Showing 174001 words to 177000 words out of 226732 words
ke cin Popcorn duk ta ɓata hannunta da madara. Hafsat kuwa ɗaki ta shige gudun kar AlHassan ya gan ta. Sallamarsa ta yi yanayi da ta AlHassan, hakan yasa Fatima wurgi da ledar Popcorn a guje ta nufeshi idanunsa akan Dada, ya durkusa ya ɗaga ta cak kafin ya rungumeta. Dada tsam ta miƙe jiki na rawa tana mai ƙuramasa idanu, a hankali idanunta suka ciko da kwalla. Nan da nan ta shiga zubar da hawaye, ta kalli AlHassan ta dubeshi, da sauri ya ajiye Fatima wacce ta yi turus tana kallon wanda ya ɗaga ta alhalin ga babanta a baya ya shigo. Da sassarfa ya isa ga Dada ya rungumeta kawai sai hawaye masu ɗumi suka zubomishi.
"Dadata." Dada ta lumshe idanu ta bude, shakka babu ba mafarki ta ke yi ba. Da sauri ta ɗago kan Hussein ta na shafa fuskarsa da duka hannuwanta biyu. Kukanta bai tsaya ba hakan ya jawo mata rawar murya.
"Husseini, kai ne? Dagaske kai ne tsaye a gabana? Allahu Akbar."
Kawai ta kara ƙarfin kukanta. Ya ja hannunta suka zauna saman kujera, ya zame hannunsa guda cikin nata. Ya shiga sharemata hawaye.
"Ni ne Dada, Hussein dinki ne. Na dawo gareki Dada. In sha Allah ba zan ƙara nesanta kaina da ke ba. Ki yafemin, wallahi ba ni da laifi."
Ta shiga girgiza masa kai amma ina! Ta kasa magana don kuka sai kuma ta shiga dariya da hamdala.
"Yaya Hussein?" Hafsat ta fadi a hankali bayan fitowarta daga ɗakin hayaniya ta ƙi ƙarewa. Ta ƙarasa itama ta rike hannunsa, kallonta ya ke yi da mamaki kafin ya yi ƴar dariya ya dubi Dada.
"Auta kenan?"
Ta yi murmushi kawai, ba ƙaramin mamaki ya yi ba.
"Shekaru bakwai fa Husseini, jiya ba yau ba. Tun kana da shekaru ashirin da takwas muka rabu da ganinka."
Hawaye Dada ta share tuna irin jinyar da ta yi adalilin rashinsa.
"Ya isa kukan please Dada. Mu godewa Allah tunda yanzun ya cika buri."
AlHassan ya furta don har ga Allah ba ya son ganin ana kuka, musamman ma kukan Dada.
Nan fa aka shiga nan nan da Hussein, abinda ya fi so a baya, wato fura da kuma dambun shinkafa, shi Dada ta sa Hafsat ta yi. Dakyar Hussein ya rarrasheta akan a bar Dambun dare ya yi sai zuwa gobe.
Bayan sun gabatar da sallar isha'i suka zauna zaman hira. Shiru ya yi yana jin AlHassan na waya da su Hajiya yana sanarmata cewa sun sauka lafiya. Bayan ya kammala ne aka shiga hira. Tiryan-tiryan AlHassan ya ba Dada labarin komai tun daga farko har ƙarshe. Dada kuka ya dawo sabo. Takaicinta yanda matar ta ɓatawa ɗanta ƙuruciyarsa.
"Me ka ke jira ba za ka saketa ba Husseini?"
Murmushi Hussein ya yi gami da ɗan matsa ƙafar Dada kaɗan.
"Komai yana da lokaci My Dada, ki kwantar da hankalinki."
Ba haka Dada ta so ba, sai dai kuma ba ta tsoron komai tunda ta san ki mene yanzun da asiri a ciki. Da yardar Allah kuma hakan ba zai ƙara faruwa gareshi ba.
Tahir dai kallonsu yake kawai, ya lura da ɗan sauyin da Hussein ya soma gwadamishi tun da ya ji alaƙarsa da Kawu. Bai yi mamakin komai ba don ya san dama za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Shi kam yana tunanin fasa tafiya Kano da zai yi a goben sai zuwa jibi duk kuwa da irin wayar da Kawun ke dokamishi akan ya dawo.
Washegari da safe dangi suka cika ganin Hussein, Gwoggo Karime har da kukanta, takanas ta tahowa da Hussein lafiyayyen farfesun da ta girka da hannunta. Hakanan shima Kawu Adamu, hatta da sauran yaran Inna da ke a Adamawa da yaran Hajjo sun zo ganin Hussein. Gida ya cika ana murna, ya yi mamakin yanda suka sauya. An sha hira kamar ba gobe. Fatima tunda ta gane dan uwan mahaifinta ne ta maƙale masa, wannan kaunar nata da ya soma yi tun bai san dangantakarsu ba yana nan daram a ransa sai ma ƙaruwa da ya yi. Kowa ya yi Allah wadai da Hajiya Zeenatu, har da masu kuka.
Ranar dai har dare bai samu kansa ba sai dakyar. Hajiya Zeenatu ta kira sai hakuri ya ba ta ya nunamata ana ta tambayarta da son ganinta.
"Ko na biyo hanya gobe na zo?"
Ya yi murmushin mugunta jin irin wannan wauta daga matar da ta kusa dosar shekara hamsin.
"Aa Hajjaju, ki yi zamanki, idan zan ƙara zuwa sai mu dawo tare. Dawowar dindindin."
Wannan amsar ya ba ta sai ta ɗan yi turus, a karshe dai ya yi mata dabara ta sake kafin su yi sallama.
Ƴan Maiduguri labari ya riskesu su ma sai murna. Hussein ya san zama bai gan shi ba, zaga dangi ya zamar masa dole.
***
BAYAN SATI BIYU..
KANO
Ta fito daga motarta a farfajiyar asibitin Baba Dakta. Amrah aka yiwa aiki sakamakon faɗuwar da ta yi a bandaki da ya jazamata naƙudar dole, cikinta bai jima da shiga wata na takwas ba, an ciromata Baby Boy. Yaron sai ka rantse ya shiga watansa tara cif sannan ya fito duniya. Ta zagaya ɗayan gefen ta ɗauki kwandon abincin da ta kawomusu Da ka ganta za ka fahimci tana cike da farin ciki. Tun da ta ji labarin auren da Chairman zai yi na huce haushi take jin ta kamar an mata albishir da gidan aljanna. Yanzun ta kara tabbatarwa babu abinda zai ƙara haɗa ta da shi. Ta sha adonta cikin laffaya dark brown mai adon milk flowers a ƙarshensa. Fuskarta babu wani heavy make up, hoda kawai ta shafa sai man leɓe mai danƙo. Ga duk wanda ya ganta sai ya ƙara kalla, Allah Ya ba Ramlat ƙira mai kyau, sai ka rantse ba ta taɓa haihuwar ko ƙwai ba ballantana ɗan mutum. Da wannan takun ta ƙarasa cikin asibitin zuwa dakin da aka kwantar da Amrah. Ta murda kofar da sallama ta shiga.
Umman Amrah na zaune gefe tana kurɓar ruwan shayi, ta karasa suka gaisa. Amrah na bacci. Ajiye kwandon ta yi ta ƙarasa ga gadon Babyn, murmushi kawai ta ke yi tana ƙaremishi kallo, duka-duka yau kwanansa hudu a duniya.
"Ki ciro shi mana Ramlat, ke da ɗanki."
Ta juyo tana dariya kadan.
"Um um, gwara ya yi baccinsa Umma. Ni gani ya yi yana juyewa zuwa kamannin Zaituna."
Umma ta yi murmushi.
"Gashinan dai, sai sauya kamanni ya ke."
Ta jinjina kai.
"Naga kin warware sosai yanzu, ko don kin ji labarin auren Chairman ne?"
Umman ta karashe da dariya, itama dayake abinda ke ranta kenan sai ta sa dariyar.
"Umma bari kawai, sosai fa na ji dadin rabuwa da alaƙaƙai."
Dariya sosai ta ba Umma.
"Kai Ramlatu ba ki da dama, wato alaƙaƙai? Ko ya suka ƙare da Kawunnaki?"
Ta ɗan taɓe baki. Chairman a farko cewa ya yi dole Kawu Bello ya biyashi kudaden da ya kashemusu, daga karshe dai ya yafemasa ya ce komai ya wuce.
"Yanzu ki ka zo?"
Muryar Amrah ta katse su. Suka dube ta.
"Yanzu na zo, sannu ya jiki"
Amrah ta amsa tana kokarin mikewa zaune, cikin sauri Ramlat ta karasa ta taimaka mata. Ita ta yi mata rakiya bandaki ta yi fitsari da kuma brush sannan suka dawo. Umma kuwa ta gyara shimfidar ta kwantar da ita.
Ramlat ba ta wani jima ba ta yi musu sallama ta fice zuwa wurin aikinta. Tana tafe tana tunani, idan har Hussein zai iya mance ta ko a whatsapp bai neme ta ba, ita kuwa meyasa ba za ta dangana ta hakura da shi ba? Ta gama saddaƙarwa babu ita a ransa, ba ya ta tata. Don haka tana ji har zuciyarta ta hakura da soyayyarsa. Da gaskiyar Auta A'isha da ta taɓa ce mata gani take kamar Hussein ya fi ƙarfinta, yanzun kuwa ta yarda kuma ta gasƙata. A hankali ta sa bayan hannu ta share kwallar da ta cika idanunta. Muddin zai faɗomata a rai to fa sai ta ji kwalla.
Wayarta ta ɗauki ƙara, ta kai duba. Baban Hanif, kamar yanda ta sanya sunansa, wani ne da ba su yi ko sati da haɗuwa ba, ta kai yara shopping, a farko ya dauka tana da aure don haka ya hakura, sai dai haduwarsu ta biyu a kofar gidan Hisham kasancewar shi gidansa a Badawa Layout yake, ya ganta. Ya san Hisham don haka bai ƙasa a gwuiwa ba ya faka motarsa ya sauko suka gaisa da Hisham, ta gaidashi ta shige cikin motarta. A bakin Hisham ya ke jin cewar ba ta da aure, anan ya nunawa Hisham yana so. Hisham ya yi shiru a sannan, a karshe ya nunamasa ba ruwansa ya nemi soyayyarta. Da kansa ya yiwa Ramlat magana ta fito daga motarta, ta tsaya ta dan saurareshi. Ita kuwa ganin tunda har Hisham bai hana ta kulashi ba, kuma aminin Hussein ne, to tana da tabbacin babu alamar Hussein na sonta. Wannan yasa ta dangana ta hakura ta ba Baban Hanif dama.
Sauke ajiyar zuciya ta yi ganinhar wayar ta katse ba ta ɗaga ba. Ya ƙara kira ta ɗaga. Bayan amsa sallama ta ba shi uzurin tuƙi dole ya hakura.
***
"Shi kika tsayar kenan matsayin miji?"
Tambayar Baba Dakta ya sa gabanta ya faɗi, kanta a ƙasa yayinda yake zaune saman darduma idanunsa sanye da gilashi yana duba wani littafi na addini. Ta haɗiyi miyau, ta hakura yanzun za ta auri Baban Hanif. Ko ba komai ta yaba da hankali da nutsuwarsa. Hatta da Hajiya wannan karon da ma yan uwanta kansu, hankalin ya kwanta da shi.
"Eh Baba."
"Ramlat, kamar yanda ki ka amince da aurensa, bana son jin wata magana ta ɓullo daga baya."
A hankali hawayenta ya zubo, ba wanda ya fadomata a rai sai Aliyu da kuma yanda aka yi gumurzu a lokacin bikinsu. Abbanta ta tuna wanda a yanzun ta ke kallon Baba Dakta kamar shi. Basu da hadi sai zumunci tun shekara da shekaru da ya kasance Baba Dakta har yana da karfin ikon yanke hukunci a kan iyalin Abbansu, kuma ta zauna.
"Na ba ki nan da kwanaki uku, ki yi tunani dakyau, idan har kin amince ki zo ki sanar da ni. Zan ba shi damar ya turo magabatansa. Allah Ya zaɓamaki abinda ya fi alheri."
Ta kasa amsawa a fili sai a zuci, jiki a sanyaye ta mike ta mishi sai da safe ta kama hanyar gida. Kiran kenan daman, koda ta isa gida ba ta ɓoyewa Hajiya komai ba. Hajiya ta yi murmushi.
"Yaron ya san abinda ya ke yi da alama, kuma ko ba komai ɗan babban gida ne tunda Kakansa ma abokin Kakanki ne, wato Mahaifina. Zuri'ar Imam Shu'aibu Lawwali bani da shakku a kansu da yardar Allah. Kuma ke a dadinki ma tunda ba gida daya zai haɗaku ba da matarsa."
Ramlat ta yi shiru jikinta a sanyaye kawai tana sauraron Hajiya. Ta daure ta yi murmushin da bai kai zuci ba. Tana ji a ranta ko mutuwa za ta yi, wannan karon ba za ta ba iyayenta kunya ba. An yi ta kuma an ƙare.
A wannan yanayin Munir ya shigo gidan a fusace, suka dube shi. Oyoyon da su Affan ke mishi bai amsa ba. Bayan zamansa Hajiya ta dubeshi bayan amsa gaisuwarsa.
"Lafiya kake kuwa?"
Ya yi kwafa.
"Hajiya, wallahi Bilkisu ta haukace. Ba ta da hankali. Akan zama a gaban mota ta kama Hunainah da duka."
"Da cikin?!" Fadin Hajiya da Ramlat har suna hada baki.
"Na gaji! Wallahi na gaji da wannan rigimar ta Bilkisu. Haka kwanaki ta kawo wannan ƴar iskar ƙanwarta Salma, yan iskan samarinta na zuwa tafiya da ita night club ni kuwa na kora ta gidansu ba zan iya ba."
"Kai ba wannan ba, ka ce ta daki yarinya, yanzu ya ake ciki?"
Munir da har lokacin bai huce ba yana aikin karkaɗa mukullin hannunsa, ya dubi Hajiya.
"Ba ta yi mata rauni ba, ni ne dai na raunata Bilkisun, kuma na kora ta gidansu na sake ta."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Kana da hankali kuwa? Yanzu kai ba za ka iya hakurin zama da mace ba? Haba Muniru! Ai idan rai ya ɓaci, hankali ke dawo da shi."
Ya saki baki don mamaki, duk irin cin kashin da Bilkisu ke yi amma ana kiran meyasa ya sake ta? Hajiya sosai ta yi faɗa ta ce ta ba shi nan da gobe ya maida aurensa da Bilkisu kafin ransa ya ɓaci. Ganin bai samu goyon baya ba haka ya tattara ya fice sai gidan Baba Dakta. Nan ma dai duk kanwar ja ce, sai dai ɗan saukin da ya samu jin cewar Baba Daktan zai kira Kawu Jamilu su je gidan tare a washegari.
***
Kwanaki ukun da Baba Dakta ya ba Ramlat na cika, bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ƙara kiranta don jin ta bakinta. Kai tsaye cikin fawwalawa Ubangiji lamarinta ta ba shi damar yi mata zaɓi a wannan karon.
"Idan har shi ka zaɓarmin Baba, na amince zan zauna da shi kuma ba zan ba ku kunya ba."
Baba Dakta sosai ya ji dadin batunta, ya sa mata albarka karshe ya ce duk abinda ya yanke daga baya za ta ji. Da wannan suka ajiye maganar.
"Kar ki yi gaggawar amincewa da Baban Hanif." Amrah ta furta bayan Ramlat fitar Umma daga dakin kasancewar ta dawo gida an sallame su. Ramlat da ta ƙurawa Zayyan idanu, yaron Amrah, ta yi murmushi.
"Ba zan yi ba in sha Allah. Watakila shi ne alherina, na dai bar wa Allah zaɓi, duk abinda Baba ya yanke kaina shi ne daidai. Idan ya amince da aurena da Baban Hanif shikenan."
"Ba ki tunanin Hussein kan iya dawowa watarana?"
Ta hadiyi miyau a kokarinta na danne damuwarta.
"Koda ya dawo mene ne haɗina da shi? An faɗamaki kalmar so ta taɓa shiga tsakaninmu?"
Amrah ta sauke ajiyar zuciya, ta sani da gaskiyar Ramlat. Hussein bai furta yana sonta ba, kuma ko a waya ba ya nemanta.
"Amma sai naga kamar yana sonki."
Ta girgiza kai.
"Tunaninki kenan, yanzu dai a bar zancen ba shi da wani amfani."
"Ai shikenan. Allah Ya yi maki zaɓi na alheri."
Daga haka Amrah ba ta kara tada zancen ba.
***
BAYAN KWANAKI UKU...
BAZATA.....
Tana kwance a saman doguwar kujera tana karatun wani littafin hausa mai suna KE ALHERI CE a wattpad, dariyar Nene ta ke yi sosai har ɗankwalinta na zamewa. Tana sanye cikin riga da siket ƴan kanti da ya yi mata kyau. Ummi da su Ansar suna farfajiyar gidan su na wasa, sai ji ta yi su na ihun oyoyo Uncle. Ta yi ƙasaƙe tana sauraro can kuma ta yi murmushi don jikinta ya ba ta idam ba Hisham ba toh Hilal. Mikewa zaune ta yi ta gyara zaman ɗan kwalin kanta, ta mike gaba daya da zummar ɗauko mayafi, sai dai sallamar wanda ta ji ya katse dukkan yunƙurinta.
"Wane ne ya zo ne nake jin...Au, Husseini?"
Hajiya dake fitowa daga daki bayan idar da sallah ta ke tambayar, ganin wanda ke tsaye bakin ƙofar suna kallon kallo da Ramlat yasa ta katae tambayar. Ramlat da sauri ta fada daki don ɗauko hijabi, shi kuaa ajiyar zuciya ya sauke ya ƙaraso ya durkusa yana gaida Hajiya da bakinta ya ƙi rufuwa. Gaba daya ya sauya sai ka ce wanda ya fita ƙasar waje, ya ƙara kyau da ƙiba abinsa.
"Dama za ka dawo ɗannan? Ni na ɗauka kuma sai dai mu bi bayanka da kayanka. Nan abokinnaka shima ya zo ya gama jajensa."
Dariya ta ba shi.
"Ayi hakuri Hajiya, na yi laifi ko a waya ban sanar maku batun zuwana ba."
"Ba komai ai."
Nan kuma aka shiga hirar yaushe gamo, Hajiya ta aiki Ummi kiran Maminta don kawo ruwa. Ta fito cikin dakin ba ta ko kalli inda yake ba ta shige kicin. Hussein yana nazarinta a hankali. Har ta kawo ruwa ta ajiye da murya ƙasa-ƙasa ya ce.
"Kin fi koyaushe kyau."
Ta ɗan dubeshi, ya watsamata lumsassun idanunsa yana murmushi. Ta kauda kai kirjinta na bugu da sauri-sauri. Zubamishi ta shiga yi a kofi hannu na rawa. Koda ta miƙa maimakon ya karɓa sai ya ɓige da tambayar Hajiya.
"Na yi zaton zan tarar an yi bikin Ramlat."
Ta dube shi ranta na zafi, wato dai yana kara tabbatar mata babu ita a shafin rayuwarsa. Ta mike ta nufi daki sadda Hajiya ta soma ba shi labarin yanda ta kaya da Chairman.
Bai katse ta ba har ta kammala.
"Allah Ya kyauta." Shi ne kadai abinda ya furta. Daga bisani ya sanyo wata hirar daban inda a karshe ya kira Dada a waya video call ya haɗa su suka gaisa, Dada godiya ta shiga yi sosai da sanyawa Ramlat albarka. A karshe ta nemi gaisawa da Ramlatun, Ummi ta karɓi wayar ta shige dakin a guje ta kai wa Ramlat da ke kwance saman gado.
"Mami, ga Dada."
Tana shirin magana sai ganin fuskar Dada ta yi saurin mikewa zaune ta maudo fara'arta. Suka gaisa har ta ba Hafsat ma suka gaisa. Godiya kam ta sha shi, tuni Ummi ta fice daga dakin. Daga bisani suka yi sallama ta katse kiran, dama a wayar Hafsat ne. Hankalinta ya kai ga hotonsa dake saman screen din, ya rungume throw pillow guda a kirjinsa yana kwantar da kai yana murmushi. Sai take ganin kamar ita ya ke yiwa murmushin hakan yasa ta yi saurin jan guntun tsaki gami da hararar wayar kadan kafin ta cillar da zummar sai Ummi ta shigo ta maida mishi.
Kwanciya ta yi har sai da ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayarta. Ta jawo ta duba, lambar da ba ta sani ba. Ta bude.
_*"Wayartawa itama raba ni da ita kike son yi yanda ki ka yimin iyaka da HEART?"*_
[3/17, 9:18 AM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA HAMSIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1013598891?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=1t7u8q%2B2i2CmVekKWI5wFx%2BLsRJJivM5TtUSxqfucEgX0H3IsSDvgfmbOaj%2FRM2R1oO3SAwAvV7%2FIJ95dbqOXcbxCoIbZ9MIciCSdP0fW4VijXfBR0gyHI42Cn5Za4Rc
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
54)
Ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci, takaici ya sa ta wurgi da wayar gami da hararar wayarsa da ke ajiye ta ja tsaki. Ta rasa gane me Hussein ya ke nufi da ita, ba ta san wane matsayi ya ajiye ta ba. Ta cije lebbanta tana karkaɗa ƙafa daidai sadda Ummi ta faɗo ɗakin a guje.
"Mami, wai inji Uncle.."
Ba ta bari ta ƙarasa ba ta yi saurin yi mata nuni da wayar.
"Maza dauka ga ta can ki miƙa masa."
Ummi wacce ba shi