Showing 120001 words to 123000 words out of 226732 words
da matsala babba ta wannan fannin.
Da wannan tunanin ya isa gida cike da tsantsar damuwa. Hajiya Zeenat ba ta nan wannan yasa shi kai tsaye nufar ɗakinsa, sai da ya rage kaya ya yi wanka kafin ya sauko ƙasa. Nan ya iske John ya jera kwanukan abinci saman tebur. Budewa ya shiga yi kafin ya ja tsaki ya maida ya rufe, babu ɗaya da ya burgeshi balle ya ji zai iya ci. Wayarsa ya jawo ya shiga dannawa, kai tsaye whatsapp ya shiga.
Shi ɗin ba ma'abocin bude Status bane, sai dai yakan bude na mutane masu muhimmanci a wurinsa. Sunan HEART da ya hango a jerin wadanda suka dora Status ne yasa kansa tsaye ya bude.
Hotonta ne zaune saman kujera a falo, ta rungume wata kyakkyawar yarinya suna dariya. Kirjinsa ya bada dam! Ya kara zooming ya kurawa yarinyar idanu. Da ace ya taɓa haihuwa, ba abinda zai hana ya kira yarinyar da ɗiyarsa. Can kuma ya tuna kamanni ne kawai, murmushi sosai yake yana kallon yarinyar da ita kanta RAMLATUN. Sun burgeshi sosai, yarinyar ta shiga ransa ainun. Ya yi niyyar screenshot sai ya fasa, wannan ba halayyarsa ba ce don haka suka ya zaɓi turamata saƙo kamar haka.
"Mutane sama da dari biyu sun ga Status dinki. Hakan daidai ne?"
Yana aikawa ya saki murmushi gami da sauka daga whatsapp din. Wayar ya ajiye, hakanan sai ya ji wani kwarin gwuiwar ya ci abincin. Ya kuma rasa ta ina.I just published "BABI NA TALATIN DA TAKWAS" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/IcdWtyGJpbb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
38)
Shigowarta dakin kenan bayan sun yi sallama da Hajiya. Wani hamma ta saki tana mai rufe baki, a gajiye liƙis take jin ta. Kakkaɓe gefen da za ta kwanta ta yi, hankalinta ya kai ga wayarta, shaf ta mance da ita a chaji, ta cika tun awanni biyu ma da suka wuce.
Zareta ta yi ta shiga cikin whatsapp ganin saƙonnin da suka faɗo daga kunna Data.
Saƙon Hussein ya sanyata dariya ba kaɗan ba, ta maidamishi amsa.
"Ba fa celebrity ba ce."
Daga haka ta yi zaman jiran amsa har gyangyaɗi ya soma fisgarta, can dai ta hakura ganin ba ya kusa ta kashe wayar ta yi addu'a ta kwanta.
***
Ruwan da ake kamar da bakin ƙwarya ya sa ta barin yara a gida don sun kammala jarrabawa kusan wasa kawai ake a makarantar yanzun, itama ba don fitar ta zama dole ba da babu inda za ta je. Amrah ce ba lafiya, abin tsoron kuma lokacin haihuwarta da saura don duka-duka cikin bai kai wata shida ba.
"Ki je zuwa anjima ma leƙa. Kar dai ki manta da kiran Kawunnaki. Ki karasa Yakasan idan ruwan ya tsagaita."
Wani ɗaci Ramlat ta ji da bayanin karshe na Hajiyarta, tasan kiran da Kawun ke mata bai wuce akan aure ba. Ita shikenan yanzu kowa idanunsa a kanta, an takura akan sai ta yi aure. Dama tun da Hajiyar ta soma batun kai yara dangin Babansu don su ci hutunsu a can, ta soma jin ba dadi. Babban takaicinta yanda tun rasuwar Abulle babu wanda ya kara nemansu banda Malam da ke kira lokaci zuwa lokaci su gaisa ko kuma ita ta kira. Hakanan Justice duk sadda zai yiwa yaran ƴan uwansa kayan sallah toh zai haɗa da su. Kannen Aliyu ta yi musu uzurin aure, amma a ganinta hakan bai kai dalilin da zasu dauke ƙafa da hankalinsu daga kan yaransa ba. Ko ƙafarsu ba ta tako ba ai akwai waya.
"Kin yimin shiru kina wani ƙunƙuni, idan ba za ki je ba sai ki kira ki faɗamasa."
Hajiya na kaiwa nan ta mike a fusace ta yi ɗakinta. Sauke ajiyar zuciya Ramlat ta yi, ranta har sannan babu dadi haka ta gyara zaman mayafin abayarta maroon ta fita rike da kwandon abinci. Idan ka ganta ba za ka ce ta haifi yara har uku ba, Allah Ya yi mata baiwar jiki mai kyau kuma wanda ya samu kulawar da ta dace.
Har ta iso asibitin da Amrah suke ba ta cikin walwalarta. Ɗahiru ta soma kiciɓus da shi a barandar emergency, suka gaisa ya fadamata lambar dakin sannan ya fita. Ta karasa, Amrah na kwance tana bacci sai Umma a gefe. Ta karasa suka gaisa da Umma.
"Wai, gaskiya kin yi kokari, ana wannan ruwan kika fito?"
Murmushi ta yi.
"Umma ai dole ne, ƴar uwata guda ba lafiya fa."
Ƴar dariya Umma ta yi.
"Kinga da sauki ma, likitan ya ce wai Malaria ce kuma kinsan ba'a son Mai ciki da ita, amma yanzu Alhamdulillah. Ba ta jima da samun baccin ba ma."
Jinjina kai Ramlat ta yi tana maida dubanta saman fuskar Amrah, duk ta ajiye wani kumatu.
"Allah Ya bata lafiya."
Daga nan ta ajiyewa Umma kwandon suka shiga hira kadan-kadan. Sun kai kusan mintuna sha biyar kafin Amrah ta farka.
"Ya jikin?"
Umma ta furta tana dubanta. Gyada kai ta yi tana kokarin miƙewa zaune.
"Alhamdulillah, kan ya sauka ma."
Yanda ta furta ma ka san ba lafiyar. Suka yi mata sannu. Da taimakon Ramlat, ta shiga banɗaki ta yi alwala ta wanko baki. Suka dawo ta zauna, Ramlat da kanta ta zubamata farfesun naman ragon da ta kawo wanda ya ji karas da ɗankali. Ta haɗamata shayi sannan ta haɗa na Umma, itama ta zubamata farfesun.
Suna ci su na taɓa hira. Ruwa na tsagaitawa Umma ta wuce gida da zummar za ta turo kanwarta (ita Ummar), Magajiya ta zo ta zauna da ita.
"Ya na ganki wani iri?"
Amrah ta watsowa Ramlat tambaya tana dubanta. Murmushin yaƙe ta yi.
"Ba komai."
Girgiza kai Amrah ta yi.
"Karya ne wallahi. Dama shiru nayi don Umma na wurin amma tun da na dora idanu a kanki na gane akwai matsala."
Shiru Ramlat ta yi kafin kuma ta soma fitar hawaye, a yau dai zuciyarta ta motsa da kewa mai yawa na Aliyunta. Da ace za ta rasa duk abinda ta mallaka don kawai Allah Ya ba ta damar ganinsa su yi magana ko sau daya ne, da tuni ta aikata hakan. Sai dai kuma ita mutuwar gaskiya ce, barin duniya ce ta har abada da babu dawowa sai dai ka je ka tarar.
"Lafiya kuwa?"
Cewar Amrah kusan hankali a tashe, ganin tana neman jefa mai juna biyu cikin matsala ta yi saurin dauke hawayenta ta hau murmushin yaƙe.
"Ke ba fa wani abun tada hankali bane."
Nan ta kromata dukkan abinda ke faruwa, murmushi Amrah ta yi. Ta lura ba maganar kai yaran gidan kakanninsu ne tashin hankalin ƙawarta ba sai maganar auren da ake budemata wuta a kai.
"Yanzu don Allah Ramlat kin fi kaunar ki yi ta zama haka ba aure? Kina zaton hatta Abba idan ace yau yana doron ƙasa zai yi murna da zamanki haka? Ko a tunaninki Aliyu zai yi farin ciki da zamanki haka babu aure? Wallahi kin ji na rantsemaki cikinsu babu wanda zai so ki ƙare rayuwarki a haka. Kema fa mace ce, a karon kanki sai dai ki ɓoye, kinsan cewa kina bukatar auren. Kina son wanda zai kula da ke da rayuwarki."
Amrah ta ci gaba da kwantarwa Ramlat hankali ta hanyar nasiha da rarrashi. Tun Ramlat na jin haushin maganganun har ta soma gane dagaske duk abinda ta fadi babu ƙarya ko sharri a ciki.
"Batun yara kuwa kema kinsan ba ki isa hanasu zumunci da dangin mahaifinsu ba koda su din ba sa ta su."
Murmushi kawai Ramlat ta yi a nan.
"Ke ni ina Muhibbat ne? Kwana biyu na ji ta shiru a WhatsApp."
"Tana nan, ko juma'ar da ta wuce mun gaisa. Ta yi rashin lafiya kwana biyunnan wai."
"Allah Ya bata lafiya." Cewar Amrah.
Zuwan Baba Magajiya kanwar Umma ne ya ba Ramlat damar yi musu sallama ta tafi. Yayyafi-yayyafi ake yi garin ya yi luf-luf da sanyi mai sanya nutsuwar zuci.
Tana tafe tana tauna zantukan Amrah har ta isa ga motarta.
***
YAKASAI..
Kanta kamar ya tsage biyu, bakinta ya yi mata nauyi yayinda ta ƙurawa Kawu Bello idanu don ji take kamar babu sauran laka a jikinta. Ta rasa ma me za ta ce, ta kasa fahimtar idan bayanan suka dosa. Batun dai zai bayar da ita ga CHAIRMAN ALIYU DIKKO ya fi komai ba ta mamaki da kuma dariya.
"Kin yi shiru kin tsuramin idanu kamar wani sa'anki?! Sarai kin ji ai abinda na ce! Mun gaji da zubamaki idanu, ke ba ki kawo wani kin ce kina sonsa ba, kuma ke ba ki ba masu sonki dama ba! Toh na bayar da ke ga Chairman, zai soma zuwa hira wurinki ku fahimci juna. Nan da sati uku ma zan dauramaku aure."
Ya ƙarashe yana fitar da wani huci har da muzurai, bakin ciki ya sa hawayen ma kasa zubowa. Wato Chairman shigo-shigo ba zurfi ya yi mata kenan? Ta ya akai ma ya san gidan kakanninta?
"Ki je ki saurari zuwansa cikin satinnan, saura kuma wannan karon kamar yanda kika nunamana a baya, yanzun ma ki nuna ba mu isa da ke ba. Dama ai mai hali ba ya fasa halinsa. To mu zuba da ke."
Wasu zafafan hawaye suka zubomata, ta kasa duban Kawun har ya mike ya bar mata dakin. Jiki a sanyaye ta share hawayenta, ta mike ta koma sashen Dada. Nan ne ta samu Dada ta shiga kwantar da hankalinta da hanyar nasiha da nunamata muhimmancin auren a gareta. Ita dai ji ta yi gidan duk ya isheta, sallar la'asar kawai ta gabatar kafin ta yiwa Dada sallama ta yi ficewarta.
A zauren suka yi kiciɓus da Kamal.
"Ashe Ramlat arzikina kika raina ban sani ba, kin nunamin ba za ki iya aurena ba saboda a gidanmu ba'a sonki, yanzu ai gashinan da wannan maigidannaki ya fito kin kawoshi har ya ga Kawu. Ki dai bi a hankali duniya ce, ta fi bagaruwa iya jima!"
Yana kaiwa nan ya gifta ta ya wuce, ta bishi da kallo sannan ta fice, a hanyar tana tafe tana hawaye sosai. Komai ba ya mata dadi, wannan ne yasa ta zaɓi kaɗaicewa ita ɗaya ba tare da kowa a kusa da ita ba. Wani Rainbow Park ta je, wuri ne mai karancin hayaniya, mutanen da ke a wurin tsilli-tsilli, ba ruwansu da harkar kowa. Wannan ne yasa ta zaɓi can wurin da za ta je ta samu nutsuwar zuciya.
Cikin wata rumfar kara ta nufa inda aka jera kujeru, iska mai dadi wurin ke bayarwa. Akwai ƙarancin jama'a a Park din adalilin ruwan da aka yi.
Tunani kawai take tana fitar da hawaye masu ɗumi. Duniyar da abinda ke cikinta take ji sun ishe ta, an ce bazawara nada ƴancin zaɓin wanda ta ke so, amma tana ji kamar ba ta da wannan damar.
***
Tafe yake a hanyarsa ta zuwa wurin Gym. Tafiyarsa yake cikin nutsuwa yana sauraron yabon Ya Habibal Qolbi na Sabyan Gambus. Waƙar sosai yake jin dadinta, murmushi yake. Hankalinsa ya kai ga motar da ko a mafarki, lambarta ba za ta ɓacemasa ba. Ɗan tattara gira ya yi don son tabbatar da abinda idanunsa suka gani, ya nemi wuri ya yi parking.
"Me ta ke yi anan?" Ya samu kansa da furtawa a fili alhalin ya san babu mai amsawar.
Fitowa ya yi ya kara kallon lambar don tabbatarwa. Can kuma ya fito ya shiga Park din don son tabbatarwa kansa.
Sanye yake da wando da riga na kamfanin Adidas, farare da layi-layin navy blue a gefen hannu da wandon. Ƙafafun cikin farin canvas.
Gashin kansa ya kwanta luf-luf har a ƙeya, baza dara-daran idanunsa ya shiga yi wanda gashin ido ke kokarin rufewa duk sadda ya kyafta.
Har ya juya cikin fidda ran ganinta a wurin, idanunsa ya kai gareta cikin rumfa. Tana zaune ta ɗora gwuiwar hannunta saman kujera ta kama dage kanta da tafin hannu.
Kamar tunani take yi mai zurfi, kamar kuma hawaye ne saman fuskarta. Don so ya tantance, sai ya ƙarasa. Sallama ya yi amma ga mamakinsa ba'a san ya yi ba. Jan kujera ya yi da ke fuskantarta ya zauna. Wannan ƙarar ce ta maidota hayyacinta, ta dubeshi da idanunta da suka ƙanƙance suka yi ja. Shima zubamata nasa kwayar idanun ya yi fuskarsa da wata kwantacciyar damuwa.
Ta yi saurin share fuskarta, sosai ta kaɗu da ganinsa a wurin, ta kuma yi mamaki.
"Assalamu alaikum."
Ya kara maimaitawa, ta amsa a ciki-ciki. Miƙewa ta yi da niyyar barin wajen, ya yi saurin riƙe gefen dankwalin abayarta wanda ba shiri ta koma ta zauna.
"Lafiya?" Ta fadi murya a ƙasan maƙoshi. Murmushi ya yi.
"Ke zan tambaya, daga ganina sai ki gudu. Zauna ki ci gaba da hawayen ni tayaki kawai na zo yi."
Ta kauda kai daga barin kallonsa, ba ta ce uffan ba, zuciyarta ba ta cikin nutsuwar da za ta yi wani murmushi har ta kai ga darawa. Yau an motsa mata dukkan damuwarta. Yau ta tuna da mutane biyu masu ƙima da daraja a wurinta kuma mafi soyuwa a zuciyarta da ta rasa.
"Kiyi hakuri, komai na duniya mai ƙarewa ne. Wannan hawayen faɗuwa ce a wurinki ba nasara ba. Babu abinda zai yayemaki. Kema fa kin sani. Wani abin muna ji muna gani amma yake gagararmu tankwarawa saboda ba mu isa ba, sai yanda aka ce da mu, sai yanda akai da mu."
Ya fadi hankalinsa na kanta. Ta dubeshi, lokacin da ta ji saukar wasu sabbin hawayen, ba kanta kawai ta tausayawa ba, kalamansa na karshe kamar dan tsakure ne daga tasa matsalar a iyakar fahintarta domin kuwa ba shi da masaniya akan nata.
"Ka san damuwata ne? Ya akai ka san ina nan?" Ta furta kanta tsaye a sadda ta ke kokarin share hawayenta. Ya yi murmushi.
"Gashinan rubuce saman fuskarki."
Ta kara tsuke fuska ganin ya share tambayarta ta biyu.
"Kinsan me?"
Ta dubeshi gami da girgiza kai. Ya maida hankali kan wayarsa dake ringing, ganin sunan Hisham na yawo saman screen ya ɗaga.
"Ba zan samu shigowa ba." Abinda ya ce kenan bayan sun gaisa. Ramlat ta saci kallonsa, ba shiri ta kauda nata idanun ganin irin duban da yakemata.
Tana jin muryar Hisham na tambayar dalili.
Murmushi ya yi mai sauti.
"Ina tare da Heart."
Daga nan ya katse kiran. Kalmar Heart da ya furta ta sanya gabanta faɗuwa, ta dubeshi, ganin ya ɗagamata kira ta kauda kai. Ya ajiye wayar saman teburin.
"Tambayarki ta biyu ce ni kaina amsarta nake nema. Nasan dai a wautana motarki na gani, na haddace lambarta fiye da zatonki. Sai dai na rasa ya akai jikina ya bani ke ɗin ce ke jan ta, kuma har na zaɓi shigowa nan na ga wanda kika zo gani. Sai kuma na ganki ke ɗaya kina hawaye. Nan take tunanina ya bani cewar watakila faɗa ku ka yi ya tashi ya bar ki ko kuma bai zo ba. Ma'ana, ya yi disappointing dinki."
Murmushin takaici ta yi.
"Babu ko daya cikin hasashenka, asalima a karon kaina na zaɓi nan matsayin wajen da zan samarwa zuciya da kwakwalwata nutsuwa."
"Kina zuwa kenan?"
Ta ɗan taɓe ƙaramin bakinta gami da girgiza kai. Ya bi bakin da kallo ya kauda fuska yana murmushi.
"Heart." Ya furta a hankali, sai dai ta ji shi sarai. Miƙewa ta ƙara niyyar yi ya hanata ta hanyar rike mayafin karo na biyu. Dole ta zauna.
"Tafiya zan yi."
Yanda ta furta kusan a fusace sai ta ba shi dariya.
"Ba ki isa ba ai, uzuri ne fa da ni kika dakatar da ni."
Ta saki baki da mamaki.
"Yaushe?"
"Yanzu mana."
"Ni na faɗa?"
Ya girgiza kai.
"Abar maganar, kawai dai shawara zan ba ki. No matter what, ko meke damunki kar ki bari hakan ya sa ki zo irin wuraren nan. Ki yi hakuri, babu matsalar da wani ko wata zai magancemaki. Ki miƙa wa Allah lamuranki. Ki dage da kai kukanki gareShi. Wannan shi ne babban kuskurena a baya wanda a yanzun ya ke farautana."
Ya ƙarashe cike da tsantsar damuwa, ta dubeshi da kulawa.
"Ban yi zaton kana da damuwa ba, Allah Ya maka dukkan ni'ima. Kuma.."
"Ke Allah bai miki dukkan ni'ima ba?"
Ta kauda fuskarta daga kallonta.
"Ni kuwa Allah Ya yiwa ni'ima. Ya bani lafiya, Ya ban iyaye da ƴan uwa masu sona, Ya ban ƴaƴa. Alhamdulillah."
Tana kaiwa nan ta saci kallonsa. Kamar ta so karantar damuwarsa da yanda ya sauya lokaci guda. Can kuma ta ga ya ɓige da jinjina kai.
"Yes, you are right. Alhamdulillah."
Yanda ya yi maganar a sanyaye sai ya bata tausayi.
"Gwara ki tafi, yamma ta yi."
"Kana da ƴan uwa a garinnan?"
Abinda ta ce kenan. Wani banzan kallo ya watsamata da ya razanata.
"Ba ki damar shiga rayuwata hakan ba yana nufin har da lasisin da za ki tambayi abinda ya shafi rayuwata bane. Ya kamata ki san wannan."
Yana kaiwa nan ya mike a fusace ya yi gaba.
Ta bishi da kallo duk sai ta ji hankalinta ya tashi, bata taɓa ganinsa a yanayi makamancin wannan ba. Labarin da Hisham ya ba ta sadda magana makamanciyar haka ta haɗa su shi ya fado ranta. Da sauri ta mike ta dauki jakarta da zummar mara mishi baya. Wayarsa ta gani ajiye, ta dauka ta bi bayansa. Sai dai har ya kai ƙarar fita. Kafin ta karasa har ya shige mota ya tayar. Zagayawa ta yi da sauri ta bude mazaunin gefe ta shiga.
Ya buga sitayari murya a kausashe ya ce
"Fita!"
Girgiza kai ta yi hawaye na zuba.
"Ka yi hakuri don Allah, wal..."
"I said get out!!"
Ya faɗi cikin tsawa hadi da buga sitayari iyakar karfinsa har sai da ta razana. Idanunsa kamar an watsa barkono. Yanda jikinsa ke rawa itama haka nata jikin ke yi. Ta bude murfin motar ba shiri ta fita. Bai bari ta karasa rufewa ba ya fisgi motar har yana kokarin buge wani mota. Mai motar ya dakata da sauri yana duramasa ashar. Hussein bai ma san yana yi ba. Ita dai Ramlat kirjinta je dukan tara-tara da irin gudun gangancin da ta hangoshi yana yi, hawaye kamar famfo take fitarwa ba ta ko damu da kallon da jama'ar wurin