da gidaje da dukkan matsayin da na cancanci ki so ni dominsu, amma ke wannan duk bai sa kin saduda ba. Idan don matana ne, wallahi wallahi ba zan haɗaki gida ɗaya da su ba. Kin ji rantsuwar ɗan musulmi. Ya kike nema ki yimin wannan kwalelan?"

Ta dubeshi duba na raini, ita dariya ma ya soma bata.

"Ni kudi bai isa ya siyeni ba, hakanan ba kuɗi ake nema a zamantakewar aure ba. Yarda, biyayya, kauna, so, mutunci, daraja da ƙima dama sauransu, su ake neman a aure. Babu ko daya da ka samu a idona. Ina kara neman alfarma akan ka rabu da ni ka fita daga rayuwata. Ba zan iya aurenka ba."

"Idan kudi na siyan soyayya! Wallahi Ramlatu sai kin aureni koda ba kya so! Mu zuba ni da ke!!"

Ya fadi a tsawance, kalaman sun faɗarmata da gaba, ta dake ta yi murmushi.

"Allah Zai tsayamin."

Daga haka ta sa kai ta fice dama ba da niyyar zama ta zo ba. Maimakon ta yi gida sai ta nufi gidan Amrah da aka sallama, ƙara duba jikinta.

Ta sameta kamar ba ita ba don Magajiya har ta koma gida. Tun a asibitin suka sauya shawara, da ace ta dawo gida gwara Magajiyar ta biyota gidanta su kwana tare.

"Ya na ganki wata iri? Ke kullum dai da damuwa kike zuwarmin." Amrah ta ƙarashe cike da zolaya. Harara ta samu daga Ramlat. Sai kuma ta ja tsaki.

"Ke kinsan dalilin wai da yasa Kawu ke nemana?"

Amrah ta girgiza kai. Nan ta labartamata komai da komai har haduwarta da Hussein da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login